Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   11 / 25

30K to 33K   out of 73.5K words

cikin wata ?ar lalita, cike da son kare kansa ya ce "Wallahi kin san dai ba yin kaina ba ne, Dodo ne ya samu kuma kinga aikinsa mu ke yi ba zai lamunce mu ?i yi don ki na son Sahun Keke ba, wannan kuWin ma da ki ka gani ba nawa bane na waWannan ne" ya faWa ya na nuna abokan aikin nasa wanda su ke zazzare ido kamar na mazarin tsire a kasuwa, sun tsorata da ganinta don dukansu ba wanda bai san halinta ba, ana cewa mace akwai tausayi amma ita ta fi wani namijin rashin imani.

?wafa ta yi kafin ta ce "?an Kurada ka je don kanka kai ba zan taSa ka ba amma tabbas sai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro." Jin haka ya sa sauran mi?e su na neman wajen tsira, a hankali ta taka ta doshi inda suke, baya-baya su ka fara yi su na bata ha?uri gami da bata yadda aka yi amma ko saurarensu ta ?i yi, sai da su ka ?ure da bango sannan su ka dakata.
Cikin dakakkiyar muryarta ta ce "Da ku da suwaye ku ka aikata??' Asabubu ya ce "Wallahi ?an Kurada ne babbanmu, sai wannan sai sauran yaran Oga, ni ba abinda na yi masa wallahi." ya ?arasa maganar ya na yi mata nuni da na kusa da shi.

Wata lafiyayyar wu?a ta zare a ?ugunta ta na zuba musu idanunta masu ban tsoro, sai da ta goge wu?ar sannan ta ce "Ya zama dole ku WanWana!!" ta yi maganar tare da ketawa Asabubu wu?ar akan cikinsa, ihu ya zunduma sabida azabar da ta ratsa shi har cikin ?o?on ransa, cike da rashin tausayi da imani ta ?ara kafta masa sara a kafaWarsa hakan ya sa dole ya zube a wajen.
Takawa ta yi da gudu ta bi Wayan da tuni ya tsela a ta kare ya na neman ceto, kafin ya kai ga fita ta cimmasa, ta na dan?o shi ta shata masa yanka a hannunsa kan jijiyar gaSar hannun ai kuwa jini ya ce salama alekum, ri?e hannun ya yi ya na wulwula shi cike da azaba, ba ta saurara masa ba ta burma masa wu?ar a ciki ta zareta gami da sa ?afa ta harbatsa shi can gefe.

?an Kurada da jikinsa ke ta tsuma ta kalla ta na huci kamar wadda aka danne za'a yanka, "Wallahi Tallahi indai ka ?ara taSa Sahun Keke sai na raba kanka da gangar jikinka, ka je ka gayawa Dodo na Wauki mataki akan yaransa, duk hukuncin da zai yi mini ina jira, don Uwar babassa ko me zai yi ya yi, kuma daga yau na bar aiki a ?ar?ashinsa, nima ?ar kaina ce kuma ina da tawa dabar, ku iya takunku tin kafin na hallaka ku."
?an Kurada ya jinjina kai alamar ya fahimta, da kyar ya harhaWo magana ya ce "Amma bai kamata ki bar ?ar?ashin Dodon Lungu ba, na san ma don kin yi haka ba zai ce komai ba." "Idan ma ya faWa ba ni da asara ka je ka gaya masa sa?ona." ta na gama faWen haka ta fice fuuuuu kamar iska.

Husnee
Ko da Amadu ya kai ta makarantar cewa ta yi ba za ta shiga ba gwara ya kaita wani wurin idan lokacin tashi ya yi sai su koma gida.
Cikin sanyin jiki ya ce "Innata ni yanzu ina zan kai ki don Allah?"
"Mu je bakin titi kawai ka ajiye motar zan zauna a ciki" Amadu kamar ya fashe da kuka ya ce "Hakan fa bai da amfani ki yi ha?uri mu koma gidan dai tinda ba kya son makarantar."
"Ba na son gardama don Allah kawai ka yi mini abinda na ke so." rausayar da kai ya yi sannan ya kunna motar gami da fara tafiya.

