Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   24 / 25

69K to 72K   out of 73.5K words

sosai domin tin da ya rasa mahaifiyarsa bai ?ara samun wata uwa mafi kusanci da shi ba sai ke. Mayar da kallonsa ya yi kan Rislan gami da cewa "Dattijo! ba na son na ji saSani a tsakaninku, kuma ka sa a ranka indai na samu haka kai ne me laifi." ya gyaWa kai alamar ya gamsu.

Husnee kuwa ta yi tsit!!!! kamar ruwa ya cinyeta , kalaman Abee sun yi bala'in ratsa Zuciyarta kuma sun jefata cikin tunani iri daban-daban, ga tarin tambayoyi da ta rasa wa za ta yiwa su Akiee Win ko Abee Win?.
Nasihu Abee ya yi musu sosai wanda suka ratsa Zuciyar Husnee jikinta ya yi sanyi salam! Zuciyarta ta tsumu kuma ta samu nutsuwa, bayan ya kammala ya rufe da Addu'a sannan suka bar sashin nasa tare da Zara ita ma ta wuce ?akinsu.

Suna komawa ta haye gado don kuwa ba abinda take bu?ata a yanzu sai bacci, Rislan kuwa sai bayan ta yi baccin ya haura kan gadon ya kwanta kusa da ita gami da janyota jikinsa, da haka shima baccin ya yi awon gaba da shi.
Daidai lokacin da ya saba fita daga cikin gidan yau ma ya fice ba tare da Husnee ta sani ba hakan ya sa ta yi tunanin bai ma kwana a gidan ba.

Da rana tsaka kawai sai jin Sallamar mace ta yi a gefen ?akinta, ta zumbuWa hijab sannan ta le?o a tsorace cike da shakkar wadda za ta gani.

Matashiyar macece fuskarta Wauke da murmushi "Sunana Rahma Daddy ne ya aiko mu mu kawo miki kaya, da fatan ba damuwa, in kuma da damuwa sai mu koma sai kin shirya domin mun shigo miki gaba-gaWi" duk da ba ta gane kowacece ba kuma ba ta gane inda zantukanta suka dosa ba sai ta washe baki ta na murmushi ta ce "A'a ba komai, amma ban gane wanda kike nufi Daddy ba , ko dai Daddyna? in haka ne kuma ai ban san ki ba."
Rahma ta girgiza kai sannan ta ce "A'a ba Daddynki ba, Mijinki shine Daddy a wajenmu, Kayan lefenki ne da kuma kayan ?aki muka kawo, idan ba damuwa za mu shigo da su."
Husnee ta cika da mamaki da jin furcin Rahma, cikin alamun mamakin ta ce "To ku shigo ba komai." Rahma ta yi godiya sannan ta koma zuwa waje.

Suman tsaye Husnee ta yi lokacin da suka gama dire mata akwatinanta a gabanta, Saiti ne kala-kala masu shida-shida, shidan kuma sau Shida, in an haWa duka Akwati Dozin uku kenan, guda Talatin da shida. Banda dukan shalugude ba abinda Zuciyarta ke yi, ta matu?ar girgiza da lamarin Akhiee, lokaci guda Zuciyarta tafara yi mata sa?e-sa?e kala daban-daban.
Ta na nan tsaye wasu ?aratan Maza suka fara shigo da Sif, Ba?a ce me yarfin fari irin me shidan nan wadda ta sha kyawun ?ira daga gani Naira ta yi kuka, Madubinsu ma kanshi abin a zo a gani ne, ya sha ado ta ko ina, sai kujeru guda uku Fallatsa-fallatsa masu numfashi, irin wanda ba dai a gidan Malam Shehu ba sai dai me hannu da shuni, ga wasu plowers na adon Waki masu bala'in kyau da burgewa.
A gefe guda kuwa kayan Kitchen ne aka tsibe su tari guda manya masu shegen kyau, ko makaho ya shafa zai gane an zuba miyagun kuWi wajen mallakarsu.

