Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   17 / 25

48K to 51K   out of 73.5K words

da cewa "Dama kin iya faWa? sai naga kin yi kyau a cikinsa; ke sai fa kin je ko kuma in Wauke ki da kaina in zuba ki a Mota, wata cikal-kal da ke har wani hargowa ki ke yiwa mutane? to ki gaggauta shiryawa in ba haka ba zan Waukeki ko babu gyale."
Ba ta ce masa komai ba ta fice daga Kicin Win ta na kuka ta nufi Wakinsu.

Iya da Talatu na zaune sun ci gaba da hirar da su ke yi ta shigo ta na kuka, Iya ta ri?e haSa gami da cewa "Oo! Duniya, me ya yi miki ki ke kuka haka?? ni fa ina ji miki tsoron yaron nan, me ki ka ci masa me yake ta zawarcenki??"
Cikin shashshekar kuka ta ce "Ba abinda na yi masa haka kawai yake mini haka, wai yanzu ma in shirya in raka shi, ni dai ba zan je ba ko me zai yi mini."
Talatu ta yi karaf ta shiga zancen da cewa ''Ke wallahi ki bi shi ki ga inda zai kai ki, ai dai ba zai sayar da ke ba ko." cikin takaici iya ta zabga tsaki gami da kaiwa Talati duka ta na cewa "Ja'irar gora, to in bai sayar da ita ba ai zai rabata da darajarta, ki na gani in uwar ba ta nan yadda yake yo safarar Mata ya na kawowa gidan." Talatu ta ce "Eh kuma fa haka ne..."
Ma'u kuwa ?ara fashewa ta yi da kuka jikinta sai tsuma ya ke yi gabaki Waya ta ?ara firgicewa.

Sun Wauki lokaci a nan Talatu da Iya su na maida yadda aka yi Ma'u kuwa ta na razga kuka.......
Kamar daga sama su ka jiyo muryarsa ya na ?walla mata kira, ta ?ara sautin kukanta cike da tsoro da firgici.
Iya ta rausayar da kai kamar marigayin zakara kafin ta ce "To Allah i tsare sai ki tashi ki je, amma ki dinga Addu'a." Talatu ta na jin haka ta tashi ta Wakko koWaWWen Hijab Winta ta fara ?a?aba mata, ta na turewa ta na komai amma sai da ta sa mata shi sannan ta Wakko mata takalmi ta ajiye mata ta na cewa "Gwara ki bi shi ta maslaha kar ki yi masa abunda zai cuceki a banza, sai ki dinga Addu'ar."

Sai da kyar da siWin goshi suka lallaSata ta fito wujiga-wujiga da ita sai murza kuka take yi kamar an yi mata wahayinsa.
Shi dai ba abinda ya ke iya yi banda kallonta, har cikin ransa ba ya jin daWin kukanta amma ita ta kasa ganewa.
A wani rafkeken Super Market ya yi Parking, ido ya ?ara zuba mata kamar zai cinyeta, kanta ya na ?asa har lokacin ba ta dena kuka ba.

Cikin wata karyayyar murya ya ce "Ma'u me yasa ba za ki saki jiki da ni ba? ba zan iya cutar da ke ba Ma'u hasalima burina a koda yaushe in ga ki na farin ciki, kuma ina so farin cikinki ya Wore har Abada, ki temaka ki gaya min damuwarki domin ina so in zamo miki Bango." Ya sosa mata inda ke mata ?ai?ayi, ai kuwa ta ?ara fashewa da wani sabon kukan filll, cikin shashsheka ta ce ''Ba zan iya ba!!"
"Yau na ji ikon Allah, kuka na ?ara sa ki? to Allah i ba ki ha?uri na dena, ki kwantar da hankalinki, Nasan ki na tunanin wasu halaye nawa ke ba ki yi kama da irin waWannan matan ba, ke mace ce wadda ya kamata a yi kishinta, ki zo mu je to, sayayyar kaya zan yi miki sai ki zaSi abinda ki ke so." "Ni ba zan je ba" ta ba shi amsa cikin kuka.

Bai matsa mata ba ya wuce shi kaWai, bayan wani lokaci ya dawo Wauke da tir?a-tir?an ledoji guda biyu wanda aka sha?esu da kaya, bayan ya zuba a Motar ya shiga mazauninsa sannan ya ja ta.
Har su ka dawo gida Ya na zuba mata surutu ita kuwa ba ta da aiki sai kuka, muryar ta shi ma duk ta gaji da ji; ji take kamar ta kashe shi ta huta.

