Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   23 / 25

66K to 69K   out of 73.5K words

akanmu, amma ina ganin indai har ba zai dinga cutar da ita ba kawai kar a ce za a rabasu don hakan ma wani aikin ne babba, kuma ta riga ta faru sai ha?uri, ko an rabasu dai abin ya riga ya shiga kundin tarihi ba wanda zai manta."
Abee ya yi murmushin manyance kafin ya ce "Wannan gaskiya ne, ya yi kuskure amma ana bu?atar yafe masa; Wai ni ko akwai abinda kuke Soye min dangane da shi ne Magajin Malam?, a gidan nan kowa ba ya laifi sai shi kaWai? ba a faWen aibun kowa sai na shi, anya kuwa ba wani abin kuke Soye mini ba?, ko kuma don shi Maraya ne yasa ku ke yi masa hakan?"
Hawayen da suka cika idanun Sheikh Auwal suka samu damar zubuwo, goge su ya yi cikin sauri kafin ya ce "Abee nima fa maraya ne, da ni da shi da Zahra Mahaifiyarmu Waya kuma ba ta raye a Duniya, kawai dai shi ya bambanta da kowa ne, ya fi son ya yi abinda ra'ayin kansa ne ba ya jin bari, kuma irinsu su na da wuyar sha'ani".
Abee ya ce "Allah ya jaddada Rahma garesu ita da sauran ?a?anta da mu ka rasa, amma akwai abinda ba kowane ya san shi ba a tare da Dattijo, kuma ba wanda zai iya fahimta har sai wanda Allah ya bawa iko; a gaya masa ina bu?atar ganinsa."
Sheikh Auwal ya amsa sannan ya mi?e.

Yazeed a hankali ya fara buWe idanunsa da suka yi masa nauyi suka rirri?e kamar an yi ya?in basasa a cikinsu, da ledar ruwa da Allurai ya fara yin tozali hakan ya tabbatar masa a gadon Asibiti yake, wani marayan kuka ya saki me cike da tausayin kansa, "Me rayuwa take nufi da ni? me yasa zan kamu da son wadda ta tsaneni? me yasa ba za ta tausayi min ba?" tambayoyin da wani sashi na Zuciyarsa ke yi masa kenan sai dai ba shi da amsarsu.
Hajiya Laure da ke zaune a gefen gadon ta zuba tagumi ta yi saurin juyowa gareshi sabida jin sautin kukansa, "Sannu Yazeed, Allah ya baka lafiya, me ya jawo maka ciwon Zuciya Yazeed?" ta ?arasa maganar a marairaice tamkar da ance ar za ta fashe da kuka.
a hankali ya ri?o hannunta kam ya na cije leSensa, da alamu azabar da yake sha ta wuce kwatance, cikin sar?a??iyar murya ya ce "Mommy! mutane nawa kika zalumta a Duniya? Mutane nawa kika wula?anta a Duniya?? Da ni da ke na san har da Daddyna mun kasance baragurbi a cikin Al'uma, ban taSa ganin inda muka gina Alkairi ba; Daddyna kulluyaumin burinsa ya za a yi ya kere Abokin kasuwancinsa ko ta hanya me kyau ko marar kyau, ban taSa ganin inda ya kyautatawa marasa ?arfi ba, ko Islamiyya bai taSa ginawa ba bare Masallaci, Haka kema burinki kawai kar ya yi miki Kishiya, muradinki ki kere sa'a a cikin ?awaye, aikin kenan biye-biyen bokaye, ba ku da tunani sai haka, shi yasa kuka manta da ni kuka kasa Ba ni tarbiyar ?warai wadda kowa zai gani ya yaba, na kasance mazinaci Wan shaye-shaye; ban taSa yi muku nasiha akan abinda ku ke yi ba, nima duk da na samu damar da zan kyautata amma ba na kyautatawa kowa sai abokan ta?adirancina, Kaiconmu Mommy!!, rayuwa ta riga ta sauya kuma daga yanzu har wani lokaci a koda yaushe kina iya rasani, kuma na yi imani da Allah ire-iren kusakuran nan namu su ne suke bibiyarmu, shi sharri Wan aike ne da zarar ya isa zai juyo zuwa ga wanda ya aika shi, ni dai Mommy ba na bu?atar ki ?ara bawa wani boka Dukiyata, da ita zan gina Alkairin da muka kasa ginawa a baya ko hakan zai sa mu samu sassauci, zan nemi Malamai da Shaidu a biya waWanda suke bin Daddy bashi sauran kuma a sallameki nima a sallameni, in ya so sai ki yi duk abinda za ki yi da naki."

