Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   15 / 25

42K to 45K   out of 73.5K words

amsa a gadarance gami da mi?ewa ta bashi wuri, a cewarta ya katse mata magana.

KashingiWa ya yi a kan kujera ya na lumshe ido, sanyin AC na ratsa shi, Kwatsam! tunanin Ma'u ya faWo masa, musamman yanayinta a da ta na da fara'a ga ladabi da biyayya ba ruwanta da shiga shirgin da ba nata ba "To wai meye ya sameta da ta dena walwala?" tambayar da ya yi wa zuciyarsa kenan sai dai ba shi da amsarta, ya daWe ya na tunaninta kafin ya yanke hukuncin zuwa ya tambayeta ko za ta faWa masa damuwarta.
mi?ewa ya yi ya fice daga sashin Mommy ya nufi Wan sashin da aka ware domin ?an aiki.
Da Iya ya fara kaciSuss ta yi saurin buWa masa hanya gami da gaishe shi, bai amsa ba ya ce "Ni fa ba na so ki dinga gaishe ni tsofai-tsofau da ke"
Ta ce "To ?annan ai ni baiwarku ce, Hajiya ta yi mana umarnin mu dinga gaishe da kowa."
?an tsaki ya yi kafin ya ce ''Ni ba na so, yanzu dai ina wannan ba?ar yarinyar Ma'u?"
Iya ta ce ''Aff! Ta na kicin ita da Talatu bari in kira maka ita."
Da sauri ya ce "No ba bu?atar hakan zan je can in sameta."
Iya ta amsa da "To" a ranta ta na mamakin neman nata da yake yi.
Ta na cikin yankan Albasa kamar ance juyo ta na kallon hanyar shigowa idanunta su ka yi katari da shi, Gabanta ya yanke ya faWi har ?asa, da sauri ta sunkuyar da kanta ta na jin wata irin tsanarsa da shi da mahaifiyarsa, shi kuwa kallonta kawai yake yi kamar tsohon maye.
Sai da Talatu ta gaishe shi sannan ya farga ashe ba su kaWai ne a wurin ba.

HaWe fuska ya yi cike da manyance da nuna isa ya ce "Maza ki bar nan" Talatu ta ce "To" jiki na tsuma ta ajiye abinda take yi ta raSa ta kusa da shi ta wuce.

Ma'u kuwa jin abinda ya cewa Talatu ya ?ara firgita ta jikinta ya Wau karkarwa, tunanin abinda Mommynsa ta yi mata ne ya fara dawo mata, musamman irin tashin hankaki da azabar da ta fuskanta a wajen Boka.
Ta lula duniyar tunani hakan ya sa ba ta san ya zo kusa da ita ba sai jin muryarsa ta yi har cikin ?wa?walwarta tamkar an kauWa mata ba?in ?arfe a ka, zaburar da ta yi ta sa wu?ar hannunta ta kufce ta shigi Wan yatsanta, da sauri ta watsar gami da dam?e yatsan ta saki ?ar ?ara.
Zazzaro idanunsa ya yi a kanta yana sa cewa "Lafiya??" ganin ta ri?e Wan yatsa ya sa shi saurin ri?o hannun nata ya na cewa "Mu gani?" ?o?arin fizgewa ta fara yi ta na yi masa magiya akan ya saketa.
kamar zai fashe da kuka ya ce "Sannu! Ki dinga bi a hankali, kin ga kin yanke kanki ko tunanin me kike yi oho." ya na sakar mata hannun ta yi sauri matsawa gefe ta na fashewa da kuka.
Cike da takaicin kukan nata ya ce "Ai ka ji!!!! dama na zo tambayarki akan matsalarki ne amma yanzu kin ?ara ?ir?iro wata matsalar."
Cikin kuka ta ce "Ba abinda yake damuna don Allah ka dena nemana"
"Dole in nemeki mana tinda kin barni cikin tunaninki? ki faWa mini damuwarki ki ka sani ko zan iya yi miki maganinta?"
"Ba abinda yake damuna fa!' ta yi maganar ta na shashshekar kuka,
Wan tsaki ya yi kafin ya ce "Ke na ga abin kukan ma ba ya yi miki kaWan, ranar da ba kya kukan sai ki gaya mini abinda aka yi miki" ya faWa tare da juyawa ya nufi hanyar fita Zuciyarsa sam ba daWi.

