Chapter 57 Reading CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx Arewa Novels

CINNAKA (BAI SAN NA GIDA BA) BOOK COMPLETE BY F$F.docx

Author :  F&F Category :  New Hausa Novels 2026

Chapter   57 / 64

168K to 171K   out of 190.4K words

bai kamace ta bah a barta taji da abinda ke damun ta she is totally broke maza sun sire mata tsoron su take a halin yanzu balle ta zaune dasu a inuwa daya daman cen ta riga da ta masu fassara tun akan mahaifiyar ta abinda take gudu saida ya faru itama akan ta su tausaya mata mana......

Muɗan waiwayi baya kaɗan abin da ya faru anan shine ................

[16/12, 10:01 pm] Teemah MS 🥰💖: CINNAKA 🐜🐜🐜

      BAI SAN NAH

           GIDAH BAH

                SAI YA CIZAH

STORY

   &

WRITTEN BY

    F&F

(PERFECT PAIRS 🌺)

 



  62.........

 

   Abinda ya faru  kiran gaggawa da grandpa yai paah a waccen rana kan Magana ne itace dalilin zaman grandpa kasar bawai iya saboda case ɗin miran ba Alh. Sada aminin grandpa ne sosai kuma abokin aikin sa tun kafin  auren miran na farko yaso yai magana da granda yai nauyin baki saidai yaji aana shelanta katin gayyatar auren a social media shiyasa a waccen lokacin yaja baya baiyi mah granda maganar bah bayan da yaji duk labarin mutuwar auren ta da duk abinda ya faru bai yi kasa a gwiwa bah a ranar ya tuntuɓi grandpa da maganar tun kafin ya iso kasar tun a wayar grandpa ya nuna rashin amincewar sa duba da yanayin da miran take a wannan lokaci da kuma irin kallon da duniya ke mata Alh. Sada maiko yayi murmushi kawai yace zaizo kasar sai su ida maganar grandpa yace ba sai yazo bah yana tafe in yazo sa ida maganar a guess house na paah nan suka haɗu a nan Alh. Sada ke mah grandpa duk wannan bayanin ko kaɗan bai amince bah musamman da yaji wai ɗan yake nema aure akan wannan maganar saida sukai sama domin Alh sada ya nace har yana cewa "in ka hana ni auren yarinyar Kamar baka son haɗa zuri'a dani ko matsayi na ne bai kai ina tunaninn ina da kimar da zan iya neman ko minene a wurin ka na samu shiyasa nai takakkiya da kai na ban turo shi yaron bah babu wata suka da za'a kowa min game da jikata da zata sauya min rayi a ɓangare na insha'Allah baza'a samu matsala bah saidai in kaina zaka hana auren nan" shiru grandpa yai don ya gama kashe mashi jiki yanajin nauyin Alh. Sada ya nemi abu wurin shi ya hana shi yai mashi halacci a rayuwa bayan jeen shine mutum na biyu daya tallafa mashi lokacin daya zo kasar nan bai san kowa bah kuma baida kowa ammh yadda ya nace akan neman auren nan abun ya bama grandpa mamaki duk wata hanya da zai sirar mashi da magana ammh bata zama hujjar da zai sauya ra'ayinsa bah yana ce sosai akan maganar ranar juma'a kuma yake son a ɗaura auren grandpa ya nemi ya bari sakamakon likitoci su tabbatar da ainahin abinda ke damun ta sannan sai su yanke maganar.