Husnee dai ta kasa cewa komai sai ido kawai take zarewa kamar an tarfa Sarauniya a Kasuwa, "Anya kuwa Akhiee ba Wan fashi ba ne?" tambayar da wani sashin na Zuciyarta ya wurgo mata kenan, yayin da wani Sangaren ya cafe kalmar kuma ta yi Waram a Zuciyarta, don kuwa in ba fashi yake yi ba ta ya zai iya sayen waWannan ma?udan kayan kuma a lokaci Waya? sai dai da yake bai san darajar kuWin ba tinda sata yake yi. wannan tunanin take ta yi tana daga jikin bango a raSe tamkar garafuni a jikin danga.

?iftawa da bismillah sashin ya cika da tarkacen Matan gida da Yaransu sun zo kashe kwarkwatar idonsa, dandanan wurin ya Wau cecekuce kowa na tofa albarkin bakinsa, sun kamu da tsananin mamaki da Al'ajabi na ganin irin wannan kirimSa ta Rislan. Ko kunyar idon Husnee da su Rahma ba su ji ba suka dasa zancen cewa ai Sarawo ne dama har fashi da makami yake yi, wasu ma cewa su ka yi ?ila shagon masu sayar da kayan ya je ya yi musu fashin kayan ya Webo.

Laita ta so ta tanka musu Rahma ta hanata don kuwa Inna ta jaddada musu kashedi akan kar su sake su biyewa matan gidan a yi da su.
Zara da Ru?ayya da Musa su ne suka temaka musu wajen yin jere da duk sauran aikace-aikacen.

Kayan da ke cikin Wakin waje aka yo da su aka sanya sabbin, da yake ?akin da girmansa duk sai da ya cinye komai kuma dama sai da Rislan Win ya kimanta shi kafin ya san irin kayan da zai zuba masa.
Dandanan ya Wau kyau ko ina gwanin sha'awa. Duk hassadar su Inna Huwaila su Innajo duk wadda ta le?a sai ta yaba sai dai ta ciki na ciki, musamman Matan Yayyen Akhiee da suka kasance faccaloli a wurin Husnee sai suka ji ba?in ciki ya ?ara kama su don sun tabbatar ta yi musu fintinkau, da kuwa har sun fara tsegumi akan iyayenta ko tsinke ba su kawo mata ba.

Kayan kitchen kuwa a Waya ?aramin Wakin aka jera su tsaf, bayan an buga kanta doh kuwa da masu aikin suka tawo kafin su gama jeren Waki an gama bugata. Komai ya ji banda tsiya in ji maro?a.

Tamkar Macijin da aka zarewa Dafi haka Husnee ta koma, sai ta ji duk gidan ya ?ara matseta ta ji tamkar a kurkuku take sabida abubuwa da dama da suka sha mata kai, tin daga kan kayan har zuwa maganganun da Faccalolinta suke jefar mata.
ba ta ?ara shiga tashin hankali ba sai da ta ga har ma?ota shigowa suke yi kallonta lokacin Zuciyarta ta yi karyewar da ba za ta iya jura ba dole ne ta yi kuka ko ta samu sassauci, bayan Wakin ta zagaya ta zauna a ?ar?ashin Waya daga cikin bishiyoyin wajen ta fara mazgo kuka.

Sai bayan Magrib su Rahma su k yi mata sallama suka tafi, da za su tafin ne Laita ta ke cewa "Ranar nan Inna sai yi miki nasiha take yi akan ha?uri da matan gidan nan, to wallahi kar ki sake ki yi ha?uri da su, duk wadda ta yi miki ki yi mata mu za mu tare miki, irin waWannan indai za ka yi musu sau?in kai to ka shiga uku." Husnee dai murmushin ya?e ta yi kawai gami da yin ?asa da kai don kuwa ba ta da abin cewa.
Zabira ma ta ?ara da nata nasihun na shiririta, ita dai Rahma aikinta dariya, da haka su ka yi sallama sannan suka tafi.

