Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   20 / 25

57K to 60K   out of 73.5K words

wata Kotu, gwara ma ku dena wahalar da kanku kowa ya je ya yi baccinsa, Asma'u tawa ce saSanin ni kuma sai dai Mutuwa domin zan zubda jini akanta.

Inna Huwaila Matar Baba Sa'idu ta sa salati da sallami kafin ta ce "Kai Wannan ka ji tsoron Allah, wai ni Huwaila ina ganin masifa a gidan nan!!, Yaro Waya amma ya zama wake Waya me Sata miya??"
Ai kuwa kamar jira su ke yi ta buWe musu hanya nan fa wasu daga ciki suka fara sako tasu maganar, duk cikinsu ba me faWar da daWi sai ba?a?en maganganu abin har ya wuce kansa ya koma kan Mahaifiyarsu, wasu ma cewa suke yi ba Jinin gidan ba ne.

Sheikh Auwal dai da abin Duniya ya ishe shi sai ya zame jiki ya wuce Turakarsa, ya na shiga ya nemi wajen zama dirshan sannan ya bawa kukan da ke cin ?arfinsa damar fitowa.
"Allah ka fi mu sanin abinda ke tattare da Yaron nan, Ya Allah ka sani Mahaifiyarmu ba halinta ba ne haka Mahaifinmu ma Ya Allah indai ba jininmu ba ne Allah ka nesanta mu da shi ka fitar da shi daga cikinmu ka bayyanar da gaskiyar asalinsa."
Addu'ar da yake yi kenan a cikin kukan nasa, Zuciyarsa cike take taf da ?unci da tarin damuwa ga zafi da ?unar abinda ke faruwa a cikin wannan Babban gida nasu.

Zara kuwa ta kasa fitowa daga Wakinsu, ta na jin yadda suka ?are masa tatas ba abinda ta iya yi sai aikin kuka, har cikin ranta ta na ba?in cikin irin abinda ake yiwa Wan uwan nata.

Sai da ya gama saurarensu Waya-bayan-Waya sannan ya kakkaSe rigarsa ya tashi, kai tsaye Wakinsa ya wuce ya zauna gefen gado ya zuba tagumi, jin idanunsa yake yi tamkar an Wora su akan garwashi ana gasa su, Zuciyarsa kuwa har wani turnu?u take yi tamkar za ta fito ta baki, da zai iya yin kuka da ya yi ko zai samu salama sai dai kash!!! shi da kuka sun riga sun yi hannun riga tin kafin Mutuwar Mahaifiyarsa.

"Come hare my son!" muryar Mother ce ta karaWe kunnuwansa ya yi saurin ware idanunsa domin ganin ta inda ta Sullo. Kasancewar Wakin ba haske ya sa ba ya ganinta sai dai hasken idanunta da su ka yi kalar Golden ya iya gani.

Da sauri ya mi?e ya nufi inda take ta yi saurin rungume shi tsam!!!!. nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke Kafin ya fara maga cikin rarrabewar Murya "My Mo...therh!!!... me..yasa..... suke yi min haka??? Shin da gaske..... ni ba.....Jininsu ba ne???????"
Yadda yake maganar ba ?aramin taSa Zuciyarta abin ya ?ara yi ba, ranta ya ?ara Saci Zuciyarta ta ?ara dugunzuma, a gefe guda kuwa tsananin tausayin Wan nata ya na ?ara taso mata, ba ta iya bashi amsar tambayarsa ba sai dai ta ce "Yau ban amince ka kwana a gidan nan ba, ka kasance tare da ni ?ana....."
Ba ta jira abinda zai kuma cewa ba ta Wauke shi su ka Sace daga Wakin.







