Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 25

54K to 57K   out of 73.5K words

Wan tsagaitawa ya yi kafin ya ci daba da ce "Ba lallai na samu halartar Jana'izarta ba; ki FaWawa Inna ba na so ?ananun Yaran nan su san abinda ke faruwa."
Zulaihart ta amsa da "To" gami da ci gaba da kukanta.

Ajiye wayar ya yi ya na ci gaba da tunane-tunane, ji yake kamar kansa zai yi tsawa ya tarwatse sabida tsabar ruWanin da ya shiga.
Wata muguwar bugawa Zuciyarsa ta shiga yi, wadda ke tabbar masa ba lafiya ba, karaf Husnee ta faWo masa a rai, idanunsa ne su ka ?ara girma sabida razani. Daidai lokacin ?aya daga cikin Dakarun Aljanunsu ya ?araso wajen bayan ya gaishe shi ya sanar masa halin da Husnee take ciki.
Rai Sace Akhiee ya nufi wajen Tare da Dakare Adnanu.

"Yau zan kasheki in huta da Sacin ranki!!! Shishshigin naki har ya wuce yi masa magana sabida ke mayya ce sai da kika sa ya aureki; yau taki ta ?are sai dai in na kasheki nima ya kasheni"
Tankar Ya?i ta faWa ta na zazzarowa Husnee garadan idanunta da su ka ci kwalli kamar a ciki aka haWashi, Fuskarta sam babu alamun wasa.
Zuciyar sai bugun sama da ?asa take tamkar za ta zillo ta faWo ?asa, sake fashewa ta yi da wani irin kuka me cike da tsoro razani da rashin sanin abin yi ga uwa uba nadamar kuskuren da ta yi na fitowa.
Jikinta duk ya Wauki karkawa kamar ana kaWawa Wan tauri gangi, magiya ta shiga yi mata gami da ban ha?uri akan kar ta kasheta, ita kuwa tamkar shaiWaniya haka ta yi kunnen uwar shegu da ita, Zuciyarta ta riga ta ?e?ashe sam ba ta jin wani Wumi-Wumin imani bare tausayi.

"Rufe mini baki kafin na soka miki wu?ar nan a ciki!" ta faWa cike da tsanar Husnee.
a memakon ta yi shirun sai ta ?ara Sarke baki ta na cewa "Wallahi ba zan kuma fitowa ba don Allah kar ki kasheni ki ?yaleni ba zan kuma ba."
Tasss!!!!! ta wanketa da wani bahagon mari wanda ya sa kukan nata da maganar da takeyi su ka Wauke a lokaci Waya, gabaki Waya wutar kanta ta tsaya cak!!, ba ta gama dawowa hayyacinta ba ta ?ara wanketa da wani zazzafan marin.
Husnee ta dur?ushe kan guiwoyinta ta na girgiza kanta da ke wata muguwa hajijiya, a take gefen bakinta ya fashe, fuskarta kuwa ta yi kozai-kozai shatin yatsu sun fito raWa-raWa kamar sa yi magana.
Cikin rashin imani ta Waga wu?ar hannunta gami da kaiwa Husnee suka a gefen wuyanta.
Husnee ta rintse ido da ?arfi gabaki Waya ta sadda?ar, cikin Zuciyarta kuwa Kalmar Shahada take maimaitawa.

Caraf!!! ta ji an ri?e hannun nata katamau sabida azabar matsar da aka yi masa tamkar ?ashinta zai tsage.
Wata ?ar ?aramar ?ara ta yi gami da sakin wu?ar ta faWi.
Juyowa ta yi a zafafe don ganin wanda ya ri?eta, rass! Zuciyarta ta buga yayin da idanunta su ka yi alaragab da na Rislan.
Yaranta kuwa su na ganinsa su ka fara gudun ceton rai sai waigawa ta yi ta ga babu su ba alamunsu.

