Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 25

63K to 66K   out of 73.5K words

ne."
Jaafar ya yi saurin cewa "Wallahi nima haka, ni har Addu'a ma nake yi Allah ya nuna min wannan ranar."
Yasayyadi Jameel ya ce "Ai kuwa ba za ku ganta ba don wallahi Abhie ya ma fi son shi, kuma ban ga dalilin da zai sa ya ce ba Wansa ba ne."
"Yanzu duk ba wannan ba, ya za ayi mu samu Abiee ya raba Auren?" ya jefa musu tambayar gami da yi musu zuru da ido don jin ta bakunansu, nan fa su ka fara tattaunawa kowa na kawo ta shi Idea.

Wayar Inspector Khalil ce ke ta famar ?ara yayin da yake banWaki ya na watsa ruwa, Zulaihat ce ta Wauka ta na cewa "Ana kiranka ko in Wauka ne??"
Rass gabansa ya yanke ya faWi, da sauri ya ce "Kar ki Wauka ina zuwa."
TaSe baki ta yi sannan ta mayar ta ajiye masa, ba tare da ya shirya ba ya ganganWa ya fito, ya na fitowa ya aiketa kawo shayi don kar ta ji abinda zai ce, ta na fita ya yi sauri ya Wauki wayar ya maida kiran ta na shiga aka ?auka, muryar DCP Khashim Bello ce ta ratsa kunnuwansa..... "Shi farin ciki yake yi abinsa ?arshe ma har da Aure ya yi, kai kuma ka na kwance ka na bacci ko??"
"A'a yallaSai, ai naga JD ya shiga lamarin ne shi yasa na janye jikina."

"Don JD ya shiga ai ba ya na nufin kai ka fita ba, hakan dama ce ta samu wadda za mu dinga rarraba masa hankali; a memakon ka hanashi sakewa a matsayinka na Jami'i amma ka bar shi sai abinda yake so yake yi, idan ba za ka iya ba za mu tuSeka mu kawo wani; mu na bu?atar shigo da kaya amma ka ?i yin komai a kai."
IP Khalil ya ce "Sorry sir, zan ci gaba da ?o?ari, na Wauka an bani hutu ne shi yasa." DCP Khashim Bello ya rafka tsaki kafin ya ce "Last warning, kar ka kuma yin sake kamar yadda ka yi."
"Yes sir!" ya faWa cikin girmamawa.

Zulaihart da ke tsaye a bayansa ta na saurarensa ta kalleshi cikin Sacin rai ta ce "Ni dama na san ba banza ba, na san ba tsakani ga Allah kake aikinka ba, yanzu meye ribarka don ka na yiwa ?an ta'adda aiki suna biyanka kuWi? da kai da su fa ba ku da wata maraba."
"Ni haka na ce miki aiki nake yiwa wasu? da DCP nake magana fa ba da wani ba kuma akan matsalar tsaro ne" ya faWa cikin borin kunya da rashin sanin abin yi, murmushin takaici ta yi gami da cewa "Hmm! idan da gaske ne ai da CP ya kamata ka yi magana ba da DCP ba tukunna, kuma naga ya na yawan kiranka har da ma wani JD ko?, ko za ka shiga kogin rantsuwa ba zan yarda ba, kuma sai na gaya maka gaskiya, ka dena sabgar nan ka koma Jami'in ?warai tin kafin lokaci ya ?ure maka."
"Don Allah ni ki ?yaleni, duk abinda na yi ai umarni na karSa ko?, kar ki sa min ido akan aikina ki barni ni na san abinda zan yi "
"Au haka ne? to Allah ya temaka, amma ina yi maka fatan shiriya, kuma na san wata mana?isar kuke shiryawa.
Banza ya yi mata itama sai ta bashi wuri.


Tin ta na sa ran ganin Akhiee har ta dena bacci me cike da mafarkai daban-daban ya yi awon gaba da ita..........






*??INDO*
[9/8, 12:07 PM] INDO: *>ػ?S-K>ػ?*
Ep 24




Misalin ?arfe 03:00 na dare ya shigo Wakin cikin tafiyarsa me kama da sanWa, wajen Drower ya wuce ya ajiye duk wasu tarkacen makamai na jikinsa sannan ya buWe sif Winsa, kamar kullum sabuwar riga fil ya Wakko don kuwa ba ya saka kaya kuma ya maimaita su, da ya yi sawa Waya sai dai ya bayar ko ya jefar, sai dai in ya na son irinsu ma ya kuma yi.
Doguwa ce har ?asa maSallanta guda uku ne a jiki kacal a iya tsakiyarta, sama da ?asanta a buWe yake, sai Wan ?aramin wandonta iya guiwa.

