Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   14 / 25

39K to 42K   out of 73.5K words

Wan numfasa sannan ta ce "I already voted for you, tin tuni kai na zaSa shi yasa ma na gaya maka iya gaskiyata"
Cikin sassanyar murya me sanya nutsuwa ya ce "Kin tabbata?"
kai ta gyaWa gami da cewa "Eh"

Bai ce uffan ba ya kama tsintsiyar hannunta ya shiga janta, da kallo ta bishi a ranta ta na tambayar kanta ina zai kaita? kuma gashi ta kasa cijewa ta dena binsa.
Haka ya ratsa jama'a da ita ba tare da damuwa da kallon da ake yi musu ba, sai da su ka dangana da wajen da Amadu ya ajiye mota sannan ya tsaya, daidai lokacin Zara ta ?araso da gudu-gudu hankali tashe ta ce "Ina za ki je Husnee??" "Nima ban sani ba tambayi Akhiee" ta faWa ta na kallonsa.
"Ki koma makaranta kar ranki ya Saci" ya faWa ya na zuba mata wani shegen kallo wanda ya sa ta yi saurin juyawa.


Amadu tuni ya fito daga cikin Motar cike da mamaki ya ce "Lafiya dai?" Akhiee ya ce "Ki shiga mota Ni zan tafi akan Dokina, amma kar ku bari na Sace muku duk inda na yi nan za ku yi."
Amadu ya Wan yi gyaran murys cike da tsoro ya ce "To Malam ina za mu je haka?"
Rikitattun idanunsa ya watsawa Amadu gami da cewa ''Kar ka bari ka yi mini ba daidai ba." daga haka ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Dokinsa.

Husnee dai sai rarraba ido ta ke yi duk ta rasa ma tunaninta gabaki Waya.
Amadu ne ya katse mata tunani da cewa "Innata ki na ganin mu bi shi ko kuwa?" buWe motar ta yi ta shiga ba tare da ta ce komai ba hakan ya sa shima ya shiga ya bata wuta ya shiga bin bayan Akhiee.
Bakin wani masallaci ya tsaya wanda Almajirai ke ta karatu a ciki da wajensa.
wajen Motar ya dawo ya Wan le?a gami da cewa ''Ki jirani anan Asma'u! kai kuma ka zo mu shiga ciki" gyaWa kai ta yi gami da sa hannu ta buga tagumi ta na tunanin abinda ke shirin faruwa sai dai duk iya nazarinta ta kasa fahimtar komai.

A cikin Masallaci kuwa gaban Babban Malamin Makarantar Allon su ka dur?usa daga shi har Amadu.
Malam Kabiru da fara'a akan fuskarsa ya ce "A'hh! yau Wan namy ne a gabana haka?"
Akhiee ya ce "Ni ne Baba Kabiru, wata alfarma na zo ayi mini." Malam Kabiru ya jinjina kai cikin dattako da manyance ya ce "To ina saurara Allah i sa abinda bai fi ?arfina ba ne, duk ya wajen manyan ina Baban naku ya na lafiya? kwana da yawa ban zo mun gana ba"
Akhiee ya gyara zama sannan ya ce "Yana lafiya, Aure nake so a Waura mini a yanzu-yanzu, Baba Kabiru kai Aminin Mahaifina ne, hakan ne ya sa ba ni da wurin zuwa ayi mini haka in ba wurinka ba"
Kamar saukar aradu haka Malam Kabiru ya ji maganar Akhiee ta faWo masa, tsananin mamaki da kaWuwa su ka lulluSe shi lokaci Waya, sai dai abin manya sam bai nuna alama ba, cikin nutsuwa da kuma tattausar murya ya ce "Muhammad! Aure fa ba abin wasa ba ne, idan har da gaskr ka ke yi mini me yasa ba ka sanarwa Mahaifinka da ?an-uwansa ba? me yasa kuma sai yanzu-yanzu kake so a Waura?"
Sam ba ya son yawan tambaya don kuwa ransa Saci yake yi, amma da yake Malam Kabiru tamkar uba yakw a wurinsa sai ya danne.

Kai tsaye ya ce "Ba bu?atar kowa ya sani har sai bayan anyi, ka manta da batun gaya musu kawai."
"A'a fa, ko ba ka so Malam Muhammad ya sani ai ya kamata ko yayyenka ka sanarwa, Muhammad Aure fa ba a yi masa gaggawa, idan aka jira lokacinsa ya yi sai a yi shi cikin kwanciyar hankali, kafin ?aura Aure ana bu?atar Dangin ?iya domin a gana a san juna kuma a nemi yardarsu."


