Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 25

15K to 18K   out of 73.5K words

kake yi mini, yanzu na Wau haske na fahimci komai, ai bakinku Waya da kai da makasan dama, to wallahi da kaina zan Wauki mataki, yanzu ba na bu?atar temakonka, don me za ka ce ba ka da hujja bayan ka san wanda ya aikata har ka kama shi sabida bakinku Waya sai ka sake shi, shine fa ya ba?unci mijina a ranar da aka kashe shi, to in ba shi ba waye zai yi kisan?"
IP Khalil zai yi magana ta katse shi da cewa "Kar ka gaya mini komai!! ba na son ji, na ha?ura da temakonka ka je ka yi Allah na nan kuma kuWin da na biyaka Allah ya isa, ni zan bi ta wata hanyar in Wauki fansar mijina, wallahi tallahi sai na jefa wannan yaro cikin bala'in da sai ya kashe kansa, kai kuma ta Allah ba taka ba munafukin banza" ta na kaiwa nan ta katse wayar ta na huci.

IP Khalil ji yake tamkar ya yi ta bin layika da kwararo ya na zunduma ihu ko zuciyarsa za ta yi sanyi, nan take wani mugun zazzaSi da ciwon kai na wahala da tarin tunane-tunane su ka lulluSe shi.

Huci Hajiya Laure ke yi kamar bujimin sa ya ga wu?ar yanka shi, Yazeed da ke zaune gefenta ya ce "Shima munafuki ne Wan sandan nan ko??"
"Yo eh mana, in ba haka ba ta ya za ka kama mutum ka sake shi bayan ka san shi ya aikata, wallahi zan Wauki mataki akansa nan ba da daWewa ba, je ka fito mini da mota fita zan yi."
Yazeed ya mi?e ya na cewa "Amma da kin bari kin gama takaba sai ki yi ko me za ki yi."
"Ubanka!! na ce ubanka kai da takabar! kamata ta yi ace ka fi ni damuwa da mutuwar ta shi amma sabida kai butulu ne duk wannan so da ?aunar da yake nuna maka sai ka ce in bari in gama takaba? to kai da takabar na ci buhun ubanku, ?an butar duma kai?"
"Allah i bada ha?uri" ya faWa cikin sanyi sannan ya fita domin gyara motar da za ta fitan.






SHARE FISABILILLAH



Na KuWi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ?arin bayani =?I?


*??INDO*
[8/14, 8:18 PM] INDO: *>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 9

??
Ayeesha Abdulkareem INDO


*M.W.A>؅?*



"Asma'u!!!!!!" kira ya ?walla mata da ?arfi cikin tsananin kaWuwa da tashin hankali, cikin zafin nama ya finciko hannunta da mugun ?arfi hakan ya sa ta dawo kansa, garin daidaita tsayuwarsa ya taka Sawon ayabar da ta jefo masa santsi ya ja shi, gabaki Waya su ka yi wata muguwar sufa su ka rikito daga saman benen su ka nufi ?asa, rimmm!!!!! sai gasu a tsakiyar harabar makaranta.

Ihu ?an matan da ke kaikawo a wurin su ka sanya gami da tarwatsewa kowacce ta na neman wurin Suya.
Hankali tashe Akhiee ya ture Husnee da ke kwance akan ?irjinsa ya mi?e ya na zuba mata idanu don sanin halin da take ciki, hankalinsa ne ya ?ara dungunzuma ganinta a sume ta wani irin Washe ta ?ara haske kamar ba jini a jikinta, da sauri ya sanya hannunsa cikin tafin hannunta ya dam?e jikinsa na wata irin tsuma sabida tsananin Sacin rai.

