Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   1 / 64

1 to 3K   out of 190.8K words

17/02/2024, 13:31 - Les messages et les appels sont chiffrés de bout en bout. Aucun tiers, pas même WhatsApp, ne peut les lire ou les écouter. Appuyez pour en savoir plus.
12/06/2024, 12:12 - ‎Ma Saji a épinglé un message
07/12/2024, 14:40 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ɗaya (1)*

*TALLAH TALLAH TALLAT*









LABARI

'Ba lalle ne a gane yarena ba, ba lalle bawa ya fahimci abinda ya saka nake saurin nan ba, bani da lokacin ba kowa hakuri, ba zan iya dakatawa na gaishe da kowa ba, a irin yannayin da nake jin kaina wannan alewar da ta sa na fito a irin wannan lokacin da yamaci ya yi daga gidanmu dan shegen kwadayi da son sai na lasa ta zamo min alkakai, tabas tana iya janyo min dukkan mutuwa a daren nan, hankalina gaba daya baya jikina, burina na ganni a cikin gidanmu kafin mahaifina ya shigo gidan!' Wannan shine abinda matashiyar budurwar ke ayanawa a cikin zuciyarta , jikinta sanye da hijab har kasa tana jefa kaffafuwanta da mugun sauri da gudu gudu bata gane kowa da komai bata iya gaisar da mutanen anguwarsu, burinta ta karasa gidansu du kuwa da irin yadda wasu ke mamakin gannin ANMI ba zata girma da gudu ba? dan kuwa a shekarunta ta kai mizanin budurwar dake iya shiga dakin miji .

Baban gida ne ta nufa, irin gidan da kana gani zaka san gidan masu kudi ne a cikin wannan garin,

Da sanda ta kama karamar kofar gidan ta tura cikinta na kwasar wani irin kugi sakamakon motar da ta gani a harabar gidan a parker wajen ajiyar motoci wato karkashin rumfar motoci, hakan na tabatar mata da dodonsu ya iso gida kuma bata nan
hannaye ta ɗora saman kanta tana furta" Na mutu na lalace"

Nan take ta ji alewar ta sire mata a rai, ta ji babu abinda zai iya wucewa ta wuyanta a irin wannan lokacin, koda kuwa yawun bakinta ne, domin wata azabar ai ta fi wata

Jiki na rawa ta karasa bangarensu wanda yake hade da iyayensu, wato matan mahaifinsu ta haye ta shiga tana rabe rabe da raraba idannuwa cike da tsoron abinda ka je ya zo

Kau!, karar saukar mari a fuskar ɗan uwanta ya sakata sakin alewar dake hannunta jikinta ya kwashi rawa

Neman tsugunawa take yi a lokacin da ta ga mahaifinsu ya janyo ɗan uwanta ya damki wuyan rigarsa ya shiga zabga masa dorina irin bulalar nan ta dukan jakai murya sama sama yana fadin" A gidan nan y'ata ke fita gabanin magariba ace ba'a san inda ta tafi ba? y'ar budurwa matashiya? kai ka ga fitarta ama ka kasa hanna ta? lalle yau sai na ga ubanda ya tsaya maka, da kai za'a hadu a cuce Ni? in kashe ka na kashe banza dan babu ubanda zai ja da Ni, sai in tsine maka ma nan da ka ganni na kuma tsinewa banza dan babu abinda za'a yi, dan iska ina cen ina neman abinda zan kawo ku ci kunna nan kuna neman karya min haki a ido?"

Jiki na rawa matarsa, mahaifiyar matashiyar budurwar nan wato Hajia Usaina ta karaso tana neman shiga tsakani jikinta na wani irin rawa na dukan da yake yiwa saurayin nan, in da sabo yaci ace sun saba da gannin ire iren halayan nan na Elhaji, babu ranar banza da ba zai shigo ya zane ya'yansa ba, a wajensa babu laifin da za'a iya kyalewa, a rayuwarsa horo shine abinda ya dace a yiwa yaro mai tsanani dan ya zamto shiryaye kuma kimtsatse a cikin al'umma, idan yana dukan yaransa babu furucin da baya fitowa daga bakinsa, mutun ne mai fushi, fushi mai girman gaske, yawancin lokuta kuma yakan sauke fushin nasa ne a kan iyalinsa, Bama kamar ya'yansa, sai dai ba zasu taba iya sabawa da wannan abin ba, kuma a kulun sunna yi masa fatan shiriya da samun cenji a wannan halaya tasa.

