Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 64

15K to 18K   out of 190.8K words

mike tana yi masa sannu

Hannu kawai ya daga mata ya karasa inda Hajia ke zaune ya zauna yana sakin murmushi ya bi kwaliyar da ta yi cikin babar atampa ta kashe dauri, sai kanshin turare mai sunna Faiza take , ta ɗora kafa daya kan daya kamar wata sweet 25 ko dan bata yi haife haife da yawa bane? ko kyan jiki ne kawai? matarsa dai masha ALLAH yar carassss da ita

Ya sake sakar mata murmushi amarya kuwa ta yi shekeke cike da mamaki,dan bata cika fitowa zaman falo ba sai ta san za'a yi masifa, yau kuwa yadda suka yi balaki da safe ta sani ne in ya dawo da yama za'a yi wanda ya fi 'a safen, ta yiwu ya saketa kowa ya huta, sai ga wani tashin hankali a idannuwanta ya shigo yana ta wani doka murmushi kamar me ita kuwa ta daure fuska ta basar kamar bata ganshi ba

A tausashe ya ce" Gimbiya gimbiya, ta Elhaji mai komai dozin kike, maman sidiku, Karima, Lubna, firdausi, Habby, A'isha, Hafizu, Abdul Rahman, Hamza da Anmi ikon Allah, takawarki lafiya hajiata in sha Allah bana zaki koma ki karra sauke farali , menenene Ni na bata fuska wani marar hankalin ya taba ki?"

Da mamaki ta zuba masa ido, kwarai wasu lokutan yana da ire iren halayan nan, sai kun yi tashin hankali da shi sai ya dawo yana rarashi, sai dai bai taba zuwa da irin wannan salon rarashin ba sai yau

Idannuwa ta dan kankance tana kallonsa , shi kuwa ya sauke hular kansa yana fadin" Walahi na tsufa, kin ji bayana? wai ina ya'yan baba suke? ina ya'yan Elhaji suke?"

Daga ita har amarya sai da suka kame haba, Hajia ta sake kallonsa ta ga sai wani fifita yake du kuwa da iskar fankar da ta gama hade dakin dan ba zafi
Kai ta dauke tana tabe baki ta ki motsawa, gannin haka sai ya dubi amarya ya mata wani murmushin da ya sake shaketa da bakin ciki ya ce" Je kirawo min yayana mana kina ji ina cigiya"

Ajiyar zuciya ta sauke hadi da gyada kai ta juya a ranta tana ayana' lalle matar nan balaki ce, tabas Malaminta dan balaki ne, lalle zan yi dakon ranar da bata nan in shiga dakinta in yi bincike ko me take anfani da shi zan dauko nima in yi, idan ban yi da gaske ba tabas sai ta rabani da gidan nan ina ji ina gani, wannan wace irin masifa ce?"

Kasa kasa ya ce" Ke wai a gaban kishiyarki zaki ringa cicinma mijinki magani so kike yi a samu lagonki a samu abin zaginki da shi ko a fi ki a wajen mijinki gobe?"

Da wani mamakin ta sake zuba masa ido, sai kawai ta idasa yarda da abinda yake so, dan haka ta ki sakewa yadda ya so ta sake hade fuska tamau har yaran suka iso kowane na rabewa a jikin dan uwansa, dan lubna mai saurin kula da tsoron balaki tuni take kukanta tana ta tambayar amarya me suka yi? ama amaryar ta ki ta fada ta yi gaba ta barsu cikin zumuli da tashin hankali

Mikewa yayi ya nufe su zai yi magana ya ga du sun nemi ririke junna sunna raraba ido sunna kallonsa, masu saurin kuka tuni sun fashe da shi, hakan ya sa ya dakata yana kallonsu yana jin kamar wani abu na son damunsa a cen kasan zuciyarsa kamar kuma ba komai bane, karshe dai ya tabatarwa kansa ai gwara haka ya zamo da wanda suke jin tsoro ya fi alkhairi a wajen kowa da ace basa tsoron kowa, sai ya ja baya yana cewa" Yayanki sun iya shari, taba ku na yi da zaku wani cure kunna kuka? shikenan bari in je bangarena, in kin gama da su ki same Ni a cen "

Yana bada baya amarya ta bi bayansa da sauri , hakan ya sa ya dakata yana kallonta yace" Lafiya ke kuwa?"

ta yi tsuru tana kallonsa kafin tace" Na ga ita din tana halin rashin sallah, ai Ni zan kuma da kai har ta warke "

Ya girgiza kansa ya ce" A'a, ranar girkinta ta zo ta kwonta, ranar taki ki zo, ama yanzu kam ba girkinki bane, ke kina jin tsoron Allah kuwa? haka jiya kika kwana a bangarena bayan girkinta ne, ki je kawai wannan sai ki kona Ni walahi, irinku ne ke tura namiji yana aikata rashin adalci karshe ya zo ya kone ku ko oho, to ki je ya girkin gimbiya ne"