"Me ka yi mata??" muryar Yasayyadi Jameel ce ta dawo da shi cikin makarantar saSanin da da duk hankalinsa ya yi nisa, sai a lokacin ya lura da mutane sun yi da'ira akansu kowa ya zubawa sarautar Allah ido.

a fusace Yasayyadi Usman ya ?araso wajen ya ri?o Wayan hannun Akhiee ya finciko shi, ba tare da nazari ba ya afka masa wani lafiyayyen mari, "Uban me ka yi mata?? ba tambayarka ake yi ba?? me yasa ba ka jin magana kai?"
Wago hannu ya yi zai ?ara tsinka masa wani marin Akhiee ya fizge hannunsa ya doki ?irjin Yasayyadi Usman da ?arfi sai da ya yi taga-taga zai faWi su Yasayyadi Jameel su ka daddafe shi.

Idanunsa da suka canja kamanni ya zubawa sauran Walibai ?an kallo kafin ya ce "Kowa ya Sace daga nan ko na illata masa rayuwa wallahi; kai kuma kar ka ?ara gigin marina in ba haka ba zan tarwatsa maka farin cikinka, idan ta tashi sai ku tambayeta idan akwai tsiyar da na yi mata."
Ya na gama faWen haka ya koma inda Husnee ke kwance ba alamun numfashi a tare da ita.
?an makaranta kuwa tuni sun fice da gudun ceton rai, sai WaiWai da ba su ?arasa fita ba. rungumarta ya yi a ?irjinsa ya nufi cikin ajinsu ba tare da ya bi takan kowa ba, ajiyeta kawai ya yi ya fito ya sa kai ko kallon su Sheikh Auwal bai yi ba ya fice daga makarantar, tafiyar kawai yake yi amma bai san inda ma zai dosa ba don kuwa ransa ya gama kaiwa ?ololuwar Saci, bai san inda zai nufa ya ji daWi ba.

Su dai sun tsaya curko-curko kamar dangin Kaji an rasa me yin ko ?wa??warar magana.

"Za ka ci Ayaba?" ta faWa gami da mi?a masa ragowar wadda take ci. girgiza kai ya yi alamar a'a, ta ci gaba da cin kayarta hankali kwance, jin bai ce ?ala ba ya sa ta cewa "Akhiee! yau ba za ka yi mini magana ba ne? ni fa so nake in ga dariyarka, kullum sai dai ka dinga haWe rai kamar hadarin gabas"
Kyawawan idanunsa ya zuba mata cikin lallami ya ce "Ni fa ki ?yale a yadda nake don ni ba na dariya." da sauri ta ce "To sabida me?" shiru ya yi kamar ba zai bata amsa ba sai kuma ya ce "Ta na karya min tambaya ne" "Iyye?!!" ta faWa gami da sakin baki, "Ni fa ba na gane wannan yaren naka, ka faWa min da hausa" ''Ai ba za ki gane ba sai dai ki wahalar da ni." turo baki ta yi cike da shagwaSa ta ce "Don Allah ka yi dariya ko da sau Waya ne na san za ka yi kyau" banza ya yi mata kamar ba da shi take ba, jifansa ta yi da Sawon ayabar da ta cinye gami da cewa "Sai ka ri?e abarka ba a so ma, kuma na yi fushi ba zan ?ara kula ka ba" daga haka ta juya fayau-fayau da nufin barin gurin cak!!!!!! ta tsaya sabida muryarsa da ta karaWe kunnuwanta.

sun daWe a tsaitsaye jiki duk a sanyaye kafin Yasayyadi Jameel ya ce "Mu dai mu na ganin takanmu a rayuwa, wannan yaro ko annoba?"
a sirrince Sheikh Auwal ya goge zazzafar ?wallar da ta fara gangarowa daga cikin idanunsa, cikin dakiya da mazantaka ya ce "Kar ku damu in Allah ya yarda ba abinda zai faru, ku ci gaba da Addu'a watarana sai labari."
Yasayyadi Usman dafe da ?irjinsa da yake jin kamar maWaukansa (?ashushuwan ha?ar?arinsa) sun kakkarye cike da tsanar Akhiee ya ce "A tunaninku wannan shaiWanin zai shiryu ne?? ai kuma ya yi nisa ba zai taSa jin kira ba, Wai har Abhi ya ce wani kar a ?ara zuwa ana zancensa, ai abin faWen yake yi ba dole a faWa ba?"
Malam Zayd ma ya taya Yasayyadi Usman su ka ci gaba da yi, takaici da tashin hankali sun hana Sheikh Auwal yin magana, gashi ya na son shiga ya ga halin da Husnee ta ke ciki sai dai ya na tsoron abinda zai tarar.