Ta rasa yadda za ta yi don haka ta fashe da kuka ta na cewa "Wallahi indai ba ka Aureni ba sai na kasheta na kashe kowa nima na kashe kaina."
A fusace ya watsar da ita can gefe ta zube kamar kayan banza,
Ko kallon inda take bai kuma yi ba, Jiki na tsuma ya matsa inda Husnee ke dur?ushe ta na wani marayan kuka.
Cikin zafin nama ya finciko hannunta ta kusa faWuwa amma da yake ?azamin ri?o ya yiwa hannunta sai ta tirje.
tatass!! tass!!!!! ya watsa mata wasu lafiyayyun maruka har guda biyu a jere, cikin mugun Sacin rai da zafin Zuciya ya ce "Ban ce kar ki sake ki fitowa ba?? Na rantse da Allah ko me ya sameki sai ya samu Danginki, na rantse da Ubangijin da ya halicci Duniya akan danginki zan Wauki Fansa; kuma indai ba za ki ji magana ba to za ki gamu da Sacin raina."
Ido kawai take zarewa domin kuwa zuwa yanzu azaba da tashin hankalin da su ka mamayeta ba za su barta ta yi kukan ba.
Jan hannunta ya yi gami da cewa "Mu je na mayar da ke gidan; kin san Allah kika ?ara fitowa sai ranki ya yi mummunan Saci, kuma ni faWar zan yi nake yi, ba na shan Alwashi, indai na ce zan yi to zan aikata ."
ba ta iya amsawa ba shima daga haka bai ?ara magana ba ya shiga janta kamar kara, sauri take yi iya yinta amma duk da haka sai tuntuSe take yi kamar za ta faWi sabida ya fi ta zafin nama.

Bai damu da ana kallonsu ba haka ya dinga ratsa layika da ita har su ka dawo ?ofar gidansu sannan ya tsaya.
Idanu ya zuba mata tamkar me yi mata kallon ?arshe yayin da hannunta ke ma?ale cikin tafin nasa hannun.
Sun daWe su na kallon kallo kafin ya kawar da kai, ya sassauta murya sannan ya ce "Asma'u in na rasa ki ne akwai tashin hankali, zan yi Sarna sosai domin kuwa haukacewa zan yi!!! don Allah ki tayani kula da kanki kar ki bari a illata mini ke."
?asa ta yi da kai ba tare da tace komai ba, sai a lokacin zafafan hawayen da ke kawo-kora a cikin idanunta su ka samu nasarar zillowa su ka yo wajen.
lumshe idanunsa ya yi gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya.

A hankali ya buWe idanun gami da zubawa kyakkyawar fuskarta su, cikin wata irin murya me rikita lissafin me saurarenta ya ce "Da gaske nake Asma'u, ba na iya Soye miki sirrin Zuciyata, tabbas idan aka cutar da ke an yi mini Lahani, ki tausayawa Mijinki Asma'utah!!."
wani mugun haWaWWen shauki ne ya ratsata ta ko'ina, ba ta san lokacin da ta FaWa cikin faffaWan ?irjinsa ta na ?ara sakin wani sabon kuka me ?unshe da wani salo da sirrin shagwaSa ba.
Dimm!!! dimm!!! bugun Zuciyarsa ya ?ara sauya salo, hannayensa ya sa duka biyun ya zagayota gami da gyara mata kwanciya a jikinsa, cikin sassanyar murya ya ce "Ba na son jin kukan nan Asma'u, ko so kike Zuciyata ta karye??"
ba tare da ta dena kukan ba ta girgiza masa kai.
A hankali sautin bugun Zuciyarsa ya fara sauya mata tunani hakan ya sa ta yi shiru ta na sauraren Zuciyar tashi.
Jin ta nutsuwa ne ya bashi damar zaro wani siririn Diamond ring Waya daga cikin Zobuka goma da ke hannunsa, ya ri?o hannunta na dama ya zubawa zaratan yatsun natsa ido kafin ya zura mata shi a na kusa da na tsakiya, wato na kusa da Wan ?aramin yatsa.
?o?arin zamewa daga jikinsa ta fara yi amma ya ?i bata dama, cikin muryarsa me sanya mata nutsuwa a duk lokacin da ta saurara ya ce "Kasancewarki tare da Zoben nan tamkar kasancewa tare da Mijinki ne, kar ki bari ya fita daga hannunki komai wuya komai rintsi."
GyaWa kai ta yi alamar eh, don haka ya ya buWe hannayensa gami da cewa "To jeki gida, kar ki ?ara fitowa fa."
"To" ta faWa tare da sauke nannauyar ajiyar Zuciya.

