Sawun Keke Hausa Novels Compelet Aysha Abdulkareem Indo.doc

Author :  Aysha Abdulkareem Indo Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   8 / 25

21K to 24K   out of 73.5K words

sau?i.
Khausar ce ta shigo ta na cewa "Anti Husnee wai ba za ki ci abincin ba?" kamar za ta yi kuka ta ce "Ke dalla na ?oshi" Khausar ta ce "Wallahi ba ki da lafiya, dole ma ki ga likita bari Daddy ya dawo."
Husnee ba ta ce komai ba don maganar ma ba son yi take ba.
Sai da aka yi kiran Sallar magrib sannan ta fito ta Waura alwala, Yaya Muneer ne ya dubeta a tsanake ya ce "Ya jikin naki?" da sauri ta Wago ta na kallonsa a ranta ta na tunanin ''Wai ce musu aka yi ba ni da lafiya?" a zahiri kuwa cewa ta yi "Da sau?i" Yaya Muneer ya ce "Ba ki da lafiyar amma ba za ki faWa ba sabida Allura ko?" da sauri ta girgiza kai alamar a'a, kafin ya yi wata maganar tuni ta gudu Waki.

Bayan an idar da sallar isha'i ta na zaune kusa da Mommy, duk sauran yayyenta dake Parlon su na hira da raha amma banda ita.
ta yi nisa a duniyar tunani Ahmad ya yi sallama, ko zama bai yi ba ya ce "Ina Me hawaye ba kukan nan?, ya jikin?" ya yi maganar ya na dariya.
ZumSuro baki ta yi gami da cewa "Ni fa lafiyata ?alau."
Yaya Muneeb ya ce "A'a gaskiya dole akwai wani abin da ke damunki, ke da surutu kuma har a zauna hira ba ki ce komai ba?" Ahmad ya ce "Ku ?yaleta ?ar zafi ce ta isheta, ai an gaya mini abinda ya sameta." Daddy ne ya dube shi a nutse ya ce "Zauna Ahmad" zaman ya yi a kan carpet ya na ?ar dariya ?asa-?asa ya na kallota gami da yi mata gwalo, ita kuwa hankalinta duk ya tashi, fargabarta Waya a faWi wani abinda zai sa su gane cewa ta gama yin zurfi a cikin shishshigewa Risslan.

Daddy ya ce "Nutsu ka gaya mana abinda ya faru da ita, ba ma son shiririta."
Ya ce "To Daddy, maganar gaskiya ko me ta ce ?arya ta ke yi, daga saman makarantarsu ta faWo, ba ma fa daga ?afar bene ba daga can sama, in gaya muku gaskiya gwara ku kaita National Orthopaedic Hospital ta cancanci ganin likitan ?ashi."
Ido warwaje Mommy da Khausar su ka furta "Daga sama???" Ahmad ya ce "?warai kuwa ga ta nan ku tambayeta."
Mommy ce ta kama hannunta gami da cewa "Ke tashi in ganki, ai wallahi da gaskiyar Ahmad gaba da Orthopaedic ma sai a kaita." Husnee ta mi?e kamar za ta yi kuka ta na cewa "Ni fa ba na jin komai kawai ciwon jiki na ke ji kaWan."
Ba wanda ya tanka mata sai ma ido da suka zuba mata, Mommy ta ce "Taka in gani, jeki kusa da Ahmad ki dawo." ba dan ta so ba ta taka zuwa inda ya ke don dai kawai ta na son tabbatar musu ?alau take.