Amadu direban gidan su Husnee ya shigo ya na ?walla sallama, Sheikh Auwal ne ya amsa ya na ?o?arin daidaita nutsuwarsa ya nufi hanyar ?ofa don ganawa da Amadu.
Musabaha su ka yi kana Amadu ya ce "Malam na ga kowane Walibi ya fita ne to banga Husnee ba shine na ?araso in tambaya ko ta yi laifi ne an tsareta?"
jim!! Sheikh Auwal ya yi kafin ya ce "Ba laifi ta yi ba kasan yau da gobe sai Allah, larura ce ta sameta."
Hankali tashe Amadu ya ce "To fa ikon me sama, me ke faruwa Malam?" "Ai ba wani abin tayar da hankali bane da sau?i in sha Allah.
Amadu ya ce "To to to, ai ba komai Allah i bata lafiya, za ta iya fitowa mu koma gida ko?"

a hankali ta buWe idanunta da su ka yi wani nauyi jingim kamar an Wora musu dala da gwauron dutse, tunanin abinda ya faru ne ya fara dawowa mata, ba za ta iya cewa ga abinda aka yi ba don kuwa tin wannan kira da Akhiee ya ?walla mata ba ta ?ara sanin abinda ke faruwa ba.

Yun?urawa ta yi ta tashi da ?yar jikinta duk ya hau ciwo kamar wadda aka yiwa duka da sanda.
Cikin rashin ?warin jiki take takawa har ta fito harabar makaranta inda malamai suke tsaye duk sun rasa abin yi, ganin ta fito ya sa duk suka tsaya kallonta, Yasayyadi Usman sam bai so farkawarta ba,, ya so rigimar ta ?ara girma ta yadda zai huce takaicin ciwon ?irjin da Akhiee ya sa shi.

Farin ciki ne ya lulluSe Sheikh Auwal a ransa ya godewa Allah a zahiri kuwa ya cewa Amadu "To ga ta nan ma" Amadu ya washe baki gami da cewa "Ma sha Allahu ai da sau?i sosai."

Husnee dai da ta duba gabas da yamma ta ga saura ita kaWai a cikin Walibai sai ta fashe da kuka, hakan ya ?ara sanya zargi a zukatan su Yasayyadi Usman.
Malam Zaidu ya ce "Ke Husna me Akhiee ya yi miki?" girgiza kai ta yi alamar ba komai don kuwa ba za ta iya magana ba, Amadu ne ya ?araso wajen ya na cewa "Sannu Husna! Sannu Innata! Allah i sauwa?e, mu tafi gida sai a je asibiti ko?" ba ta kula shi ba ta fice shima ya bi bayanta da sauri, gidan baya ya buWe mata ta na shiga ta kwanta ta ci gaba da rera kuka.

Cikin sanyin jiki Amadu ya ce "Ki yi ha?uri Innata, kanki ke ciwo ne? kar dai wannan Wan daban ne fa ya yi miki wani abun don na lura kamar malaman nan ba wata gaskiya garesu ba."
Jin surutun da yake ya sa ta danne kukan nata cikin muryarta da ta yi sanyi kamar yadda jikinta ya yi ta ce "Ba na so ka faWa a gida cewar wani abu ya sameni, nima kaina ban san abinda ya faru ba kawai dai na fahimci cewar na suma ne, kuma ?ila ma Aljanu ne, ni yanzu ba abinda yake damuna don Allah kar ka faWa za su hana ni zuwa makarantar ni kuma hankalina ba zai iya Waukar hakan ba" cikin tausayawa ya ce "To shikenan ba zan faWa ba Allah i ?ara lafiya."
Ba ta ce komai ba sai ma ?ara yin lamo da ta yi ta na tunane-tunane.

baya........

