Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
yi kokarin nan ko a dace"
Muhammad ya yinkura a nutse ya ce" Baba gaskiya wannan ba hurumin malan bane, wai me zai hanna a kwabi yarinyar nan a koya mata hakuri da juriya da addu'a har a ga an cinyewa jarabawa? mema ta taɓa ganni na gigitar rayuwa ne Ni ita?, dan girman Allah a haka tana tunanin ko auren nata yayi zai mutuntata ? shikenan ita ba'a ce mata a'a ko me ta yi niya amsa ake yi ace da ita shine daidai? fisabililahi a garin hausawa muke sannan musulmai ne mu, ina hadin malan ya je ya nuna zai je kauye neman maganin da zai dawo ya yi mata dan ta hadu da matsalar iska, ya zamo a nuna mamanmu bata nan kennan ina zata je? ana neman alfarmar ta je gidan da mutumen suka yi soyaya ya tare da matarsa yau yau ta zauna wai har malan ya samo maganin saboda ba za'a iya tafiya da ita Niamey a haka ba, fisabililahi sai kace muna garin da babu mafada shikenan yanzu ko su suka nemi ta je ta zauna a gidansu ai an kiya bale ace mune zamu nemi alfarmar a wulakantamu? shin ba'a aiki da daraja da mutunci ne? wai kudin dai shine kawai mai mutunci fisabililahi? yaya za'a yi ace a yi wannan abin ita yaya zata je ta rayu a gidan ne hankali kwonce? bafa alkhairi zata aikata ba dai shari saboda idannuwanta sun riga sun rufe, kunna ganni sai kiransa take yi kamar wace ba zuciya a kirjinta???? dan Allah baba ku duba lamarin nan ku yi shawara mai kyau, kamata yayi ace kun kwabi Mufeeda, ku nuna mata ba fa lalle abinda kake so bane Bama yake zame maka alkhairi, ku nuna mata ta gyara halinta ta je ta kadaice kanta ta nemi mafita a wajen wanda ya haliceta, na rantse Allah zai kawo mata sauki cikin ruwan sanyi ta same shin da shi da zuciyarsa da dukiyarsa kaf ba tare da an wulakantar da kai ba"
"YANZU Abdullahi kana zaune d'anka ke wulakantani? Muhammad baka san waye Ni ba ko? dan ka ganni a cikin gidan nan a zaune da iyalina ne zaka raina min wayo? kai har me ka sani da rayuwar da duniyar baki daya? me kake takama da shi da har zaka budi baki ka ringa nuna min cewa y'ata bata da tarbiyya a kan abinda yake gaskiyar ta? kai har ka isa ka shiga tsakanina da d'an uwana?, me kake takama da shi ne? kai ka isa ka hanna shi sama min mafita? Mufeeda sai ta je ta zauna a gidan nan ta yadda za'a yi gagawar daura nata auren da shi itama, babu ruwanka da maganar wai ya so ta ko akasin hakan, karma ya so tan mana!, kai ka san irin son da yake yiwa Mufeeda? duk inda y'ar mahaukacin nan ta fito asiri aka yiwa AL'WALID da har ya kai kansa gidan wannan mutumen ya auri y'arsa, da gani yadda bashi da kyau haka itama y'ar take!, Abdullahi a gabanka ko? ko dai da gaske yake ba zaka yi min wannan alfarmar ba?????? ina sauraronka yaronka har yayi girman da zai shiga tsakanina da kai????"
ELHAJI Maiga ya fada sama sama, ya zamo Malan Abdullahi kansa a kasa jikinsa har rawa yake yi ya rasa madafa ga tashin hankali
Dagowa yayi lokacin da Muhammad zai karra yin magana a kausashe ya ce" Wato Ni zaka saka a gaba da kanina ka wulakanta? to shikenan gama, karasa abin fadin dake ranka sai ka rufe mu da duka"
Matarsa ta sake dubansa , yau kam ta gaza hakura, a hankali ta ce" Malan"
Da sauri ya dubeta idannuwansa har sun tara kwallah ya ce" Na'am Humaira? kema yau kin fito ki wulakantanin ne?"