Ganin ta na tafiya sak! ba alamar ciwo ko buguwa ko Wingishi ya sa Ahmad cewa "Kai anya kuwa Daddy yarinyar nan Aljanu ba su shafeta ba? ka ga ?ar da ta faWo daga sama? tangaras abinta ko targaWe babu? wallahi ni Aliyu cewa ya yi mini da ta faWo ma suma ta yi sai daga baya ta farko amma kalleta don Allah." Daddy ya numfasa kafin ya ce "Kai fa Ahmad akwai ka akwai shiririta, wane irin Aljanu kuma ana zaune ?alau?" Ya Muneeb ya ce "Abin dai da alamar tambaya akai, daga kan keke ma idan mutum ya faWi jiki yake ji bare ta faWo daga sama amma ta mi?e garau" Ya Muneer ya ce "To ai ma abin tambayar anan shine, asali me ya gusar mata da hankali har ta faWo daga sama? ko tsokanar wata ki ka yi ta Webeki ta watso?" girgiza kai ta yi alamar a'a Mommy ta ce "Ni dai barkana, tinda ?alau take ai ta kwana gidan sau?i, mu ga hannunki" ta faWa ta na mi?a mata nata hannun, ba musu ta mi?o duka hannayen nata, Mommy ta mammatsata ta ji dai ba ta yi ko gezau da sunan an taSa mata inda ke mata ciwo ba, sakinta ta yi ta na cewa "Ikon Allah, Allah ya tsareki Husna" Khausar da ta saki baki ido da hanci ta na bibbinsu da kallo sai lokacin ta ce "Gaskiya ke ?ar baiwa ce Aunty dama ni ce" Ahmad ya ?yal?yale da dariya ya na cewa "To Bugun la'asar, ke daWina da ke muguwar tafki ce, ta faWo daga saman ki ce dama ke ce? to idan ke Win ce ki ka faWo kuma ki kwararraSe fa? ita Win ma ?ila Aljanu ne su ka shafeta."
Zuwa yanzu surutan nasu sun fara Satawa Daddy rai, a tsawace ya ce "Kar na ?ara jin wani ya ce wai Aljanu gareta! ku ba ku san kiyayewar Allah ba? sau nawa ake yin haWari har wasu su mutu amma a ciki sai ku ga wasu ma abin bai shafesu ba kamar ba sa ciki, amma don ta faWo daga sama ba ta ji ciwo ba sai ku ce Aljanu ne? ba ku san cewa Allah na kare bayinsa ba? ya kuke abu kamar ba musulmi ba?"
Ahmad ya ce "Ayi ha?uri Daddy mun dena."
Husnee kuwa komawa ta yi ta zauna ba tare da ta ?ara bi takansu ba.

Washegari ba wanda bai yi mamakin ganin Husnee ta dawo makaranta ba don a zatonsu ko za ta kuma zuwa sai bayan ta yi doguwar jinya, sai kuma su ka ganta katsam, su kansu malaman sun yi mamaki, su Yasayyadi Usman Waya bayan Waya sai tambayarta su ke yi abinda Akhiee ya yi mata, ita kuwa gaskiyarta take faWa musu cewar ba ta san abinda ya faru ba dole su ka gaji su ka ?yaleta.

Yamma ce li?is.....
Tankar Ya?i da Abokananta su na zaune a wani fili wanda suke kira Bakin Kwalta, anan su ka saba zaman shaye-shaye da hira. yau ma kamar kullum kowa na shan abin mayen da ya fi yi masa daWi amma banda Tankar Ya?i gabaki Waya ta kasa yin komai hankalinta ya tafi akan tunanin Risslan.
?an Kurada ne ya lallaSo kusa da ita ya zauna, cikin murya me cike da maye ya ce "Meke faruwa ne Ta gidan Oga? waye ya taSa mana ke mu taSa shi?" kallonsa ta yi ta kawar da kai sannan ta ce "Tunanin wanda na ke so na ke yi, Wai ?an Kurada akwai wani abun kushewa a jikina??, shin me yasa Risslan ba ya sona? me yake so a wurin mace wanda Allah bai ba ni ba?"
?an Kurada ya wul?ita idanunsa da suke wani galmi-galmi kafin ya ce "Ba abinda ba ki da shi ta gidan Oga!!, amma fa ina ga zaren ne ba kalar yadin ba, kin san Oga na sonki fa amma ke kuma ki na son Abokin gabarsa, anya ki na ganin hakan zai yuwu?"
shiru ta yi ta na Wan nazari na Wan lokaci sannan ta ce "?an Karada!!! ni fa gaskiya zan iya rabuwa da Dodo akan Sahun Keke, kuma kai ma ka sani gabar da ke tsakaninsu ce ta sa na san shi ma har na ji na kamu da son shi, ko fa me za'ayi sai dai ayi amma ni ba zan bar abinda nake so ba, kuma wallahi indai ka ga bai aureni ba to ko shakka babu zai mutu ba aure don duk wadda ya so ko ta so shi sai na rabata da ranta."
?an Kurada ya yi dariya me isarsa sannan ya ce "Za ki aikata ta gidan Oga!! ni ina bayanki ki yi yadda ki ke so wallahi mun Waure miki abin."
Murmusawa ta yi a ranta ta ma ?issima abubuwa iri daban-daban.