Sai da ta kimanta lokacin tashi sannan su ka nufi gida, Mommy na harabar gidan ta na duba shuke-shuke su ka shigo, baki a sake ta tsaya kallon Husnee wadda ta yi jemai-jemai da ka kalla za ka gane a bala'in wahale take.
"Ikon Allah kwanan nan dai duk in ki ka fita ba kya dawowa ?alau, me yake faruwa ne??"
Numfashi ta ja ta sauke shi tare da nannauyar ajiyar zuciya, cikin muryar da ke ?ara nuna tsantsar damuwar da take ciki ta ce "Ba zan ?ara zuwa makarantar nan ba har sai bayan wani lokaci."
"Oo ni ?asu, to dalilin me?" "Mommy Ba ni da lafiya kuma shine su ka doke ni, don Allah Mommy kar ki matsa mini akan hakan ki barni duk ranar da na yi niyya zan koma." Mommy ta rausayar da kai kamar kazar da ke jin yunwa, a sanyaye ta ce "Shi kenan, Allah i ba ki lafiya, dama ke ki ka zaSi makarantar ai ba ni na zaSa miki ba, ranar da ki ka ga dama kya je, kuma idan yayyenki su ka tambayeki dalilin rashin zuwanki sai ki san abin gaya musu."
GyaWa kai kawai ta yi alamar ta yarda da hakan, ba ta ?ara cewa kanzil ba ta wuce ciki, tinda ta zauna ta doka tagumi ba abinda take tunani sai irin tsatstsauran matakin da Akhiee ya Wauka akanta, a yanzu ba ta da zaSin da ya wuce ta ?aurace masa na wani lokaci, kuma ta dinga addu'ar Allah i yaye mata duk abinda ta ke ji akansa, tunane-tunanen da ta ke yi kenan gabaki Waya hankalinta ya tafi akai.


Hajiya Laure da Hajiya Saudah ne zaune a gaban Boka Barore sai tsitstsilla idanu su ke yi sabida tsoro da fargabar abinda zai fito daga bakinsa.
shi kuwa Dariya kawai ya ke tilli?awa kamar an yi masa wahayinta, ya kai a?alla minti biyar ya na yi sannan ya ci mur kamar ba shi ba, kallonsu ya yi Waya bayan Waya kafin ya fara magana ya na yi ya na zare musu munanan idanunsa, "A kwana uku na ce ku dawo, shine ku ka ?i dawowa sai yanzu da ku ka yi niyya, to aikinku ya tarwatse, wadda mu ka turawa aikin a lokacin ta na tare da shi kuma ya temaketa ya hana aikin shiga jikinta, kuma ba ku dawo lokacin da mu ka ce ba kun tarwatsa komai, ShaiWanun Aljanu sun Fusataaa!!!!" ya kai ?arshen maganar tare da wani ?araji da gurnani tamkar mahaukacin zaki.

