Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   21 / 25

60K to 63K   out of 73.5K words

ya kaste shirun da cewa "Ki na da babban matsayi a wajena, kar ki cutar da kanki ta hanyar bin son Zuciyata, ki nutsu ki yiwa kanki zaSi duk hukuncin da kika yanke na amince; Asma'u! ba wani abu da zai sa na sake ki sai dai in kece kika furta cewar ba kya sona ko kuma ba kya so ki rayu tare da ni, indai kin furta hakan a take nima zan sakeki, saSanin haka kuma ba zan iya rabuwa da ke ba, indai kina son farantawa iyayenki ta hanyar rabuwa da ni kina da dama; Ki yi bacci sosai Sai mun haWu a Kotu gobe."
Daga haka ya katse ba tare da ya bata damar ta yi magana ba, bin wayar ta yi da kallo kalamansa na dawo mata, nan take su ka shiga yi mata juyi a ?wa?walwa, menene mafita? ta bi iyayenta ta rabu da shi? ko kuwa ta zaSeshi a matsayin abokin rayuwarta??, shawarwarin da take nema kenan sai dai ba ta da me bata.
Cikin wannan yanayin bacci me nauyi ya yi awon gaba da ita.

Washegari jirgin su Abhie da Jaafar ya sauka kuma yau ne ranar komawa Kotu.
Tinda ya iso ya fara tambayar Akhiee, su Yasayyadi Usman masu jiran kaWan suka fara rattaba masa abinda ke faruwa, ga mamakinsu sai su ka ga sam abin bai Sata masa rai ba sai ma albarka da yake sawa Auren jin haka ya sa suka ja bakinsu su ka tsuke.


Kamar dai ranar nan kowane Sangare sun halarci Zaman, kowa da nashi Burin a Zuci, duk da sun yi tarayya ta wajen son raba Auren sai dai daga cikin Dangin Akhiee akwai masu son ganin wani mummunan abun ya faru da shi bayan haka.

Abinda ya matu?ar Waure musu kai, bayan gabatar da ?an Hujjoji da ?an ?alabusai d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aga bakin Lauyan da ke Kare masu ?ara kai tsaye Mai Shari'a ya ce "Bincike ya tabbatar da cewar Wannan Aure ya ?auru, yanzu Husna Matar Muhammad ce shi yake da hurumin sakinta, har sai ya Amince sannan Saki ya yuwu."
Turusss! suka yi kowa ya kasa wani kyakkyawan motsi, duk a tunaninsu Kotu za ta raba auren ta ?arfin tsiya.
Ko da aka tambayi Akhiee buWar bakinsa ya ce "Ni a karan-kaina ba zan iya rabuwa da Matata ba, amma indai ta ce in saketa zan saketa." daga haka ya ja bakinsa ya tsuke.
Asma'u kuwa ya jefata a wahala, ta shiga tsitstsilla ido ta na kallonsa ta na kallon Mommy da Daddy har ma da su Muneeb da suke ta yi mata muzurai, wasu zafafan hawaye ne suka shiga tsere akan fuskarta, ta zubawa Akhiee ido tamkar ba za ta ?ara ganinsa a Dunyar ba.............




*??INDO*
[9/7, 8:15 PM] INDO: *>ػ?S-K>ػ?*
Ep 23



Ta daWe ta na kallonsa shi kuwa ya ?i bata damar su haWa ido sai ya yi tamkar bai ganta ba, rintse ido ta yi da ?arfi kafin ta fara magana cikin rawar murya "Ina son shi! da shi nake so na rayu har lokacin mutuwata, sai da na riga na zaSeshi a matsayin abokin rayuwata kafin ya Aureni, don Allah kar ku rabamu.
Mai Shari'a ya numfasa ya gyara gilashin dake kan idanunsa sannan ya ce "A barwa me Mata Matarsa itama yarinya a Bar mata Mijinta, Kotu ta Amince da Auren Husna da Muhammad, a bisa sharaWi na ci da sha tufatarwa da sauke ha??in iyali duk ya rataya a wuyansa, Kotu ba ta Amince wani daga Sangaren Miji ko Sangaren Mata ya tayar da wata hatsaniya akan Hukuncin da ta yanke ba.
Daga haka ya bubbuga ?ar gudumarsa Kotu ta tashi.