Husnee misalin 02:40 juyi kawai take yi akan katifa yayin da bacci ya ?auracewa idanunta, ba abinda take tunani sai Akhiee da kuma abinda zai iya faruwa idan iyayenta su ka san gaskiya, ta yi nisa a tunanin ta ji motsin wayar da ya bata wadda ta zo ta turata a ?ar?ashin filonta don gani take idan ta ajiye a wani wurin kamar za a iya dubawa a ganta.
Da sauri ta tashi ta zauna ta na dube-dube, babu alamar kowa a kusa Khausar ma sai baccinta take lakadan, zaro wayar ta yi daidai lokacin da wani sabon kiran ya kuma shigowa, Lamba ce sabuwa ma'ana ba save, gabanta ya yanke ya faWi dandanan jikinta ya Wau karkarwa ta shiga firgici da razani gami da kokonto akan me kiran nata da tsohon daren nan, shawarwari take yi akan ta Wauka ko a'a wata zuciyar ta na gargaWinta wata kuma na tunzurata akan ta Wauka Win, zuciyarta na dakan sha-lugude ta taSa kore gami da Wora wayar akan kunnenta..............


SHARE FISABILILLAH



Na KuWi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ?arin bayani =?I?


*??INDO*
[8/26, 4:38 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG


*>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 18

??
Ayeesha Abdulkareem INDO


*M.W.A>؅?*




"Kin ?i yin Bacci ko??" muryarsa ce ta doki dodon kunnenta, ta zazzaro ido a Wan razane kafin ta sauke nannauyar ajiyar Zuciya ba tare da ta yi magana ba,
Jin ta yi shiru ya sa shi ?arawa da cewa "Me yasa to?" kamar za ta fashe da kuka ta fara magana cikin muryar shagwaSa, "Tsoro na ke ji Akhiee!!" Wan jim ya yi kafin ya ce "Haka ne? ko in zo mu tafi gidanmu?"
?ara firfito da zara-zaran idanunta ta yi "Tsakar dare ne fa yanzu!! kai ka na ina ba ka tafi gida ba??!" ta yi maganar cikin firgici.
Cikin wata kasalalliyar murya ya ce "Asma'u ni dare ba ya hanani yawo hasalima ban fiye bacci da daddare ba da rana nake yi, ina kusa da ke in ki na so na zo mu tafi zan zo idan kuma ba kya so to ki yi baccinki cikin kwanciyar hankali."
Ajiyar Zuciya ta sauke gami da sassauta murya a sanyaye ta ce "Ka na kusa da ni Akhiee to ta ya kenan?"
?auke wayar ya yi daga kan kunnensa kafin ya furzar da wata zazzafar iska, ya so ya yi Saram-Satama kuwa, kiran sunansa da ta yi ne ya dawo da shi hayyacinsa, cikin nutsuwa ya ce "Ina nufin ki sa hakan a ranki kawai, Sai da safe yanzu zan shiga gida." da sauri ta ce "Akhiee!!" cikin wata irin shagwaSa ta yi maganar kamar wata ?ar shekara biyu na kiran Ummanta, rasss zuciyarsa ta buga ya lumshe idanunsa da su ka fara canja launi kafin ya mayar mata da martani ta hanyar kiran nata sunan "Asma'uhh!!" murmushi ta saki kafin ta ce "Da gaske ne ka na kusa da ni? kuma ka na tare da ni Akhiee? "
"Kin san ba zan faWa miki ?arya ba don hankalinki ya kwanta, ki yi baccinki ina tare da ke, kuma za ki yi mafarkina." gyaWa kai ta yi ta na murmushi cike da farin ciki da shaukin sonsa ta ce "Allah i tsare min kai Akhiee."
kai kawai ya gyaWa ba tare da ya yi magana ba ya kashe wayar.
Sumar kansa ya cafka gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya me tafe da wata Zazzafar iska.

Ji ya yi an dafa kafaWarsa ya yi saurin cewa "Russlan!!" Russlan ya zauna a gefensa kan katafaren gado irin na sarakuna da yake zaune a gefensa.
Cikin sanyin jiki Russlan ya ce "Ko shakka ba na yi ka na son matarka Risslan, ya zama dole ka dinga iya bakinka kar ka faWa mata abinda dole ne sai ka kasheta da hannunka." jinjina kai ya yi kafin ya yi magana "Ban san me yasa Asma'u take da tasiri a kaina ba, na kasa samun nutsuwa sai tunaninta na ke yi, ji nake tamkar na je na kwana a kusa da ita domin na bata dukkan kulawata."
Russlan ya ce "Na gane hakan ai duba da yadda ka ke zagewa ka na gaya mata gami da nuna mata iyakar abinda ke Soye a Zuciyarka wanda ba kowane me wannan Darajar ba, amma fa ina ji maka tsoron Uban Dawa kar ya hukuntaka akan aurenta ba tare da sanin iyayenta ba."
Shiru ya yi na Wan lokaci kafin ya ce "Asma'u! itace mahaWin rayuwata ko da so ko babu da ita zan rayu, ko da Father zai yi fushi zan jure duk hukuncin da zai yi mini, abu Waya kawai na yarda da shi kuma na sa a Zuciyata, ko da ta sanadin Asma'u za a yi mini izayar da ban taSa fuskanta ba duk tsawon rayuwata ba zan Saketa ba ina tare da ita kamar yadda na yi mata al?awari har sai in itace ta so rabuwa da ni wannan zan iya amincewa; Bayan haka kuma sama da ?asa, Duniyar Mutane da ta Aljanu har ma da sauran Duniyoyi babu wanda ya isa ya sa ni sakinta duk azabarsa, Allah ne ya halicceta kuma ya jefota cikin rayuwata kuma ina komai ne da ikonsa shine kaWai zai rabani da Asma'u ta kowace hanya, ko a raye ko muce Russlan kai ma ka ri?e hakan."