Da karfi ya saka hannunsa ya hankadata bayan ya sauke mata bulalar da zata sauka a kan saurayin nan, a birkice ya mika hannu ya warto budurwar nan ya aniya zane mata jiki tamkar Allah ne ya aiko shi, cudarta yake yi har sai da hijabinta ya cire ya ci gaba da cutar farar fatar jikinta sai da ta zama tamkar bayan kado dan birdi sannan ya saketa yana muzurai ya ce" Bari ku ji, Gabannan duk ubanda ya kuma yin shiru idan daya ya fita a gidan nan a kansa zata kare, daga uwar har ya'yan, dan babu wanda zai lalata min tarbiyyar y'ayana ina ji ina gani, mararsa mutuncin banza da wofi yan iska!" Yana gama fada ya juya ya fice fuuuuuuuuuuuuu ya nufi bangarensa

Yana tafiya Lubna ta sauke nanauyar ajiyar zuciya na masifafen tsoron da ya rike mata zuciya ta mike tana share gumin fuskarta ta wuce dakinta tana godewa Allah da yau lafiyar jikinta bata tabu ba, kai innalilahi, ya zamo a rayuwa kulun sai Anmi ta ja masu masifa? Tabas da yau ta sa an daketa da sai ta bi dare ta yi mata kanshin mutuwa!

kusan kowa haka ya mike ya yi gaba abinsa ya nufi dakinsa domin duk yawan Yaran nan kowa da dakinsa ne suka wuce dan shiryawa domin zuwa karatun dare da malaminsu ke zuwa ya yi masu na islamiyya,

Amaryar dake girki kuwa dama tunda Elhajin ya zo ta wucewarta bangarensa, ya yi saura mahaifiyar matashiyar budurwar nan da ita dake rizgar kuka a takure waje guda jikinta harda wajen dake fitar da jini jini haka na dukan bulala

Da kyar matar nan ta ja jiki ta nufi dakinta ba tare da ta bi ta kansu ba, tana shiga ta wuce kuryar dakinta a hankali ta silale saman gadonta mararta na wani irin daurewa mai azabar zafin tsiya ta saka hannunta ta dafe kanta da gefen fuskarta wani irin zazafan hawaye na bale mata

Dago idon da zata yi ta ga y'ar tata tsaye daga jikin kofar tana susar bayanta tana kukan nan mai taba cen cikin zuciya

a hankali ta share hawayenta tana kallonta ta ce" Thgmassss naunuj marda" (Masoyiya zo in ji)

Karasowa ta yi tana kallon fuskar Maman nata, dan ba zata so ta sake yin wani laifin ba, domin maman nata bata son rashin ji, duda ita bata bugu ama tana shayinta sosai ita dinma

a hankali ta duka nesa da ita sosai, hakan ya sake karya zuciyar Hajia, ama ta jure ta mika hannunta ta janyota sosai kusa da ita tana kallonta a tausashe ta ce" Anmina, me yasa kika fita ba tare da kin tambayi izinina ba? shin ina kika je ne haka goshin magariba?"

Murya na rawa yarinyar ta ce" Mama, wajen Ummu tsohuwa na je ta bani alewar da ban amsa ba jiya , kuma itama ta min fadan kar a dake Ni, ban sanar maki ba dan na san idan na fada maki ba zaki barni tafiya ba"

Uwar na kallonta a ranta ta ayana' ai kuwa d'an kuka ya gama janyowa uwarsa jifa' a bayane sannan tausashe kuwa ta ce" To ama, ai kin san muna da alewa a dakin nan ko? me yasa ba zaki tambayeni na baki ba, bayan wannan Anmi ke shikenan ba zaki girma ba da shan alewa?"

Kai ta sada ta gaza bada amsa, hakan ya sa mahaifiyar Tata a tausashe ta ce" Kar ki kuma fita ba tare da kin tambayi izini ba kin ji? ko kina so a ringa zane maki jiki ne?"

Da sauri ta girgiza kai, mahaifiyar Tata ta yi murmushi a hankali ta ce" To shikenan , ki share hawayen hakanan ki je dakinki ki yi sallah in malan ya zo ya tafi sai mu gasa jikin naki sannan ki sha magani ko mamana?"

Kai ta gyada wannan karron ma tana jin sanyi a ranta, mahaifiyarta ta dafa kanta a tausashe ta ce" Allah ya miki albarka, tashi ki je maza y'ar kirki , idan kin yi sallar ki yi min addu'a ki yiwa babanku kuma ki yiwa yan uwanki da ke da al'ummar Musulmi baki daya ko?"