A hankali ta sada kanta, kirjinta na zafi sosai, innalilahi wa inna ilaihi raj'une wannan wace irin jarabawace mai zafin gaske da kulun ta kasa cinyewa, ? mu'amalar mijinta da d'an uwansa kazantaciyar mu'amala ce da musulunci baya so, sam ba zumunci bane kaskanci ne da wulakanci da raini da shiga hakin mutun
Malan Abdullahi a raunane sosai ya dubi Elhaji Maiga ya ce" Kana nufin in je in samu Elhaji Hamza da batun Mufeeda ta je ta dan zauna min in je kauye in samo magungunnan da suka dace dan a yi mata magani, in nuna maman yaran nan ta tafi biki gida, kuma ba za'a iya yin tafiya da ita yarinyar ba?, haka dai kake nufi?"
Elhaji Maiga ya ce" Eh haka yayi Abdullahi "
Malan ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Yanzu me zai hanna mu samu wata mafitar? yaya zamu ɗorawa yarinya ciwo irin wannan da bashi da dadi ko kadan ? a ganina ba mafita bace, in dai shawarata kake so in bayar, me zai hanna mu saurari bayanin shi Elhaji Hamza din tunda da kansa yace zai yi magana? ko ba komai idan suka neme mu da kansu zai fi ko Maiga? duba da yannayin nan na rayuwa ko yaya kake gani?"
Mufeeda ta ɗora kanta saman mahaifiyarta ta daki kuka mai tsuma mai saurare, hakan ya sake dagula lissafin mahaifinta, har jikinsa rawa yake yi ya dubi malan a kausashe ya ce"
07/12/2024, 15:14 - samiraharounayacouba: *FARKON GANIN IDONA*
PAGE 35
TALLAH TALLAH TALLAH TALLAH
*Zumar 3in1 zumace ingantacciya mekyau megyara jiki sosai zatasaka kayi bulbul breast sugyaru hips yafito kiyi yar duma duma hajiya bazakigane abundanake fadaba dai kinshata zakigane*
*08030861857*
*Zumar breast Zumar hips duk munadasu masu inganci sosai da sosai*
*Akwai pills na 3in1 shima aikinsu Daya da zumar 3in1 gawayanda basashan zumane mukayi daminsu*
*08030861857*
*Infection flusher Ingantacce maganine mai magance dukwata matsalar mara Kai harda rashin haihuwa yanayi banahaufi akai don angwada angani mace indai rashin niima ne na cutar sanyi yararaketa kuraje kaikayi dattin mara zonabaki infection flusher kisha mamaki yar uwa Insha Allah zakigodemin*
*Kayanmu guarantee ne sai angwada akansan nakwarai location gombe munaturawa koinah Insha Allah* *08030861857* Kira KO WhatsApp Insha Allah
LABARI
A kausashen nan ya ce" Kana nufin dai ba zaka yi ba?, ba laifi ku tashi mu je, ku tashi"
Matarsa ta fara mikewa tana sake turo dauri gaba, dan dama ba shiri suke yi da yan gidan ba baki daya, saboda ita bata son mutun mai kumbiya kumbiya da son nuna shine na Allah din nan
jikin Malan Abdullahi gaba daya ya kwashi rawa kamar zai kifa ya mike yana hada hanya da kyar ya riko Elhaji Maiga ya ce" Ka yi hakuri Maiga, mafita na so sama mana da ta fi wannan, ama tunda haka kake so in sha Allah sai ka saka ranar da zamu je sai mu tafin, ama wai kana tunanin zasu fi jin maganata Ni talaka ba kowa ba a kan taka??? "