Hajiya Laure har su ka isa gidan Aminiyarta Hajiya Saudah masifa take zazzagawa kamar zararriya.

A falo ta samu Hajiya Laure ta hakimce ?ar aikinta na yi mata tausa, jin muryar ?awarta ya sa ta fara fara'a ta na cewa "Hajiya Laure manyan ?asa me ke faruwa ne na ji kina ta ?an surutai tin daga nesa?? wai ma ina takabar taki?"
"Hmm!! abinda ya fi haka ma ai zan yi, bar ni da batun takabar nan a cikinta nake, amma hankalina ba zai taSa kwanciya ba indai wanda ya kashe Alhahi Salisu ya na yawo a gari, abinda ya sa ki ka ganni anan neman shawararki na zo yi don ke ce kaWai za ki share min hawayena."
Hajiya Saudah ta ce "A'ahh ban gane ba ina kamashi da ?an sanda su ka yi?" "Yo ?an sanda ko ?an iska? bayan kawai kuWina Inspector Winnan ya ci ?arshe ma ashe sun sake shi? ai cewa na yi na gaji da shigo-shigo ba zurfi gwara na zuba kuWi a harra?a min shi lokaci Waya."
shu'umin murmushi Hajiya Saudah ta saki kafin ta ce "Ke Baraka bamu wuri."
Mi?ewa ?ar aikin ta yi ta basu wuri, Hajiya Saudah ta numfasa kana ta ce "To yanzu ta wace hanya ki ke ganin za mu bi?" "Ni fa wallahi ta kowace hanya ma zan iya bi, ni fa shawara na zo nema kawai ni ki bani shawara.
"To ai in hagu ta ?i sai a koma dama, in da dama sai a dama, gobe in Allah ya kaimu ki shirya mu je Wan tsibirin boka Barore, in gaya miki ba ya tsoron Allah ko kaWan, kashe mutum a wurinsa ?aramin aiki ne, Wai baki ga yadda na yi damfareriya da ni ba na yi ?iba abina? ai wurinsa na je neman sa'a kuma na samu, wallahi in gaya miki Alhaji Bara'u yanzu ko Wan ciki na sai haka, ita kuwa kishiya tini ma Allah na tuba wa ke zancenta? tuni na sa ya saketa shegiya dangin mayu, yanzu da ga ni sai Alhajina sai ?an ?a?ana kar ki ga yadda yake mini biyayya kamar ba shine me tsaurin ra'ayin nan ba."
Hajiya Laure ta tattaSe baki ta na matse ?walla gami da cew "Allah i ji?an Alhaji Salisu bawan Allah, wallahi ya na yi min iya bakin ?o?arinsa ni tin wancan zuwan da mu ka yi gangare shikenan muke zaman lafiya da shi, amma nima ina mutunta shi kuma ina yi masa biyayya, shine wannan yaron tsinanne ya kashe shi, ba ma dole hankalina ya tashi ba fisabilillahi fa!!"
Hajiya Saudah ta dafa ?afaWarta cikin sigar rarrashi ta ce "Kwantar da hankalinki ?awata, indai Boka Barore ne sai ya kashe miki ko waye ki ke son ya kashe, ke dai ki shirya gobe mu je, sannan ki tanadi kuWi kin san ni ba ni da matsala da Alhaji ko bai sani ba na fita ma ba zai ce komai ba, ai kina ?o?ari ke ni ai na fi so miji ya zama shine zai nemi Aljannah a ?ar?ashin ?afata ba dai ni na nema a ta shi ba, kwantar da hankali bar zubda hawayenki a banza ?awata."
Cike da farin ciki Hajiya Laure ta ce "Na gode sosai Hajiya Saudah, wallahi gobe za ki ji ni da wuri ma kuwa don ba a bori da sanyin jiki."
"Yauwa ai gwara dai" Hajiya Saudah ta faWa sannan su ka ci gaba da hira.