Jikin Haj Laure ya yi sanyi salam tamkar an zare mata laka, wani sashin na Zuciyarta ya na son gazgata zantukansa musamman idan ta tuna irin abubuwan iftila'i da masifa da ta fara gani ta silar bin bokaye, wani sashin na Zuciyarta kuwa zigata yake yi akan cewar zafin ciwo ne ya sa Yazeed yake waWannan surutan, ba ta iya ce masa ?ala ba sai ma tagumi da ta buga ta lin?aya a cikin duniyar nazari.

Sai misain ?arfe goma na dare ya shigo don zuwa kiran da Abee ya yi masa.
Husnee na zaune a bakin gado ta zuba tagumi da duk hannayenta, jin motsi ya sa ta Wagowa ta zubawa bakin ?ofa idanunta da su ka kumbura tulu-tulu sabida kuka, har ya ?araso ya zauna a kusa da ita idanunta na kansa, shi ma ya zuba mata nasa idanun na Wan lokaci kafin ya ce "Kuka kika yi ko? me yasa ma ba ki yi bacci ba?" cikin muryar kuka ta ce "Ta ya ba zan yi kuka ba Rislan? ta ya zan iya bacci bayan tin jiya rabona da ganin iyayena da ?an uwana? kuma ban san halin da suke ciki ba, kai ma kanka sunan ina tare da kai amma tin jiya ba ka ?ara waiwayata ba ni kaWai na kwana a Wakin nan, gashi ban san kowa ba kuma na ga ba sa ?aunata ?an gidanku Zara ce kawai take tausayina, haka suka dinga li?owa suna kallona kamar ni ba kutum bace, kowa da irin kalma marar daWi da yake faWe a kaina, kai kaWai zan gani Zuciyata ta yi sanyi amma ka ?i bani damar hakan!!!" ta ?arasa maganar gami da fashewa da wani kasalallen kuka me taSa zuciyar me saurarensa.

Mashin tausayinta tuni ya daWe da huda Zuciyarsa, a hankali ya sanya tattausan tafin hannunsa ya shiga goge mata ?wallar sai dai da ya goge da wata ta zubo. cikin nutsuwa ya ce "Kinsan ba na son ganin kukanki, za ki sa na yiwa kaina tsatstsauran hukunci."





*??INDO*
[9/10, 1:17 AM] INDO: *>ػ?S-K>ػ?*
Ep 25





"To ai kai ne tinda ka tafi ka bar ni jiya ba ka ?ara nemana ba, ko kaya fa ba ni da su da na yi wanka ma sai na jikina na mayar, don Allah ka kai ni gida in Wauko kayan daga nan sai na yi magana da su Mommy."
Tsirawa bakin nata ido ya yi ya na kallon yadda take maganar cikin yanayi me kama da shagwa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Sa. Ga abinda take faWa masa amma shi tunanin da yake yi daban, a hankali ya sauke babban Wan yatsansa zuwa kan laSSanta ya na shafasu cikin nutsuwa da wani irin salo, cak!! kukan ya tsaya ta Wago ido ta zuba masa ta na jin wani irin yanayi har cikin ranta, sassanyar iskar da ya hura mata a fuskarta ta sa ta yi firgigit ta Wan tsorata gami da faWawa jikinsa ta ?an?ame shi ta na sauke nannauyar ajiyar Zuciya.
"Zan sa a kawo miki kayanki gobe, ba zan bari ki je gida yanzu ba."
ya faWa cikin wata kasalalliyar murya me sigar raWa.
Sake cusa fuskarta ta yi a cikin ?irjinsa ta ?ara lafewa sannan ta yi magana cikin sanyin murya, "Me yasa ?an gidanku ba sa sona???"
Hannunsa na dama ya sanya ya tallafo haSarta hakan ya bashi damar kallon fuskarta, cike da tausayinta ya ce "Ba ke ce ba sa so ba ni ne, ba ki da wani aibu wanda zai sa a ?i sonki Asma'u, ba sa so na yi farin ciki ne shi yasa suke son rabuwata da ke, Babana ya na gidan nan Da shi da Zara su kaWai ne danginki; ko da Zara ba ta nan ki dinga zuwa wajensa ki na zama kin ji ko?"
"Amm...." saurin katse mata hanzari ya yi ta hanyar girgiza mata kai don haka ta yi shiru gami da yin ?asa da kanta.
Sun Wauki Wan lokaci a haka ba tare da kowa ya yi magana ba, Rislan ne ya katse shirun da cewa "Ki duba a cikin kayana akwai Jallabiya na san akwai wadda za ta yi miki sai ki sakata, zan je wurin Abee na dawo sai mu je ki gaisar da shi."
Yanzu ma kai ta gyaWa masa ba tare da ta ce komai ba, cikin nutsuwa ya zameta daga jikinsa ba don ta so ba, bai ?ara kallon inda take ba ya fice ya nufi sashin Abee.

