Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 25

1 to 3K   out of 73.5K words

??ࡱ?>?? 
/??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????+????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F0WordDocument????, 0Table?????????
Data
???????????????????? P??
KSKS?, ?c???????pp5555??l5??
?
?
?
?
?
?
?
?
$?? *p55?
?
5555?
? ?? ?
?
? ?
?
5 [8/12, 4:55 PM] INDO: *>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 1

NA
Ayeesha Abdulkareem INDO

Marubuciyar....
DOGON YARO
TAJMAHAAL
IDO HU?U
WATA HANYA
A JINI ?AYA
AAMINAT (Bazawara)
da sauransu...

4/8/2023

*Mikiya Writer's Association*


Bismillahirrahmanirrahim


Garin Kano
Misalin ?arfe 03:00am.... Dare mahutar bawa,, a duk lokacin da dare ya tsala sahu kan Wauke kowane Wan Adam ya killace kansa a makwancinsa domin samawa ruhinsa salama.

a wannan dare yayin da Asbahi ke shirin ?aratowa daidai lokacin hadari ya fara gangami, cikin lokaci ?an?ani ya gama haWowa ya fara sakin iska me ?arfi gami da wal?iya me tsananin haske ya na wani irin rugugi kamar zai ci babu.
Ya Wan Wauki lokaci cikin wannan yanayin kafin ya saki ruwa me ?arfin gaske.

Sai da aka kira Sallar Asbahi sannan ruwan ya tsagaita ya koma yaf-yaf a hankali a hankali, ba shi ya tsaya cak ba sai da gari ya fara haske.

mamakon ruwan da aka sha ya haddasa lullumi gami da wani irin sanyi me matu?ar daWi.

kasancewar safiyar Lahadi ce ya sa titina har ma da cikin unguwanni babu yalwar jama'a kowa ya nabba'a a gida, tin daga kan ?an makaranta har ?an kasuwa, tsirarun mutane ne kurum ke yawo sai ababen hawa na haya su ma ba su gama fitowa ba, domin kuwa yadda ?asa ta sha ruwa ta ji?u ga sanyi na ratsa jikkuna ba kowa ne zai so fitowa a irin wannan lokacin ba.

HOTORO

Hajiya Laure ce zaune kan Waya daga cikin haWaWWun kujerun Falon, ta harWe ?afa ta na danne-dannen waya fuskarta ba alamar walwala, ta haWe cikin leshi Winkin Buba ta doka Waurin ture ka ga tsiya, adon nata ya ?ara fito da asalin suffarta ta Hajiyoyi, Jiran shigowar Alhaji Salisu kawai ta ke yi don ta sauke masa buhun masifar da ta kwana ta na ?issimawa akansa.

Yazeed ne ya shigo falon ya na tafe ya na jan ?afa zagaraf-zagaraf bai bi ta kanta ba ya saita hanyar bedroom Winsa, cike da takaici ta ce "Ai ko ba za ka gaishe ni ba ya kamata ka faWa min inda ka je." fasa wucewa bedroom Win nasa ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna idanunsa ?asa-?asa ya ce "Why are u doing this to me?? you're my mother fa kin fi kowa sanin ba yaro bane ni Mummy, maganar gaskiya kin fiye kishi da ni" tsaki ta doka kafin ta ce "Ubanka ne ya lalata ka ba wani ba, na san ba zai wuce daga biye-biyen ?an mata ka ke ba, inda zan yi kishi da kai kuma ai ba zan ma haifeka ba yaro, kawai don ba ka son gaskiya ne."
TaSe baki ya Wan yi cikin ko in kula ya ce "Ina Daddy?" a masife Hajiya Laure ta ce "Ka ban ajiyarsa ne?? tin jiya ya yi min al?awarin zai dawo ya same ni amma ya ?i dawowa." "Wani gurin ya je??" ''To ai in wani gurin ya je ma da ?auna, ya na sashinsa, wai wani ba?o zai yi za su tattauna shine har da ce min kar in sake in zo sashinsa har sai ya dawo ya same ni, to ka ga da bai iya cika al?awari ba ya ?i dawowa, sai ka tashi ka je gurin nasa tinda dama ai shi kaWai ya haifeka ni ?ar karere ce, idan ka je kace masa ya fito ina jiransa." Dariya Yazeed ya yi gami da cewa "Gaskiya kina da yawan faWa Mum, ki dinga ha?uri mana Daddy fa ya na da aiyuka sosai ki dinga yi masa uzuri, kuma ba na so in ji ki na cewa ba na martaba ki Winnan Please Mum, martaba ki ya zama dole bayan ke ba ni da wata." taSe baki ta yi ta juya masa ?eya alamar ba ta gamsu ba.
Tashi ya yi ya wuce sashin Daddy ya na jiyo Hajiya Laure na mita shi kam sai dariya yake don abin nata dariya yake ba shi.