SHARE FISABILILLAH



Na KuWi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ?arin bayani =?I?
AN FARA PAYMENT

*??INDO*
[8/24, 9:23 PM] INDO: *>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 17

??
Ayeesha Abdulkareem INDO


*M.W.A>؅?*





"Wannan shine Wakilinta" ya faWa ya na nuna Amadu, kafin ya Wora da cewa "Ni kuma kai za ka yi mini komai; Ba na so na aikata ba daidai ba shi yasa na ke bin komai a maslaha."

(Ohh! ni Indo su Amadu an zama Wakili>?#?)

Zaro ido Amadu ya yi cikin matu?ar razani da firgici ya ce "Iye? wallahi Malam Allah Waya ba zan iya ba, a je a nemo wani dai don Allah." wani shegen kallo Akhiee ya aika masa wanda ya sa shi saurin haWiye surutun nasa.
Malam Kabiru ya san halin Akhiee sarai, zai iya tuSe rigar kunya ya zuba masa rashin mutunci duk da cewar Abokin babansa ne don haka ya jinjina kai kana ya ce "Shi kenan, na san zan iya yi maka komai amma ina son sanin dalilin da ya sa kake so ayi hakan."
"Ina so ta dawo ?ar?ashin kulawata ne sabida za'a iya cutar mini da ita idan na tsaya Sata lokaci, Yanzu abin da za'ayi ka tattaro dattawan Abokanka Winnan ku yi komai tare."
Malam Kabir ya ce "To Sadaki fa?"
"Yanzu za a kawo" ya faWa a ta?aice.

Malam Kabir dai a gefe cike yake da fargabar Waura auren don kar wani abun ya je ya zo, a gefe guda kuma ya na shakkar iya shegen Akhiee, don haka ba shi da zaSin da ya wuce ya Waura Auren kawai a huta.
?aya daga cikin ?alibansa ya tasa ya ce ya je ya gayyato masa Dattawan da ke zaune a wajen Masallaci.

Ba tare da wata daWewa ba suka shigo Tare da su Salansa.
Kusa da Akhiee ya zauna sannan ya mi?o masa kuWin, Akhiee ya ce "Ka lissafa?" "Eh Dubu Tamanin ne kamar yadda ka ce" bai ce komai ba ya mi?awa Malam Kabiru gami da cewa "Ga shi nan idan da ciko su yi bayani zan basu ko nawa suke bu?ata."
Malam Musa ne ya dubi Malam Kabir cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa ya ce "Me za a yi ne Malam?"

Dalla- dalla Malam Kabir ya yi musu bayanin duk abinda ya faru da kuma wanda zai faru anan gaba, ba su yi musu ba su ka gyara zama domin Waura Aure.
Malam Kabir ya mi?awa Amadu ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?da ya gama rikicewa kuWin gami da cewa "To gashi, idan an yiwa iyayenta bayani idan suna bu?atar wani abin sai a sanar" Amadu ya karSa hannunsa na rawar mazari, ko uffan ma ya kasa cewa.

Tare da sauran ?aliban Malam Kabiru manyansu da yaransu aka Waura Auren. Bayan an gama su Gwaja su ka kawo Alewa da Biskit da Dabino aka rarraba, sannan kowa ya san inda dare ya yi masa.

