Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   7 / 64

18K to 21K   out of 190.8K words

shekara ashirin da daya yanzu ka manta ne? shekarunta ashirin da wata tara cifffff a watan azumi aka haifeta a shekarar da na zo gidan nan, aure kuwa ba zaka yi mata na dole ba a barta ta yi karatunta ta fitar da zabinta ko ta iya jurewa da hakuri da halaya idan Allah ya bata wanda sai an jure din zata fi yi in tana sonsa kafin ta tsane shi!"

Tana fada tana nufar hanyar fita ne, dan walahi ba zata iya masifa ba, irin yadda ya mike kuwa tabas a yau sai sun raba hali, ai kuwa yana gannin ta fita ta rufo da karfi ta murda kyyyy ya bi ta dayar hanyar rai bace ya bude ya nufi baban falon da idan ya je dole sai ya tashi ya'yan, ama ba wannan bane damuwarsa burinsa ya rigayi gimbiya isa bangaren ta kar ta rufe dakinta bai rama abinda ta masa ba, shi? shi gimbiya zata wulakanta? shi? walahi sai ya rama

Yadda ka san maii kannanun shekaru haka ya bude da gudun tsiya yana shigowa tana murdawa dakinta ky


Ai kuwa ya ja ya dakawa kofar kutuho yana bude murya da karfi ya ce"
07/12/2024, 14:50 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na Shida (6)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*


*META FORCE*

*menene meta force*

business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force

*shidai meta force crypto currency* ne

kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency

akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba

yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai

*TACTILE*

1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars

hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira

*Spillover*da*over flow*

wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu

to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*

*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja







LABARI



Rai bace ya ce" Ni zaki wulakanta da girmana da darajata in ringa fadi kina gasa min magana a kan y'ayana malakina? to ki hanna in kin isa ki hanna In gani, aikin banza aikin wofi an fada maki tsoronki nake ji da zan ringa lalaba ki kina min bore?"

Tun kasarniyar bude kofar mama da budowar tasa kofar suka tashi jama'ar gidan, sai dai yaran sun saurara ne sunna sauraro, amarya ce kawai ta fito a gigice tana kallon ikon Allah, murya a rarrabe ta ce" Elhaji lafiya? me ya faru?"

Sama sama ya ce" me zai faru da ya wuce wannan mata dake son nuna min iyakata da gidana da y'ayana? dama sai da aka min hannunka mai sanda a kan auren yar boko, yau an zo karnin da Ni miji zan cewa matata wai zan yiwa y'ata aure tace ba za'a yi ba? har Ni zata kalla ta zagi auren soyayya? tana nufin Nine banzan kennan? ki fito gimbiya ki ban fashin bakin yarenki!" Ya karashe da karra daga murya

Amaya ta ja baya, ta rasa farin ciki zata ji ko akasinsa, fada dai tana so ta ga sunna fada ama wannan sam bai wani birgeta ba

Baba ya ci gaba da fadin" Aikin banza, ke kin isa ki min isa da abinda na haifa, ko Khadija ai baki isa ki hannani rawar gaban hantsi da ita ba bale Karima, in sha Allah ki rubuta ki ajiye na yiwa Karima aure na gama, sai in ga wanda ya isa ya hanna"

Amarya ta yi gaggawar fadin" Au, wai da Karima ka yiwa miji tace ba haka ba? lalle Hajia akoy kokari, to ke ai baki isa ki hanna uba iko da ya'yansa ba ko?"



Kasa kasa mama ta ce" Haka fa, ki kama min baki, kin san halina sarai walahi zan gigita maki tunani, ki bar uban y'ar yayi ikon da ita in gani, Elhaji ka rubuta ka ajiye in dai ba yarinya tace ta yarda da wannan lamari ba ba za'a yi mata ba, kai sai in maka ka wajen yan human right fa, baka Sanni bane!"