?an madai-daicin Parlor ne wanda ya ji kayan Alatu na more rayuwa, an zuba kuWi wajen tsara shi da ?awata shi komai ya ji banda tsiya inji maro?a.

Banda sanyin AC gami da ?amshi ba abinda yake tashi.
a tunanin Yazeed ya na shiga zai tarar da Daddynsa a Falon ya na karatun Jarida kamar yadda ya saba don haka ya fara cewa "Dad!!! ka na ina? ka shirya faWa da Mum don kuwa ta yi fus........" maganar tasa ce ta ma?ale a ma?oshinsa, cikin zazzaro ido ya ke kallon jini da ke kwance malala har ya gangaro ?ar?ashin Kujera ya fito kasancewar saitin kujerun a tsakiya suke.
cikin tsananin firgici ya zagaya don ganewa idonsa abinda ke zubda irin wannan jinin haka.

Ihu ya kurma gami da yin tsalle ya yi baya idanunsa kamar za su faWo ?asa sabida zaro su da yayi, dandanan jikinsa ya Wauki wata irin tsuma, zuffa ya shiga karyo masa duk da irin sanyin AC da sanyin gari da su ke kaWawa.

Baya-baya ya fara yi ya na cewa "No!! wallahi ba dai Daddyna ba, lallai yau na tabbata Jaki, naje na sha giya ta zo tana nuna min Daddy cikin jini haka? Impossible! dole ma in dena shaye-shaye!!" maganar yake cikin fitar haiyaci don kuwa tashin da hankalinsa ya yi ya wuce mizani.

Da gudu ya juya ya koma Parlo ya na ?wallawa Mummy kira, gabanta ne ya yanke ya faWi Rimmmm!!!!!!! ta yi saurin tashi ta na cewa "Me ya faru??" Yazeed ya na haki ya ce "Daddyyy!!! zo mu je ki gani, na fara haukacewa!!." ya ?arasa maganar ya na jan hannunta, cikin sauri gami da sassarfa ta bi bayansa su ka koma Falon Alhaji Salisu.

Sai da ya danganata da gawar Alhaji Salisu sannan ya saki hannun nata ya koma baya ya ri?e ?ugu ya na jiran ta ce masa ai giya ta sa ya fara gane-gane.

ya na kwance cikin jini ko ina a jikinsa raunin wu?a ne faca-faca anyi masa wani mugun kisan gilla wanda ko Dabba mutum ya ga anyiwa dole hankalinsa ya tashi bare Mutum Wan uwansa.



Hilis Share Mutanena ?an Amana=?
?

Paid Book ne.....
09079885632



??INDO
[8/12, 4:55 PM] INDO: *>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 2

NA
Ayeesha Abdulkareem INDO

*Mikiya Writer's Association>؅?*




Ihu da kururuwa Hajiya Laure ta fara yi, ba ta bi takan Yazeed ba ta fice ta na ihun neman Wauki.

