Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
allurar barcin ko an samu jinnin nata ya sauka
Ransa ya karra ษaci matuฦa, yana duban JARUKE ya ce" Me kuka sani ya haษata fada da shi AL'WALID din?"
Mahaifiyarta ta dube shi ta ce" Bana tunanin zata yi masa wani abu da zai sa har ya yanke irin wannan hukuncin a kanta, ko ba komai Mufeeda mai sonsa ce ba makiyiyarsa ba, ama ba komai itama yanzu sai ta kama kanta ta nemi mai sonta ta yi aurenta!"
Da mamaki ya dubeta ya ce" Ta nemo wani? kema kin san abu ne da ba zai yiwu ba, walahi babu wanda zai kashe min yarinya, shi ya san ai tana sonsa, ko me ta masa sai ya yi hakuri dan a kusa kusa ba zai taba samun wace ke sonsa irinta ba, ku je wajen nata bari in je gidan nasu, a san yadda za'a yi da yarinyata ko a hade in bata hakuri a mata kishiya ko a yi da ita!" ya karashe yana ruruko idannuwansa, wa'inda kana gani zaka gane mutun ne mai fitina da wulakanci
Ita dai uwar ranta a cinkushe yake, ta sani y'arta ta janyowa kanta wasu abubuwan, ama kuma har ga Allah ta ji haushin irin cin amanar da aka yi musu! sun dauki haka matsayin cin amana shi yasa ta so su kyale su, ama kuma uban ya nuna ba haka ba
----------------------------------------------------------------
Motarsa ya sake shiga suka dauki hanya tare da direbansa , motar sai kauri take yi na doguwar tafiya gashi ba'a shirya mata haka ba ama suka sake nufar gidan Su Elhaji AL'WALID
Sai dai sun taki rashin Sa'a, a yau an bude kofar baya ne kawai ana ta wanke gidan da shirye shiryen ranar gobe, ya zamo a kofar da suka zo shiga manyan dakarun sojojin mu masu hautsina hanjin ciki ne suka samu, basu samu fuskar yin maganar da su Bama, kawai bakin bindiga aka nuna musu cewar motarsu ta juya, domin a wannan ranar du isarka da takamarka ba zaka wuce ta wannan hanyar ba sai an gama wankin gidan da ake yi, kuma wankin na dan lokaci ne sai dai rashin sani ya sa basu zauna jira a nesa da gidan ba ya koma asibiti ransa a mugun bace suka zauna tare da ya'yansa da masu masa aiki ya kudiri aniyar kafin nan kafin ta dawo hayacinta zai san yadda yayi ya hadu da Elhaji Hamza, dan kuwa shi kadai yake son gani, ya san idan ya sanar masa halin da y'arsa ke ciki tabas zai dube shi, zai sam masa mafita, bai wani nemi d'an uwansa ba dan ya san babu abinda zai iya yi masa!..........................
*Precius dy, wato Babar rana, Rana mai daraja*
07/12/2024, 15:13 - samiraharounayacouba: ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*FARKON GANIN IDONA*
๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*๐ณ๐ช
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da tara (29)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ
๐0912 262 1080
LABARI
RANAR DAURIN AURE
Daurin aure ne da bai taba tunanin zuwansa nasa ba a kwana kusa kusa, sai gashi an fadi ranar da aka yanke za'a daura masa shi, da macen da ba zai nuna kamaninta ba, harma safiya ta yi aka tisa shi a gaba da shirin da ya jima bai yi ba, shiri irin na manyan kaya masu darajar gaske, dinki mai darajar gaske, wanda Baba Hamza ne da kansa yayi tsaye ya ciro kala uku ya da jikokinsa manya su hudu zaba , wa'inda a cikinsu du sa'anin AL'WALID din ne, domin girmarsu da yayi bai wuce da yawan shekaru biyu ko uku ba, ya katse masa motsa jikin da ya je ya fara ya tiso shi a gaba ya sha shiga ta babar Gari da y'ar ciki harda kafa hula tamkar shine angon sai kanshi yake bazawa fuskarsa kuwa ya kwace da fara'a tamkar gonar auduga suka nufo baban falonsa nan ya samu brothers dinsa suma sun sha shiga ta alfarma sai fira suke cikin fara'a da farin ciki
Dubansa ya sauke a kan Jameel dake kashe masa hoto yana fadin" Elhaji karami, bari a fara ajiye maka hotunan da zamu hada befor daurin aure, hanyar daurin aure, lokacin daurin aure da kuma after daurin aure"
Dariya Badamasi yayi ya ce" Wannan zane haka? Elhaji karami yau babar ranar sai ka motsa jiki? idan ka tadawa kanka gajiya fa?"
