Chapter 25 Reading CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx Arewa Novels

CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx

Author :  F&F Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   25 / 64

72K to 75K   out of 190.4K words

bazasu bari wani nasu ya aure ta bah kasan tsanar da sukai mata gara ka barta ko saukar ta samu inda rabo Allah ya taimake mu ta haɗu da ƘADDARAR TA daman shine fatan mu bana so ai mata aure mai kama dana sadaka ita ɗin AMANAR MUCE.  "Uhmmm" kawai Arɗo yace yana karanta addu'ar gama alwala ya tashi ya nufi masallaci.

Ina daga ɗaki ina jin su hawaye kawai nake sharewa na cigaba da haddata cikin suratul Isra'il kaɗan ya rage na haɗe da Kahf ni kaina ina tausayin rayuwa ta yanzu ji yadda ake neman maraba dani kamar annoba watau na zaman masu allaƙaƙai inda ya AJMAL na nan wa ya isa yai min haka hawaye na kuma sharewa na cigaba da karatu na ina jin shigowar Apio ya dawo daga aiken da inna tai mashi suna er tsama su Apip nacewa shi zai hura mata wutar gawayi, dariya inna tai ta tasan duk cika baki ne ta san ba abinda ya iya  yadda suke gaba da hayaƙi bai ƙaunar hayaƙi ko misƙala zarratin wani lokacin in ana sawwa baya zama gidan drama suka sha sosai ni dai ban fita bah bare ba ɗauko maku rahoto 😛 ina dai jin dariyar su har tambaya yake ina nake Adda tace ban jin daɗi barci nake jin ina barci yasa bai shigo bah ya zauna ya kasa ya tsare shi ala dole sanwa zai koya dashi za'ai sanwa so yake ya iya saboda tsaro ba don tsoro bah ko misalin in yayi aure ya ringa taimaka ma matar shi don ya lura daga aure sai a fara ciwo ta kalmi inna ta jeho mashi ya kauce Adda tace Allah ya shirya ka Apip da ameen ya amsa yana ficewa daga gidan.

A yau data kama Asabar tunda safe na tashi na fara gyaran ɗaki na bayan na gama sallah Asuba lokaci guda ina duba ruwan kunu dana ɗaura so nake  in gama aiki na da wuri yau nayj Alƙawarin zuwa islamiya ko ana ha maza ha mata  haƙuri na ya ƙare wuraren 8:30am na gama komai na gyaran gida kalaci da wanke wanke ɗakunan su ne kawai ban shiga bah basu tashi barci bah  ina tsaka da soya  awara da jiya Adda tai dawon ta ta ajiye yau ai kalaci da ita  Apip ya fito sai baƙin rai yake yaja kujerar dake kusa dani yana en harare harare ni dariya ya bani saida na murmusa shegiyar ce ke cin sa ya tashi kuma ba'a gama ba da murmushi a fuska ta na ce.............................

[11/7, 3:27 PM] Fatima 1@1: CINNAKA 🐜🐜🐜

             BAI SAN NA

                     GIDAH BAH

                            SAI YA CIZAH

STORY

&

WRITTEN BY

    F&F

    (PERFECT PAIRS 🌺)

  30............