Yazeed kuwa jin haka ya tabbatar masa ba gane-gane ya fara yi ba da gaske Daddynsa ne aka kashe, jaSar ya zauna a ?asa dafa'an murar kwaWi, gami da fashewa da kuka kamar ?aramin Yaro ya na cewa "Wallahi ko waye ya kashe min Daddy sai na kashe shi ba zan taSa ?yale shi ba." abubuwan da ya ke ta faWa ya na maimaitawa kenan.

Hajiya Laure kuwa ta na fita harabar gidan me gadi ya taso da sauri ya na tambayarta, cike da masifa ta ce "Maza-maza kira min ?an-sanda wallahi ba zan yarda ba duk wanda ya aikata da me hannu a ciki sai na yi shari'a da shi kuma sai na sa an kashe shi, maza ka kira min su!!." ta ?arasa maganar cikin tsawa, jiki na tsuma Tala ya ce "Hajiya ai bansan me zan ce musu ba ne"
Kamar za ta cinye shi da masifa ta hayayya?o masa ta na cewa "Ka ce musu Alhaji Salisu aka kashe, su yi sauri su zo tin kafin wanda ya aikata ya bar garin su kama shi don wallahi ba zan ?yale ba ko uban waye shi."

Jin furucin kisan Alhaji ya ?ara Waga hankalin Tala me Gadi, cikin rawar murya ya ce "To Hajiya ku na da lambar ?an-sandan??" tasssss ta wanke shi da wani lafiyayyen mari, jikinta ya Wauki tsuma sai huci take sabida Sacin rai gami da tashin hankali da su ka yi karo da juna a cikin Zuciyarta.
"In banda kai Wan iska ne? a kashe Alhajin shine za ka zauna ka na tambayata lambar Police Dan Ubanka? kai ba za ka iya zuwa da kanka ka nemo su ba? Ba akwai mukullin mashin Win da nake aikenka a wajenka ba??"
Ta yi maganar ta na huci kamar bujimin Sa.

Tala Me Gadi ya na jin haka ya juya Wakinsa da gudu, ba daWewa ya Wakko mukullin ba tare da ya dawo gurin Hajiya Laure ba ya zabari mashin ya fice kamar ya tintsira sabida sauri.

Har su ka dawo tare da ?an Sanda Hajiya Laure tana harabar gidan ta na zagaye, daga ta kai mari sai ta kai gwauro, sai surutai ta ke yi tamkar sabuwar mahaukaciya.

Ta na ganin ?an Sandan ta yo kansu ta na cewa "Wai kamar ni za a kashewa Miji?? Alhaji Salisun za a kashe?? shekararmu kusan Talatin da Aure amma yau Waya a kashe min shi? Inspector lallai ka kama kowaye ya aikata sannan ka tabbatar an hukunta shi, wallahi ko me ka ke so zan baka, kai ko duka dukiyar da Alhaji ya bari ce zan baka ni ban damu da cin gadon dukiyarsa ba kawai Fansar Ruhinsa nake bu?ata!!!."
Inspector Khalil ya jinjina kai kana ya ce "Mu je ki raka mu inda abin ya faru." kafin ya rufe baki ta juya ta na cewa "Ku tawo."

Bin bayanta su ka yi zuwa Falon Alhaji Salisu, har lokacin Yazeed ya na gurin ya na Sarza kuka tare da faWin sai ya Wau Fansa.
Har ?an Sanda su ka gama bincike-bincikensu su ka yiwa Hajiya Laure da Yazeed da Tala tambayoyi ba abinda su ka fuskanta game da kisan, illa iyaka sun shaida wanda ya yi kisan ba ?aramin makashi bane don kuwa ba wata alama da ya bari wadda za ta nuna cewar shi ne.