Sai a lokacin ta gane ita cikakkiyar Marainiya ce a yanzu, a lokacin da take cikin tsananin damuwa da tashin hankali, yayin da sawu ya Wauke ya rage daga ita sai wannan tarin kaSakin kaya nata wanda in ta kallesu take jin Zuciyarta ta yi wawan zillo tamkar za ta fito ta baki.

zama ta yi ta buga tagumi ta na kallonsu, wata Zuciyar ta na zugata akan ta buWe Akwatinan ta ga meye a ciki wata kuwa ta na yi matsa tsawa akan kar ta buWe, tana cikin wannan halin ne Zara ta yi sallama a Wakin, fuskarta Wauke da fara'a ta ce "Ni fa Anti Husnee Allah ma ya sani na zo ganin kaya ne; Allah ya sa mu a danshinku ." ta ?arasa maganar tana dariya cikin sigar Zolaya.
Husnee ba ta iya cewa komai ba sai ta yi ?asa da kai, hakan bai damu Zara ba ta ?arasa inda aka jere akwatinan wata kan wata ta fara saukesu ta yi musu WaiWai a tsakar Wakin suka cika ko'ina sannan ta fara buWewa bakinta Wauke da bismillah.

Tin Husnee ta na kan gado sai da tashin hakali ya jefota ?asa, ashe a Wazu ba komai ta gani ba face shafar mai. dallatsa-dallatsan Atamfofi, Leshika, Shaddodi, Matarial, sun kai kala talatin-talatin, kuma dik cikinsu ba wanda ba a Winka ba duk a Winke suke, Winki kala-kala masu bala'in kyawu irin na manyan mata.
Sai jerin su Abaya, da dogayen riguna dangin ?an kanti, da kayan bacci iri daban-daban su ma kansu yawansu sun fi gaban irgawa. A gefe guda kuma wasu irin kaya ne na sa?i Irin na da, wanda aka yi musu ?irar kayan Sarakunan Asali, dakakku masu kyau da burgewa.
sai takalma da mayafai kowane kaya da nashi, sai hijabai, sai dangin sabulai turaruka kayan kwalliya da sauransu gasu nan barkatai kamar kayan banza.

Wata ?ar madaidaiciyar Akwati Zara ta janyo ta buWeta, idanunta ne suka ?ara girma Zuciyarta ta yi wata muguwar buguwa wadda ta sa ta kusan shiWewa......... Husnee kuwa da ta yi tozali da abinda ke cikin Akwatin kawai sai ta fashe da wani mugun kuka tamkar an yi mata ba?in albishir da Mutuwar iyayenta..............