    Grandpa ya fara bincike tun daga kana hajja data nace akan miran ɗin sai tayi aure da mutanen gidan da sukai sadakar ɗiyar su (ai dole a kira auren ta dana sada) aure ba bincike kawai sun sadaukar da ita da ita kanta miran ɗin akwai abubuwan da yake zargi da yawa a cikin gidan da ko su mazauna cikin basu gama fahimtar komai ba balle bako hankalin sa ya kasa kwanciya akan abinda ke faruwa da miran ɗin shi yasan da wani abun. Dr. Fa'iziyya (likitan miran) ita tai mashi duk wani gamsashen bayani akan ciwon miran kamar yadda tai mah Aunty sugra anan ne ya fahimci miran babu idda akan ta ciwon ta ya karfafa shi wajen amsar tayin Alh. Sada a halin yanzu baya bukatar jikar tashi ta kara tozarta basu da tabbacin ga mijin da zai aure ko zata mah iya samun mijin aure nan gaba idan ta samu shin zai daraja ta ya ruke ta ta da kima ya taimaka mata ta cinye jarabawar da take ciki duk da grandpa bawai hankalin sa ya kwanta da Alh sada bane 💯 baida wuffi akan saida  ya samu gamsashen bayani daga bakin Alh. Sada sannan ya amince suka tunkari Paah da maganar shima ya nuna rashin amincewar grandpa bai yi mamakin hakan yasan hakan zata iya faruwa shiyasa ya toho tare da shi ma nemin auren da malan ma'aruf (maɗaurin auren babban limami ne a wannan lokacin) ammh duk da hakan paah kin yarda yayi saboda a halin yanzu baida niyar aurar da miran a ganin shi duk wnada zai aure ta  ba ba don Allah zaiyi bah da wata manufa a ranshi kuma ya ɗauki matakin kare mutunci er sa komai zai faru ba zaya yarda ta kara tozarta a idon duniya bah ko ya laminci abinda zai shiga cikin rigar mutuncin ta zaiyi ƙoƙarin ya kareta ko ba komai ita ɗin ɗiyar sa ce baya iya kankare ta daga jikin sa kuma kaddarar sa insha'Allah zai kokarin rungumar ta da mumushi ya cinye ta da addu'a daga karshe ya amince saboda mahaifin shi bawai har zuciyar sa bah.

Tun daga ranar yake ciwo a tsaitsaye jiki ba dadi shiyasa hankalin en gidan nasu ya kasu gida gida ga paah da maah ga miran a ɗayan brngaren  ranar.  juma'a kamar yadda Alh. Sada ya nema aka ɗaura auren wanda yai dai-dai da ranar da akan ɗaura nawa auren a kuma lokaci guda saida ba wuri ɗaya.

^_________^

   Maganar da taji Aunty sugra nayi yasa ta kalle ta da sauri saida Aunty sugra ta kwashe da dariya irin ta takaici tana kallon su su duka kafin nan tace "ko addini ya koyar da mu illa maimaita aji kuna manta da cewa ba'a sarin mumini a rani ɗaya sau 2 ko farfaɗowa baku bah daga sarin farko zaka kara tsindima kan ku a karo na biyu ku sake maimaita kuskuren ku،, wannan itace maslaha a ganin ku kuna wasa da ni'imar da Allah yai maku kuma sani dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa karku yarda lokaci ya kure maku baku farka bah ita ɗin amanace a gare ku kuma halittace mai rauni Ehhh miran tayi kuskure na ɓoye halin da take ciki tun a karon fari ammh in za'a bi ta ɓarawo dole ne abi ta mabi sawu kuma kuna da naku camassion  musamman ke yaya ke uwa ce ke uwa ce ke ya kamata kifi kowa sanin er ki batun yau bah nake guje maki irin wannan ranar en uwan ta duk maza ne ba komai zata iya buɗe masu bah ko su........." 

  Cikin katse mata hanzari hajja tace "ya ishe ki haka ki tattara tsumman rayuwar ki ki ja gefe

Ki barmu muji da abi da ke damun mu haba sai sabbatu kike mana. "Dakata min" itama cikin katse mata hanzari tai maganar  sororo hajja tai tana kallon ta  daman ba wani jituwa suke bah gaisuwa ce kawai tsakanin su itama nesa nesa sallar kura .