Wani irin hawaye ya kuncewa Muhammad, ya sada kansa kirjinsa na zafi sosai, mahaifiyarsa kuwa tuni dama ta yi ciki tana kukan dake fitowa tun daga cikin zuciyarta......., wato basa Sannin su ba kowa bane sai sun hadu da wannan bawan Allah da yake jini dan uwa shakiki na wanda yake jagora a duniyarsu, sun iya talaucinsu hakan ya sa ko a anguwa ana mutunta su banda idan wannan bawan Allah na kasa, in fa ya zo basu da sukunin zuciya saboda a gabansu yana iya wulakantar da jagoran rayuwarsu
Elhaji Maiga ba kunya ba komai ya ce" Sai da na gama yin dogon nazari kafin in kawo maka wannan maganar, walahi sun fi jin kunyarka fiye da tawa saboda ilimin addinin musuluncin da Allah ya baka, baka ga ko gaisheka AL'WALID zai yi sai ya dan rage tsayinsa ba? kuma ai ba kai ka haifi Mufeeda ba ko? kawai daraja ce irin ta wanda ya riki Alkur'ani Allah ya baka, in dai ka je din zasu dubeka da daraja fiye da Ni, ba na je ba? a falonsa na baki fa ya barni da kakan yayi hayewarsa sama , kawai ka shirya Gobe nake so mu je, in sha Allah gobe ma zo mu dauke ka mu wuce"
Malan Abdullahi ya gyada kai a sanyaye ya ce" Na zata a nan zaku kwana ai duba da dare yayi?"
Elhaji Maiga ya dan dafa kafadarsa ya ce"A nan? To a ina su zasu kwana? ka ga Ni ina iya kwana a dakinka, matsalar sune ba zasu iya kwana a nan ba, ama zamu zo din goben kawai in sha Allah"
daga haka suka wuce da iyalansa malan Abdullahi kuwa yana tsaye kamar an dasa shi a wajen, da kyar ya juyo ya ga Muhammad kansa a KASSSSS
Zuciyarsa sai da ta yi rauni sosai, ya karaso ya zauna daf da shi a sanyaye sosai ya ce " Ka san me yasa nake ta hakuri ina cin kowani irin kashin Maiga? saboda amanar da mahaifiyarmu ta bari a tsakaninmu da alkawarin yin zumunci da junna har muma mu bar duniyar a lokacin da take cikin ciwo, ka san a da ba haka yake ba, kai ko farkon soyayar yarinyar nan da wannan mutumen shine ke tsawatar da wasu abubuwan , daga baya ne abin ya cenza ya zama wani iri, inaga tun lokacin da ya fada muguwar damuwar nan da aka kusa rufe shi saboda kudin gwamnati shi Elhajin ne ya shiga lamarin bayan ya bashi kudi masu ƙarfin gaske , to sanadiyar sa har girma ya samu a ma'aikatar tasu, shine dalilin da yasa ya zama baya ji baya gani a kan lamarin da ya shafi yarinyar nan da maganarta da mutumen nan, kuma ban ga laifinsa ba ai kowa da yadda yake daukan rayuwa, idan kana kara mutun kuwa ai bashi da kamarka da zarar anfanin da kake masa ya kare ne kuma sai ka ga ya bi wani sarkin, wato wani dan adam din sai Allah kawai, kana ji Muhammad? na san ciwon kaina fa, Sannin ciwon kan nawa ne ya sa na jajirce a kan dole sai na yi zumunci dan in kasance cikin wa'inda Allah zai duba da rahama sanadiyar wannan zumunci nawa...., in ka kula ba haramun bane mu yi haka din, saboda a hannun mata masu nagarta ne zamu sakata in har an anshemun, kuma in har auren nan ya tabbata Allah ya san me ke boye a cikinsa...., dan Allah Muhammad Ku yi hakuri kun ji? komai nada lokaci ku tayani samun ladan zumuncina, ku kawar da kai ku min addu'a, idan kuna haka mahaifiyarku gazawa zata yi, in ta gaza kuwa in bi ina in ji sanyi????, ku yi hakuri Muhammad ka ji?"