Talatu jiki na rawa ta fara zaro kayan ta na dubawa sai murna ta ke yi kamar ita aka bawa.
Dogayen Ruguna ne wanda yawancinsu Abaya ce, sai riga har ?asa me wando, sai kayan ciki su pant, da su turaruka, da Alewoyi da chocolate kala-kala .
Iya da Talatu sai yabawa su ke yi yayin da Ma'u ta ke jin Zuciyarta na wata irin ?una, lokaci guda zazzaSi ya rufeta bayan ta gama masifa da cewa ba za ta yi amfani da komai a ciki ba ta haye yamutsatstsiyar shimfiWarsu ta kwanta, ba abin da ke Waga mata hankali idan ta tuna sama da surutan da ya dinga yi mata a hanya kamar mahaukacin da ya ?wato da ga gidan Masu rangwamen hankali. Sai da su ka gama gani sannan su ka mayar su ka ajiye mata, ita kuwa ko wajenda kayan suke ba ta ?ara kalla ba.


Washe-gari Ranar litinin kenan, Ranar jirginsu Abhi da Jaafar ya Waga zuwa Saudi Arabia, hakan ya mugun yiwa Akhiee daWi ya san duk rigimar da za a yi za ta ?are kafin Abhi ya dawo.

Gidan Su Husnee
Komai ya yamutae lokaci guda ta zamo tamkar Mujiya a cikinsu kowa ya ?i saurararta hatta Khausar in ta kulata sai Mommy ta doka mata tsawa, FaWa kuwa ba irin wanda ba ta sha ba Muneeb har da kai duka.
Cikin kwana Waya ta wani zuge ta zube ta yi zuru-zuru ta dawo tamkar tsumungiya, ga wani ciwon kai da ya sakota gaba ko abinci ta kasa ci, Ta rasa inda za ta sa kanta ta ji daWi.
Wata Zuciyar ce ta bata shawarar kiransa ta sanar masa abinda ke faruwa don haka ta Wakko wayar ta lalubo lamba ta tura kira.

Ya na tsaye a kan wani tsauni hannayensa harWe a bayansa, sai ?arewa ko'ina kallo ya ke yi Zuciyarsa cike ma?il da tunane-tunane, jin motsin wayar ta shi ya dawo da shi hayyacinsa ya Wauka ba tare da ya ce komai ba.

Cikin Dasashshiyar muryarta ta ce "Akhiee!!" "Asma'u ki na lafiya? waye ya taSa ki?" goge ?walla ta yi kafin ta ce "Ba wanda ya taSa ni kawai ina cikin tashin hankali ne, iyayena da ?an uwana duk fushi su ke yi da ni, na fahimtar da su na basu ha?uri amma duk hakan bai yi tasiri ba, kuma sun ce sai sun rabamu."
?ar ?aramar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Asma'u Calm dow........" kafin ya ?arasa faWen abinda ke Zuciyarsa ya ji anyi masa wata muguwar runguma ta baya wadda ta sa Numfashin da Zuciyarsa su ka dena aiki na wucin gadi, ya rintse idanunsa da ?arfi gami da cije gefen leSensa.
Ya na jin Husnee na kiran sunansa gami da tambayar lafiyarsa amma ba zai iya ce mata uffan ba a wannan yanayin.
a hankali sautin kukanta ya fara karaWe kunnuwansa hakan ya sa tsigar jikinsa su ka hau tashi. katse wayar ya yi gami da sakinta ta faWi ?asa, cikin wata irin rikitacciyar murya ya ce "Raziahh!!!!!"
Cikin shashshekar kuka ta ce "Kai fa Mijina ne Risslan me ya sa za ka haWa ni kishi da wata? ka san kai kaWai nake so kuma ina kishinka shine za ka je ka auri wata? me yasa ni ba za ka so ni ba?"
Cikin wata irin murya me matu?ar gusar da hankalin duk wanda ya ji ta take maganar, a sannu ya zagayo da ita gabansa su na fuskantar juna ya jefa idanunsa wanda su ka canja launi cikin nata, kamar wanda aka tilastawa yin magana ya ce "Amma duk da ke matata ce wajibi ne na nemawa kaina Abokiyar rayuwa, kin sani dai ba jinsinmu Waya ba, babu Worarren aure tsakanin Mutum da Aljan, ko ba ma haka ba Asma'u ta cancanci hakan, ki yi ha?uri"
Sake ?an?ame shi ta yi ta na cusa kanta cikin ?irjinsa gami da sake wani sabon salon kukan, cikin wata shu'umar murya ta ce "Nima zan zamo Bil-adam domin na rayu da kai, idan babu kai a rayuwata zan sha wahala, Don Allah ka dena guduna Mijina ka amince mini mu rayu tare, ina azabtuwa da banzatar da ni da ka ke yi; ka sa Uban Dawa ya Waure ni kawai sabida ina kasancewa tare da kai, idan laifi na yi maka ka hukuntani ta wata hanyar amma ba ta wannan ba Don Allah!!!!!!"
Ta ?arasa maganar ta na kwallan idanunsa da ke cikin nata.
dukkan hannayensa ya sa ya rungumeta tsam gami da tura fuskarsa cikin wuyanta, cikin fitar hayyaci ya ce "Ni ma ba a son raina hakan ta ke faruwa ba, sai dai ni ba na bu?atar mace a rayuwata dole wata rana za ta hana ni yin abinda ya dace, amma ni ban taSa ?in ki ba hasalima ko da yaushe ki na cikin Zuciyata!!!"