*??INDO*
[9/6, 7:41 PM] INDO: *>ػ?S-K>ػ?*
Ep 22



Tinda ta Waukeshi bai ?ara sanin inda kansa yake ba har sai da Asbah ta yi da ya ji Masallacin cikin gidansu an yi kiran Sallah sannan ya farka.
Tin kafin ya buWe idanunsa ya ji Wumin Mutum a kusa da shi, ya yi shiru ya na sauraren Bugun zuciyarta da ya tabbatar masa ba kowace ba ne face Razia. Cikin nutsuwa ya sauke wata nannauyar ajiyar Zuciya kafin ya buWe idanunsa ya Worasu akan kyakkyawar fuskarta.
Bacci ta ke yi cikin mutsuwa da kwanciyar hankali, kallo Waya ya yi mata ya gane ba ?aramin jin daWin baccin take ba don da alamu ma ta daWe ba ta yi me daWinsa, a take kibiyar tausayinta ta soki Zuciyarsa, ya zuba mata ido tamkar ba zai dena kallonta ba, ya daWe cikin wannan yanayin kafin ya ?ara janyota jikinsa ya ringumeta tsam, ya na jinta har cikin ransa.
Cikin baccinta ta ?ara jin sauyin yanayi don haka ta ?ara du?un?uneshi ta ja mumfashi ta sauke ta ci gaba da baccinta.

Mother ta ce shigo ?akin cikin suffar Mage, bayan ta zo daf da Gadon ta koma suffar Mutum, cikin tattausar muryarta ta ce "Rislan! kar ka biyewa Razia ka makara a Sallah fa."
Lumshe ido ya yi gami da sauke wani gwauron nishi kafin ya yi magana tamkar wanda aka yiwa dole "Uhm! Uwa zan tashi; ba na so na nesanta da ita ne ta farka."
Mother ta murmusa kafin ta ce "Abinda ya zama dole ne ?ana, a Masallaci fa har an idar da Sallah."
Bai ce komai ba ya janye Razia daga jikinsa a hankali ya gyara mata kwanciya sannan ya sakko ba don ransa ya so ba, haka kawai yau ya tsinci kansa da son kasancewa tare da ita.

Ya na idar da Sallah ya yi musu Sallama ya wuce wajen su Rahma don jin yadda suka kwana.

Yau Ta kasance Ranar Alhamis, Ranar da wasu ke Wokin zuwanta wasu kuwa su na cike da fargabar ganinta.

Sheikh Auwal, Babban Yaya, Baba Sa'idu, Akhiee

Daddy, Mommy, Muneeb, Muneer, Husnee...

Malam Kabiru, Malam Usaini

Duk sun hallara a cikin Kotun yayin da ta Wauki shiru kowa ya mayar da nutsuwarsa akan abinda ke faruwa a cikinta.

Ana kammala sauraren ?arar Wasu aka karanto ta su Akhiee, Me Shari'a ya bu?aci Matar da Mijinta su fito.

Bayan sun fito inda aka tanadarwa duk wanda zai yi magana su ka tsaya, Mai Shari'a Ya yiwa Husnee tambaya akan da gaske ne an ?aura Aure ta amsa masa da eh.
Sannan aka dawo kan Akhiee aka tuhumeshi akan amsa laifinsa sai dai shiru bai ce ?ala ba, juyin Duniya ya yi musu banza har mai Shari'a ya gaji ya Waga ?arar tare da cewa Akhiee ya nemo Lauya.

Da haka aka tashi ba tare da an cimma wata matsaya ba kowa ya san inda dare ya yi masa tare da tunani iri daban-daban, musamman a Sangaren Husnee wadda ta cika da tsoro da firgici sabida jin ya yi shiru, ta na matu?ar tsoron ya ce zai saketa.

Akhiee kuwa ko ta kansu bai ?ara bi ba shima ya kama gabansa, Su Yaya Babba sai faWa su ke yi kamar za su ci babu, shi dai Sheikh Auwal ya yi musu banza.