Muhammad da girmansa da komai ya fashewa mahaifinsa da kuka yana sada kansa a hankali ya ce" Baba ka yi hakuri dan Allah ka ringa kiyaye idannuwan mu, baba mun gaza, walahi zuciyarmu ba zata iya ba, mun ga na yarinta mun ga na fara girma, yanzu mun fa kai wajen da burinmu sisin wani ma ba zaka Duba ba bale tasa, baba burina a rayuwa in ga na kai wajen da zan daga martabarka kaima ta hanyar aljihu, dan na kula an riga an yi rikicewar da idan baka da komai kai ba kowa bane, sai dai kashhhh du dogon karatun da na yi na jajirce ba dare ba rana na gama aiki ya gaza samuwa sai dan buga bugar nan, ta yiwu a haka zamu gama har mu mutu, alhamdulilah a haka dinma tunda har Allah ya bamu ci, sha da sutura, kwadayi ne da burin gannin samun ci gaba a kulun nake karra rokon karri, in sha Allah zamu tayaka, ama ka ringa kiyaye idannuwan mu baba, zan zo in raka ka, dan walahi zuciyata ba zata taba samun nutsuwa ka bi shi kai kadai ba, domin ya riga ya san cewa har kasa ta nade kai nasa ne komai tsiya kuma kana tare da shi , yana iya yi maka du abinda ya so"
Malan Abdullahi ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" To shikenan, jibeka kato da kai kana rusa min kuka share hawayen tashi maza ka je gidanka, bari in je in bada hakuri Ni dinma "
Ya karashe yana murmushi, shi dai Muhammad ya share hawayensa ya mike ya ja babur dinsa ya fitar sannan ya nufi gidansa zuciyarsa cike da kunci da riko mai girman gaske na uncle dinsa, du yadda mahaifinsa zai guji abin nan ba zai yiwu ba, ba zai taba iya gannin girman mutumen nan ba saboda a gabansa yake wulakanta iyayensa.
Washe gari a gidan Aba
Tunda safiya ta yi amarya ta samu Mama a dakinta bayan ta nemi izinin shiga ta bata dama ta zauna tana dubanta ta ce" Hajia maganar salama da aka bada na masu kai amarya jiya, ai kin san kanaina basu je ba saboda Elhaji yace ba zasu je ba, ama kuma sa yi jiran nasu ai ko? tunda dai sunna gidan nan komai aka yi da su"
Mama ta dubeta ta ce" Salama?"
Amarya ta ce" Eh, ba na ji jiya da suka dawo sunna cewa Elhaji ga adadin kudin da aka basu dan kawai sun kai amarya?, wai wanene aka aurawa Anmy haka?"
Mama ta dubeta da dan mamaki , sai kuma ta basar ta ce" Salamar dai zan anso masu a wajen su Fateemar, ai ba zata taba ba sai ta zo an ba kowa in sha Allah kar ki damu"
Amarya ta dan tabe baki, ba wai asalin maganar salamar ce ta kawota dakin ba, zuwan nata biyu ne, so take yi ta san waye takamaimai mijin da aka aurawa khadija da har za'a dauki makudan kudaden nan a basu dan kawai sun kaita dakinta? Sannan tana so ta gane maganar cikin nan, domin abubuwan nan biyu sunne ke hannata barci a kwanaki biyun nan , yadda take gannin rana haka take gannin dare idan ta shiga dakinta, gashi ita ko batan wata bata yi da shi ba tunda ta zo gidan, kuma ai ya haihu da sauran matan ko? Bayan Khadeeja ma ai ya haihu da wasu biyu , ko dai tsabar kiyayar matar nan tana iya yi mata abinda zai hannata haihuwar ita? hankalinta na mugun tashi idan ta yi wannan tunanin, ta yi kiran malamanta kowane ta bashi damar yi mata bincike mai sunna bincike dan kuwa in har ita ta yi mata asirin nan walahi sai an daga musu Alkur'ani a gidan dan ba zata yarda ba.