Akhiee ma sallama ya yiwa Malam Kabiru sannan ya fito, su Salansa na biye da shi ciki kuwa har da Amadu da jikinsa duk ya gama mutuwa.
Ta na ganin sun fito ta fito daga cikin motar ta tsaya ta na binsa da kallo.
Tinda su Gwaja su ka faWa mata abinda aka yi ta fara kuka ta cika da tsoro da fargabar abinda za ta tarar a gidansu.
Har ya ?araso inda take shi take kallo har ya zo gaf da ita, idanunsa masu matu?ar Waukar hankali ya zuba mata ya na jin kukan nata har cikin ransa, wani farin hankicif ya zaro a Aljihunsa ya fara goge mata ?wallar ya na hura mata iskar bakinsa a hankali, hakan ya sa ta fara fizgar numfashi ta na sauke ajiyar Zuciya, cikin wata tattausar murya wadda duk wanda ya jita zai so ya ?ara saurarenta ya ce "I'm so sorry Asma'u, ba ni da zaSin da ya wuce haka, Allah ya riga ya ?addara ke ce abokiyar rayuwata, kuma abubuwa da yawa na cutarwa su na bibiyar rayuwarki shi yasa na yanke wannan hukuncin, da zarar na kai ki gidanmu babu wani abu da zai ?ara barazana wa rayuwarki sai dai in kin fito daga cikinsa."
Wan jinkirtawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Ki dena kuka, ko da duk Duniya za ta juya miki baya ni ina tare da ke, tinda ki na so na a ganina ba abin tashin hankali ba ne hakan, kuma ba na yi ne dan na Sata miki ba sai dan ba na son na ga kin cutu, ki na da muhimmanci a rayuwata kuma ke ta musamman ce a wurina; Yanzu ki bi Amadu ya kai ki gida kafin na zo ?aukarki."
Sunkuyar da kanta ta yi ?asa zuciyarta cike da tunane-tunane, ganin ta kasa ko motsawa ya sa shi kamo hannunta ya buWe mata motar gami da cewa "Shiga mana" shigar ta yi har lokacin ba ta ce ko uffan ba, wata tamfatsetsiyar waya ya zaro cikin Aljihunsa ya mi?a mata gami da cewa "Ga wannan a koda yaushe idan ki na nemana za ki sameni, lambobin ciki duk nawa ne."
KarSa ta yi gami da gyaWa kai ba tare da ta yi magana ba, ido ya zuba mata a ransa ya na jin kamar ya tafi da ita tin a yanzu sai dai ya na so iyayenta su fara sani ya ga iya gudun ruwansu, don ya san mawuyaci ne su amince da shi.
Cikin sigar zolaya Salansa ya ce "Me House ko za ka bi ta ne?"
rufe motar ya yi gami da yin baya, Su Salansa kuwa sai dariya suke a ciki-ciki don kar ya ji su.
Amadu ne ya matso kusa da shi kamar zai fashe da kuka ya ce "To YallaSai ni dai wannan ?a a matsayin amana take a wurina da zarar na rabota da gidan iyayenta, sai gashi yanzu kai kuma ka mallaketa ta hanyata ba ta hanyar iyayenta ba, nima na shiga matsala ban san wane kallo za su yiwa hakan ba, ina fatan ba don cutarwa ka yiwa wannan baiwar Allah haka ba."
Dafa kafaWarsa ya yi kafin ya fara magana cikin salonsa na izza "Ita Win matata ce kuma mallakina, Ka kula mini da ita sosai, ba ka cikin matsala don kuwa ina da kafaWun da zan iya Waukar komai akanta, inda zan iya cutar da Asma'u da na daWe da rabata da rayuwarta ko kuma wani abu mafi muhimmanci nata, ku je kawai a gaishe mini da mutan gidan".
Amadu ya jinjina kai, yanzu ya samu ?warin guiwar da zai iya komawa gidan saSanin da da ya cika da tsoro.

Sai da motarsu ta bar layin sannan Akhiee da tawagarsa su ka Waga.
Kai tsaye Makwantarsu su ka koma inda suke yiwa la?abi da suna Masarautar Sar?a.
Har cikin Fadarsa su ka raka shi a memakon su bashi wuri kuma sai su ka zauna su ka mamaye shi, kowa cikinsa cike taff da tambayoyin da yake son yi masa, ciki kuwa har da su Laita da duk sauran yaransa.

Zabira ce ta fara buWe musu fagen tambayar da cewa "Wai dama ka na soyayya Abba?"
Da sauri ?an Bakwai ya ce "Yauwa!! abinda nake son ji kenan nima, daWina da ke kanki ya na kawo wuta ta gidana"
Nan fa kowa ya fara tarkato tashi tambayar ya na jefowa, shi kuwa Akhiee sai shan wiwi Winsa yake yi ya ?i cewa komai.
Sai da su ka gama su ka fara yin slow sannan ya Wan yi gyaran murya duk su ka nutsu, "Ni ba na soyayya hasalima ban san ya akeyinta ba, abinda nake so ku sani shine Asma'u ita kaWai gareni, idan a cikinku ne aka illata wani to ina da wani, amma ita duk Duniya ba ni da tamkarta, kuma ba ni da wadda za ta zamo kamarta, duk tsawon rayuwarku da ni bayan Iyalina akwai wata mace da kuka taSa ganin ina saurara?" amsawa su ka yi da "A'a" ya ci gaba da cewa ''Nima kaina na yi mamakin ta yadda aka yi na fara saurararta har ta yi nasarar sa ni abubuwa da dama a cikin waWanda ba na yinsu, haka kawai nake jinta tamkar Ruhina idan aka cutar da ita tabbas an yi mini babbar cuta, hakan ne ya sa nake so ta dawo ?ar?ashin kulawata hankalina zai fi kwanciya, ga bayani nan na yi muku wanda bai fahimta ba kuma ba zai taSa fahimta ba don haka ku tashi ku ban wuri ba na bu?atarku a yanzu."

mi?ewa su ka yi su na ta murna su ka rankaya su ka yi waje, can gefe su ka haWa majalisa su ka fara tattaunawa, Gwaja ya ce "Ai na godewa Allah tinda yanzu ya samu mata mu ma ?ila zai barmu mu dinga kula mata har mu yi Aure"
"Mewtchh!!!" Salansa ya doka tsaki kafin ya ci gaba da cewa "Kai ta Aure ma ka ke yi, idan shi ya iya kula da ita kai yadda kake kai a sama Winnan ba abinda za ka iya yi mata, ?arshe ka sa ya kasheka a banza" Wan sassauta murya yayi kafin ya ce "Wai kun san me? ya ce bai san so ba ko? to wallahi sonta yake yi."
Laita ta yi dariya kafin ta ce ''Bar Wan iska ya na son kayarsa mana." su ka ?ara kwashewa da dariya, hira su ka ci gaba da yi cikin farin ciki domin kuwa su daWi abin ya yi musu.