Zuwa yanzu Russlan tsananin tausayun Wan uwan nasa ya gama kama shi, ya san a zaman tare dole wataran za ta gane gaskiyar waye shi, kuma hukuncin wanda ya yi hakan kisa ne, bayan haka akwai ?alubale da yawa a gabansu wanda shi Risslan ba ya hangosu sabida idanunsa sun rufe, "Risslan na yarda da kai kuma na san za ka aikata amma ka sani akwai sauran rina a kaba."
"Na san da hakan Russlan, ka koma gida kawai nima zan wuce gidanmu Gadon nan ka sa Dogarai su kwashe shi kar safiya ta yi Bil'adam su dinga karo da shi."
Russlan ya ce "Okay sai ka fito goben, Mu haWu a Daji in an isa."
a hankali Risslan ya ce "Ka san fa ni ba kamar kai ba ne, musamman ina cikin wannan yanayin da akwai mutane da yawa waWanda su ke bu?atar kulawata."
Russlan ya ce "Okay shi kenan see you later."

Risslan bai ?ara magana ba ya Sace Satt! sai gashi a kusa da Dokinsa.
Prince na ganinsa ya fara haniniya ya na Waga ?afafu sama ya na direwa, Risslan ya shafa shi cike da ?aunarsa hakan ya sa ya sunkuyar da kansa ?asa kamar ba shi ya gama dara ba yanzu, wata kyakkyawar sufa Akhiee ya yi ya dire akan Prince tare da Komawa asalin Suffarsa ta ?an'adam wanda kowa zai iya ganinsa saSanin Da da ya koma Suffar mutanen Soye.

Hanyar komawa Hotoro yankinsu ya Wauka ya na tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da wata fargaba ba.
Cijewa Prince ya yi gami da Wangale ?afafunsa ya na wata irin haniniya hakan ya tabbatarwa Akhiee wani abin ya gani.
Bai gama nazarta yanayin ba ya ga Alburushi ya nufo kansa gadan-gadan sunkuyawa ya yi ya wuce sannan ya Wago, kafin ka ?ifta ido ka buWe wasu murtuka-murtukan mazaje sun bayyano ta kowace kusurwa ta filin, sanye suke cikin ba?a?en kaya kowanne fuskarsa a rufe, su na Wauke da wasu lafiyayyun bindigu wanda suka rufe bakunansu ta yadda ba za su yi ?ara sosai Ba.

Harbi suka fara ba shi ta ko'ina ba ?a??autawa idanu a lulluSe neman makasarsa su ke yi.
Abin da ya yi bala'in basu mamaki gami da dugunzuma hankulansu, kasancewar ?wararrun maharba ne ba sa saSa saiti bayan Alburushin farko ba wanda su ka harba masa ya faWi duk sun same shi sai dai da zarar Alburushin ya sauka a jikinsa zai gangare ya faWi ?asa ba tare da ya ratsa shi ba, duk da suna ganin hakan kuma sun razana amma ba su fasa ba don kuwa ganu suke yi kamar za su iya cimma nasara in suka ?o?arta.

Wani wawan juyi ya yi gami da buWa hannayensa ya yi wani wurwuro kamar fanka sannan ya diro ?asa hannunsa ri?e da manyan bindigu guda biyu.
Turus su ka tsaya kallonsa ido a warwaje, sun kai ma?urar tsoro da firgici ganin bindigu sun bayyana a hannunsa bayan ba shi da su ba shi da dalilinsu.

Cikin rashin imani da tausayi Na Akhiee ya fara sakar musu harbi a matu?ar fusace, ganin haka ya sa su ka ci gaba da harbinsa su ka fara artabu tsakaninsu, sai dai shi harbi Waya yake yi musu su baje don dai su na da yawa.
ba Sata lokaci duk ya ?arar da su saura mutum Waya wanda Alburushi ba ya shigarsa don kuwa shi ma babban shege ne.