Amarya ta ce" To ai baki bani amsar sirikin namu ba, wannan baban kamu da muka yi haka?"
Mama ta dakatar da jan carbin da take yi, a nutse ta fuskanci amarya ta ce" Sunnansa kawai na sani kamar yadda kika sani, ko wanene kuma wannan Sannin gaibu sai Allah sai kuma lokaci zai bamu damar Sannin halayarsa, ko kuwa idan a kagauce kike ki samu mijinki ku yi bayani, ki yi hakuri carbi nake ja kafin yan kai Gara su taru a hau wani aikin kuma"
Daga haka Mama ta sake jan hijabinta da kyau ta ci gaba da jan carbinta a nutse
Kasa magana amarya ta yi zuciyarta na kunna sosai, kawai sai ta juya ta fice a dakin tana ayana' ba zaka taba Sannin abinda ke cikin wannan munafukar ba, a gama taron nan ki gani zan je da kaina a min binciken da ya dace a kanki kuma zan dauki matakin da ya dace!, in kuwa wani cikin ne da ke shima sai ya bi dayan in dai ina raye'
Bayan ta fita Mama ta jima tana kallon kofar da ta bi ta fita kafin ta sauke ajiyar zuciya ta dan hada tagumi na tunani......, wato ita dai ba zata taba so ace ƴaƴanta sun biyo hanyar da ta bi ba, shi yasa tun jiya har zuwa yau cikin tunani da addu'a take, tana yi musu fatan inma auren wata mijinsu zai yi kar a hade su, ita kam bata ji da dadi har ga Allah, bale wannan yarinyar so take yi karfi da yaji sai ta kaita inda za'a ce lah Usainar da kanta ce ta yi abu kaza?
Ajiyar zuciya ta sake saukewa kawai ta mike gannin takwasss ce zata yi ta cenza hijab dinta ta feshe jikinta da turare ta nufi bangaren Elhaji saboda ta ji bayani a kan masu kai garar dan ta tabbata yanzu sa hadu a je a kai a gama, cen kasan zuciyarta kuwa da Anmy ta kwana, tana ta tunanin yaya yarinyar take? duba da bata da lafiya.
A nutse ta tura kofar bayan ta bude daga baya ta shigo, sai ta ja ta tsaya sakamakon muryarsa da take ji yana fadin" Yauwa Habu, irin kallon nan da ka yi a gidan cen shi zaka fara yi, ya zama wajibi mu ci uban mutumen nan, uban budurwar mijin Anmy ai kishiyanmu ne, in an jima karfe hudu na yama ku hau shadojin nan ku sameni a shago mu shiga motar mu je, Ni da ALLAH ya bani zaradan samari, in sha Allah sai mun ci ubansa, ku tashi ku je ku fara shiri"
Sunna mikewa mama ta shigo da sauri tana dubansu ta ce" Kai, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, kai ku dawo min nan ku dawo"
Zaratan samarin nasu biyar suka dawo kawunnansu a KASSSSS saboda sun gama hardace Muryar mamansu ta zaman lafiya da akasin haka
Aba ya dubeta ya ce" To Gimbiya lafiya da shigowar sasafe haka?"
Mama ta dube shi , eh lalle, haka fa, zai ce haka kam
A tausashe ta zauna tana dubansa ta ce" Yanzu babansu fisabililahi ka kyauta kennan? me kuma kake son koyawa yaran nan? kar ka manta fa du abinda ka koya musu zasu zo su baka harda a gida ne ko ba dade ko ba jima"
Ran Aba ya fara ɓaci yana dubanta ya ce" Kin ga gimbiya ki kiyayeni? kin ga ki kiyayeni? su bani harda kamar yaya? so suke su shiga wuta ne? na ga ai ubansu ne Ni Ko?, to bari ki ji y'ayana sun san zafina, nan na zo jiya nace maki an min rankwashi an harbeni a tumbi kika yi biris da Ni, yanzu da Allah ya bani masu tsayawa