Saida aunty sugra ta ɗauke kan ta daga kan momy da shigowar ta kenan sannan ta cigaba da cewa "Kina mamaki ne na mayar maki da martani toh daga yau na daina shiru duk kece tushen matsalar nan ke kika haifar da komai  wallahi wallahi wallahi mudum ina raye bazan yara ki kara cutar da rayuwar miran bah kuma madamar auren nan tace bata so ta zaune ba wanda ya isa yai mata dole inna ce kowa ina nufin dukan ku bazan yarda a kara mata auren son zuciya bah itama 'ya ce mai enci haba a hana yarinya sakata gidan uban ta duk wanda yaji yana da ja da hakan a shirye nake ya ɗaukaka kara daga nan har kotun sama bazan janye bah"

Tashin maah daga wurin da shigowar grandpa ya katse Aunty sugra da takai kololuwar wajen fusata ita kaɗai tasan abinda take gani cikin gidan nan don sunga an zura masu ido a tunanin su tsoron su ake suke yadda suka ga dama lokaci yayi da zata take masu birki su gane gaba da gaban ta duk wanda yace zaya kawo mata wargi wallahi zata bashi mamaki miran kwainuwa ce dashen Allah nan gani nan bari dukiyar uban wani babu yadda zasu iya da ita ta ɗauki alkawarin bazata kara barin su ci galaba akan ta ba ko mai zai faru .

Dogon tsaki taja tana kallon irin tsinanan kallon da hajja ke mata da alama macewa tai a tsaye tai sai huttai take bata kula ta ba murmushi tai kawai don a halin yanzu bata da lokacin ta she don't waste word to those who don't deserve them.

Wurin miran ta koma ta kama hannuta suka haye upstairs  duk da kallo suka bi su musamman su ya Aiman da basu fahimci komai bah bah su gano bakin zaren maganar tata bah jikin su yayi sanyi sosai basu taɓa ganin Aunty sugra a irin wannan yanayin bah mutum ce mai faran faran da mutane dole su shiga damuwa.

Big Aunty ta gama tsurewa sai zare idanu take tashi tai bayan momy data fita amsa waya  don ji ta take kamar a saman kaya ganin haka yasa samha yasa samha mikewa ta bi bayan su miran.

Lokacin ne likitan yasa mu damar magana "condition ɗin shine na baya yake kokarin tashi ko nace ya dawo sabo dole za'a nisan ta shi da duk wani abu da zai dame shi ko zai tuna mashi da baya ina nufin abinda ya gabata a rayuwar shi in bah haka yanyin nashi zai fi na baya haɗari dole sai anyi taka tsantsan an bi komai a sannu kafin abubuwa su daidai ta yanzu ya samu barci in ya tashi shi zai bamu damar fahimtar condition ɗin shi"

  "insha'Allah za'a kiyaye in ya farfa  maji yadda za'ai"

Shiru ya ziyarci dakin bayan Dr. Ya tafi sosai hajja dake shawarar kwalla akai akai tana zububuɗo mah paah addu'ar samun sauki, A hankali ya Aiman ya mike ya nufi grandpa gaban shi ya durƙusa fuskar shi tayi masifar ja cikin rawar muyar yace "Grandpa kafaɗa min ya zanyi da zuciya ta na samu saukin tafasar da take min ciwo take min sosai na kai matakin da bazan iya jurewa bah abubuwan sun min yawa tamin nauyi iyaye na dukan su kwance basu tare da wadatacciyar  lafiya suna fama da ciwon da ban san mafarin sa bah ga miran a ɗaya ɓengaren ban san ta ina zan fara maka bayanin halin da zuciya ta take ciki game da ita i can't take it any more don Allah ka faɗa min abinda ya nace nayi ko wani laifi ko wani laifi na aikata ne dana cancanci irin wannan hukuncin a yau a karo na 2 an kara yi mah miran auren bazata bana fatan makamanci abin da ya faru a farko ya kuma maimaita kan sa duk da ina kyautata maka zato ba zaka cutar da rayuwar ta bah ammh a tsorace nake"