*??INDO*
[9/11, 8:40 PM] INDO: *>ػ?S-K>ػ?*
Ep 26




Jiki na rawa Zara ta fara zaro kayan, dan?ara-dan?aran Ababen Ado ne dangin su Sar?a, Awarwaro, ?an Kunne, Zobe. daga yanayin kyawunsu da Waukar ido ko ba a faWa ba za ka gane na zallar Lu'u-lu'u da Zinare ne, wato Gold da Diamond, gasu nan kala-kala kowanne da nashi style Win.
Ita kanta Zara lokacin da ta kammala fito da su sai da ta kasa jurewa ba tare da ta shiryawa kuka bata fara yinsa.
Daidai lokacin Ru?ayya ta yi sallama a Wakin tare da shigowa gadan-gadan "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!!!!" ta faWa cikin kaWuwa gami da firgici, cike da rashin sanin abun yi ta ?arasa kan kayan ta dur?usa, har lokacin bakinta a buWe kamar ?ofar gari sai jinjina kai take yi ta ma rasa abin furtawa.
Zara ce ta fara ?o?arin mayar da kayan cikin sauri don kuwa ba za ta so mutan gida su san irin abinda ke cikin Akwatinan ba, sai a lokacin Ru?ayya ta ?ara samun ?warin guiwar cewa "Zara! anya kuwa Akhiee ba Wan Mafiya ba ne???" ta yi maganar cikin tsananin mamaki da fitar hayyaci.
Cikin shashshekar kuka Zara ta ce "Haba Ru?ayya! kamar ba Wan uwanki ba? ko a titi kika gamu da mutum bai dace ki dinga jifansa da irin wannan kalamin ba, Allah shi ya barwa kansa sanin inda ya same su, ban ga amfanin ku zauna kuna faWen mugayen kalamai akansa ba."
Ru?ayya ta taSe baki gami da cewa "Tab!!! Allah ya sittiri bu?ui in ji kishiyar me doro, gaskiya ce dai ba kwa so kuma dole a faWa, don in ba Wan mafiya ba banga a inda zai samo waWannan gwala-gwalai da kayan ba, dama indai shan jini ne ai ya saba, ?ila in ya kashe mutum tsafi yake yi da shi."
a fusace Zara ta ce "Tashi ki bar Wakin nan Ru?ayya!! ba na son ?ara ganinki anan don Allah ki ?yalemu!!, abinda ya shafemu ne ba bu?atar ki ?ara sa baki a ciki, kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce ka faWi Alkairi ko ka yi shiru."
"To Alawadaran naka ya lalace, jakin dawa ya ga na gida." ta faWa tare da tashi jikinta har Sari yake tsabar za?uwa da son ta je ta bada labari.

Tana komawa Sangaren nasu ta fara ?walla kira, "Innajo! Umma! Inna Kulu! Inna Huwaila! Umma Azima! Yaya! Yaya Lantana! duk wadda ta ji ni in bata tsakar gida ta fito."
Inna Huwaila dama itace ta aikata don ta gano abinda Zara da kuma Husnee Win suke yi kuma ta yi sa'ar shiga, da yake abin boni na iya ne tamkar kiran Allah haka suka gaggauta bayyanowa, Innajo da Umma Azima da sauran yara dama suna tsakar gida.
Nan fa suka yi rukuni Ru?ayya ta zayyana musu abinda ta gani, har da ?ara zuzutawa abinda yake ?arami ta kumbura shi ya zamo babba.
Nan fa suka fara magana kowacce ta na gwaSo tata sobaWanar, haka suka dinga luliya zancen har wasu daga cikin mazan gidan suka dinga shigowa suna iskar labarin su ma sai a zauna a Zana musu abinda ya faru. Duk wannan abin da ake yi Inna Huwaila ba ta iya cewa komai ba sabida wani miki da ya ma?ale a cikin Zuciyarta, ba komai take tunawa ba sai Kisan da Rislan ya yiwa Wanta, da ya bar shi a raye da tuni ya na nan yana rayuwa amma shi ya kashe shi sannan ya zo ya na tashi rayuwar ba abinda ya sha masa kai. Da wannan tunanin ta gama ?uluwa ta fara mugayen sa?e-sa?e a ranta.
a ?angaren Yaya Fiddausi Matar Yaya Aminu, abin ya fi ?arfin ta yi magana don kuwa wani mugun kishi ta ji ya tokare mata ma?ogoro, ji take ina ma itace ta samu irin wannan hamsha?an kayan daga mijinta?, Da a kaf gidan Mijinta ya fi kowa bajinta, ta fi duk sauran mata sanya tufafi masu kyau da Waukar ado, duk itace tauraruwa, amma yanzu gashi wata Yarinya ?arama kuma Matar wani Banza mara galihu ta zarceta, sai ta ji kamar ta sokawa Zuciyarta wu?a kawai ta mutu, "Ta yaya ma zan bari wata Faccala ta fini komai? ya zama dole in san abin yi domin duk gidan nan ni ce Tauraruwa domin Iyayena ma masu kuWi ne, bai kamata wata kucaka ta zo ta nuna mini iyakata ba, gwara ko kasheta ne na yi na kwashi abinda zan kwasa a cikin kayan nata."
Wannan tunanin kawai take maimaitawa a cikin Zuciyarta wadda take Waci da raWaWi. Fuuuu!! ta tashi ta koma Wakinta don ta gaji da jin maimaicin labarin kayan.