Kallon Kallo Hajiya Saudah da Hajiya Laure su ka yi cikin tsoro da shakku kafin Hajiya Laure ta ce "Ranka ya daWe Boka Barore me zamani, wallahi rashin lafiya ce ta kama ni ba zato ba tsammani kawai sai na tashi da cuta har ba na iya ko tashi zaune sai an temaka mini, amma yanzu na ji sau?i shine fa na yi maza na garzayo, abin dai ya na raina amma tsautsayi ne ayi ha?uri manyan mutane" ta ?are maganar cikin sigar rarrashi.
"Hahahahahahaha! Ta baya ta wuce, za ayi aiki me wahala kuma za mu ?ara tura shi ne kan wannan yarinya, amma muddin ku na so aikinku ya yi kyau sai kun cike sharuWana" Hajiya Saudah ta ce "Meye sharaWin? ai tinda da akwai mafita komai me sau?i ne Boka" ''Ina bu?atar yarinya ?ar shekara ?asa da ashirin, za ku kawota gobe bayan ta yi kwana uku za ku zo ku Wauketa, muna bu?atarta!!!!."
Hajiya Laure cikinta ya bada wani ?ulululu!! ita duk irin wannan manyan asirce-asircen ba iya yinsu ta yi ba, abinda ta fi ganewa ?ar mallakar miji da Wan abinda ba a rasa ba shima mallakar ba irin ta muguntar nan ba.
Ganin ta ruWe ya sa Hajiya Saudah ta ce "Za mu kawo Boka, indai za mu yi nasara dole ne za mu nemo mu kawo."
Boka ya yi dariya me isarsa sannan ya ce su zube kuWi ya sallamesu.

Suna fitowa Hajiya Laure ta ce "Haba Hajiya Saudah, yanzu ina zan bi in samo yarinyar mutane in kawowa boka? haba a dinga tunawa fa a duniyar muslimci muke ba ta kafirai ba."
Hajiya Saudah ta yi wani Shu'umin murmushi kafin ta ce "Hmm!! kin Wauki duniya da wasa ?awata, ki na son Waukar fansar mijinki, amma ki na tsayawa sanya, samun budurwa ba wani abu ba ne ba fa, kuma ba wai kasheta zai yi ba kawai ina tunanin zai Wan ci amarci da ita ne" ta ?arasa maganar ta na dariya, ita ko a ?asan silifas Winta.
Hajiya Laure dai har yanzu abin bai yi mata ba, cikin sanyin jiki ta ce "To yanzu wa zan samu in kawo masa a goben nan?"
"Ba ki na da ?ar aiki ba? ?ila ma ba Waya ba to a cikinsu za ki zaSa ki darje kawai ki ce ta zo ta raka ki, indai boka ne da ya gama abinda zai yi ya rufe bakin shegiya shi kenan."
Hajiya Laure dai ba ta iya cewa komai ba sai tunane-tunane, wannan Damar Hajiya Saudah ta samu ta zizzigata ta kwantar mata da hankali har ta ji ta yi na'am da hakan.

Washegari kamar yadda su ka shirya tin wuri Hajiya Laure ta ci ado ta gaiyaci Ma'u ?ar aikinta rakiya, su na zuwa su ka direwa boka ita su ka yi nasu wuri.
anan fa Ma'u ta ga tashin hankali, tin ta na kuka da hawaye har su ka gaji su ka dena zubowa.

Bayan kwana uku.

a cikin ?ar bukkar Boka Barore su na zaune gabansa sai fara'a su ke yi da alamu dai duniyar ta buWe musu, Ma'u kuwa ta na gefe ta haWe kai da guiwa tsirit da ita.
Hajiya Laure ta ce "Boka Wana ya takura mini akan hakan, ban san ya zan yi masa ba." Barore ya yi dariya sannan ya ce "Za mu rufe masa baki, ba zai ?ara hanaki yin abinda ki ke so ba" ta ji daWin hakan ta yi masa godiya kana su ka mi?e, yau ma kwana uku ya basu su dawo.
Ma'u dai da kyar da kyar take iya tafiya, duk ta zama kamar sokuwa ba um ba um-um, su Hajiya Laure ma ?yamarta su ke ji da sun kalleta sai su tsartar da yawu su yatsine fuska, da haka har su ka dawo gida.

Hajiya Laure ta yi Sa'a da su ka shigo gidan duk ba kowa a kusa don haka ta yi sauri ta balbale Ma'u da masifa akan ta je ta yi wanka ta dawo daidai, cikin yanayinta me kama da sokunta ta aiwatar da abinda Hajiya Laure ta ce.
Ba laifi ta Wan dawo hayyacinta sai dai tana nan sukuti da ita.