Hajiya Laure
Sanye take cikin lintsumemiyar Atamfa tsadaddiya Winkin riga da Zani ta cokara Wauri ture ka ga tsiya.
Cikin takun ?asaita ta fito Falo Wagwas-Wagwas kamar budurwar agwagwa. Ma'u da Talatu su na ta ?an gyare-gyare kasancewar Yamma ce, kafin ta zauna ta kallesu fuska a dake cikin nuna ?yama da wula?anci ta ce "Menene haka? wannan aiki ku ke yi ko iskanci?? wai ba na ce kar wannam ?azamar ta ?ara shigo mini Falo ba ma??"
Ta ?arasa maganar ta na tsare Ma'u da idanu. Ma'u kuwa tin da ta ganta jikinta ya Wau karkarwa domin kuwa mugun tsoronta gami da tsanarta ta ke ji, ko hanya ba ta son haWawa da ita a yanzu.
Talatu ta rissina gami da cewa "Ayi ha?uri za mu gyara."
Dogon tsaki ta lafta kafin ta ce "?azamar banza tarin najasa; za ku fice ku ban wuri ko sai na daddallawa Yarinya mari?? ?a?an matsiyata."
Jiki na rawa Ma'u ta yi gaba ta na kuka ?asa-?asa Talatu ta bi bayanta cikin sanyin jiki.

Hajiya Laure ta yi ?wafa kafin ta karkace ta yi jaSar a kan Sofa. wani mugun ihu ta zurmu?a jin ta zauna akan wani abu tamkar Allura, azaba ta ratsata har tsakiyar kanta, a dur?ushe ta mi?e ta ma kasa tashi tsaye sabida azaba gabaki Waya mazaunanta sun Wauki wuta, lokaci guda idanunta su ka ciko da hawayen azaba.

Sai da ta Wan huce sannan ta juya ta dudduba inda ta zauna Win ko za ta ga wani abu sai dai fayau ba wani abu ba alamunsa.
Canja mazauni ta yi zuwa kan kafet don kuwa ta ji attaruhu ko za ta ?ara zaman kan kujerar ba yanzu ba, a ?asan ma a karkace ta zauna ta na yi ta na yatsine fuska don kuwa har yanzu ba ta dena jin zafi ba.

Ta na nan zaune ta na hutawa ba a fi minti biyar ba ta ji wani irin taku ?waras-?waras ya na tinkarota, ta shiga kalle-kalle amma ta ga fayau kamar ba a taSa halittar mutum ba, tsoro da firgici su ka Warsu a Zuciyarta lokaci Waya, Talatu ta fara ?walawa kira da tunanin ko itace a wajen, jin shiru kuma ga takun ta na ji ya sa ta yun?ura ta mi?e cikin sauri ta nufi hanyar da zata bar Falon.
Garam!! ?ofa ta rufe, nan take wata muguwar dariya irin ta Boka Barore ta karaWe Kunnuwanta, Ihu ta fara kwararawa sai dai kash!! ta na farawa ta ji kamar an sa buredi an toshe mata ma?ogoro muryar tata ta dena fita.

Inuwar Mace ta gani a gabanta ?ar siririya sai yalwar gashi har ?ugu shima ga inuwarsa nan buzu-buzu, Haj Laure ta ?ara zazzaro ido gwale-gwale kamar sa faWo ?asa, Zuciyarta na wani mugun duka tamkar ana surfe da sussuka a cikinta.

Da kyar ta samu ta taka da gudu don komawa Bedroom, ta na zuwa ?ofar bedroom Win taga wannan inuwar a gabanta, sai juyi take ta na kwarkwasa ga Wan ?ugun nan tamkar na babe sai faWin mazaunai ?an ciri-ciri.
Wani mugun burki ta ja wanda ya sa ta kusa shiWewa sabida Salon bugun Zuciyarta da ya canja.

Tsere su ka shiga yi ita da Inuwar a Falon ta na gumi ta na kuka ta na majina ta na yarcewa ita kuwa Inuwa ta na ci gaba da razanata, sai da ta galabaita sosai har ta kai ba ta iya tafiyar ta zube a wajen turuss!! sannan inuwar ta matso daf da ita ta na wata mahaukaciyar dariya, ba tare da ta dena dariyar ba take magana cikin murya marar daWin ji "Ba a raina aikin Boka Barore!!!, sannan ba a cin Amanarsa a canja wuri, ba a zaginsa ko a bayan idonsa!!!!, idan ya fara yiwa mutum aiki har sai ya yi nasara yake denawa ba zai taSa ?yale ku ku je wajen wani Bokan bahahahaha!!!!" ta ?arasa maganar gami da ?aro sautin dariyarta, Ta kai minti Waya a haka sannan ta Sace tamkar ba ta taSa wanzuwa a wurin ba.