Akhiee ya yi wani ?wa??waran taku gami da watsar da bindigun a gefe dandanan su ka Sace Satt!! sai kuma wata lafiyayyar farar wu?a ta bayyana a hannunsa, duk da dare ne hakan bau hana ?yallinta da haskenta fitowa ba, kan Maharbin ya nufa gadan-gadan hakan ya sa ya arta da gudu domin ceton ransa, jefa masa wu?ar ya yi cikin sa'a kuwa ta ratsa ?ashin bayansa, ya saki ihu gami da zamewa ya kife a rubda ciki, Akhiee ya ?arasa gabansa ya dur?usa kafin ya ce "Duk wanda ya ga wannan Sirrin nawa mutuwa ce makomarsa ba za ka iya tsere mini ba, amma kafin ka mutu ina son sanin wanda ya aiko ku." cikin ?arfih hali Mutumin ya kama dariya ya na cewa "Wani Jarumi ne, kuma ya riga ya sa ka a tarko ta kowace fuska, ya yi mummunan shiri na kawo ?arshen hatsabibancinka, kuma ina me tabbatar maka ruhina ba zai tafi a banza sai ya Waukar mini fansa, Gobe za ka samu gawar ?a?anka mun ci moriyarsu don haka za mu dawo maka da su, ka shiga matsala Sar?a, duk hatsabibancinka sai wannan Shu'umin ya ga bayanka shi ba kanwar lasa bane zazzafa ne, kuma jama'arsa daga kowane State na Nigeria har ma da ?asashen ?etare sun shigo Nigeria sun yi maka ?awanya, in ka isa ka tsira hhh!!!".
Ya ?arasa maganar ya na ?ara ?yal?alewa da dariyar mugunta a wahalce.

A fusace Akhiee ya zare wu?ar da ke ma?ale a bayan Mutumin ya suka masa ita a wuya, ko shurawa bai ?ara yi ba tuni ya mutu idanunsa a bubbuWe.
Akhiee ya mi?e jikinsa na wata irin tsuma sabida Sacin rai, tuni wani irin duhu ya mamaye idanunsa kansa ya fara wata irin yamutsawa.
Bai bi ta kan Dogarawan Aljanun da suka kewashi ba ya haye kan Prince ya ci gaba da tafiya.
Aljanun su ka koma kan mutumin da ya kashe daga ?arshe shi ma su ka Wauke gawar ta shi sauran kuwa tuni sun kwashe su sun kai su bakin wani Daji sun zubar.
Ba su gushe daga wurin ba sai da su ka gyara shi tsaf ba alamun jini ba alamar Alburushi ba ma me cewa wani abu ya faru a wurin.

ya na isa bakin get Win gidan ya dire daga kan Prince ya dafa ?ofar nan-take ta buWe ba tare da hayaniya ba, ya shiga gidan tare da Prince sannan ya ?ara dafa ?ofar ya rufe, sakatu harda Pad lock Win da ake sawa get Win duk su ka koma su ka rufe kamar dama ?ofar tinda aka rufeta ba wanda ya ?ara taSata.

Kawai sakin Prince ya yi ya tafi makwancinsa da kansa shi ma ya nufi na shi makwancin, ta bayan gidan ya bi inda ya fi kusa da Wakinsa ba sai ya ratsa sassan gidan ba, ita ma ?ofar bayan kulleta ake yi amma ya na Wora hannunsa akanta ta buWe ya shige sannan ya rufeta, kwata-kwata a wannan daren bai yi bacci ba tunane -tunane sun yi masa katutu.

Husnee ta na gama waya da Akhiee ta ji wani irin sanyi na ratsa dukkan sassan jikinta har cikin Zuciya da ?o?on ranta, nan take farin ciki ya ziyarce ta fara manta dukkan Damuwarta, ba ta daWe cikin wannan yanayin ba Bacci me nauyi ya yi awon gaba da ita.
Cikin Baccin kamar yadda Akhiee ya faWa mafarkansa ta dinga yi, har abinda ya faru tsakaninsa da waWanda su ka farmake shi sai da ta gani, wani Sangaren kuma soyayya su ka zuba a mafarkin kamar ba za a mutu ba, haka ta dinga yinsu kala-kala har Allah ya wayi gari.
Jiki a muce ta tashi yau hakan ya sa ba ta yi yun?urin fita makaranta ba, sai da yamma ta shirya tsaf sannan ta fito, Amadu da me Gadi su na zaune su na hira ta fito Wogal-Wogal wai ita makaranta za ta je.
Baki a sake Amadu ke kallonta har ta ?araso inda suke, cikin siririyar muryarta ta ce "Malam Amadu Makaranta zan je fa"
jinjina kai ya yi gami da cewa "Tir?ashi!!!! ai kuwa ban amince ki fita ba har sai kin tambayi mijinki."
Kamar za ta yi kuka ta ce "Makaranta fa zan je". "Ko nan da ?ofar gida za ki je indai ni zan kai ki sai kin tambayi Mijinki bare makaranta, sai in ke kaWai za ki fita to wannan alhakin bai shafe ni ba ko a wurin Allah ba

15 / 25