Al'walid ya sakar masa harara ya ce" Yaran nan ba zasu daina nemana da rigima ba, sunna manta ฦดaฦดansu ne ni ko baba?"
Baba Hamza ya ce" Mu je dai, so kake sai na gaji dan in kasa katabus a wajen daurin auren bayan amarya zan gyalo sabuwa dal, mu je ka yi wankan"
Dubansa ya yi a tausashe ya ce" Inace mu Hausawa Bama zuwa daurin auren mu"
Baba ya yi masa kallon shekeke a nutse ya ce" Muna zuwa kam, mu je sai fa ka je daurin auren nan"
Murmushi yayi ya shige cikin dakinsa ya rufo ya karasa direct bayi
Wanka yayi cikin nutsuwa ya fito daure da tawul ya karasa wajen turarukansa yana goge ruwan dake jikinsa yana hangen wayarsa dake saman gado tana haske tana daukewa
Karasawa yayi wajen wayar ya dauka ya duba domin numbar dake cikin wannan wayar numbarsa ce ta sirri
"Allah ya sanya albarka a aurenka, ina nan har yanzu ina jiran ranar da zan amsa sunnan wace ta fi kowa kusanci a duniyar ka, i love You so much gudaliya" Message din dake cikin wayar kennan bayan miss call guda biyu
A hankali ya lumshe idannuwansa kirjinsa na btng fiye da ka'ida
Idannuwan nasa ya bude sakamakon alamun bude dakin da ake ta gwadawa duda an gane a rufe daga ciki ba'a hakura ba, wannan kuwa ya san aikin baba Hamza ne
Karasawa yayi ya kimtsa jikinsa ta hanyar saka tufafin da aka ciro masa, sai dai bai dora babar rigar ba, hular kawai ya kafa bayan ya saka turarensa mai daraja da sanyi, sannan ya saka takalminsa kafa ciki ya riko rigar da agogonsa yana tafe yana sakawa hadi da soke wayarsa a aljihunsa
Yana fitowa falonsa ya ja da sauri ya tsaya zuciyarsa na wani irin amsawa sakamakon cikar da falon yayi da dangi, wa'inda zuwan wasu bangaren nasa a irin wannan lokacin saboda fitowar da aka yi da Hajia inna saman keken guragu
A hankali yake kallonta zuciyarsa na sake karyewa, a tsayen nan kuwa da yake sai ya kasa karasawa inda suke, domin ya jima rabonsa da ya ga an fidota, ita da kanta ne da ya matsa cewar a ringa fito da ita ta nuna masa a'a bata so a barta kawai, a dole ya hakura dan bashi da damar takura mata
Ya Allah, wannan ita ya sani uwa, ita ya sani mama, saboda shi dama da aka haife shi dan gidan kanani ne, kulun yana nan tun yana baby , bale a lokacin Hajia lafiyarta kalau
A kan Hajia ya tashi da zuciyar tara dukiya, tunda ta fara ciwo burinsa ya kaita asibiti da kudinsa, Duda Elhaji Hamza ba talaka bane, ama shakuwa da soyayya dake tsakaninsa da hajiarsa ya sa yake fadin shine zai kuma da lamuranta a nan duniya, shine zai riritata zai siya mata dukkan abinda take so
Sai dai kashhhh, bai taba yarda cewa ba komai kudin ke iya siyawa mutun ba sai da ya gama tarawa yayi yawo dukkan kasashen duniya da Hajia aka rasa injin da zai tashi hajiarsa, Hajia duka duka shekarunta nawa? ama gatanan ciwo ya gama karar da komai nata sai imani da ibadar da ya rage mata
A hankali ya sado dubansa inda aka kama hannunsa
Hakoranta a fili suke tana watsa masa dariyar da ta samu yan kwanakin nan na farin cikin da yake gani kamar fa kurma na son zarce gona da iri
Da sauri ta nuna masa time sai kuma ta yi gagawar rike ipad dinta wajen rubutun nan ta rubuta abu kamar haka" Tsohon mutun na ta fada Aba, gayacen a kofa kar ya sake zuwa bamu je an bamu sabuwar maman nawa ba, mu je Aba mu je"
Bayan ya karanta dan murmushi kawai ya kakaro da hannayensa ya mata alamun ta yi kyau abinta, domin ta sha lesh ne dandatsetse wanda aunty sharifat ta zo mata da shi , dan Kurma bata da dinke dinke na kece raini, du kayanta yan waje ne da uban ke siyo mata ko Mufeeda, to waye zai yi mata dinke dinken, kowa yana abinda yake gabansa?