Haj Laure ba ta iya tashi ba sai ?ara bajewa da ta yi ta kwanta ta saki wani Wanyen kuka me matu?ar taSa Zuciya.

Su Ma'u su na fita su ka ci karo da Yazeed ya na ?o?arin shigowa, ya na ganinta tana kuka ya yi caraf ya ri?o hannunta, a zafafe ta fara ?o?arin fizgewa sai dai ya hanata damar hakan, Cikin sassanyar murya ya ce "Ki nutsu don Allah ki faWa min abinda ke damunki, Mommy ce ko???"
A tsiwace ta ce "Ni ka ?yaleni, ka sakar min hannuna ni ba ?ar iska ba ce wallahi, kuma zalumcin da aka yi mini Allah zai saka min."
"Ke Talatu yi tafiyarki" ya faWa ya na kallonta, ta sunkuyar da kai sannan ta ci gaba da tafiya.
mayar da hankalinsa ya yi kan Ma'u tamkar me shirin fashewa da kuka ya ce "Don Allah ki yi ha?uri ki saurareni, ki karSi kukana sannan ki ji?aina Ma'u! maganar gaskiya kin jefani cikin wani yanayi, na rasa nutsuwata ba dare ba rana tunaninki nake yi, ina son sanin abinda ke damunki."
Cikin tsananin tsanarsa ta ce "Ba zan taSa gaya maka abinda ke damuna ba azzalumi, kuma ka ?yaleni ba na son ganinka na tsaneka!!!" ta yi maganar ta na kuka tamkar ranta zai yi fitar burgu ya bar gangar jikinta.

KiWimammun idanunsa da su ka rikiWa zuwa kalar ja ya zuba mata na Wan lokaci kafin ya fara magana tamkar zai yi kuka "Ma'u gareki sam ban zamo azzalumi ba kuma ba zan taSa zamowa Azzalumi gareki ba, burina kullum na inganta rayuwarki domin ina bu?atar rayuwa tare da ke, Ina...sonki Ma'u, ko da za ki tsaneni hakan ba zai sa na canja ba, sai dai in kasheni ki ka yi shine na san dole zan barki, kuma in na mutu ki sani na mutu da tsananin Sonki, ko da ba ki kasheni ba idan na mutu ko a yanzu ko anjima ke ce silar mutuwata domin ba ni da wata damuwa a yanzu face ke!!" ya ?arashe maganar cike da son nuna asalin gaskiyarsa.

"Ni ba zan taSa yarda da kai ba, kuma ba zan taSa sonka ba, na tsaneka!! na tsaneka!!!! kuma tsakanina da ku sai Allah ya yi mana Hisabi, ni ka sake ni in tafi."
Gudun zuciyarsa ne ta ?aru, lokaci guda yanayinsa ya ?ara canjawa damuwa da tashin hankali su ka kawo masa hari lokaci Waya, "Ma'u me na yi miki? me yasa ba za ki soni ba??, indai wani hali nawa ne ba kya so Wallahi zan dena indai har za ki zamo gatana; Ma'u Bansan ya akai ba kawai na wayi da narkon Sonki a Zuciyata, wallahi ji nake idan na rasaki tamkar zan rasa raina, idan na ji kin ce kin tsaneni tamkar ana watsa min ruwan wuta haka nake ji, ki tausaya min kar ki hukunta ni ta wannan hanyar ko da kuwa na yi miki laifi, wallahi ba wasa ba yaudara a cikin zancena; duk yawan Matan Duniya ke kaWai nake yiwa irin wannan Makahon so, Ma'u kar ki bari rayuwata ta salwanta ta sabauce sabida soyayyarki Please!!!" daga yadda yake maganar za ka gane ya na cikin mawuyacin hali gami da tashin hankali, Ma'u kuwa ta gaji ma da jin muryarsa, ji take da akwai wani makami a kusa da ita ba abinda zai hanata buga masa ta ?wace hannunta, ba ta ce masa cikal ba sai kuka da take yi kamar ma?ogoronta zai tsage sabida shashsheka.