Husnee na kwance kan gado ta na malelekuwa kamar yadda ta saba don kwanan nan aikinta kenan, Mommy ce ta ?wala mata kira, ta amsa cikin muryarta da ta gama dashewa, Mommy ta ce "Zaman Waki da kwanciyar nan naki ya isheni ya ishi kakata INDO ba dole cuta ta ?i warkewa ba ki na famar kwanciyar kamar Wan malele? anyi allura ansha maganin amma abu ya ci tira, fito ni ki tayani girki ko kya ji ?warin jikinki."
Da kyar ta iya amsawa da "to" sannan ta yun?ura ta tashi ta na bibango sabida wani Wan jiri-jiri da ke Wibarta.

Ta na fitowa daga Wakin daidai lokacin ?ullin asirin Boka Barore ya nufota gadan-gadan, ?iris ya rage ya faWa mata Razia ta faWo kanta da ?arfin gaske hakan ya sa ta ?walla ihu gami da faWuwa gefe ragab, a take ta sassan?are kamar gawar sababi. tsafin Boka Barore kuwa ya faWi ?asa ya ?one ?urmus tuni ya bi iska ya san inda dare ya yi masa.

Hankali a matu?ar tashe Mommy ta yo kanta ta na kiran sunanta, ta na taSata ta ji ta sandare komai na jikinta ya dena aiki sai zuciyarta ce kawai ke bugawa, Addu'o'i ta fara jerowa ta na tofa mata nan fa hankalinta ya ?ara ?ololuwa wajen tashi ganin Husnee ta fara kanannaWewa ta na wani irin lan?washewa kamar jikin tsutsa gareta, ma'ana dai tamkar ba ?ashi a jikinta.

Mommy ta fashe da kuka ta na ?ara karanto addu'o'i gami da janyota jikinta ta rungume ta na ?o?arin hanata lan?washewar sai dai kash abin ya ci tira.
Ta Webi kusan minti shidda cikin wannan halin sannan kuma jikin nata ya dawo daidai ya wani saki lakaf kamar gawar da ta samu ziyarta lahira yanzu.

wani azababben kuka ta saki ta na cewa "Mommy zan mutu kaina zai fashe wayyo Allah na" jin haka ya sa Mommy ta ?ara rungumota ta na cewa "Ki yi ha?uri Husna ai cuta ba mutuwa ba ce, ki yi ta addu'a za ki samu lafiya in sha Allahu." inaa kukanta kawai ta ke yi ba ji ba gani don ko fahimtar inda Mommyn ta dosa ba ta yi ba bare ma ta yi addu'ar, su na nan zaune Mommy na Kuka Husnee na yi har wani lokacin kafin ta saki kai ta kama ciki ta na kukan cikinta na ciwo, ita dai Mommy ta ga tashin hankali, Ayatul Kursiyyu gami da Suratul Ba?arah da sauransu take karantowa in ta saki wancan sai ta kama waccan gabaki Waya ta burkice.
Ta na cikin haka ta ji wani hucin zafi ya bugeta itama ta zame ta kwanta a wajen a sume.

Russlan ne ya yi dirar mikiya a wajen ko ?asa bai sauka ba ya fizge Razia daga jikin Husnee su ka yi sama, nan take Husnee ta ji kamar cirar ?aya sai dai ko yatsanta ta kasa motsawa ji take kamar an daddatsa ta da adda, idanunta ma kansu sun yi mata nauyin da ko buWe su ta kasa yi, Mommy kuwa itama ta na kwance a sumenta ba me tashin wani tsakaninsu.

Su na cikin wannan halin Muneeb ya shigo fakam-fakam tare da sallama bai bari an amsa ba ya ci gaba da cewa "Mommy kin ganni da wuri yau fita zan yi." da yake hanyar banWakin tsakar gida ya nufa sam bai lura da su ba sai da ya le?a banWakin ya fito da nufin ajiye wayoyi da tarkacen jikinsa kafin ya shiga wankan, nan fa idanunsa su ka yi alaragab da su a sheme.
cikin hanzari ya yi kansu ya na tambayar lafiya.