Gawar Alhaji Salisu ?an Sanda su ka Wauka zuwa Asibiti, wurin ya rage daga Inspector Khalil sai Constable Saleh sai Hajiya Laure da Tala.
Har zuwa lokacin ro?onsa take kamar ta yi masa sijjada akan ya nemo mata wanda ya kashe mata miji.
Cikin salonsa na iyayi da kwainane ya ce "Kar ki damu Hajiya ai hakan aikina ne, yanzu kamata ta yi mu je Asibitin mu gani don haka ke ki yi gaba ina zuwa, zan tafi da wannan me gadin naku don ba yadda za'ayi a ce bai san anyi wannan kisan ba dole da sa hannunsa."
Hajiya Laure ta sharce ?walla gami da majina cike da farin cikin jin furcinsa ta ce "Na gode IP sai kun zo Win." kai ya gyaWa mata kana ya nufi hanyar fita cikin takunsa na ?asaita da jin kai, Hajiya Laure ta bi bayansa, Constable Saleh kuma ya cukumo Tala me gadi.

Har Inspector Khalil ya Waga ?afa zai shiga mota Constable Saleh ya dakatar da si da cewa "Sir!! na yi ?o?arin danne abinda ke raina amma na kasa, wallahi da alama ka fara aiki a wannan Office da ?afar hagu domin da alama SAR?A ta yi Rikicinta a wannan gida."
Fasa shiga motar ya yi cikin rashin fahimtar inda kalamansa su ka dosa ya zuba masa idanu kana ya ce "Me ka ke nufi da haka? wacece SAR?A??"

"Ba mace ba ne, Sunansa na gaskiya MUHAMMAD RISLAAN MUHAMMAD amma kowa da kalar sunan da yake kiransa sabida ya buwayi duniya, Sir! ina ganin a lallaSa Hajiyar nan a rufe wannan Case Win in ba haka ba kai ma zaman Office Winnan sai ya gagareka, na ga irinka da yawa waWanda su ka zo su ka koma sabida buwayar Yaron nan."
Murmushin rainin hankali Inspector Khalil ya yi kafin ya ce "Ina ne gidansu??"
Cikin zaro ido Constable Saleh ya ce "Ka yi mini rai ka gafarce ni YallaSai kar ka ce za ka kama bawan Allahn nan, wallahi idan ya san ni na gaya maka shi kenan na mutu, YallaSai ina da mata da ?a?a uku yanzu ma ta na Wauke da juna biyu, ka temaka min kar ka yi silar zaman iyalina marayu."
Inspector Khalil ya dafa kafaWarsa cikin sigar rarrashi ya ce "Kai fa Jami'i ne akan me za ka ji tsoron wani karankaWa miyar mutum? kar ka damu ba zan bari ya san kai ne ka faWa ba, yanzu bani information nashi, a ina za mu same shi?"
Jiki na rawa Constable Saleh ya ce "Ban sani ba YallaSai shi kamar iska ya ke ba shi da tabbas, idan ka ganshi anan a yanzu za ka ganshi a can, amma ina da lambar ?an uwansa malamin wata makarantar Islamiyya idan ka kira ka tambaya tayuwu ya na makarantar amma fa sai sa'a za a same shi."


Cike da jin daWin hakan Inspector Khalil ya Wan bubbugi kafar Constable Saleh ya na wani irin murmushi me cike da ma'anoni, cikin salonsa na iyayi ya ce "Jami'i me basira, ba ni lambar."
Cikin rawar jiki Constable Saleh ya mi?awa Inspector Wayarsa ba tare da ya ce komai ba don kuwa ya hau dokin tsoro da firgici, ya gama sallamawa ya sa a ransa kwanansa ya ?are.

sai da kiran farko ya katse a na biyu aka Waga tare da yin sallama, Inspector Khalil ya amsa sannan ya ci gaba da cewa "Ina magana da Sheikh Auwal ne??" a Waya Sangaren Sheikh Auwal ya ce "Eh ni ne amma ban gane me maganar ba."
"Sunana Inspector Ibrahim Musa Rano wanda aka fi sani da Inspector Khalil, ina neman Muhammad Rislaan Muhammad ne."