Tattausan gashin ya Aiman grandpa ya shafa yana sakin murmushi irin na su na datttawa da zaka samu fuskar shi koda yaushe dashi " Aiman kenan babu wanda yasan gaibu saboda mabuɗan a hannun Allah suke  sannan ubangiji maji kan bayi ne baya haɗa maka zafi biyu a lokaci guda komai kaga ya faru da ɗan adam musamman akan jarabawar rayuwa matakin nasarar ne ya ƙara sama in ka fahimci wannan dai ka tuna Allah bai jarafce ka bah sai don ya ɗauakaka, gaba kaɗan zaka fahimci manufar zance na jeka kira min sugra ta same ni a sashe mahaifin ku" babu su yace toh ya mike yana juya kalaman grandpa a zuciyar sa.

✿✿✿🤍✿✿✿ 

       Hawayen fuskar ta ta share ta kalli grand paah da ta tabbatar yakai karshen zancen nashi a karo na farko tunda ya fara koro mata bayani ta  jikin ta yai la'asar  sannan ta kalli aunty sugra dake gefe tana mamakin canjin ta lokacin guda ta rasa miye grandpa ya faɗa mata ta yarda da auren nan tunda sukai magana ɗazu da granda grandpa ta lura ta zubar da makaman ta duk da bata san mi suka tattauna ammh tana ganin tasiri kalaman grandpa tattare da ita. Fahimtar bawai magana zatai bah yasa grandpa gyara zama ta cigaba da cewa " miran bawai auren dole na shirya maki bah kamar wancen karon dama ce Allah ya bani dana dade ina fatan samu wadda bazan iya bari ta kuɓe ce min shiyasa  nai amfani da ita na dama ta hanyar aminta da auren  nan  in har baki so anan take zan iya warware shi bazan taɓa maki dole bah  ammh ina son ki sani ina hango Alkhairai masu yawa a cikin haɗin nan shiyasa hankali na ya kwanta dashi  "Ammh grandpa kaga abinda ya faru a aure na na farko ban ji da daɗi ban son na kara maimaita irin wannan rayuwar ina jin tsoron auren nan "bana ce bah miran ammh dana san aure nan zai zama illa a gareki da ba zan goyi bayan a ɗaura sa bah duk da bansan abinda gobe zatai bah ammh tun daga laraba ake gane juma'a mai kyau ina da yaƙinin zaki iya yaƙi ne akan ki mai ruɗanin gaske karki yadda memory rayuwar ki ta baya ya zama raunin ki karki ringa waiwayen ta yin hakan damuwa ce lokutan sun riga da sun wuce kuma bazasu kara maimaita kansu bah, Alkhairin da mutane ke gani tattare dake shine suke ribibin  kwata ta ko wace fuska basu duba akan faɗin tashen da ki kai kafin ki taka matsayin baki taɓa lura bah babbar bishiyar data fi yawan ya'ya ita tafi yawan shan jifa da sannu a hankali zaki fahimci komai ke dae ki kasance mai dangana da yawan kyautata mah Allah zato zaki sha mamki"

Har cikin zuciya ta kalaman grandpa sun matukar yin tasiri akan ta tabbas a rayuwa ba wanda zai cimma nasara daga kwace sai ya miƙe da kafafun sa saboda ita nasara bata da kafafun da zata zo maka kai ke dasu dazaka cimma mata matakin farko na cin nasara a rayuwa shine failure and is the foundation of success kasan you must go through challenges before you win doguwar ajiyar zuciya miran taja tana sabunta karfin gwiwar ta  bai kamata ta sare a lokacin da yafi dacewa ta tsaya mah kanta bah a baya ta tsaya ma wasu balle yanzu da ake Maganar mommy's girl da kanta tasa a ranta bawai iya shiri zatai akan wanda akae ikirarin an aura mata bah dashi ba harta waɗanda suka zamo silar shigar ta wannan halin sai tayi fito na fito dasu sai ta kwatar mah kanta hakkin ta.