Sai da ta daWe a zaune a wurin sannan ta iya tashi ta nufi wajen sif ta buWe, kaya ne a ciki masu tarin yawa kuma duk Winsu sabbi ne ba wanda yake nuna alamar an saka shi, bayan ta gama ?are musu kallo ta ri?e haSa ta na cewa "Oo!! ikon Allah a ce cikin kayan mutum kwata-kwata ba tsoho? ko dai ya kai wanki ne??"
Kasancewar ita kaWai ce a Wakin babu me bata amsa ya sa ta rufe bakinta ta ci gaba da burkita kayan don ganin wadda ta yi mata, sai da ta gama ruwan ido sannan ta Wauko wata doguwar Jallabiya Maroon ita Win ma ta yi mata yawa daga faWin har tsayin, amma da yake abin aro ne haka nan ta sanya sannan ta Wauki lafkeken hijab Winta ta saka ta koma ta zauna jiran shigowarsa.

"Abee ka san dai ina da hankali kuma na san ciwon kaina, to don me zan yi abinda ba shi ne daidai ba?, kawai don ba sa son farin cikina ne shi yasa suke cewa haka, ni da Asma'u duk mu na son mu rayu tare, na san kai ma ba za ka so a rabamu ba."
Abee ya jinjina kai kafin ya ce "Wannan Gaskiya ne, shi yasa dama sam ban goyi bayan kowa ba don na san mafi yawancin abinda za ka yi me kyau ne." numfasawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa ''Yarda da kai da na yi shi yasa nake maka wannan shaidar kuma na Amince da abinda ka yi, ba na so ka ban kunya ka ji Dattijo?" ya ?arasa maganar cikin Sigar lallami, gyaWa kai ya yi sannan ya ce "In sha Allah Daddy."
"Ita Matar Aure ba wai abar muzgunawa ba ce ta na da daraja da kima, sannan a ri?e amana kar wani abu ya sa a ci amanarta da iyayenta, sannan a mayar da kai wajen sauke ha??inta da kuma kare shi, Allah ya yi muku Albarka." nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke tare da amsawa da ''Amin, bari ta zo ta gaisheka Abee" ya faWa tare da mi?ewa tsaye.
Zara ta ce "In zo in raka ka??" juyowa ya yi ya maka mata wani banzan kallo, ta yi saurin sunkuyar da kai gami da haWe bakinta, ya yi ?ar ?wafa bai ce komai ba ya fice.

Shiru ne ya ratsa na wani lokaci kafin Abee ya katse shirun ya na murmushi ya ce "Allah Sarki Dattijona; Zahra'u labarin me muke yi ma kafin ya shigo??" ta ce "Labarin rashin lafiyata, Wallahi Abee idan mutum ba shi da lafiya sai ya ji ?unci ka ga ko fita ba na iya yi sai dai in ga kowa ya na ta yawonsa ba me kulawa da ni, don ma yanzu ka dawo."
"To ai jikin naki ya yi sau?i sosai ko?, to ai Zahra'u ciwo ba shi da daWi ko kaWan, kin ga ni shekaruna goma sha ina zaune ba na iya tafiya ba na iya tashi komai sai an yi min, don ma Allah ya azurta ni da zuri'a, kuma hakan ya na daga cikin baiwarsa, babu wanda rayuwarsa ba ta tafiya tare da jarrabawa kuma kowa da irin ta shi, sannan a rayuwa abubuwa da yawa suna da silar faruwarsu."
gyara zama Zara ta yi cike da al'ajabi ta ce "Wai da gaske Abee da ka na tafiya?" tambayar tata sai da ta sa shi dariya, ba tare da ya dena dariyar ba ya ce "Da garau nake tamkar ke, kamar yadda na gaya miki komai ya na da sila to nima hakan ce ta faru da ni."
"To Abee meye silar?" kafin ya yi magana Akhiee ya yi sallama hannunsa Wauke da Husnee wadda ya rungumeta a ?irjinsa tamkar ?ar jaririya sai da ya zo gabansu sannan ya direta ya na cewa "Abee gata nan." Abee dai lamarin na Akhiee ya sa shi kasa cewa komai, Zara ce ta yi ?o?arin cewa "Ciwo ta ji a ?afarta ne Akhiee?" idanunsa a ?asa ya ce "Wai tsoron duhu take ji, kuma ba ta san kan gidan ba shi ne kawai na Wakkota."
Abee ya murmusa ba tare da ya ce uffan ba, zuwa yanzu ya gama gazgatawa kansa ba ?aramin so Akhiee yake yiwa yarinyar nan ba, indai kuwa haka ne ta cancanci shi ma ya so ta domin alamu sun nuna itace silar farin ciki da kuma sauyawar rayuwar Wan nasa."