Ya na tsaye har ta shige gida sannan ya Sace ya yi nasa wuri.

Hajiya Laure Da Hajiya Saudah.....
Wani haWaWWen Sa?ago su ka gani ya na tinkaro su, ya na tafiya cokal!! cokal!!! cokal!!!! da siri-sirin ?afafunsa tamkar za su karye, sai uban kai rangwameme kamar zai rinjayi Wuyansa, gashi ?wargwan-?wargwan zallar ?ashi sai tarin muni, ga ramin ido zuru-zuru ga ha?ora kacar!!! kamar tsangayar ?ashi.
Wannan Dalilin ne ya sa su ka ?ara shiga Firgici bayan wanda suke ciki, har ya jawowa Haj Saudah suma.
Hajiya Laure kuwa kururuwa kawai ta ke yi idanunta a rintse.

Ta daWe cikin wannan yanayi na tashin hankali da fitar hayyaci idanunta a rintse, bayan ta Wauki lokaci me tsayi ba ta ji ta mutu ko kuma ta shiga hannun Sa?agon ba ya sa ta sassauta ihun da take yi ta fara buWe idanunta da suka WaWWaure suke wata azaba tamkar an yi dakan Barkono a cikinsu, a hankali a hankali har ta buWe idanun nata garas! ta shiga ?arewa wajen kallo, ganin babu wannan sa?ago ba alamunsa ya sa ta sakin ajiyar Zuciya wadda ta tawo tare da wani sassanyan kuka na daWi.

Da rarrafe ta ?arasa wajen da Haj Saudah ke kwance kamar gawar sababi, ta fara jijjigata ta na kiran sunanta amma shiru, wani sabon kukan ta saki ta na cewa "Wayyo Allah yanzu ya zan yi idan Saudah Mutuwa ta yi ai na shiga uku."
Zama dafa'an ta yi ta na rero baitin kuka kamar don shi aka kawota Duniyar. Bayan wani Wan lokaci ne ta tuna da Motar da su ka zo ba za a rasa ruwa ba don haka ta tashi ta na jan ?afafunta da su ka yi tsami ta isa wajen Motar, cikin sa'a ta na dubawa ta samu ta Wakko ta dawo wajen Haj Saudah ta yayyafa mata ruwan. A firgice ta farka ba tare da ta jira wani abu ba ta mi?e za ta ci gaba da gudu, Haj Laure ta sa iya ?arfinta ta ri?ota ta na cewa "Ki tsaya mana, tinda Allah ya sa kin farko ki yi maza ki shiga Mota mu gudu."
Haj Saudah ta na jin haka ta yi saurin buWe Motar ta shige ta rufe baram don kar ma wani abun ya biyota.

Haj Laure ma cikin sauri ta Wakko wata babbar Darduma da ta gani a cikin Motar ta Waura a ?ugunta domin Soye Sacin da kayan jikinta su ka yi.

Haj Saudah ta zama ba baka sai kunne, Haj Laure ma ba magana, tinda ta fara tu?a motar Ta ke ?an addu'o'inta ta kama waccan ta saki ta kama waccan.

Sai da ta biya ta ajiye Haj Saudah ko sallama ba su yi ba ta shige gidanta, Haj Laure ma ta ?arasa nata gidan da ?yar don kuwa tuni zazzaSi ya rufeta.