KHADIJA ta gyada kanta ta ce" In sha Allah mamana " Sai dai a zuciyarta ayannawa take yi' Zan yiwa kowa adu'a banda baba, tunda shi kulun kulun sai ya dake ni'

Uwar na kallonta har ta fita a dakin sannan ta sake mayar da idannuwanta tana barin kukanta zuwa, ga wani irin azababen ciwon mara dake sake rufeta tamkar zai karta kiyama dan jinsa take yi sosai yana hauhawa

Da kyar ta lalaba ta yi sallar magariba da isha'i, ta mike da carbinta a hannunta ta bude hanyar baya ta nufi bangaren Elhaji tana ji a cikin ranta zata je su yi wace zasu yi, dan walahi yau ba zata iya yin hakurin wulakancinsa ba, tana zaune har yanzu a gidansa ne dan ya zame mata dole, tana jiran lokacin da zata bar gidansa, abu biyu kawai ke zaunar da ita, yaran nan nasa wa'inda a ciki ita daya ce kwal tata, sai kuma Mahaifiyarta da kulun burinta kowa ya zauna a dakinsa duk rintsi duk wuya

kofar ta saka dan makuli karami ta bude ta shiga ta rufe sannan ta yaye labulen dakin ta karasa da salama a bakinta idannuwanta na sauka kan amarya da ta kashe dauri tana zubawa Elhaji abinci a plate naman zabi zuku zuku tana murmushi ta yiwu dadadan fira suke yi wace ya'yansa basu isa su gani ba sai dai ya yiwa matansa

Salamar da ta yi ya amsa, yana kallon yannayin fuskarta ya daure tasa shima fuskar ya cire kai yana tunanin tabas rikici ya kawota kuma daidai yake da ita, in bama jarabtar Allah dake yiwa bawansa ba ina shi ina ita , y'ar talakawa ama dan balaki du ya fi sonta a cikin matan da ya aura da wa'inda yake aure a yanzu!

"Barka da warhaka, magana na zo mu yi Elhaji" Ta fada a nutse bayan ta zauna

Amarya ta wani tabe baki bata ce da ita komai ba, dan tana gudun balakin matar Elhaji wasu lokutan da shi kansa Elhajin, kwarai ko makaho ya shafa zai gane Hajia zaman amana take yi da Elhaji , kuma ko makaho ya ji irin zamansu zai gane Elhaji kansa yana yiwa kowa ya zauna dasss abinsa ba tare da ya bi baya ba banda Hajia.

"Ama ba zaki iya hakurin har ranar girkinki ba? kar a fara shiga hakin mutane fa gimbiya" Ya fada cikin basarwa yana karra dauke kai,

Yana kiranta da gimbiya ko a gaban waye, sunna ne da ya dasa mata tun a lokacin da ya nemi aurenta, kuma Gimbiyar ce domin mace ce mai cike da iza wanda Allah ya halittar mata a cikin jinnin jikinta ya aureta ne auren budurwa, tabas ba y'ar mai kudi bace ita, sai dai kadarar da masu kudi suka yi wawa ce , jarin mai kudi ce ita, takamar uwar dakan mai kudi ce

"Ka yi hakuri, ba zan iya hakura har jibi ba!" Ta fada a takaice a kuma kamilance

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" To bismillah ina jin ki"

Hajia ta kalle shi da kyau, ta kalli amarya, sai kuma ta basar ta ce" Dangane da abinda yake faruwa a gidan nan idan ranka ya bace ne, Elhaji ina so ka ringa sasautawa kana duba yaran nan da mu baki daya ka sani furucin baki dafi ne a rayuwar yayanmu idan ya zamo munana , yan amen na amsa an gama, ina kyautata zaton ko Ni bakinka na iya kammawa bale na y'ayanka, rayuwar duka nawa take, duniyar duka nawa........."

"Ki ce zuwa kika yi ki koya min yadda zan yi da yayana na cikina, ko kuma ki ce zuwa kika yi ki nunan bacin ranki dan na daki y'ar so ko y'ar da na haifa da cikina?" Ya katseta da sauri yana sake hade girrar sama da ta kasa ya ce" Gimbiya kin san cewa babu wanda ya isa ya shiga tsakanina da y'ayana, ko me zan yi tarbiyya nake basu, babu wanda ya isa ya koya min yadda zan kula da su ai ina fatan kin san da haka ko? " Ya fada yana dada hayayakowa tamkar zai tashi ya maketa

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonsa, a nutse ta ce" Elhaji, me yasa ba zaka zauna mu yi magana ta fahimta ba? wace zamu samu matsaya guda ba? ban isa na koya maka yadda zaka kula da yayanka ba, ban kuma zo nan dan ka daki Anmina ba, na zo ne dan in karra tunatar da kai cewar idan kana duka ka daka, ka karya du Kai ka gano tunda kai zaka dawo ka yi fadi tashin magani, ama ka kiyayi bakinka, kana fadin kalamai irin su yan iska, yan tasha, yan kaza da kaza....mahaifi kake,, idan yan amen suka amsa suka zamo mana yan iskan mu shiga ina? dan Allah dan annabi ka ringa sasautawa ka rufa mana asiri , komai ya yi zafi ai maganinsa Allah, ina anfanin wan....."