Jiki na Wari-Wari IP Khalil ya amsa kiran DCP Khashim Bello, don kuwa ya san kwanan zancen, shi kuwa abu ya fara fin ?arfinsa, da kyar ya ce "Hello!" a Waya Sangaren DCP ya ce "Na kasa samun kyakkyawan labari daga gareka, in ce dai ba ka manta Sarnar da Muhammad Muhammad ya yi mana a kwanan nan ba, JD ya fusata iya matu?a kuma ba abinda ba zai yi ba akan wannan dukiya ta shi da aka ?ona, bayan haka ma yanzu duk harkokinsa sun tsaya sabida takurawar wannan yaro, ya hana shi shigo da kaya ta kowace hanya sannan shi kuma ya na shigo da Wiwi Winsa ya na sayarwa, wai duk zaman me ka ke yi hakan ta ke faruwa?"
mi?ewa ya yi ya na takawa cikin sigar rarrashi ya ce "Ayi mini uzuri yallaSai, ba dare ba rana idanuna na kansa kuma ina nan zan yi maganinsa don Allah a ?ara bawa JD ha?uri kwanan nan zan yi iya ?o?arina, zan kama shi a matsayinsa na Dilan Wiwi kuma dole doka za ta yi aiki akansa."

"Hahahaha!" DCP ya yi dariya sannan ya ce "Wanda ba ya bin doka ai ba amfanin binsa a dokance, yanzu ba ta doka za mu bi shi ba, za mu yi masa zagon ?asa ne ta yadda sai ya ji zaman duniya ma ya ishe shi, JD ya riga ya fusata kuma ya zuba kuWi ayi masa aiki akansa, cikin kwanakin nan za mu ji kyakkyawan labari, kwantar da hankali Inspector Ibrahim Musa Rano, sai ka ji ni" daga haka ya katse kiran, murmushin farin ciki ne ya buwaya a fuskar IP Khalil ba ?aramin daWin albishir Win ya ji ba, ko ba komai shi yanzu zai samu kyakkyawan bacci shi kuwa Risslan lokacin nasa baccin ya ?are.

Tin ranar da su ka faWo daga sama Akhiee bai ?ara ziyarta makaranta ba har sai da ya yi kwana tara.
Husnee kullum zuba ido ta ke yi ko za ta ganshi sai dai har rana ta fito ta koma ga ubangijinta ko me kama da shi ba ta gani, gashi idan ta tambayi Zara sai ta ce itama ta daWe ba ta sanya shi a idanunta ba. duk ta shiga damuwa har wani Wan zazzaSi take yi, ta yi wata ?ar rama ta yi wu?i-wu?i da ita.