Tankar Ya?i
farar budurwa ce kyakkyawa son kowa ?in wanda ya rasa, ta na da dogon hanci da manyan idanu masu kyawu, da Wan madaidaicin bakinta me Wauke da lips coffee collor me duhu.
Sanye take cikin ?ananun kaya ba?a?e, riga me dogon hannu sai matsatstsen jeans wanda ya kama jikinta sosai, P-cap ce akanta wadda ko gama rufe murtuka murtukan kitson doka da ke kan nata ba ta yi ba, idanunta sun ji kwalli rabajau tamkar da taSarya ta saka, ba ko siririn abu a jikinta da sunan lulluSi bare batun mayafi ko hijab.

Cikin nutsuwa take takawa cike da ta?ama da izza gami da jin kanta, tura ?aramar ?ofar dake ma?ale a jikin ?aton get Win kangon ta yi a sannu ta sanya ?afarta ciki, mabiyanta na shirin bin bayanta ta Waga musu hannu su ka dakata.

Ciki ta ?arasa ta na tafiya Wagwas-Wagwas kamar wadda ake ce ta fito ayi zaSen sarauniyar kyau ta Duniya.

Laita na kwance kan benci ta yi matashin kai da cinyar Zabira hannunta ri?e da taba ta na zu?a cikin salo da ?warewa, ita ma Zabira ta-ta na hannunta ta na ja ta na lumshe ido.

Kamar daga sama su ka ga Tankar Ya?i akansu sai wani binsu take da kallon tara ahu, Cikin hanzari Laita ta tashi daga kwance ta zauna gami da Wora ?afarta Waya bisa Waya ta na zubawa Tankar Ya?i mazajen idanunta.

Zabira ce ta mi?e kai tsaye ta tinkari inda Tankar Ya?i ke tsaye ta karye ?ugu ta cilla ?afa Waya gaba ta coge ta na kallonsu, "Ke kuma Kazar waye? rasa hanyar gidanku ki ka yi ne??" Zabira ta tambayeta gami da tsatstsareta da idanu.

Cikin shan ?amshi da iyayi Tankar Ya?i ta ce ''Babanku nake nema, Kazarsa ce ni!"
Zabira ta juya ta kalli Laita kafin su sa dariya su na binta da kallon sokunta, Laita ta ce "Tambayeta ta rasa tunaninta ne? amma fara tambayarta waye take nufi Babanmu?"
Zabira ta ce "Kin ji abinda ta ce ko??" Tankar Ya?i ta ce "Sammin abar hannunki" ba musu ta mi?a mata tabar, ta karSa ta Woshana a nata bakin ta yi mata wani mugun ja ta busar kana ta shiga takawa Waya bayan Waya, sai da ta yi taku biyar cif sannan ta juyo ta na kallonsu, ba tare da tsoro ko shakka ba ta ce "Ina nufin SAHUN KEKE!!!!"
"Sahun Keke!!!!!" Laita ta maimaita sunan cikin sigar tambaya.




SHARE FISABILILLAH


Na KuWi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ?arin bayani =?I?


*??INDO*
[8/15, 2:32 PM] INDO: *>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 10

??
Ayeesha Abdulkareem INDO


*M.W.A>؅?*




Kafin ta ce "Ke dalla kar ki zo mana da raini mana, shi ai ba irinki bane ya na da kamun kai, ko me zai yi da ke ma ki na famar tafiya a karkace?" Zabira ta ce "Gaggauta fita daga nan kafin mu rabaki wallahi, mara kunyar banza ?aramar ?ar kwalta!" wani shu'umin murmushi Tankar Ya?i ta saki kafin ta ce "Idan ba ku san ni ba shi ya san ni, kuma ba wurinku na zo ba, ku gaya min inda yake tin kafin na shiga nemansa da kaina,

6 / 25