Inna Huwaila ta na ankare da ita, duk ta lura da yanayinta don haka ta saki wani shu'umun murmushi don kuwa alamu sun nuna mata ta samu makamin da za ta ya?i Rislan ta hanyar Cutar da Matarsa, KakkaSe zaninta ta yi ta mi?e ta na cewa "Uhm!! mun dai godewa Allah da muka samu haihuwa me rana ba mu haifi annoba ba, Ita dai Hadiza ba ta yi sa'ar zuwanta Duniya ba."


A Sangaren Zara da Husnee kuwa har yanzu Husnee kuka kawai take yi ko motsawa daga inda take a zaune ta kasa yi, Zara ce ta yi ?arfin halin mayar da kayan ta na yi ta na sharce ?walla don kuwa ita ma abin ya taSa Zuciyarta matu?a gaya, kowane Wan-adam idan ya ga waWannan kaya kuma a ce sun samu ne daga wurin Akhiee sai ya dasa alamar tambayoyi ba ma tambaya ba. Bayan ta kammala Mayarwa ta koma kusada Husnee ta zauna, kafin ta yi magana a sanyaye "Anti Husnee ki yi ha?uri don Allah ki dena kukan nan, shi dama Akhiee haka yake, ko a karan kansa idan ya saka kaya sau Waya ba ya ?ara saka su, idan aka lissafa kayan da yake sawa yau da gobe kinga waWannan ma ba komai ba ne, Ba sata yake yi ba don ban ga alamar shi Sarawo ba ne, kuma ya na da sana'a sai dai sana'ar ta shi ba me kyau ba ce tinda Dilan Wiwi ne, yanzu ki kwantar da hankalinki idan ya dawo ki ce masa ya rage kayan ko ajiyewa ne ya yi a wani wurin in ya so in wasu suka tsufa sai ya kawo miki sauran kin ji?" ta ?arasa maganar cikin sigar rarrashi, gyaWa kai Husnee ta yi alamar ta gamsu da hakan, Zara ta ?ara da cewa ''Yawan kukan nan zai kawo miki wata larurar, don Allah ki rangwanta, kuma kar ki ce ba za ki yi amfani da kayanki ba don ransa zai iya Saci, kuma sai kin dinga lura don za a iya a dinga Waukar miki abubuwanki, Ni yanzu zan tafi in kwanta sai Allah ya kaimu" ta ?arasa maganar tare da tashi ta nufi hanyar fita.
HaWe kai da gwiwa ta yi ta na sauke Ajiyar Zuciya akai-akai, a haka wani yamutsatstsen bacci ya yi tafiyar ruwa da ita.

Ya na shigowa Wakin ta yi firgigit ta buWe ido sabida jin motsi da ta yi, ba ta yi zaton shi ne ba kawai sai ganinsa ta yi tsaye a kanta, ta zazzaro masa idanu ta na binsa da kallon tuhuma, ya buWi baki zai yi magana ta katse ahi da cewa "Kai ?an fashi ne Rislan??" sai da idanunsa suka ?ara girma sabida jin tambayar tata don kuwa ta zo masa a bazata, cikin nutsuwa ya zauna a gefenta daga kan gado sannan ya ce "Ni ban taSa sata ba Asma'u, ina da sana'o'i daban-daban, kuma bayan haka ina da masu yi mini komai ko da ba ko sisina a ciki."
Cikin disashshiyar muryarta ta ce "To amma

24 / 25