A gefen gado ya ajiyeta sannan ya shiga toilet, bayan ya fito ya zura rigar sannan ya nufi kan Gado.
A gefenta ya zauna ya zubawa fuskarta da take a cukurkuWe idanu tamkar don ita kaWai aka halitta masa idanun ko son ?iftawa ba ya yi, daga yanayinta ya fuskanci a cikin damuwa da takura take yin baccin da alamu ma ba jin daWinsa take yi ba, gashi ta du?un?une cikin lafkeken Hijab wanda ko likafani za a yi mata da shi zai isa.

Cikin nutsuwa ya Wora tattausan hannun akan fuskarta ya na shafata a hankali a hankali, "Asma'u!! ji nake tamkar tamkar garkuwa ce ke gareni, zan so na kasance me sanya ki farin ciki a koda yaushe, sai dai ba zan iya ba rayuwata cike taf da abubuwa iri-iri, a memakon ki yi farin ciki sai dai ki kasance cikin zubda Hawaye Asma'u" a zahiri yake maganar ya na yi ya na kewaye hancinta da kan idanunta da babban yatsansa, har zuwa lokacin kallonta yake yi tamkar wata sabuwar halitta ba mutum ba.
Ya Webi Wan lokaci cikin wannan yanayin kafin ya janyota jikinsa ya rungumeta a cikin ?rijinsa ya fara ?o?arin cire mata hijabin a hankali ta yadda ba za ta farka ba, har ya cire ya ajiye shi can gefe ba ta farka ba sai ma numfashi dogaye da take ja ta na ?ara lin?aya a cikin baccin, ga dukkan alamu ta samu sauyin yanayi wanda ya sa Zuciyarta ta samu sakewa, har ila i yau bai dena kallon fuskarta ba kai ka ce haWiyeta yake shirin yi, idanunsa sai wani irin she?i da ?yalli suke yi su na ?ara canja kala.
Hannunta ya ri?o ya zuba masa ido, ganin zobensa ya na nan a jikinta ya sa shi sauke wata sirrintacciyar ajiyar Zuciya, "Asma'u ina bu?atarki a rayuwata, ki kasance tare da ni ."
Ya faWa cikin wani irin yanayi wanda ya na da nasaba da shaukin sonta, wanda shi kansa bai san da hakan ba.

Har 04:00am daidai ya na rungume da ita sannan ya zameta daga jikinsa ya kwantar da ita, sai da ya ?ara Wibar lokaci me tsayi ya na kallonta sannan ya sauka daga kan gadon, Alwala ya Wauro sannan ya canja rigar jikinsa ya zura wata sabuwar jallabiya Brown ya sanya hula ?ar ?arama taSani ka ji hadisi sannan ya fara Sallar nafila.
Sai lokacin da aka kira Sallar farko sannan ya tashi daga kan dardumar ya fice daga gidan bakiWaya.

Sai bayan an idar da sallah a masallatai Allah ya bata ikon farkawa firgigit kamar wadda aradu ke shirin faWowa a ka.
Zazzare ido ta shiga yi ta na duba ko'ina ko za ta ga Akhiee amma fayau ko ?yallin rigarsa ba ta gani ba, wayarta ta jawo ta duba agogo ganin lokacin salla na neman ?ure mata ya sa ta yi saurin direwa ta fito daga Waki ta na dube-dube ko za ta ga banWaki, Waki biyu ne a wajen daga wanda ta fito daga ciki sai wani da alamu dai ba banWaki, gashi ko ina a bushe yake ba alamun akwai ruwa.
Komawa ta yi Waki da zummar Waukar waya ta kira Rislan don jin inda za ta samu ruwan ta na komawa idonta ya sauka akan ?ofar toilet na cikin Wakin, duk da ba ta da tabbas amma ta na kyautata zaton shi ne don haka ta nufi wajen domin ganewa idanunta.
Sai da ta sauke ?ar ajiyar Zuciya ta jin daWi sannan ta Wauro Alwala ta fito, ta na idar da sallar ta yi addu'a ta zame ta kwanta akan dardumar daga haka bacci ya sake surarta.

Yazeed kwana biyun nan sam ba ya iya baccin kirki sabida tunanin Ma'u, har ?agara yake a kira Asbah da ya fita masallaci ya dawo ko Wakinsa ya ba ya komawa sai dai ya zauna a harabar gidan don kuwa in ya koma ma ba shi da abin yi sai damuwa anan kuwa ko shuke-shuke ya kalla zai rage zafi.

Yau ma kamar kullum ya na zaune ya buga tagumi kamar a mafarki ya ga gilmin Ma'u da ?an ?ullin kayanta a hannu ta nufi wajen get.
Zundum!!! Zuciyarsa ta yi wata mummunar bugawa wadda ta yi daidai da tashinsa tsaye, razanar da ya yi gami da bugun Zuciyarsa suka bada gudun mawa wajen juyawar kansa hakan ya haifar masa da jiri idanunsa su ka fara ganin duhu kansa na wata irin majaujawa tamkar ana girgizar ?asa a cikinsa.