Sai da baba ya sake riƙe kofar nan ya jijiga ama ko gezau bata yi ba, da wani bacin ran ya ce" Rabe mai kofofi Allah ya isa tsakanina da kai da ka saida min kwadon kofofin gidana sa barawo kuka, lalle yau da na nunawa hajia Nine mijin itace matar, ba human right ba ki kaini kungiyar gaba da haka zan nuna maki karfin ikon mai kudi da mai ilimin boko ba daya bane, zaki gani Allah ya nuna mana mijin da na yi mata zai zo kuma za'a daura mata aure da shi, in banda rashin tsoron Allah y'ar ashe ta gandame ban sani ba, to gaba dayansu zan hade in yiwa auren su karra gaba, ai Ni in yarinya ta wuce sha takwas a gidana ciyar da itama haramun ne, zaki ga iko kuwa gannin idannuwanki"

Haka ya wuce yana ta bambami, ita kuwa amarya tana biye da shi sai hakuri take bashi kasa kasa yana sake daga murya, dan idan kana so fadansa ya ki mutuwa ya ringa yin fadan kana bashi hakuri, to fa kamar wuta ce kake zubawa fetur

Sauran yaran du kwonciyarsu suka yi banda Karima da ta ji hankalinta ya tashi ta nemi rasa nutsuwarta,
Bata jima da ajiye waya da saurayinta ba, bata jima da karbar kalaman soyaya iya kalamai da alkawaruruka ba
Bayanan nan na nufin ita Karima abanta ya yiwa miji? Kan ubancen, ai kuwa ba zai yiwu ba, tabas ba zai taba yiwuwa ba, to ai ita bata ga namijin da zai iya da ita Bama in ba wannan saurayin nata ba, yanzu haka cikin yaran shagonsa ne yake son hadata da daya ya cuceta, wannan ai cuta ce walahi talahi sakata a uku ake son yi, Bama zai taba yiwuwa ba, idanma mama bata kai shi human right din ba to ita zata kai shi a boye a boye sunnanta dan a ja masa kashedin kar ya saki ya yiwa y'arsa auren dole a bar kowa ya zabi abinsa ta yadda zai iya rayuwa da abinsa duk wuya duk rintsi, sai kace shi din an taba yi masa auren dolen tsabar mugunta irin ta babansu!, wannan tashin hankalin ya hannata barci, domin wata iriyar giyar soyaya ta gama dibarta ta saurayinta, bale irin yadda ya zamo mutun mai zinar harshe hakan yayi daidai da ra'ayinta, dan gani take yi babu ita babu ustaz domin ba zasu taba iya huce maka takaicin soyaya ba


Bayan sun dawo daga ɓangaren mahaifinsu suka shirya suka fito aka kwashe su aka kai su Makarantar boko, a lokcin ne itama Hajia ta fito a shirye ta yi tafiyarta wajen aiki, ba dan hutun da ta dauka na jinya ya kare ba, no sai dan tana bukatar samun nutsuwar zuciya sannan tana son zuwa ta gaisar da Hajiar Larabawa dan ta kwana biyu bata lekata ba


Kusan karfe goma da rabi da ya fito a shirye zai tafi kasuwa, nan amarya ta sanar masa hajiarma ta tafi wajen aiki, wannan bayanin ya karra dugunzuma ransa , ya fice a gidan ya nufi hanyar gidan Hajiar Larabawa dan kuwa walahi ba zai yarda Hajia ta masheshi shashasha ba, bata isa ba