(Ma su karatu ba ku ce min ina Husnee ba?"

Ai ya na direta ta zagaya bayansa ta Suya sabida wata muguwar kunya da ta lulluSeta, ji take tamkar ?asa ta buWe ta shige ciki, da ta rasa abin yi kawai sai ta fashe da wani Wan marayan kuka.
Zahra dai dariya take yi musu, Akhiee kuwa ba tare da damuwa ba ya zame ya koma kusa da Akhiee ya yi zamansa, cusa fuskarta ta yi a cikin hijab Winta ta na ?ara sakin wani sabon kukan.
Zahra ta na dariya ta ce "Kai Anti Husnee sai ka ce ?aramar yarinya?, Abee ne fa" Akhiee ya ce "?yaleta in ta gaji da tsayuwa sai ta zauna ko?"
Abee ya ce "A'a ba za a yi haka ba, zo nan ?ata, ki rabu da waWannan zolayarki suke yi."
Kasa motsawa ta yi don har ga Allah ji take tamkar za ta nutse, Abee ya ?ara da cewa "Zo ki zauna kusa da ni; ke ma yanzu ?ata ce ai, tamkar Muhammad haka kike a wajena, kin ga shi tamkar aboki haka ya Waukeni."
Har yanzu ba ta da niyar gusawa daga ina take tsaye, a ?ufule Akhiee ya ce "Wai ba kya ji Abee na magana ne? ko so kike sai na ?araso da ke da kaina??" ta san zai aikata fin haka ya ?ara mata wani abin kunyar don haka ta salallaSa can bayan Zara ta lafe, shiru ne ya ratsa wajen na Wan lokaci kafin Abee da yake ta murmushin farin ciki ya katse shirun da cewa "To Barka da da Dare ?ata tinda kin kasa magana."
Sai a lokacin ta tuna abinda ya kamata ta yi wato gaisuwa kuma ta kasa, murya can ?asa ta ce "Ina wuni" cikin jin kunya.

Ya na fara'a ya amsa da ''Lafiya Lau, ya rayuwa?" ba ta ce komai ba hakan ya bawa Zara damar cewa "Ki fito sarari mana ya kamata Abee ya ga fuskarki kar ya kasa ganeki gobe, kin san idon manya kaWan-kaWan suke gani." ta ?arasa maganar cikin sigar zolaya, Abee ya yi dariya gami da cewa "Na fi ki lafiyar ido Zahra'u." "To ai Abee naka idanun sun manyanta sosai, dole nawa za su fi kyau.
"Na tsofi kuma ai ya fi ?arko" Abee ya bata amsa. kafin ta ce wani abu Akhiee ya shiga zancen da cewa "Wai ke kin Wauka Abee Kakanki ne da kike zolayarsa?, Abee ka dena biye mata don Allah."
Abee ya rausayar da kai gami da cewa "To!! Dattijo su waye Abokan nawa in ba ku ba?, to a bar zancen dai, Yanzu na dawo kan ?ata." Wan tsahirtawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Asma'ul- Husna! ga amana nan ta ?ana Muhammad Rislan, shi maraya ne ya rasa Mahaifiyarsa tin bai wuci shekaru goma sha Waya ko shabiyu a Duniya ba, tin daga lokacin kuma rayuwarsa ta sauya, farin ciki ya ?aurace masa, ni kuma ina matu?ar sonsa ina son ganin farin cikinsa; za ki same shi a wani irin bauWaWWen Mutum, hakan ya na da nasaba da irin tashin hankalin da ya tsinkaya a rayuwarsa a daidai lokacin da shekarunsa ba su kai ya ga wannan tashin hankali ba, hakan ya bada gudun mawa wajen canjawarsa sosai, ni kaina na sani rayuwa da shi sai da ha?uri sai an jure, a dinga ha?uri da juna a dinga kawaici da juriya, a dinga tausasa zuciya sannan a kyautatawa juna." Wan jim!! ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Jikina ya bani cewar ke ce silar canjawar rayuwarsa, ya na bu?atar temakonki

23 / 25