Cikin wata wahaltacciyar murya ya shiga kiran sunanta duk da ba shi da tabbacin za ta ji shi kuma ta saurare shi, da yake suna linzami ne kamar gizo haka ta ji an kira sunanta, gabanta ya yanke ya faWi har ?asa, kasa juyowa ta yi don kuwa ba ta san me kiran nata ba, a wannan lokacin kuwa ba ta son kowa ya ganta don so take ta gudu, in ma ba inda za ta je gwara ta dinga tafiya ko ba ta da wurin zuwa, a tunaninta Allah zai haWata da waWanda za su temaketa, Ta Wauki ?an sakanni a tsaye ba ta ?ara jin an kirata ba don haka ta ci gaba da tafiya cikin sanWa har ta isa bakin get, sai dai abinda ba ta sani ba ko kuma ta manta da shi, me gadi ya na sa mukullai a ?ofar kuma ba wanda zai bata su sai shi ko Haj Laure, turus ta tsaya Zuciyarta ta karaya tamkar za ta fashe da kuka.
Juyawa ta yi ta na kallon Wakin me gadi tare da tunanin ko zuwa za ta yi ta ro?i alfarmarsa?
Kamar saukar aradu haka ta ji lokacin da muryar Yazeed ta karaWe Fadar cikin Masarautar Kunnuwanta, sabida firgici sai da Zuciyarta ta Wan tsaya na wucin gadi yayin da numfashinta ya sar?e kamar me shirin sumewa.
Da rarrafe ya ?araso inda take don kuwa ya na mi?ewa zai iya faWuwa, sai da ya dangana da inda take sannan ya tsaya dur?eshi akan gwiwoyinsa, idanunsa da ke gani dishi-dishi ya Wago ya na kallonta kafin ya fara magana cikin sar?a??iyar murya tamkar an sha?are shi, "Ma'u kar ki gudu ki barni, don Allah ki tafi da ni duk inda za ki je zan biki, kuma akanki zan iya jurewa kowace irin rayuwa wallahi!!"
Yadda yake maganar tamkar zautacce ya sa Ma'u ta ?ara tsorata da shi, salon bugun zuciyarta ya ?ara canjawa daga sauri zuwa gudu, kai kawai take girgizawa don kuwa yadda numfashinta da Zuciyarta suka burkice ba za ta iya furta ko uffan ba.
"Ma'u zan mutu idan ki ka gujewa rayuwata, wallahi zan iya makancewa idan idanuna suka dena ganinki, iya tashin hankalin nan da suka gani har sun fara dena nuna mini daidai, duhu nake gani, ?wa?walwata ta na juyawa alamar hauka ta fara tabbata a gareni, wallahi Ma'u ina sonki so me tsanani, irin azababben son nan da yake tarwatsa rayuwar Wan adam, ki ji?aina ki tafi da ni ko zan samu sassauci.
Abin nasa haushi yake bawa Ma'u a gefe guda mummunar tsanar da ta yi masa na ?ara zigata akan ta ci mutuncinsa ko zai gane da gaske ba za ta taSa ?aunarsa ba, cikin sassar?ewar murya gami da ?arfin hali ta ce "Ni ba zan taSa son watsatstse irinka ba, mazinaci ?azami mashayin giya wanda bai san daraja da kimar kansa ba bare ta wani, ka fita daga rayuwata in ba haka ba kashe kaina zan yi wallahi, ni na tsaneku bakiWayanku kuma Allah sai ya saka min."
Wasu zafafan hawaye ne suka yiwa fuskarsa mugun wanka, ya girgiza kai gami da dafe ?irjinsa daidai saitin Zuciyarsa, "Ma'u Zuciyata shirim fashewa take yi, don Allah kar ki hukuntani akan laifin da ba ni na aikata ba, idan wani ne ya yi miki laifi don Allah ki ?antani daga Sangarensa, ni ban kasance irinsu ba, kuma wallahi tallahi ba na iya zama na sha giya tin daga ranar da na furta miki kalmar so kika jefani cikin tashin hankali, a da na Wauka abinda nake yi shi ke kawo nishaWi na Wauka tarayya da matan banza shine more rayuwa, amma tinda na kamu da sonki na gane martabar mace, na gane duk abinda nake yi ba shine ke sanya farin ciki ba, na dena ba zan ?ara ba na tuba ki yafe min; yanzu rayuwata da mutuwata sun rataya a wuyanki Ma'u!! ina fatan ki yi mini kyakkyawan zaSi."
Ya ?arasa maganar gami da rushewa da wani susutaccen kuka tamkar ?aramin yaron da ke neman Mahaifiyarsa.
Dogon tsaki Ma'u tafka me cike fa Sacin rai da tsantsar ?iyayya, ba tare da ta sake kallon inda yake ba ta ja ?an ?ullin kayanta ta koma cikin gida cike da ba?in ciki da takaicin yi mata silar rashin guduwar da ta yi niyya.