Kamar kulun ya samu tarba ta karama a wajen sarakuwar tasa, wace da wani mai jin kunyar ne Bama zai iya kawo karar y'arta a wajenta kai tsaye ba, sai dai magana ake yi ta Baba, kai tsaye ya budi baki ya fadawa Hajiar Larabawa abinda ke tafe da shi, wanda itama hakan ya matukar bata mata rai har ta masa alkawarin magana ta wuce in sha Allah Hajia ba zata zama karan tsaye a tsakanin hukuncinsa da ya'yansa ba in dai hakan bai kaucewa addinin Musulunci ba, da wannan farin cikin ya bar gidan bale da Hajiar ta ringa kirta fadan a kan me zata fita aiki bata yi masa salama ba? lalle Hajia karama na daf da sakawa a soke maganar zuwanta aiki gaba daya ta zauna ta yi ibadar aure, wannan magana ta fi komai dadada masa zuciya har ya ringa addu'ar Allah ya sa idan aka mata fadan ta ki ji, gobema ta fita bata sanar masa ba ya dawo ya fada shikenan Hajiar Larabawa ta soke mata zuwa aikin kowama ya huta, da haka ya nufi shago zuciyarsa fesss, dan ya riga ya sani matar da yake aure an isa da ita a gidan su, shi yasa idan ta nemi tayar masa da hankali yake makata cen ya mike kafa abinsa, Allah yana gani idan yana adu'a yakan sako Allah ya karra jan da kwanakin Hajiar Larabawa ta ci gaba da tankwasa masa wannan jarabtar da ALLAH ya sako a rayuwarsa, dan ya sani Hajia jarabtar zuciyarsa ce wace bai isa ya cenza ba


Yana karasowa anguwar su Elhaji Hamza ya gane cewa tabass oga ya kusa dawowa tun daga yadda ake ta shige da fice n gyare gyaren abubuwan da sam basu wani lalace ba, ama tsabar kudi an rasa me za'a yi da su ake zuba su a wannan fannin, sai gyara ake yi ba ji ba gani, kuma sababin masu tsaro sun karra zagaye gidan Abu dai kamar za'a iya tare mutuwar daukar bawa, sai dai kashhhh da mutumen da kayan duka mallakar mai sama ne zai amshi abinsa a Lokacin da hakan ya raya masa.

Hajia na cikin adaidaita sahu a hanyarta ta tafiya gidan Hajiar Larabawa tana tunanin dalilin da yasa Hajiar tace ta zo tana son ganninta har suka iso kofar gidan ta sauka ta biya ta nufi cikin gidan tana gaisawa da almajiran kofar gidan dake karatu

Bayan sun gaisa da Hajiar ta zauna da kyau tana cire hijabinta tana fuskantar Hajia ta ce" Hajia yanzu sai in yi ciwo in warke ba zaki je inda nake ba? in na mutu shikenan na tafi bamu gana ba?"

Hajia ta yi murmushi tana muzgutawa da kyau ta ce" Abu dai kamar an girma ama yayar gambo kulun cikin abin yarinta, to Ni yanzu da ba kafar kirki ba in je gidanki in yi me? ai gashi kin warke din kin zo ke, Allah dai ya karra lafiya""

Mama ta yi murmushi tana ajiye kofin ruwan da aka kawo mata bayan ta sha

Hajia ta nutsu tana dubanta ta ce" Me ya haɗa ki da Mai gidan naki?"

Mama ta kalleta da sauri, sai kuma ta gyada kai tana ayana' Lalle, lalle Elhaji wato karana ya kawo wajen ta larabawa ko?, ikon Allah lalle Elhaji ya cika son kansa da yawa, shi kuma bashi da wanda zai tirke shin ma bale ka kai karar tasa, koda yake ba laifi tunda ya gane inada mafada!'

A bayane kuwa bayan sadda kai babu abinda tace dan bata san me zata ce ta larabawa ta dubeta ba

A tausashe Hajia ta ce" Ama ai kin san girman darajarsa a kanki bale yayanki ko? kuma kin san yana da cikaken iko a kan abinda ya haifa ko? sannan kin san ba auren wuri bane bale ace yarinya bata kai ba ko? Ni sai in rasa me yasa ya'yan yau abin a ji su da mijin su baya musu kadan, yanzu wannan abin a ji kin yi musu da maigidanki ne y'ar nan? haba karama shekaru fa sun gama taruwa zuwa yanzu ya dace ace an gama hardace dabarun hanna y'an yaya daka yajin da bashi da anfani dan kuwa nan da shekara biyu zai zamu yi fatan kina rungume da d'an jika daga wajen takwara ko? ama sai ace abin kunya geme geme da ku baku daina rigima ba? haba yayar gambo in an girma ai cinye komai ake yi a kawar da kai bale ke a nan dai a yau banma ga me ya maki ba, bawan Allah mijinki yana son ki ama kina nemansa da fitina? ki ringa tausayawa na Bugaje dan Allah ku zauna lafiya, kin san baya son shiga adaidaitar nan, kuma kika fita baki sanar masa ba? Karama a kan zaman aurenki walahi sai in haramta maki aikin nan fa?"