"Lahaula wala kuwata ila bilah, to uwata, nace sannu uwata, lalle Mala'iku sunna sama sunna tsine maki tunda har kike daga min murya!" Ya fada yana mikewa tsaye dan kamar zata masa fada ya gani bayan shi ke saka wando mai arzunzumi ita kuma ta daura zani

"Ai kam, ace Muryar mace a saman ta namiji ai ba kyau, subahanallah subahanallah " Matarsa ta cafke tana wani sisine kai

Hajia ta kalleta da sauri sannan ta sake maida dubanta kansa tana jin lokacin da wani irin murdawa da cikinta ya yi da zubar wani abu da ya bale mata mai zafin gaske da radadin ciwo nan take ta gane abinda ke shirin faruwa da ita, ama furucin Elhaji ya sa ta kasa kwakwaran motsi bale ta gane mai aukuwa ta auku, bayan dogon jira tun daga haihuwar *ANMI* Allah ya bada kuma mai abin ya masa sanadiya
Elhajin kuwa nan ya mike ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, balaki kwondo kwondo, tashin hankali kusufi kusufi yake sauke mata harda ikirarin ya sauta ba komai bane , dan walahi mai kudi yake maganin yan iska, da kudinsa yau sai ya kara mata uku reras yan sha tara su maye gurbin ta , baya son kayan wulakanci,

A hankali ta kama kujerar nan ta mike tsaye, jiri na dibanta ta bada baya dan ba zata taba iya duba abinda ke binta ba sai ta je dakinta, tana juyawar idannuwansa suka sauka a dunkulen jiki baja baja jikin hijabinta da kuma kujerar dakinsa

A rikice ya zubawa jinnin ido, murya sama sama da rawa rawa ya ce" Ke, jinnin meye wannan? jinnin me kike zubarwa bayan kina da yaron ciki? bakin ciki zaki yi min? cikin zaki zubar? walahi idan kika zubar min da ciki sai na yi shara'a da ke , innalilahi Wa inna ilaihi raj'une wannan wani irin mugun hali ne da bakin ciki?"

Dakatawa ta yi idannuwanta na gannin bibiyu uku uku, jiri na dibanta , jinnin na jikinta ta zubawa ido, kallonsa take yi tana jin wata wutar kiyaya dake mamaye duk wani digon tausayi ko son zama da mutun da ya yi saura a zuciyarta da shi na shafewa, dan ba zata kawo maganar soyaya ba, dubansa take yi ido cikin ido tana tunanin anya ba a banza ta zo duniya zata koma a banza ba kuwa? bakin cikin dake karra hauhawa a cikin ranta ke toshe duk wani kofar jan numfashin dake hancinta yana barazanar kaita kiyawa, kallon tsana ko na kaicon kai da take binsa da shi da tunanin wato ita injin haifa masa ya'ya ko? suka hadu suka rufe idannuwanta suka makata da kas a tsayen da take tana kallon sa

A birkice ya karaso inda take kwonce yana dakawa amarya tsawa yana fadin ta kama masa su dauki Hajia, dan duk wuya duk dadi ya san yana son Hajia, duk rintsi kuma ko rai ta bata yana damunsa a cen kasan zuciyarsa, shi dai ya kasance irin mutanen nan dake azabtar da wa'inda suke tare da su ciki kuwa koda masoyansu ne, kasa hakuri ya yi ya dauketa ya yi waje da ita yana ihun kiran a bude gida ya sakata cikin mota ya ja kiiiii tamkar zai tashi sama ko takalma bai dauka ba ya nufi babar asibitin rashin lafiya da ita , shi da zai kaita ta haihuwa duba da garin DAMAGARAN asibitin haihuwa daban , ta wace ba haihuwa ba daban

kasancewarta likita, kuma ta samu rakiya daga wajen baban mutun irinsa ya sa sunna zuwa aka amsheta Du kuwa da irin yadda suka gane halin da take ciki suka karbeta domin babar likita ce itama kuma su dakatar da abin ko su bata kula sunna iyawa

Sai dai yana tsaye a kan kaffafuwansa yana sake jaddada kar a saki namiji ya duba masa mata, a gaban likitocin kuwa ido da ido yake turawa duk wani likita namiji Allah ya isa da fadin sankacecen kwarata ne masu abu a hannu , sun fake da zama likitoci to walahi su da gimbiya sai dai gani sai hange matarsa da

1 / 64