Murmushi ta sakar mah grandpa ganin nashi na kara faɗaɗa  "Alhamdulillah miran Allah yai maki albarka insha'Allah zaki cigaba da ganin nasara a rayuwar ki a koda yaushe karki manta ina tare dake kuma kada sha'anin iyalin gidan ku ya dame ki da sannu duk wata tuƙa zatai warwara "insha'Allah baba Allah ya ƙara girma da ɗaukaka Allah ya ɗaura mu akan makiyan mu. "Ameen sugra kuje ku fara shiri baku bukatar komai "babu baba babu wani shiri da zamuyi in  lokacin hakan yayi zamu yi".

   Misalin karfe  6:00pm motar da grandpa ya shaida masu zata zo tafiya da miran ta iso, momy ta tisa ta gaba saida ta shiyar ta cikin tsadaddan lace navy green tai mata simple make up ita dae Miran binta kawai take bawai don tana jin dadin abinda ake mata bah ita haƙilon ta yana kan karfafa zuciyar ta ammh fargaba na kokarin kawo mata cikas sosai kirjin ta ke bugawa Aunty sugra na kara mata kwarin gwiwa miran taso sallama da maah ammh tana barci kafin wucewar likita daya duba paah saida ya duba ta itama jikin nata kara rikicewa yake kamar mai iska haka ta zama.

A compound suka haɗu da ya Aiman ya fito daga wani sashen na gidan yana warware hannun riga daya naɗe alamu sun nuna alwala ya gama saboda ga damshin ruwa nan a jikin shi har zai gitta su miran tai saurin rike hannun shi na dama sai lokacin ne ya lura dasu kwata kwata hankali shi baya tare dashi lissafi kawai yake, sosai miran ta marairaice mashi fuska tai kalar tausayi tasan ba lallai ne ya kula ta bah sai dai da mamakin ta saidai da mamakin ta sai taga ya sakar mata murmushi, murmushin data ɗau tsawon lokaci bata gani bah bata san lokacin data faɗa jikin shi bah raunin data take fafutukar yaƙi dashi saida ya bayyana ta fashe da rarraunan kuka cikin shashsheƙar kukan tace "yaya don Allah kayi hakuri ka kaini nayi sallama da paah" cak kamar an buga mashi full stop haka ya Aiman ya tsaya zuciyar shi na kyarma sosai har tsawon wane lokaci zai cigaba da shanyewa wallahi yana son kanwar sa ba wasa hango fitowar Aunty sugra yasa shi dae dai yanayin shi ya raba jikin su da miran yana share mata hawaye "kema kiyi hakuri in kura ta lafa ni dakai na zanzo na ɗauke ki nakai ki wajen shi yanzu yana cikin yanayin da bai san takura" kafin miran ta bashi amsa Aunty sugra data karaso da sassafa ta janye attention dinsu "Aiman jeka momy ku na neman ka" miya faru Aunty "matar kace ta suma "suma kuma miya faru" Aunty sugra bata tsaya bashi amsa bah taja hannun miran dake tambayar ta abinda akai ma big Aunty ta zube "karki damu da wannan mun bar mutnen suna jiran mu....................

  [16/12, 10:01 pm] Teemah MS 🥰💖: CINNAKA 🐜🐜🐜

      BAI SAN NAH

            GIDAH BAH

              SAI YA CIZAH

.

STORY

    &

WRITTEN BY

  F&F

(PERFECT PAIRS 🌺)

  63........

HAMDA 🌺🌺🌺

     Hamda ki natsu mana zai samu lafiya addu'a yake bukata daga gareki ba wannan

57 / 64