Shigowar Mama Binta ne ya sa bayan gaishe gaishen junna da ake yi ta dubi AL'WALID tana murmushi ta ce" Ni kam wai ko ka fasa min kishiyar ne Elhaji karami? , ga Babanku cen zai fara cenza kamani, ka san amarya da shiga rai kar ka sa yayi tunanin za'a fasa bashi amarya ne mana"
Dariya aka yi, a lokacin da yayi murmushi ya karasa inda Hajia take ya duka a hankali yana taba kaffafuwanta da aka saka mata su cikin silifasss, a Hankali ya ce" Inama ace kulun zaki ringa yarda ana fitar da ke Hajia"
Hajia ta yi murmushi, an luluba mata sabon mayafinta masha ALLAH, ita da kanta da aka fito sai da ta rufe idannuwanta saboda wani irin suka da suka yi mata na jimawa bata ga rana ba, Elhaji karami ba zai gane ba, ba fa bata son fitowa bane, bata son sakewa kowa wani nauyi ne, saboda rayuwa, bata so kuma a ringa yi mata dan dole, domin ba zata taba so ace sun yi zaman kyautatawa junna dan dole ba, ba zata so su hidimta mata dan yaronta na jan ragamar kula da gidan nan ba, a'a, yau da gobe kuwa ta fi karfin wasa, idan ciwo ya zama abokin tafiya yana saka naci sosai, ya zo ya zauna daram ya ki tafiya, sai ya gama daidaita bawa sannan ya hakura ya tafi da kai, to fa a dan lokacin da zaka yi shi in baka kama jikinka ba ana iya samun matsala da tarihi marar dadi
Zata yi magana baba ya dawo yana fadin" Kai, ku fito mana ku ku koma wajen baki, masu zuwa daurin aure kuwa motoci sun fara yin gaba, karfe takwas ta yi jama'a a gaggauta a gaggauta"
Da dan sauro Hajia ta mika masa hannun dan tana iya motsa hannayenta da kuma kanta, kaffafuwan ne suka shanye
A tausashe ta kama hannunsa ta ce" Allah ya yiwa aurenka albarka Elhaji karami, ka je ka amshi daurin auren nan, na tabbata ka amso alkhairi kuma zaka rayu da alkhairi, a dawo lafiya, yau ai zan wuni a falo da baki in sha Allah "
Murmushi yayi yana jin karsashi na shigarsa, daidai Baba ya dubi Hajia Binta ya ce" Wai ba zaki ja kanwarki ki mayar da ita bane? yau na bani zasu rikita Ni"
Da sauri ta karasa tana sake gyarawa Hajia inna rufarta ta ce" Kin ga mu je , mu je mutumen nan a kan amaryar nan tasa kar ya mana ba daidai ba"
Ta ringa tura Hajia sunna dariyar rikicin da baba tsoho ya tashi da shi
Fitowar suka yi tare harda Kurma wace sunna tafe tana faman hade hannaye sai ihun kuramenta take yi tana rokon a je da ita, mahaifinta na kallonta dai, ama bai amsata ba har suka fito ya ga irin yadda ake cika mota ana tafia, domin daga nan inda suke sunna hangen irin yadda baban get ya cika da baki da kuma yan tafiya daurin auren, masha ALLAH sai da abin ya bashi mamaki sosai, shi dai ya san ya dora gayatar daurin auren bisa umarnin Baba Hamza jiya da magariba fa, daga nan Baima taba wayar ba ya shigewarsa ne ya dan zauna ya huta, daga bisani kuma suka zauna da baba kan maganar inda za'a ajiye yarinyar, shi ya zatama daura auren ne za'a yi a gaba ta tare? gannin ba'a yi maganar inda za'a kaita ba, sai baban ke ce masa yana sane, yana so a fara kawota nan ne daga baya sai a kaita inda ake so, ama a yanzu yana so ta zo su rayu a gidan nan gaba daya......, kuma a jiyan ne ya fahimci wani abu, kamar fa baba ya shirya masa wani abu, domin a jiyan ya dan nuna masa alamun bayan daurin auren da kwana ko biyu yana son yin tafiya, zai baban cewa yayi to to masha ALLAH, kafin nan an sama mata passport ko? dan ka ga ai kafarka kafarta ita amaryar tamu....., to abin nan dai ya dai tsaye masa a rai, dan bai gama ganewa ba gaskiya
A nutse ya dubi Kurma dake karra rokon a je da ita, da yan yatsunsa ya mata nuni ta tafi bangaren su Hajia
Idannuwanta ta yiwa raurau zata fashe da kuka, nan take ya hade fuska hakan ya sa da sauri ta juya ta nufi bangaren Hajiar tana sakin kukanta mai haษe da boda
Baba ya masa alamun su je yana fadin" Kai wannan kuka na kurma dan Allah saurara ka ji? Allah mun tuba kamar ana barzar shinkafa, kurma rigima ne da ita walahi yaya za'a je daurin auren babanki da ke?"