A zabure mama ta dago kanta ta kalli hajiarta, da sauri ta sauko kasa ta karasa daf da kaffafuwan Hajiar ta rike tana sada kanta a hankali ta ce" Hajia, dan Allah ki yi hakuri, a bar maganar in sha Allah ba zan kuma ba, dama gani na yi yarinyar batama san mutumen da ya zaba matan ba, kar aje a tauye yarinya, ama tunda kika yi magana na bar maganar ki yi hakuri kin ji?"

Hajia ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Shikenan, ama ki tabbatar da kin same shi ki bashi hakuri, yaya kuke iya yin barci miji na fushi da ku ne y'ayan yau? Allah ka rufa mana asiri da zamani ka sasauta mana rikicin zamani"

Mama dai bata ce komai ba, dan ta riga ta san bafa komai Hajia zata gane ba, Elhaji ya riga ya cuceta da yake zuwa ya zauna ya fede laifukan da ta masa a kan gaskiyar ta a yarda a hukuntata shi kuwa a kulun yana cikin kirta rashin mutuncinsa ama bata da bakin fada bale a gane har a yi mata adalci , ta tabbata du ranar da ta rabu da shi sai ta nemo masu fara shigowa gidan nan da ita dan ta larabawa na iya yi mata baki a kan zaman aure koda kuwa wannan zaman halaka ne ga zuciyarta, nan dai ta ɗan karra jimawa dan ba zata je gidan da wuri wuri ba sai zuwa saukar yara daga makaranta



*KARIMA*

Tun a makaranta ta sanarwa mahaifiyarta abinda yake faruwa

Mahaifiyar Tata ce da kanta ta tsara mata ta yi ciwon cikin karya idan an bata damar ta je gida maza ta zo gidansu tana jiranta


Malama ce aka yiwa tunin aikinta, domin ta nuna ciwon da ya sa aka bata damar zuwa gida dan ta nuna maganin ta a gida kuma direbansu yana nan baya taba ajiyesu yayi nisa da makarantar zai iya kaita ta sha

A lokacin da ta fito daga makarantar a boye ta samu ta fada adaidaita sahu ya nufi wajen mamanta da ita tana auna lokaci dan so take ta je ta dawo su tafi gida tare

Ta samu mamanta ta sake fada mata komai kamar yadda ta ji ta ɗora da fadin" Mama, walahi ba zan yarda a min auren dole ba, ba zan taba yarda ba, kin ga Ni ga wanda nake so ama yake son min auren dole?"

Mahaifiyarta dake kallonta ta yi tsai na dan lokaci kafin a tausashe ta ce" Kin ga, saurara Karimar mama, kina ji? kar mu yi gaggawar yanke hukunci kin ji? kin ga mahaifinki baban mutun ne, idan har wani baban mutun din ya samo maki wanda zai sa ba ke ba ko ki in warke ai an gama ko autana?"

Da mamaki Karima ta ce" Mama, kina nufin idan mai kudi ne in yarda a yi? to in yi yaya da shi mudansir din?"

Mahaifiyarta ta ce" Ke kuwa, kar ki zama gaula mana, kar ace baki da wayo dai Karima, da Elhaji da D'an Elhaji ai gwara Elhajin ko? soyayar me Allah na tuba, ke ki nutsu du soyayar da ba kudi aikin banza ce,, mu dai zuba ido mu ga wanene in har wani baban ne lafiya lau sai mu sha bikinmu ita y'ar bakin ciki sai ta mutu, dan ba y'arta bace ba

7 / 64