Cikin ?asaitaccen takunsa ya fito daga inda yake tsaye, kai tsaye wurinta ya nufa ya kama hannunta ba tare da ya bi takan kowa ba ya nufi hanyar fita daga Kotun, ita dai ta bishi da ido sai Sazga kuka take yi.
Suna fita suka yi karo da cincirindon jama'a har da ?an Jarida, an zo kallo da samun labarai masu waya na Wauka su ma ?an Jarida su na Wauka.
Wani daga cikin ?an Jaridar ne ya bugi ?irji ya matsa kusa da Akhiee ya na cewa "Ranka-yadaWe Minti Waya don Allah ka amsa mana tambayoyinmu."
Tamkar da dutse yake magana haka Akhiee ya yi masa banza, sai ma wucewa da yayi wajen wata lintsumemiyar Mota me Numfashi, da ka ganta ka san ta manya ce ba ?ananu ba, nan ma mutane su ka bisu riiiiii don kar a yi ba su.
Cikin rawar murya gami da fargaba ta ce "Ina za mu je Akhiee!??"
HaWata ya yi da jikin Motar ya yi mata rumfa ya na zuba mata idanunsa da ke ta she?i da walwali, cikin wata sirrintacciyar murya ya ce "Yau tare da ni za ki kwana, ba zan bari ki ?ara nesanta da ni ba". da Sauri ta Wago idanunta da su ka kukkumbura sabida kuka ta jefasu cikin nasa tare da cewa "Akhie...." saurin rufe bakinta ta yi ganin ya rintse idanunsa gami da kamo gefen leSensa ya cije shi da ?arfin gaske, "Tell me!" ya faWa a ta?aice bayan shuWewar ?an sakanni, ?asa ta yi da kai kafin ta ce "Ban yi sallama da iyayena da ?an uwana ba, na san su na fushi da ni, ina bu?atar na nemi yafiyarsu, kuma su ya kamata su rakani Wakina!!" ta ?arasa maganar gami da sauke wata zazzafar ajiyar Zuciya.
a hankali ya buWe idanun nasa ya zuba mata sannan ya ce "Yanzu ni kike bu?ata ba su."
sharr!! hawaye su ka ci gaba da zubowa kamar dama jira suke ya yi magana, ta buWe baki za ta yi magana ya dakatar da ita ta hanyar yi mata alama da idanunsa wanda zuwa yanzu ta fara karantar Yarensu.
Janyeta ya yi gefe sannan ya buWe Motar, cikin sassanyar muryarsa ya ce "Look! she's my small Mommy."
Sai da ta goge ?walla sannan ta iya zazzaro ido ta na kallon cikin Motar, wata haWaWWiyar Mata ce Babbar Mace wadda hutu da jin daWi suka zauna, sanye take cikin dakakken Leshi Ba?i wulik an yi masa adon Orange me duhu, ya sha Beads work ta ko'ina, Mayafinta ma Orange ne an yi masa adon Beads work ba?i, komai ya ji banda tsiya in ji maro?a.
Sassanyan murmushi ta sakar musu kafin ta ce "Come hare my daughter!" a tsorace Husnee ta yi baya ta na kallon Akhiee gami da cewa "Wacece??" "Mamata ce, kema Mamarki ce kuma ita za ta yi miki duk abinda Uwa take yiwa ?arta, a tare da ita kuma akwai ?an Uwana, tare za ku tafi, ni zan tawo daga baya."
Rushewa ta yi da kuka kamar an ce gobe za ta mutu, cikin shashsheka ta ce "Ni dai tsoro nake ji ka shiga mu tafi tare."
girgiza kai ya yi kafin ya ce "Ni wanene to Amsa'u?, ki na tare da kariyar Allah ba kya bu?atar kariyata, nima shi ne yake kareni."
Matar cikin Motar ce ta ce "Mutane dai su na kallonku ?ata, ki bari idan kun haWu a ?akinku sai ku tattauna."
Sai a lokacin ta tuna fa ashe da dubban idanu a kansu, shiga Motar ta yi ta zauna sannan ta ce "Akhiee don Alla....." zuba nata idananun da ya yi ne ya sa ta fasa maganar, bai ce komai ba ya rufe Motar gami da juyawa.
Ya na jin Mutane su na bidiyo su na bada labarin wannan shine ?an Daba mafi haWari a ?asar Nigeria kuma yau ne Kotu ta mallaka masa Matar da ya aura ba bisa ?a'ida ba, bai bi takan kowa ba ya ?arasa inda su Salansa ke tsaye tare da Prince, su ma bai ce musu komai ba ya ya ci gaba da tafiya.