SHARE FISABILILLAH



Na KuWi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ?arin bayani =?I?
AN FARA PAYMENT

*??INDO*
[8/29, 5:41 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG

*>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 20

??
Ayeesha Abdulkareem INDO


*Wannan shine Last Free Pages*



LAST FREE PAGE
Da sauri ta Wago ta zuba masa blue eyes Winta ta na murmushi me matu?ar ?ara mata kyawu da jan hankalin me kallonta, cikin sassanyar muryar da ke ?ara sa shi fita daga hayyacinsa ta ce "Indai da gaske ka ke ka yi min Al?awarin za ka kasance tare da ni har abada, kuma za ka rabu da wadda ka Aura." idanunsa ne su ka ?ara girma, tamkar aradu ta rikito masa aka haka ya ji saukar kalaman nata, laSSansa har karkarwa su ke yi wajen cewa "Impossible! Razia idan ki ka rabani da Asma'u tamkar kin rabani da garkuwar rayuwata ne, ban na son rabuwa da ita kuma ba na so ta cutu, akanta na shiryawa komai ko da mutuwa ce, ta na da muhimmanci a rayuwata kuma kema ki na da shi, zan so ku rayu a ?ar?ashin inuwa Waya ba tare da cuta da cutarwa ba."
"Ba zan iya haWa Mijina da kowace Wiya ba, kuma ma ka rasa wadda za ka haWani kishi da ita sai Bil-adam, ba ka nemi zaman lafiya ba, kuma ka na ji ka na gani zan kasheta ko kuma na nakastata!!"
Ta yi maganar a fusace.
zafi da ?una kawai Zuciyaraa ke yi, ture ta ya yi daga jikinsa gami da juya mata baya cikin Sacin rai ya ce "Tinda na fahimtar da ke kin kasa fahimta zan Wauki tsatstsauran mataki akanki da zarar kin cutar da ita, ko meye ya sameta ki sani zan ninka shi akanki, ko kasheta ki ka yi sai na yi miki azabar da za ki gwammace ke ma mutuwa ki ka yi, tinda na gaya miki gaskiya kin kasa fahimta."

Ta na shirin yin magana Russlan ya diro a wajen, ransa a matu?ar Sace, ya na sauka ba tare da wani tunani ba ya Wame kwari-da-bakar hannunsa ya na shirin harbawa Razia, wani gwauron tashi Akhiee ya yi ya dira a kansa ya bangajeshi su ka faWi can gefe su ka fara mulmulawa kamar ?wallo, cikin sa'a Akhiee ya yi nasarar ?wace kwari-da-bakar ya yi wurgi da ita zuwa gefe, rai a Sace ya ce "Me ta yi maka?"
Russlan ya tunkuWeshi gefe sannan ya mi?e ya na cewa "Sabida ta raina mutane a dinga faWa mata magana amma ita kamar shaiWaniya? yanzu gashi ta sa Uban Dawa sai faWa ya ke yi mini a ganinsa ko me ta yi laifina ne, gwara kawai na harbeta mu je mu yi jinya da wannan fitinar ta-ta."
Dogon tsaki Risslan ya ja kafin ya ce "Amma ai Matata ce ko? kuma wurina ta zo ba wani wurin ta tafi ba."
"Waye ya bata izinin fita to? kawai ka ?yaleta ta karSi hukuncin abinda ta yi, ka riga ka san halinta kaima.
"Ba fa zan bari ka cutar da ita ba, laifi na yi mata kuma ta na da right Win da za ta nuna Sacin ranta, ka je kawai zan dawo da ita da kaina."
Cikin takaici Russlan ya ce "Sai ka amsa Kiran Father kai ma nemanka ake yi." Daga haka ya tashi sama ya basu wuri.

Akhiee ya maida kallonsa kan Razia da ke dur?ushe ta na kuka magashiyyan, a hankali ya taka zuwa gabanta ya dur?usa, tausayinta ya cika masa Zucuya taf, cikin tattausar murya ya ce "Razia! gardamarki ce ta sa ki ke fuskantar Sacin rai a kodayaushe, ba kya jin magana gashi ba kya aikata abu me kyau, Lokacin da za'a ?antaki ya kusa amma a bisa wannan laifin da ki ka yi na san dole Uban Dawa Zai ?ara miki lokaci, ba kya kiyaye Sacin rai, ba kya Waukar shawara, ni a yanzu ba zan iya yin komai a kai ba don nima hankalina ya fi kwanciya idan aka killace ki, fitinarki ta yi yawa musamman a yanzu da ki ka ?ara burkicewa, ki tashi mu je."
Ba ta iya cewa komai ba sai kuka, Zuciyarta tamkar ta tarwatse, ji take da Allah zai haWata da Husnee a yanzu ba abinda zai hana ta kasheta in yaso sai ayi mata Wauri me dalili.
Hannunta ya kama su ka Sace daga wurin.