Yau ta sa a ranta indai bai zo ba ita ma ta dena zuwa makarantar sai bayan wani lokaci.
haka nan take zaune cikin aji sukuti, karatun ma ba wani yi take ba, sai da aka fita sallah ta Wan ji dama-dama, tare da Asiya su ka fito daga aji ta na ri?e da hannunta sabida Wan jiri-jiri da yake Wibarta sakamakon yawan tunanin da take yi, kamar ance kalli sama ta Waga kai ta na kallon inda ta saba ganinsa ai kuwa ta yi tozali dashi, ya na sanye cikin manyan kaya shadda ruwan toka me haske da hular Zanna bukar haWaWWiya me ratsin ruwan toka, kam ta ri?e Asiya yayin da idanunta ke kan Akhiee mamakin yadda ya yi mugun kyau a cikin irin shigar ya kamata ga tambaya da take yiwa kanta "wai dama ya na sa manyan kaya irin wannan?" Asiya ce ta ankara da hankalinta ba a jikinta yake ba dalilin magana da take ta yi mata amma ta ji shiru, Waga kai ta yi ta kalli inda ta ga ta na kallo itama idanunta su ka yi alaragab da Akhiee nan take zuciyarta ta bada wani Wurum!!!!!!!, cikin dubara ta zame jikinta ta ture Husnee wadda har lokacin kanta a sama yake, ba ta ce mata ?ala ba ta zame ta yi nata wuri.
kamar wadda aka saukarwa ayar zuwa inda yake ba tare da ta sani ba ma ta fara tafiya ta na yi ta na kallonsa kamar ance in ta Wauke ido zai Sace.

Sai da ta dangana da shi sannan ta dakata ta na ?ara ware masa idanunta da su ka yi zuru-zuru ko kwalli babu.
Ya na ankare da zuwanta amma ko kallonta bai yi ba.

Cikin sassanyar murya me kama da shagwaSa ta ce "Akhiee! me yasa ba ka zuwa makatanta, hankalina ya tashi da rashin ganinka gashi ban san halin da kake ciki ba, don Allah ka dena ?auracewa ganina, idanuna da zuciyata ba sa gajiyawa da kai, don Allah Akhiee ka dinga zuwa makaranta kullum"
White Diamond Watch dake hannunsa ya kalla kafin ya yi magana cikin muryar da ba hayaniya ba tashin hankali "Asma'u! Please it's time for prayer, i'm going to the masque"
"Please Akhiee Listen to me!" ta ?arasa maganar gami da fashewa da kuka...........

SHARE FISABILILLAH





Na KuWi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ?arin bayani =?I?
AN FARA PAYMENT