   Da murmushi a fuska ta nace ya dai ƙanin ko mu gudu ne irin wannan haɗe rai haka kamar hadarin kaka wata uwar harara ya ɓallamin kamar idanun shi zasu faɗo ƙasa don girma mashallh sai harara naga ta ƙara mashi kyau " wallahi hamda ki kiyaye ni ban san raini kin sani ni ban ma san lokacin da na fara wasa dake bah kika raina ni haka murmushi nai mai cike da tsokana kafin ance "tun sanda naga makwancin ka naga yadda kake barci hannu ya ɗaga kamar zai mazge ni sai kuma ya waske da shafa sumar kanshi da ke kwance lub lub sai sheƙi take alamar a jiƙe take yai kwafa yana wani cin face shi ala dole ga babban yaya cen kuma yace "ke baki iya gaisuwa bane ko gidan ba manya cen ƙasan moƙashi naji ya furta hakan, cikin salon rainin wayau dana san yana saurin harzuƙushi na bashi amsa "kash an samu akasi duk manyan sun zaam yara" maimakon yaji haushi kamar yadda na zata sai yai murmushi yana ƙoƙarin saka hannun shi cikin gwagwar da nake tsane wara inna kwashe kafin ya gama zaɓar wadda tai mashi na fiddo spoon da nake juya ta da shi cikin mai na kwala mashi a hannu ya saki wata sangartacciyar ƙara mai cike da taɓara har saida tasa Inna da Adda suka fito ba shiri daman suna jin mu gyaran ɗaki su (wannan Kamar al'adar gidan muce kafin mutum ya fito tsakar gida sai ya gama da ɗakin shi ban da mr Apip sai dai ni na shiga na gyara mai tuni na sangartar dashi da hakan shiyasa baiyi in ban gyara bah sai mun kwashi en kallo wani lokacin nake gyaran saboda bai san ƙazanta ko kaɗan). Ganin yadda Apip ke taɓara yana shure shure shi ala dole na ƙona shi yasa Adda gilgiza kai ta koma cikin ɗaki ni da inna aka barmu da sakin baki har awarar dake cikin mai ta soma ƙomewa na maida hankali kanta inna tace "kuji min ƙaton banzan minene haka Apip anya kanka ɗaya kuwa yana safke ajiyar zuciya shiga ga wanda yasha kuka ya ƙoshi kuma fa ba kukan yayi bah "baki ga mi wannan muguwar tai man ba tai man bah jifa konani tai ta babbakamin hannu kuji fah wai na babba ka mai hannu ina rike da haɓa nake wanna zancen zucin har ya isa gaban inna ya na nuna mata hannun da bubbuga ƙafa ƙasa kafin inna tai magana Arɗo da ya shigo da sallama da alama daga gona yake ya riga ta yana mah Apip kallon baka da hankali sannan ya kalle ni tare da amsa gaisuwar da nake mashi yana nufar ɗakin shi still Apip bai bar abinda yake bah a ɗan zafafe Arɗo ya waigo ya kalle shi "wai kai wane kalar babban banza ne ka girma baka san ka girma bah kullum kana ma kanka kallon yaro iya shegen ka kullum gaba yake zanyi maganin ka don ka ga anzuba maka ido kake san ran ka" baki ya turo da wata sabuwar shagwabar yace "haba Arɗo abugi mutum a hanashi kuka ƙona ni fah tayi shine don nayi magana zaka hauni da faɗa kalli fah yaddda hannun ya sale yana maganar yana matsowa kusa da Arɗo hannun ya kalla murmushi ya kufce mashi ba shiri rigimar Apip bata da iyaka shidai maiƙon mai kawai ya gani hannun ko ja baiyi bah ya ɗaga hannu zai kai mashi ranƙwashi ya zille yana kunkuni shifa da iya gaskiyar shi yaji zafi ya shure min ƙafa sannan ya fice murmushi kawai nai ina jinjina yanayin Apip akwai gyara Cikin sa in haka zai cigaba da gudanar da rayuwar shi akwai matsala abun nashi ban san yadda zan musulta maku shiba ko ni da nake mace ban iya yin wani abun da yake maganar Arɗo tasani kallo shi ba shirii zuciya ta na tsinkewa "in kin gama abinda kike ki same ni ɗaki na akwai maganar da nake so muyi toh Arɗo kawai nace ina kallon inna da Adda kowace hidimar gaban ta take.