Yazeed na gama yin parking itama ta yi parking ta fito da kyar da kyar, turuss!! ya tsaya ya na kallonta sabida ganinta wujiga-wujiga kamar an ?watota daga bakin kura, ga Darduma da ta Waura a ?ugu jikinta ko mayafi babu.

Cikin tsananin mamaki ya ce "Mommy! meye haka kuma?? lafiya??"
wata sahihiyar kunya ce ta lulluSeta sai ta ma kasa Waga ido ta kalli Wan nata bare ta san amsar da zata bashi, suSur-suSur ta yi cikin gidan ba tare da ta saurare shi ba.

Talatu ce kawai a Falon a lokacin da ta shigo, Talatu ta zuba mata ido cike da mamaki, "Sannu da zuwa Hajiya" ta faWa ta na ?ara zuba mata ido.

Banza ta yi mata, tsabar ba?in ciki da takaici ji take kamar ta haWiyi Zuciya ta mutu, kai tsaye ?akinta ta nufa daga can ma ta wuce Toilet domin gyara jikinta.

Yazeed kuwa tinda ya saki baki ya fara tunane-tunane sai da ya kwashi lokaci me tsayi sannan ya samu ?warin guiwar shiga cikin gidan, Zuciyarsa cike taf da tambayoyi akan Mommynsa.

Husnee ta na shiga cikin gidan ta yi kaciSus da Momy a tsaye sai safa da marwa take yi hankalinta a matu?ar tashe.

RaSe-raSe ta fara yi Zuciyarta na tsananin bugawa, daga ganin yadda ran Mommy yake a Sace ta san itama nata ran zai Saci.
Mommy kuwa ta na ganinta ta yo kanta ta na cewa "Zo Dan ubanki!! wato kin kangare ba kya jin magana ko??"
Cikin rawar murya ta ce "Don Allah Mommy ki yi ha?uri ba zan ?ara......" shiru ta yi sabida fizgota da Mommy ta yi ta fara Wirka mata dundu da iya ?arfinta ta na yi ta na cewa "Dan Ubanki ashe da ?afarki ki fita? kin tashi hankalina na zata ma sace ki aka yi; gidan uban wa kika je???"
Kuka kawai ta ke yi ta na bata ha?uri amma ba ta fasa ba sai da ta gaji tukunna ta saketa, a hakan ma ba ta ha?ura ba ta ci gaba da faWa kamar ta ari baki.

Husnee ta ja ?afarta da kyar za ta wuce ciki ta na tafe ta na sharar ?walla, ?aga hannun da ta yi ya bawa Mommy Damar ganin Zoben da Akhiee ya bata, ta sanya salati kafin ta ci gaba da cewa "Zo in gani, uban waye ya baki Zoben nan?? wato wajen ?an iskan Yaron nan kika je ko? sabida ke ga gantalalliya mara mafaWa, to ba dani ba zo ki cireshi ko kuma in yi miki dukan kawo gishiri yanzun nan."
jin abinda Mommy ta ce ya sata sake fashewa da wani sabon kuka me cike da tashin hankali gami da tausayin kanta.
?oye hannun ta yi a baya ta na ce "Don Allah Mommy kar ki cire mini ki bar mini shi, wallahi in na cire ransa Saci zai yi!!!".
Kuka take yi tamkar ranta zai fita amma hakan bai sa Mommy ta tausaya mata ba.
Cikin tsawa ta ce "Ni kike gayawa ransa xai Saci?? iye??? ni abokiyar wasanki ce ina magana kina magana???"
Girgiza kai ta shiga yi domin kuwa ta kasa magana sabida kukanta da ke ?ara ?arfi.