Ya na taSa Mommy ya ji ta a sume zuciyarsa ta bada rimm!! idanunsa ya kai kan Husnee da take zubda ?wallar wahala ita ma ?ar siriri take bin gefen idanunta, hankali tashe ya ce "Ke Husnee lafiya??" ba za ta iya magana ba don haka bai samu amsa ba.
Ruwa ya lalubo ya yayyafawa Mommy ai kuwa ta ja wani gwauron numfashi ta sauke ajiyar Zuciya sai kuma ta ci gaba da kuka ta na cewa "Ina Husna, kar dai sun Wauke mini ita" cike da mamaki da tsoro Muneeb ya ce "Me ya faru Mommy?? su waye za su Wauketa??" ba tare da ta dena kukan ba ta ce "Yauwa gwara da ka dawo, ashe da gaske Aljanu sun hau Husnee kar ka ga irin wahalar da su ka bata" ta yi maganar ta na ?o?arin tashi zaune, temaka mata ya yi ta Zauna, ganin Husnee kwance a kusa da ita ya sa farin ciki ya kamata, goge hawayen ta fara yi ta na cewa "Kalleta nan kar ka ga yadda su ka dinga cukurkuWa ta kamar ba mutum ba."
sunanta ya kira ya na shafa gefen fuskarta cikin tausayawa, a hankali ta buWe ido ta na kallonsa sai kuma ta Sare baki ta kama kuka ta na cewa "Jikina ciwo ya ke yi ji nake kamar zan mutu!" ya ce ''Sannu kin ji, Allah i sauwa?e ki dena cewa za ki mutu ai mutuwa sai lokacinta ya yi." Mommy ta ce "?auketa ka mayar da ita Waki, laifina ne ni nace ta fito." ta faWa ta na goge hawaye.
Rungumarta ya yi ya kaita Waki ya kwantar ya na ?ara jaddada mata sannu.


SHARE FISABILILLAH



Na KuWi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ?arin bayani =?I?
AN FARA PAYMENT

*??INDO*
[8/21, 11:31 PM] INDO: *>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 15

??
Ayeesha Abdulkareem INDO



*M.W.A>؅?*




A Sangaren su Russlan kuwa ya na yin sama da Razia bai zame ko ina ba sai gaban Uban Dawa, ya na zaune kan haWaWWiyar kujerarsa ta zinare ya na jiran dawowarsu.
Russlan ya dur?usa a gabansa gami da cewa "Ga ta nan Father" cikin Sacin rai Father ya ce "Razia! waye ya ?antaki daga Waurin da aka yi miki har ki ka fita?" Cikin shashshekar kuka ta ce "Risslan fa......" dakatar da ita ya yi ta hanyar Waga mata hannu, shiru ta yi ta na ci gaba da Sarza kuka kamar za ra mutu don yinsa.
ba tare da damuwa da hakan ba ya ce "Maza a ?ara Waureta ba na bu?atar ?ara ganinta." Russlan ya ce "To" kana ya dam?eta ya mayar da ita keSantaccen Wakin da aka Waureta a wancan lokacin, ta na kuka ta na komai amma haka ya yi mata banza ya aiwatar da umarnin da aka ba shi don kuwa shi ma ta gama kaishi ma?urar Sacin rai.

Akhiee abin duniya duk ya ishe shi, koda Russlan ya ba shi labarin abinda ya faru ya kasa ma bambance tsakanin Husnee da Razia waccece ta fi hauka, a gefe guda kuwa ya ji daWin zuwan Razia kan Husnee don kuwa ta zo a kan lokaci tinda har ta yi silar faWuwar tsafin da aka turo mata ?asa.

Bayan kwana uku

Hajiya Laure da Hajiya Saudah an koma wajen boka ana ta murna don duk a tunaninsu

11 / 25