Har muka gama kalaci Apip bai dawo bah zan tattara kayan in wanke Adda tace a'a hamda ba anyi haka bah kije cika umarnin Arɗo ki barni da wannan aikin toh kawai nace na ɗauki doguwar abayata dake saman katifa na zura zuciya ta na bugu ganga basan mi zamu tattauna da Arɗo ba na shiga ɗakin da sallama na same shi zaune kan gadon karfen sa ya baje wasu abubuwa da bansan sumiye bah yana harhaɗa su na zauna ƙasan inna ƙara gaishe shi ba tare da ya kalle ni bah ya amsa saida ya gama abinda yake sannan ya dawo saman kujera ya zauna muna fuskantar juna fuskar shi ba alamar wasa yace " HAMDA ba buƙatar maida hannun agogo baya kin san duk abin da suka faruwa da waɗanda ke kan faruwa kin san gwagwarmayar da nake akan nauyin mahaifin ku daya ɗaura min Toh Alhamdulillah ina fatan amanar dana ɗauka in cika ta lokaci yayi dana daɗe ina fatan Allah ya nuna min shi da raina da kuma lafiya ta kuma inshallah bazanyi watsi da wannan damar bah bawai don na gaji dake bane hamda a'a sai don bani da wani zaɓin da ya wuce in aurar dake da mutuncin ki in kare maki darajara ki kuma wannan Alƙawarin na ɗaukar ma MAHAUFIN KU shekaru 19 dasu wuce"

Wani wawan lumfashi na ja indanuna na tara kwalla duk lokacin da aka ambaci mahaifi na sai in ji duniya ta ta gilgiza tai man zafi zuciya ta ta ɗatata har tunda ya danganta maganar aure na da mahaifi na magana ta ƙare banda wani sauran ja na karɓi wasiyar tashi hannu bibbiyu koda auren da suke shirin mani zai zama shamaki da farin ciki na daman na daɗe da saudaukar dashi tunda na rasa ya AJMAL ni dai fatana Allah yasa kafin lokacin muyi safkar mu farin ciki na linkuwa yake in na tuna da ranar ban kai ƙarshen tunani bah na tsinkayo muryar Arɗo nacewa na baki kwanaki 14 ki kawo min wanda wanda kike so nai maki Alƙawarin ko wanene zan aura maki shi ƙasa na ƙarayi da kaina ina haɗe hawaye na bansan Arɗo ya fahimcin halin da nake ciki "na baka wuƙa da nama Arɗo ka zaɓa min duk wanda rai da zuciyar ka suka aminta dashi na zan bazaja zaɓa min abinda zaizama mai cutarwa a gare ni bah ko wanene ina maraba dashi "Allah yai maki Albarka hamda Inshallah zaki ga ribar hakuri da biyayya Allah ya cigaba da dawwamar da rayuwar ki a mizanin farin ciki cikin jin daɗin Addu'ar na amsa da "Ameen Allah yana samin wata natsuwa cikin zuciya ta daga haka ya sallame ni.

Ina fitowa Apip na shigowa ko kallo ban ishe shi baya shige ɗakin shi kaina gilgiza ina cire hijabi na har na fara tafiya na hangi Adda na gyaran wake tana kwallo na nasan hankalin ta ba'a kwance yake tunda nashiga murmushin kwantar da hankali nai mata na ida cire hijabi na rataye ta a igiyar ina kallon lokacin da ta safke ɓayayyar ajiyar zuciya kafin na kalli Adda da fitowar ta kenan daga ɗaki "ina kalacin Apip inna" saida ta murmusa irin nasu na manya "watau lallashi zaki je yana kichen "uhmm kinsan halin mutumin kamar network hawa yake yana safka "ku dai kuka sani" ta faɗi hakan tana zama kusa da Adda suka cigaba da aikin su gwanin birgewa kamar ba kishiyoyi.