Dariar da bai shiryawa ba yayi yana duban babban da ya bude masa mota ya ce" A kalamanka babu abinda zan manta idan mun dawo in sha Allah, ka san yau na batawa Litle rai, ba laifi mun gode "
Baba ya yi dariyar shima yana kallonsa ya ce" Ka rufa min asiri so kake yi ta daina min magana ? dama fa tun a cen nace ta yi hakuri maza ne ke zuwa abinda maman nata zata zo, sai cewa ta yi sai ta je shine na kyaleta ai dan na dan uban nata daidai da ita ne, gayanan kai da yan yatsu ka kori baiwar Allah, ba ta ki rarashi ba? mu je mu je ma dawo gidan da wahala ka ga hakoran kurma yau"
Gaba daya yan uwa da aminan arziki suka rankaya gidan su Khadeeja daurin aure, kuma sun samu tarba mai daraja da mutunci, domin Elhaji Ya'u da ya'yansa da jama'arsa sun tarbe su da daraja da mutunta junna
Karfe yara na safe da yan mintuna aka daura auren Elhaji AL'WALID da NANA KHADEEJA a gaban duban shedu, Daurin Auren da ya saka jama'a da yawa mamaki, domin wasu tunaninsu a ina KHADEEJA ta gidan Elhaji Ya'u ta hadu da Elhaji AL'WALID na gidan tv da Radio? domin ba kowane ya sanshi ba, ama ana jinsa a tv da Radio sai wajajen da sakonsa ke zuwa a boye..., an dai san hamshaki mai kudi ne na bugawa a jarida, an san fitatacen mutun ne da yayi shura, daidaiku suka san ya taba aure, wasu basu san da haka ba sunna dai tunanin itace matarsa ta farko,
A cikin gida kuwa mata ne cike makil, tun daga kan dangi, da yan anguwa da abokan aikin Mama an cika sai kawo ake yi, inda amarya ke cen cikin dakan mama, mama FATEEMA zaune a bakin gado tana rungume da Khadeeja wace jikinta ya dauki zafi sosai na irin boyayan kukan da take yi, dan kuwa gaba daya abin ya zo mata wani iri, a yanzu nema da iya ta shigo da goro ta damkawa Mama FATEEMA a tausashe ta ce" Alhamdulilah, ta wajena ta zama mata a wajen Elhaji AL'WALID" ta ji sunnan ainahin mijin da aka aura matan, sannan ta ji abinda ke hade da sunnan Elhaji, nan fa hankalinta ya karra tashi, a zuciyarta ayanawa take yi' Innalilahi wa inna ilaihi raj'une Allah ya Allah ka sa mahaifiyarsa ce ta je Saudiya da shi aka haife shi aka kamo su aka koro su ta dawo gida take siyar da kunu da kosai dan su samu abinda zasu ci su yi rayuwa, ya Allah ka sa sunnan Elhajin da aka hada da sunnansa ba yana nufin abinda nake gudu bane, ya Allah kar ka sa ace mutumen nan mai kudi ne, ya Allah na tuba ka rufa min asiri...' Sai kawai ta sake saka musu kuka , suka ci gaba da aikin rarashi, abin takaicin yan uwanta yau ita suka yiwa tawaye ko? ko sunna gidan uban wama?
A kofar gida
Idan ka ga Aba a wannan rana zaka karanci tsantsar farin cikin da yake ciki a bayane a saman fuskarsa, Hakama baba Hamza, an gama daurin aure, wasu har sun juya gida ama baba Hamza sai sake gaisawa yake yi da mutane cikin farin ciki ya ki motsawa daga saman kujerar da aka fito musu na alfarma
AL'WALID dake bin mutane da kallo, yannayin fuskarsa a sake saboda tarin mutanen dake zuwa sunna gaisawa da yi masa Barka, sai dai yannayin jikinsa a sake yake sosai da wannan rana....., tabas