A ?angaren Husnee kuwa kamar Sarauniya haka ta shiga gida da sanWa, ta yi muzu-muzu da ita kamar ji?a??iyar kaza.
Mommy da Yaya Muddassir su na zaune su na hirar yaushe gamo ta shigo Falon cikin takunta me kama da na masu koyo.
Yaya Muddassir ya bita da kallo kafin ya ce "Lafiya kuwa ?anwata?" kusa da shi ta zauna kafin ta yi magana cikin muryarta da ta dishe, "Lafiya lau"
Mommy ta ce "Lafiyar Kura ba? in gaya maka gaskiya sai an haWa da addu'a don kuwa Aljanu ne su ka shafeta, ka ga yadda tafita Wazu lafiyar Allah ko? to ka ga yanzu yadda ta dawo, to haka take kan da lafiya jikin ba daWi, kwanaki haka su ka dinga lallan?wasa kamar tsutsa, ni dai naga abin al'ajabi, na ce ma zan kaita Islamic Center ko Allah zai sa a samu sau?i"
Muddassir ya bi Husnee da kallo, shi dai a rayuwarsa Allah ya Wiga masa so da ?aunar ?anwar ta shi fiye duk sauran ?annensa, tausayinta ya gama kama shi, cikin sanyin jiki ya ce "Sannu kin ji ?anwata?, meke miki ciwo yanzu."
"Ba komai" ta faWa ta na turo baki gaba.
Ya ce "Kin tabbata?, to idan ki na bu?atar wani abin sai ki gaya mini kin ji? ko mu je ki sha Ice Cream?" rasss ta ji gabanta ya faWi, "Ba ka san cewa ni yanzu matar Aure ba ce Yaya" abinda ta faWa a zuciyar kenan a sarari kuwa ta yi saurin girgiza masa kai.
Ya ce "Shi kenan yanzu ki samu ki ci abinci ki huta in anjika zan baki labarin Kaduna, kin ce ma za ki bini ko?" girgiza kai ta yi alamar "a'a" gami da cewa "Na fasa" ya yi dariya a ransa ya ce "Nima ba za ni da ke ba" a sarari kuwa ya ce "To shi kenan."
Tashi ta yi ta koma Wakinsu ba ta nemi abincin ba ta baje anan bacci me cike da mafarkai masu daWi da marasa daWi ya yi tafiyar ruwa da ita.

Hajiya Laure na zaune ta na waya ita da Hajiya Saudah, ?orafi take yi akan Boka ya ?i kiransu har yanzu, Hajiya Saudah ta ce "Ke fa kin fiye gaggawa ?awata, ki jira mana ai komai ya na da lokacinsa indai Boka Barore ne za ki sha mamaki, ai ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin faWa ne."
Hajiya Laure ta sauke wani gwaurin nishi gami da murmushi, cikin jin daWi ta ce "Allah i nuna mini wannan ranar ?awata, na ha?ura ai ni da na ji shiru har na yanke shawarar za mu canja wuri."
Hajiya Saudah ta ce "Ina!! ai ba wannan maganar, ke wai ba ki ga yadda nake ba a gidana? Boka Barore fa ba wasa ba ne in gaya miki gaskiya."
Hajiya Laure za ta yi magana ta ankara da Yazeed akanta, fasa maganar ta yi daga ?arshe ma sai ta katse wayar, ta bishi da kallon rashin gaskiya ta wani ci mur, a masife ta ce "Kai kuma mara Zuciya ?alau kake kallona? mara kishin nasa?"
Zama ya yi kafin ya ce "Ni indai irin kishin nan naki na bin bokaye ne ba ni da shi, In da ?an daba ki ka haWa ma da tuni sun yi miki abinda kike so amma sai wani ?arar min da dukiya ki ke yi akan bin bokaye, ai ?an Daba da Wan Daba ake haWa shi."
Ta yi tsaki kafin ta ce "Kai dallah rufe mini baki shashasha, kai ai soko ne na asali, yaron da ya gagari hukuma shine ka ke tunanin wasu ?an daba za su iya da shi? shima fa Wan daban ne kuma ya na da ?an daban, ni na fi son abinda zan yi masa illa lokaci guda."
"Allah ya bada sa'a" ya faWa ya na taSe baki.
"Amin" ta

14 / 25