Ɗakin Apip na nufa bayan na ɗauko break fast ɗinshi na shiga da sallama yana zaune gefen katifar shi mai tudu sosai da faɗi gaban shi akwatin kayan shine da alama wani abu yake nema nan mah bai kulani bah sallamar dana yi ban tunanin ya amsa ni dai a saman babbar darduma dake gaban katifar na ajiye sannan na zauna gefen katifar daga bayan shi in kallon yadda ruwa ke gangarowa daga cikin kanshi suna jiƙa mashi wuyan riga tabbacin bai daɗe da jiƙatah ba lura ba iya fushin yake bah har mutanen shi a kusa suke don haka cikin kwantar da murya nace "wai yayan baka ji na shigo bane ko ka daina ji dani maimakon ya bani amsa sai zakuɗawa yai ya dawo tsakiyar katifar ya kishingiɗe yana warware wata baƙar leda dake hannun shi kuɗi ne da ban san a dadin su bah ya fiddo yana kakkasa su ban kula shi bah nace 'kayi hakuri sai lokacin ya ɗago yaimin kallon ƙasan ido cikin wani kalar yanayi dana kasa bashi ma'ana kafin ya ɗauke kai cikin yanayin barkwancin sa yace "madam ban san surutu kina rikita min lissafi baki na taɓe "dan kaga ma an damu dakai ina lallashinka shine kake gara ni ga kalacin ka nan in ka ga dama kaci" ina maganar ne lokacin da nake yunƙurin mikewa tsaye sai kuma na tsaya cak jin ya riƙemin ƙasan riga na kalle shi "zauna" ya faɗa yana min murmushi da bako yaushe yake yin shi ba sai da na harare shi sannan na zauna ina miƙo mashi kunun shi gudun kar yai sanyi nasan bai sha in ya huce ammh sai ya kauda kai "na ƙoshi ya huce baxan iya sha ba bani awarar dai" awarar na miƙa mashi kamar yadda ya buƙata saida naga yayi nisa daci sannan nace " waɗannan kuɗin fah daga ina" nawane tari nake" a takaice ya bani amsa yan shan ruwa "nami" makaranta nake son in koma yana bajeqa saman katifar yai maganar ya kwanta yana fuskantar sama "wallahi kanwar ina son makaranta ina ƙaunar komawa makaranta duk sa'anni na sun wuce ni ina son in nemi nakai in tsaya da kafafuna mubar garin nan ban ƙaunar zaman cikin sa ina son na nuna masu Allah bai manta damu bah ina son su fahimci ƙaramin hakkin da suka raina shi ke tsone mah ido wallahi so nake su raina kansu cikin soyayya ɗan uwa nawa na saki murmushi "Inshallah ba iya kuɗi zakai bah yayan MULKAR su zakai kallon juna mukai muka saki murmushi fira mai daɗi ta ɗauke mu tsawan lokaci sai lallaɓa shi nake ina wani bashi girma kallo na kawai yake yana jinjina kai nasan ya fahimci mi nake nufi Amma ɗan latsin ya basar nima ban fasa ba sai zuwa can ya mike zaune yana dariyar ƙeta "wai hamda mi kike so mi kike buƙata in maki? Murmushin samun nasara nai ganin haƙata ta cimma ruwa na shagwaɓe fuska " wallahi yayan ban da lafiya jiki na ban jin daɗin shi kuma kaga duk na toye wajen suyar awara" murmushi yau yana miƙewa tsaye " kuma baki yi wanki bah so kike nai maki "laaa ya akai kasan abinda ke zuciya ta" hararar ya banko min "Aike da anga kina wannan ladab ɗin wanki ne ko guga "Ai kai ka shagwaɓar dani na murguɗa mashi baki kafin ya mayar min da martani Adda ta kwala min kirah na amsa nima ina miƙewa tsaye ban ƙara bi takanshi ba saboda nasan zaiyi in dai magana ce ta ruwa Apip baida matsala yana masifar son wasan ruwa.

Gidan su juhud Adda ta aike ni amso mata saƙo cen na shantake har akai zuhr sannan na baro gidan ina tunanin yadda zamu kwashe da Adda ammh bata cemin komi bah sai saƙon data ƙarɓa ta koma ɗaki.