A Fadar Uban Dawa su ka sauka, yayinda Da yawa daga cikin ahalinsu sun taru a wurin su kaWai ake jira.
Russlan da Arsalaan da Hidaya da sauran yara su na dur?ushe a gaban Tafkeken gadon Sarauta na Uban Dawa, anan Razia da Risslan su ka dur?usa su na mi?a gaisuwarsu.

Sai da lokaci ya Wan ja sannan Uban Dawa ya yi gyaran murya ya fara da cewa ''Risslan Labari ya iso mana na cewar ka Auri wata ?ar Bil-adam ba tare da iyayenta sun Amince ba, meye dalili?"
Da sauri ya Wago kansa cike da tsoron ta yadda Father zai KarSi Abin, Mother ya kalla cike da son ?warin guiwa daga gareta, ta sakar masa sassanyan murmushinta gami da lumshe idanunta .
?ar ajiyar Zuciya ya sauke gami da yin ?asa da kai ya ce "Sabida ta na sona ne, kuma idan ba na tare da ita komai zai iya faruwa da ita, shi yasa na yi hakan, a gafarceni Father."
Uban Dawa ya jinjina kai cikin dattako gami da manyance ya ce "Ba ka yi tunanin hakan akwai kuskure ba?"
"Ba na tunanin akwai kuskure a ciki, amma ban sani ba ko kun hango abinda ni ban hango ba."
Father ya yi murmushi hakan ya sa duk sauran na wajen su ka murmusa, cike da ?auna da kulawa ya ce "Kar ka sake wani ya rabaka da Ita, nima zan so ganinku tare."
Da sauri Razia ta Wago rinannun idanunta ta zubawa Uban Dawa gami da cewa "Father!!" cikin kaWuwa da tashin hankali.
Oum Razia ce ta yi saurin tarar numfashinta da cewa "Kul!! kar ki ?ara sako baki cikin maganar manya."
Uban Dawa ya ce "Razia ba sai kin neme ni ba ni zan nemeki da kaina domin kin yi mini laifi, indai fa ba za ki koyi jin magana ba to ba za ki dena karSar hukunci ba, Yanzu kin ninkawa kanki Shekaru a ?ar?ashin Hukunci, Arsalan maza a maida ita." ya ?arasa maganar ya na kallon inda Arsalaan ya ke
Razia ta ?ara rushewa da wani azababben kuka ta na magiya gami da bada ha?uri, amma ba wanda ya ce uffan har shi wanda ya yanke hukuncin, Akhiee kuwa rintse ido kurum ya yi don kuwa sam ba ya jin daWin kukan nata.

Cikin sanyin jiki Mother ta ce "Father! don Allah a yiwa Razia afwa, wani lokacin Zuciya ce take ruWarta da aikata abinda ba daidai ba."
"Idan ba a nuna mata kuskurenta kuma ta yaya za ta fahimci yadda rayuwa take??, idan ta gama hankalta babu me ?ara hukuntata; idan akwai wanda zai yi magana ana saurarensa."
Mi?ewa Akhiee ya yi gami da cewa "Ni kam zan fita ana nemana."
Da kai kowa ya amsa masa, sannan ya fice.

Hajiya Laure Yau har ?agara ta yi gari ya waye Sabida mafarkin Boka Barore da ta ke yi, ko ta farka da zarar ta koma sai ta ci gaba. Tin ?arfe bakwai na safe ta Wauki waya ta turawa Hajiya Saudah kira, a Sangaren Hajiya Saudah ma wayar ta na hannunta ta na shirin kiran Hajiya Laure ta sanar mata, cikin sauri ta Wauki kiran gami da kara wayar a kunnenta ta na cewa "Hajiya Laure kema kin yi mafarkin ne?"
Hajiya Laure ta ce "Hmm! na yi manaaa,, ba me daWi ba ma kuwa, ai ni gaskiya mu shirya tin wuri mu je mu ji abinda zai ce don wallahi a tsorace nake."
"To ai nima dai hakan take a nawa Sangaren, har na ji ma ina tsoron zuwa wallahi don mafarkan da na yi ba kyau" Hajiya Saudah ta faWa murya ?asa-?asa, da sauri Hajiya Laure ta ce "A'ahh! da ke mu ka je da ke za mu koma, ni

17 / 25