*??INDO*
[8/17, 1:12 PM] INDO: *>ػ?SAHUN KEKE>ػ?*
Ep 12

??
Ayeesha Abdulkareem INDO


*M.W.A>؅?*




"?an Daba ne su ka sassari Akhiee jini sai Zuba yake a jikinsa amma ya ?i yarda a kai shi Asibiti, shine duk su ka taru akansa, har babban yayanmu ma ya zo amma ya ?i Amincewa kuma wallahi ya na shan wahala sosai jininsa zai iya ?arewa"
Ta ?arasa maganar gami da fashewa da kuka mai taSa zuciyar duk wani me imani.
Husnee ta na jin haka ba ta bi ta kan Zara ba ta falla da gudu ta yo waje.
Turmutsawa ta yi tsakankanin mutanen da su ka yi masa da'ira wanda yawancinsu yayyensa.
Ya na tsaye ya jingina da bango sai ?asa-?asa yake da idanunsa da su ka ?ara wani irin haske ?wayar idon ta ?ara rikiWa ta yi ba?i siWik, fuskarsa ma kanta ta yi jawur sabida tsabar zafin rai da kuma azabar da yake ji a jikinsa, ganin yadda jini ya ji?a shaddar jikinsa me ruwan toka ta koma ja ya sa Husnee fashewa da kukan da sai da ta sa shi Wagowa ya zuba mata ido, ba ma shi kaWai ba duk mutanen wurin idanu su ka zuba mata cike da mamakin tsaurin ido irin nata, ba su gama firgita ba sai da su ka ji Tassss!!!!! ?arar marin da ta she?a masa ya karaWe kunnuwansu, cikin shashshekar kuka ta ce "Akhiee me yasa ba ka san ciwon kanka bane!!!? don me ba za ka je asibiti ba ka na fama da wannan rauni a jikinka?"
Cikin muryar da ke fita ?yar ya ce "Asma'u! ki ?yale ni ko mutuwa na yi ba su da asara tinda ba ?aunata su ke yi ba." cikin tsananin Sacin rai ta daki ?irjinsa cikin tsawa tace "?arya ka ke yi Akhiee!!! wanda ba ya ?aunarka ba zai so lafiyarka ba!!, yanzu duk wannan tashin hankalin da su ka shiga ka na nufin ba ?auna bace?? wallahi tallahi indai ba ka je ba nima sai na ji wa kaina, idan ka mutu kai ka tafi kenan mu za ka bari da tunaninka!!!!" ta ?arasa maganar gami da fashewa da wani sabon azababben kukan, "Asma'u ba zan iya ba ki ?yale..." ba ta bashi damar ?arasa maganar ba ta ?ara kwarfa masa wani shegen mari wanda ya sa ganinsa ya Wan Wauke na wucin gadi, kamar za ta yi hauka ta ce "Kar na ?ara jin zancen banzar nan a bakinka! in ba haka ba zan yi abinda ba zai yi maka daWi ba wallahi." sassautawa ya yi kafin ya ce "Asma'u Calm down cuta fa ba mutuwa ba ce, amma ba na so ki cutu sabida ni, zan so a ce kin rabu da ni kawai"
"In dai ka na so hankalina ya kwanta ka bi ?an uwanka su kai ka asibiti, in ba haka ba nima...." katseta ya yi da cewa "Na yarda zan je amma ki gaggauta tafiya gida."
Daga haka ya raSe ta kusa da ita ya wuce, a kusa da Sheikh Auwal ya tsaya ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Mu je" Sheikh Auwal ya ri?e hannunsa su ka nufi wajen mota, su Yasayyadi Jameel da IP Khalil wanda aka gaiyato tin Wazu su ka mara musu baya.

a wurin Husnee ta zube ta na ?ara sakin kuka me tsuma zuciya.
Zara ce ta dafa kafaWar ta na ?walla ta ce "Na gode Husnee kin temakemu ba don ke ba na san ko me zai same shi ba zai taSa yarda ya je ba, ki tashi ki tafi gida ki dena kuka anan kin ga mutane su na kallonki."

Husnee ba ta iya cewa komai ba sabida kukan da take yi, sai da Zara ta yi da gaske sannan ta yarda ta shiga mota Amadu ya ja su ka nufi hanyar gida.

har su ka isa ba ta dena kukan ba ta na shiga gidan ta wuce Waki ta faWa gado ta ci gaba da abinta, Mommy da hankalinta ya gama tashi ta yi mata tambayar duniya amma ta yi banza, jikinta ya yi sanyi tuni ta fara tunanin ko dai da gaske Aljanu ne su ka shafeta.
Tunanin Amadu Direba ne ya faWo mata don haka ta yanke shawarar tambayarsa, ya na zaune ya yi jugum akan Wan bencin me gadi ta iso wajen cikin sanyin jiki, gaisheta ya yi ta amsa ba yabo ba fallasa kana ta ce "Na ga Husnee ta shigo gida ta na ta kuka, na yi tambayar duniya ta ?i yi mini magana." Amadu shima kamar zai fashe da kukan ya ce "Wallahi Hajiya tashin hankali ta gani wanda dole ta yi kuka, ko ke Hajiya in ki ka gani ?ila sai kin yi hawaye don mata kuna da rauni sosai." hankalin Mommy ne ya ?ara tashi, ta zaro idanu gami da

8 / 25