Motoci uku ne su ka yi Parking a ?ofar gidan su Akhiee. Jin an dena tafiya ya sa Husnee ta ?ara sakin wani sabon kuka don yanzu ta tabbatar an zo inda za a watsar da ita.
Inna ce ta kalleta cikin nutsuwa ta ce "Ki dena kuka ki yi ha?uri, kowace Wiya mace ta gaji haka, dole ne wata rana sai ta rabu da iyayenta ta tafi gidan Miji; ki Wauka nan ma gidanku ne, kuma ina da ya?ini akan ?an Manya zai ri?e ki da daraja kuma zai kare ha??inki, Allah ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya."
Ba ta iya cewa komai ba sai dai ta sassauta kukan. Mukhtar ya ce "Yanzu shiga ciki za ku yi ko sai kun jira an zo an shigar da ku?"
kafin Inna ta yi magana Rahma ta buWe Murfin Motar ta na cewa "Mama ku fito mu shiga mana."
Maman ta ce "Okay mu je Win, kama hannunta."
Rahma ta murmusa gami da cewa "Allah Sarki yarinya mu ma haka aka yi mana muna ta kuka aka kaimu aka baro."
Husnee kuwa ta na jin haka ta ?are Sare baki, Inna ta ce "Ke Rahma kul! ki na tsorata yarinya a memakon ki rarrasheta?"
Dariya kawai ta yi ba tare da ta ce ?ala ba.
Sai da Inna ta yi rarrashi sosai sannan Husnee ta fito daga cikin Motar suka rankaya zuwa cikin gida tare da su Zabira da su Surayya.

Sun yi sallama a tsakar gidan ta fi sau goma amma an yi musu banza, Su Innajo da su Umma Uwani su Inna Huwaila su na zaune a can gefe sai kallonsu suke yi sama da ?asa suna tsegumi.

Zahra da ke kwance a Wakinsu ba lafiya ta lallaSo ta fito ta na amsa sallamar. Umma Uwani ta ce "Ke ubanki! me za ki je ki yi musu?? kin san irinsu??" kamar za ta yi kuka ta ce "Amma ko ban san irinsu ba ai mu Musulmi ne ya kamata a amsa musu sallama, bare kuma na san ba wani mugun abun ne ya kawosu ba, Husnee ce dai ba kwa so kuma Allah ya yarda ta zama ?ar gida sai dai ayi ha?uri." Inna Huwaila Matar Baba Sa'idu ta shiga tafa hannuwa ta na cewa ''La ilaha illallahu waWannan ?a?a ba kunya, ku ji itama ta kangare yarinyar nan??" ta faWa ta na kallon Innajo gami da ri?e haSarta alamar mamaki, Innajo ta taSe baki kafin ta ce "Shegiya me kama da tsintacciyar Mage, ai mun yi mata komai dole ta yi mana rashin kunya akan wannan Wan Kukar."

Ba ta sauraresu ba ta wuce inda su Inna suke ta na fara'a ta ?arfin hali, "Sannunku da zuwa, ku shigo in raka ku ?akin Akhiee inaga anan ne za ta sauka."
Inna da Aunty Rahma suka amsa sannan sannan su ka rufa mata baya.


Bayan sun huta a ?akin ne Laita ta ja dogon tsaki ta ce "Wallahi Allah na kusa hudawa Mace tumbi a gidan nan, in banda rainin hankali suna kallonmu amma sai kace mun zo musu da ajalinsu?" Zara ta ce "Allah ya baku ha?uri, halin gidan yawa ne sai Addu'a" Inna ta ce "Haka ne ?ar nan, kar ki damu mu ba mu yi fushi ba, kema FaWimatu ki bar zancen kar na ?ara ji" ta ?arasa maganar ta na kallon inda Laita take tsaye tamkar shuka.

Nasihohi sosai su Inna da su Aunty Rahma su ka yi wa Husnee sannan su ka yi mata sallama suka tafi.
?akin ya rage daga ita sai Zara sun yi jungum-jungum ba me tashin wani a tsakaninsu.
Tare suka zauna har dare ya yi sannan Zara ta yi mata sallama ta koma sashinsu.
zuwa yanzu ta ci kukan har ya yi mata karo ba za ta iya yinsa a yanzu ba, don haka ta yi shiru ta na sauraren ?arar kaWawar ganyen bishiyun da ke bayan Wakin wanda iska take kaWa su, tunane-tunane kala-kala suka sakota gaba, Jefi-jefi takan sauke ajiyar Zuciya don har yanzu ba ta gama dawowa daidai ba.