Sakar mata hannun ya yi gami da cewa "Allah ya huci Zuciyarki, ba yadda na iya ne dole sai na gaya miki, na kamu da cuta kuma ke ce kaWai maganinta."
"Allah ya sa ma ka mutu na huta azzalumi" abinda Ma'u ta faWa kenan ba tare da ta jira amsa ba ta arta da mugun gudu.
Da ido ya rakata har ta Sacewa ganinsa sannan ya kutsa kai Falon Haj Laure.

Su na gama turnu?u da inuwarta ta kwanta ya shigo. Ya yi mamakin ganinta a tile a gefe kamar kayan wanki, amma da yake hankalinsa ba a jikinsa yake ba bai bi ta kanta ba ya nemi wuri kan Sofa ya zauna gami da buga tagumi ya lula duniyar tunani.

A hankali sautin kukanta ya fara dawo da shi hayyacinsa ya yi saurin mi?ewa ya na cewa "Mom what happened to you??"
HaSar zaninta da ya kwance ta janyo ta face hanci sannan ta ce "Ba abinda bai faru ba ma, inuwar mata na gani ta na bina ta na tsorata ni, kai kuma ba ka tashi shigowa ba sai da ta tafi, inda kasheni ta yi sai dai ka zo ka Wau gawata kenan ko?" zama ya yi a gefenta ya ce "Ke ce ba ki da aiki sai bin bokaye Mommy,, ?ila ma wani kika yiwa asiri ya dawo kanki, ai ga ranarta nan sai ki dena."
Ta ja numfashi ta sauke, cikin muryar kuka ta ce "Ba za ka gane ba ne Yazeed ka barni da abinda yake damuna!"
rai a Sace ya ce "Nima ina da damuwa me tsanani ma kuwa, kuma ko shakka ba na yi kece tushen damuwar tawa; Allah ya sawwa?e to" ya na kaiwa nan ya tashi ya bar mata Falon.

Ya na fita kuwa tsoro ya ?ara kamata ta yi sauri ta tashi ta fita can harabar gidan don kar ma a ?ara ritsata a Waki.

01:32AM kowa ya rintsa amma ita baccin ya gagari idanunta, kwanciyar ma har ta isheta don haka ta tashi ta zauna gami da zuba tagumi ta ci gaba da tunane-tunane, ta na cikin wannan Halin ta ji wayarta na ?ara a ?ar?ashin filo, jiki a sanyaye tamkar wadda aka zarewa laka ta zura hannu ta janyota, zuba mata ido ta yi na Wan lokaci sannan ta Wauka da wani kiran ya ?ara shigowa.
"Yau ma ba ki yi bacci ba Ko?"
cusa kanta ta yi a tsakankanin guiwoyinta ba tare da ta ce masa ?ala ba, jin ta yi shiru ya sa shi cewa "My wife!!"
ya yi maganar cikin wata kasalalliyar murya me ?unshe da sa?onni daban-daban wanda kai tsaye ta fito tun daga ?asan Zuciyarsa, ta yi saurin lumshe idonta gami da sauke sassanyar ajiyar Zuciya, cikin muryarta da ta dashe ta ce "Akhiee!! tunani ya hanani bacci, da na rufe ido nake fara mafarkai."
"Idan ki na gaya min haka hankalina gaza kwanciya yake yi Asma'u, ki samu nutsuwa don Allah."
GyaWa kai ta yi tamkar ya na kallonta.
Sun Wauki lokaci su na sauraren numfashin juna ta wayar ba tare da kowa ya yi magana ba, Akhiee ne

20 / 25