A take a wajen wani mugun azababben tari ya sar?e shi wanda ya haifar masa da shiWewa daga haka bai ?ara sanin inda kansa yake ba.

Tin da safe da Baba Sa'idu ya je gaisawa da Abee ya gyara zama ya tankwashe ?afa kamar me shirin kwasar taushe, ya karya harshe ya rattabawa Abee maganganun son rai akan Auren Rislan da Husnee, Abee ya gama saurara sannan ya jinjina kai ya ce "Duk ina ?an uwan nasa?, a zo min da su don in ji menene aibun da suke gani a cikin hakan?" Baba Sa'idu ya ce "To Yaya" tashi ya yi ya fita don nemosu, da Adamu ya fara karo don haka ya ce masa ya je ya tarkato sauran.

Da yake duk jiran kaWan suke yi da wane gayawa wane dandanan suka cika tafkeken ?akin Abee Win, ciki kuwa harda Umma, Innajo, Umma Azima, Umma Uwani, matan Abee, sai Matan Baba Sa'idu su biyu, Inna Huwaila da Inna Kulu, sai iyalinsu cunkus amma banda Sheikh Auwal da Zara da Sauran waWanda ba sa kusa.

Duk yawansu sai da Abee ya saurari ta bakin kowa wanda yawancinsu bayan nuna rashin goyon baya akan Auren sai sun ?ara da sharri da ?arya, wasu kuma suna faWen iya abinda suke tunani, wasu kuma dai suna tsakatsaki su basu ce a raba ba ba su ce a bari ba, bayan ya gama saurarensu tsaf sannan ya yi gyaran murya ya fara da cewa "To duk na saurari kokenku, amma ni ba ni da ?ancin Sakar masa mata ko kuma na tilasta shi akan sakinta, amma zan yi magana da shi, don haka kowa ya tashi ya tafi uzurinsa, masu zuwa makaranta maza su shirya masu fita kasuwa su ma su shirya."
Kallon kallo suka shiga yiwa juna cike da ba?in cikin furucin Abee sun san tinda abin ya zama haka, ko ana ha maza ha mata ba ta yadda za a yi ha?arsu ta cimma ruwa, don haka wasu suka fara saSewa su na fita cike da takaici.

Su Innajo da su Inna Huwaila kuwa suna fita suka dasa zancen su da sirikansu, irin Su , Ummu Nusaiba, Matar Babban Yaya, Yaya Lantana, Matar Yasayyadi Usman, Yaya Asiya, Matar Yaya Habibu, Yaya Fiddausi, Matar Yaya Aminu, Umman Azima, Matar Yasayyadi Jameel. Matar Sheikh Auwal wadda ake kira Yaya ita ce ba ta fito ba ita Win ma Sheikh Auwal ne ya hanata banda haka da ita za ayi.

Hasan na shirin fita ya na ?an gungunai Abee ya kira sunansa don haka ya tsaya, Abee ya ce "A zo min da Magajin Malam" wato Sheikh Auwal kenan, sunan nan da Abee ke gaya masa ma ba?in cikin hakan suke ji, don gani suke yi tamkar ya fi sonsu. Ko to bai ce ba ya zunguri uban kai kamar damin gumama ya ci gaba fa tafiya.

cikin ?a?ansu da ke ta sha'anoninsu ya aika Waya ?akin Sheikh Auwal ya kira shi, bai ?ara bi ta kai ba ya fice daga gidan baki Waya.

Abee ya na dariya irin ta yaro man kaza ya ce "Magajin Malam yanzu aka gama kawo min ?arar Wan uwanka akan Aurensa, sai dai ban ji ta bakinka ba."
Sheikh Auwal ya rissina a ladabce ya ce "Abee kuskuren da ya aikata shi ne Aurenta ba a kan ?a'ida ba, bai kyautu ya je ya yi gaban kansa ba, mu ba mu sani ba iyayenta ba su sani ba, sannan duk ba mu amince ba, sannan ya gardame akan shi ba zai rabu da ita ba duk da cewar iyayenta suna son hakan." Wan tsagaitawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Abee! in da Akhiee ya na jin magana kuma ya na Waukar shawara, ba wanda zai ce dole sai an raba Aurensa, su kansu iyayenta da ya na yin abinda ya kamata na san ba za su ?i ba shi ?arsu ba, amma yanzu ka ga abinda ya yi kowa bai ji daWi ba, raina Saci yake yi idan na ji irin maganganun da ake faWe

22 / 25