Cikin tsananin Sacin rai Muneeb ya ce "Ai in ya san wata bai san wata ba, wallahi sai mun Waukaka Shari'ar nan in ya so a dinga yinta har Duniya ta tashi, shima Wan iskan Al?alin ai siye shi suka yi shi yasa ko bin Shari'ar akan ?a'ida bai yi ba, ba wani bincike da ya yi tinda kawai ya yiwa mutane ?ar burum-burum ne."
Muneer ya ce "Ni babban ba?in cikina ma ka ga Yanzu Mommy ba ta da lafiya sabida ba?in cikin wannan abu, ka ga Daddy ma duk ya shiga damuwa, dole ne ma mu san abin yi."
Daddy ya yi gyaran murya kafin ya ce "Ni ba wanda ya ban mamaki irin Husna, ban taSa zaton za ta iya ri?e hannun wani Wa ta tsallake ta barmu ba."
Muneeb ya yi zaram ya ce "Kuma sai gashi ta yi ba?, ai dama wani ba a gane halinsa har sai ya aikata tukunna, in banda iskanci irin nata uban me za ta ci da wannan tantirin?, ba ku ga yadda jama'a suka taru suna Waukar labarai ba? inda za ku san ba ?aramin Wan iska ba ne, wai ni abinda yake ban mamaki ma duk hannun hukumar da ya shiga sala-sa'ilin saSalula haka za ku ga sun sake shi ba tare da an Wauki mataki akansa ba, yanzu ka ga Shari'ar nan ai duk me hankali in ya duba ya san ba Shari'a aka yi ba kawai an ?ara tabbatar da Aure ne."
Ahmad da ya zuba tagumi sai yanzu ya yi magana kamar zai yi kuka "To wai duk meye amfanin maimaita zancen? ta riga ta faru ta ?are an yiwa me dami Waya sata, tinda har Allah ya sa kun gane cewa hukuma ba ta iya aiki akansa meye naku na wahalar da kanku? kun san ko kun Waukaka ?ara sai dai ku ?ara tozartamu a banza."
a fusace Muneeb yace "Yi mana shiru dan ubanka, kai ai mahaukacu ne ba ka san ciwon kanka."

Muddassir ne ya kalleshi cikin Sacin rai ya ce "To kai da ka san ciwon kan naka kar na ?ara ji ka Waga maganar in ba haka ba ranka zai Saci, haba!! Yarinya ta na da ?ancin da za ta zaSi wanda take so kuma ta rayu da shi, ina ruwanku da halayensa? ko ku za ku zauna mata da shi?"
Muneeb ya buntsire baki kafin ya ce "Amma ai ana duba kyakkyawan iri kafin a haWa ala?a, yanzu ina daWi a ce ?anwarka ce take auren wannan ta?adari....." katse shi ya yi da cewa "To sai ka yi duk abinda za ka iya, Daddy na ro?eka don Allah kai kuma ka ce ba ruwanka, ka ma dena sa damuwa a ranka kar kaima ka kama rashin lafiya, ita ma Mommy na Wan lokaci ne za ta mi?e."
Daddy ya rausayar da kai gami da cewa "Toh!! Muddassir idan ban kwantar da hankalina ba ya zan yi?, ai ba kowane ya jawo min ba face ?ar cikina, na barta ta je ta yi rayuwarta Allah ya sa albarka, amma abu Waya nake so ku ri?e shine ba ruwana da ita ta yi rayuwarta in yi tawa, sannan ku ma ban yarda wani ya ?ara zumunci da ita ba, tinda ga wanda ta zaSa ai sai mu barta da shi, kar ku ?ara Waga zancen tinda an riga an fi ?arfinmu."
Muneer zai yi magana Muddassir ya hana shi, sai ma ya bisu da wasu ?an nasihohi kamar gaske.


Wayarsa da take ruri ya Wauka gami da karawa a kunne ba tare da ya yi magana ba.
a Waya Sangaren me kiran ya ce "Sunana Abdulkadir Yahya Sumaila, ina fatan komai lafiya?"
Da sauri Akhiee ya ce "Respect ya Mai Shari'a, na gode da temakonka."
Mai Shari'a ya murmusa kafin ya ce "Ai ka wuce hakan a wurina, ai da ka sanar da ni abinda yake faruwa tin kafin ayi zaman farko da ba za a yi zama na biyun ba, sai da Abokina CP Abubakar Ado Gezawa ya sanar da ni komai sannan na gane."
"Yanayi ne ya zo da haka YallaSai!!, amma tinda komai ya yi daidai ina godiya."
Mai Shari'a ya ce "Ina yi maka fatan Alkairi tare da fatan Allah ya ida nufinka."
''Na gode" kawai ya ce ya katse kiran.

Yasayyadi Usman, Babban Yaya, Yasayyadi Jameel, Habu, Jaafar, Habibu, da sauransu zaune suke sun yi rukuni suna taWi akan abinda ya faru a Kotu, Habibu ya ce "Ai na san dama haka za ta faru wallahi, ai wannan Yaro ya buwayi Duniya ya fi ?arfin kowa." Yasayyadi Usman ya ce "Ai kuwa in ya san wata bai san wata ba, ai ta yaro kyau take ba ta ?arko, in ya saye Al?ali ai mu ba za mu sayu ba, abinda nake so mu yi yanzu shine mu kama ?afa da Baba Sa'idu mu samu mu zizziga Abhie ya ce bai yarda da Auren ba."
Babban Yaya ya ce "Ni fa har yanzu na kasa yarda ?an gidan nan ne Yaron nan, burina kullum bai wuce na ji ranar da Abhie zai buWi baki ya ce ba Wansa ba

21 / 25