Fizgota Mommy ta yi ta na ?o?arin cire zoben, Husnee kuwa ta dam?e hannunta katamau ta na kuka harda shiWewa.
Daidai lokacin Muddassir ya yi sallama ganin su na ta kici-kici ya sa shi saurin ?arasowa ya na cewa "Lafiya kuwa, me ya faru??" cikin Sacin rai Mommy ta ce "Wai Yarinyar nan sabida ta rainamu ta mayar da mu mutanen banza ita ce da fita ta tafi wajen wannan Wan iskan harda karSar zobe a hannunsa?, Ni fa ba za ta jawo min zagi ba gwara in sha?areta in ta mutu ma dan ubanta ba ni da asara."
Karyar da murya ya yi kamar wani mutumin kirki ya fara cewa "Haba dai Mommy, don zobe dai? don Allah ?yale mata mana haba? ba wani abin tashin hankali ba ne, shi so ai ba a yi masa shamaki ku barta ta rayu da wanda take so don Allah."
Mommy ta ce "Haba kai ma faWe kake yi!, ina sane dai da hankalina ka san ba zan aurar da ?ata a inda za ta dinga ci da haram ba, Yaro Wan ta'adda, ta?adari, Wan iska, Wan daba shi kake cewa mu bashi ?armu? "

"To wai Mommy ba Allah ne me shiryawa ba? addu'a ya kamata mu yi masa ba mu dinga kiransa haka ba, don Allah Mommy kwantar da hankalinki; ke Husnee wuce ciki" ya ?arasa maganar ya na kallonta, jin haka kuwa ya sa ta yi zuruf ta wuce ta na ci gaba da razga kuka.
Mommy ta raka bayanta da harara kafin ta yi ?wafa alamar zamu ?ara haWuwa.
Muddassir kuwa kwantar da kai ya yi ya dinga rarrashin Mommy gami da ha?ur?urtar da ita, ba don komai ba sai don ya na son su cimma manufarsu akan Akhiee.
Husnee duk da hankalinta ba a jikinta yake ba ta na jinsu, kuma ta fahimci Muddassir ya na goyon bayanta don haka ta wani gefen farin ciki ya lulluSeta.

Kasancewar Sheikh Auwal ya kira shi ya sa ya shigo gida da wuri tin ?arfe shaWaya na dare, Lokacin wasu daga cikin Yaran Gidan sun yi bacci, Wasu kuwa
Su na zazzaune curko-curko a tsakar gida kowa na jiran shigowarsa, wasu sun shirya yi masa rashin mutunci wasu kuwa gulma ce ta tsayar da su don su ji yadda za ayi.
A tsaye ya tsaya fuskarsa ba walwala a ta?aice ya ce "Ga ni" a tsawace Yaya Babba ya ce "A tsaye za ka tsaya mana sabida rashin Wabi'a?"
Sai da ya doka dogon tsaki kamar ya tsaga gini sannan ya dur?usa cike da tsanar ?an uwan nasa ya ce "A faWa mini abinda ya sa aka nemo ni, idan kuma bala'in ne ya motsa kowa sai ya yi nashi duk zan iya Wauka."
Yaya Aminu ya rarumo takalmi a kusa da shi ya jefo masa gami da cewa ''Buhun Ubanka! mara kunyan banza shashasha; Baba Sa'idu bashi takardar nan ya ga tsiyar da ya jawowa kansa."

Baba Sa'idu da ya zuba tagumi da duka hannayensa sai a lokacin ya ce "Uhm! to" Takardar ya mi?a masa gami da cewa "Yarinyar da ka je ka Aura to iyayenta ne su ka kai ?ararka Kotu Ranar Alhamis me zuwa za a zauna sai ka tanadi abin gaya musu, Bai kamata ka yi haka ba Muhammad, ka ga mu ba mu san ka yi ba amma ka jawo mana maganganun da zagi na jama'a, gidanmu gidan mutunci amma ta sanadinka ana yi mana wani banzan kallo, ka ?o?arta ka saki yarinyar nan tin kafin ka ?ara jawo mana wani mugun tabon."
A duniya in akwai abinda Akhiee ya tsana to na biyunsa a ce sanadinsa mutuncin gidansu ya zube, cikin Sacin rai ya fizgi takardar sannan ya ce "Ba kotu ba ko Duniyar za su haWo ta taru a kaina ba zan saki Asma'u ba bare

19 / 25