Murmushi ne ya kufce ma fuska ta ba tare da na shirya bah ganin kayan na jere bisa akwati ya wanke ya goge harda waɗanda bance bah Allah sarki ɗan uwa rabin jiki ina ji dashi irin sosan nan muyi tsiya mu daɗi Apip wani kalar mutum ne mai wani kalar yanayi mai ban mamaki karkuji kamar na cika zuzuta shi duk yadda kuke tunani. Apip ya ce nan ban san yadda zan maku bayani bah ku fahimta ammh in muka nitsa cikin rayuwar shi zamu fahimci hakan mutum ne kamar hawainiya lokaci guda yake canza yanayi kamar iska haka yake da wannan tunanin na gama shirin islamiyya na duba agogo around 2:15pm akwai sauran lokaci na shiga gyaran kayana ina jera su cikin akwati na ina buɗe akwatin da wayar da Excellency ya bani na fara cin karo murmushi ya kufce min shaf na mance da babin rayuwar shi wai nace shiya cece ni zanko faɗa gefe na maida kwalin wayar daban taɓa buɗe ta bah kayan na ida gyarawa tsaf sannan na koma saman katifa ta na buɗe wayar da bandir ɗin kuɗi na fara cin karo dollars ba naira bah nake gaya maku kyawawan idanu na nazaro kamar zasu faɗo ƙasa gaskiya mutumin nan abin tsoro ne yawu mai kauri na haɗiye lokaci guda in sakin murmushi wai mutumin nan yana tunanin zai yaudare ni da kuɗi ya siye min imani bawan Allah duk lokacin dana ɓallo mashi aiki zai shiga taitayin shi zaiyi nadamar raina wayau na ina sabbatu na ida buɗe wayar ƙirar Company iphone wayar tatafi da imani na guys ta haɗu na dade ina juya ta zuciya ta na raya min abubuwa da yawa Abinda ya ɗaure min kai miyasa yake son in ambaci sunan shi a matsayin wanda ya cece ni a AFTABUDDEEN ko ƙarshen tunanin bannkai bah zuciya ta ta rayamin "siyasa ba takara yake nema bah ai zaiyi fiye da hakan don ya saye zukatan magoya bayan shi na sani muddin mutane suka samu labarin shi ya ceceni ba abinda zai hana su zaɓarsa AFTABUDDEEN itace matsala mafi girma data fi shahara take kaikayi a zukatan al'umma ƙasar kasran ta kowace hanya burin kowa a mayar da ita tarihi.

Ammh abinda na gaza fahimta da wata manufa Excellency ya tsaya takara koko mi yake nufi nayi nisan zango a tunanin da yaja ni tsawan lokaci ba tare dana farga bah waya ta tai ringing ɗan zabura nai na maida duba na gare su mammah ce mai kiran yasa na fahimci juhud ce "wai har lokaci yayi ne na faɗa ina ƙoƙarin ɗaga wayar sai dai kafin hakan ta faru wayar ta tsinke hakan ya bani damar ganin lokaci ƙarfe 3:09 "ina hankalin ki yake hamda shirin ki da wuri zai tashi a banza" da sauri na shiga tattare tarkace da Excellency ya haɗani da su na maida cikin akwatin bana jin zan iya amfani dasu ko mai a cikin su na mayar mazaunin shi Alwala na ɗauro na zura uniform ɗin mu kalar sararin samaniya sky blue kenan na leƙa ɗakin inna tana barci banyi yunƙurin tashi ta bah na shiga ɗakin Adda itakam gyaran kaya take "zan tafi Adda har naso makara "Allah ya tsare hamda karkiyi mangarib a waje "Inshallah Adda daga haka na fice.

Akan hanya naci karo da juhud zata gidan mu sai hura hanci take tun kan tai magana nace "Al-masifatu karki balbale ni da tijara gani dai na fito mu muje" dariya sunan da na kira ta dashi ya bata saida ta murmusa muka saki babin muka kama

25 / 64