dimm!!!! Zuciyar Sheikh Auwal.
"Muhammad Rislaan Muhammad?? What Happened??" Sheikh Auwal ya faWa cike da tsoron abinda zai fito daga bakin Inspector.
"I suspect him of murder, so i will arrest him, i need his informations, ina son sanin inda zan sameshi, ka ba ni haWin kai Ya Sheikh kar ku wahalar da hukuma."

wani irin tu?u?i zuciyar Sheikh Auwal ta ke yi gami da tsalle tamkar za ta fasa ?irjinsa ta fito, cikin tsantsar Sacin rai ya ce "Kar ka kuma tambayata bayanan Akhiee domin ba shi da tabbas, yau dai ka yi sa'a ya zo makaranta, ka zo nan ka same shi."
Farin ciki ne ya lulluSe Inspector Khalil, ya murmusa sannan ya ce "Godiya nake Sheikh Auwal sai na zo Win."

Constable Saleh ya ce "YallaSai na ga ka na murna?"
"Na samu inda ya ke cikin sau?i, ka ga dole ne na yi murna, ba ka sani ba ne dominsa aka turo ni nan aiki ba zan gushe ba har sai na ga bayansa, yanzu Asibitin ya kamata mu je ko Makarantar?"
"YallaSai na san ana bu?atarka a asibitin nan ko ba za ka yi komai ba ya kamata a ganka, mu je can Win in yaso daga baya sai a je makarantar" Constable Saleh ya yi maganar cikin rawar murya kamar zai fashe da kuka.

Dariya Inspector Khalil ya yi sannan ya ce "Ka na da tunani me kyau, ya kamata ka zama babban Jami'i."
Daga haka ya shige mota, Constable Saleh ma shiga ya yi a ransa ya na cewa "Bayan ka gama kashe ni tin yanzu"
Tala me gadi kuwa banda kuka ba abinda ya ke rusawa ya rasa ma ko bakin magana bare ya ce musu shi bai san anyi kisan ba.


Kai tsaye Asibiti su ka nufa don ganin yadda komai ke tafiya a Sangaren binciken gawa.


Babbar Makaranta ce me Wauke da sassa da ajujuwa daban-daban, makarantar na Wauke da Wumbin Walibai masu yawa manya da ?anana, mata da maza, akwai wadatattun malamai masu koyar da ?ira'a daban-daban ba wanda ba'a yi a makarantar indai na Islam ne.

a wani babban Aji me Wauke da mata da maza kowanne gefen zamansu daban, duk Winsu sun du?ufa akan karatunsu, daddaWan sautin karatun Qur'ani ne ke tashi ta ko'ina a ajin gwanin sha'awa.


Sheikh Auwal na zaune kan kujerarsa ta Malami ya zuba tagumi da duk hannayensa, tunanin ma irin hukuncin da zai yiwa Rislaan ya ke, a duk iya tunaninsa ba hukuncin da zai iya yi masa wanda ya wuce yi masa shegen duka.

Mi?ewa ya yi tsaye ya na rarrabawa Waliban nasa idanunsa da su ka yi jajir sabida Sacin rai, "A dakata!" ya faWa cikin kamilalliyar muryarsa.

Shiru ajin ya yi kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa, an kai 10 second cikin yanayin shirun sannan Sheikh Auwal ya ce "Zahra'u Muhammad!" cikin sanyin jiki ?ar budurwar ta mi?e gami da cewa "Labbaika" Ganin irin halin mugun Sacin ran da Wan uwan nata ke ciki ya ?ara karyar mata da zuciya, zirrrr hawaye su ka fara sharara akan kumatunta.


Sheikh Auwal bai bi ta kan kukan nata ba ya ce "Maza ki hau sama ki kira min Akhiee, sannan ki bi duk ajujuwan makarantar nan ki tattaro min duk Malaman cikinta ina

1 / 25