Wannan bakin ciki da ya kunsa mata tana dawowa ta yi ciki ko tsayawa kasa yi ta yi bale a ci ganimar da ya kawo da ita, Ita kuwa Hajia bata damu ba ta saka yan matan ƴaƴanta da zaratan samarin nan a gaba sun bude ganimar ta ware nasa da na matarsa sauran ta basu dama suka shiga yaga sunna ci sunna labari ana shan dariya , domin dariyar tsoron su Lubna suke ta sha , "

Sai da suka gama ta tabatar da kowa ya je ya kwonta ta bi dakunnansu sannan ta nufi bangarensa dan ta sani idan bata je ba zai zo, kuma tana binsa ne dan tana son ta ga gudun ruwansa

Ai kuwa haka suka kwana cikin aminci ba fada ba tashin hankali, ko da asubahi yaran haka ya ringa jansu da fira sai ya wani sakarwa Hajia murmushi yace da ita likita kin ga y'ayanki kaza, ko abu kaza, ita dai tana biyewa sabon salon nasa ba tare da ta sakankance ba dan ta riga ta sani Elhaji zuma ne sai da wuta, ba banza ba wannan take taken nasa

Abin mamaki kwana hudu aka yi a cikin wannan lamari na kwonciyar hankali a gidansu,
Ko yau ranar girkinta ne, kuma tana tare da yan matanta a kicin sunna ta girke girke domin daga shago aka kawo zabi da kayan miya rigijib sai kawai suka shiga aiki dan kuwa ta hanna idan an yanka mata zabi a fige a cen, gida ake kawowa ta ajiye kujera yaran su fige su gyara tasss sannan su dora salale , tun basu kai haka ba suka iya aikace aikacen nan bale yanzu harta mazan sun iya girke girke dan tare suke hadewa su yi sunna shan fira , Karima ce kawai bata fito ba yanzu take haramar lekata dakinta dan ta ga ko lafiya

Sunna cikin soye soye umma tsohuwa ta shigo gidan da salamarta

Khadija ce ta fara dagowa jin Muryarta tana amsawa hadi da sakin murmushi, dan akoy shakuwa sosai tsakaninta da umma tsohuwa , kusan du wani abu da take yi sawayen umma tsohuwa take bi, kamar ta zame mata madubi ne, dan kuwa du wasu burikanta irin na umman ne, tana din zuwa gidanta ne dan tana koyon abubuwa masu yawa da mahinmancin da bata gannin Mamanta na yi a nan, domin a tare da firar Umma tsohuwa ta samawa kanta matsayar nan cewar eh zata yi aure, ama ba irin zaman da mahaifiyarta ke yi ba zata yi wannan alkawarin Nana ne!

Umma ta hade fuska tana fadin" Maida murmushinki, yau kwana cikin na shida kennan baki je gidana ba lafiya? na biyo sahu dan in ji laifin da na maki y'ar nan"

Khadija ta dan zarro ido, ta rufe baki da hannunta sannan ta dubi mamanta da ta fito rike da rudayin miya tana marabartar ummar

Umma ta ce" Hajia rike lalenli hala ke kika hanna ta wajena leka Ni kwana biyu?"

Mama ta ce" Kai umma Ni kuma yaya zan hanna zumuncinki da y'ar gidanki?"

Umma ta zauna saman kujerar da Khadija ta miko mata tana fadin" Ni in ce, ba zaki aikata haka ba, irin yadda nake jin Nana walahi kamar jikkata ta jini, kwana biyu kulun cikin jajen Nana nake, yau dai nace bari in je abin ya isa haka....."
Tana maganar ne Karima ta fito ta baya, kamar daga cikin gidan take, bayan ita kuwa ta ganta a waje daga bayan rumfa tare da mahaifiyarta da kuma wani saurayi marar jin magana dan gidan wani Elhaji a nan bayan layin yana daga motarsa sunna magana da mahaifiyar ta Karimar da Karimar

Da ido ta bita gannin ta shiga aiki tana fadin" Mama yi hakuri abu nake yi"

Umma tsohuwa ta dauke kai tana dan tabe baki ta sake kallon Khadija dake ta jera mata abubuwa ta ce" Kin ga uwar manya bani ruwan kadai in sha in koma, yan majalasi na jirana ai kin san irin wannan lokacin muke yin zama, Hajia bari in juya, ga cingan din y'ar nan dan Allah a bata abinta kar a raba mata da bataliyar gidan nan"

Mama ta yi dariya ta amshi ledar tana fadin" Bari in taka maki umma, ta gidanki kuwa ai zata bude ta raba da yan uwanta in ba haka ba itama ba zata ci shi ba"

Da wannan ta raka umma daidai gate din farko da ya musu izinin tsayawa idan suka yi rakiya sannan ta ja ta tsaya tana kallon Umma da ta dubeta da kula ta ce" Hajia?"


mama ta ce" Na'am umma"

Umma ta ce" Me yasa idan mahaifiyar y'ar cen ta zo basa shigowa cikin gida ne? ya dace a dakatar da tsayuwar nan ta bakin hanya ana kulawa yaro balaki, Duda mahaifiyarta ce Ama inaga yanzu sun fara kawowa lokacin da iyayensu zasu yi anfani da su dan su hadasa maki wata fitinar, ki kula sosai"

Mama ta yi wani irin jim da mamakin abin ta ce" Wai waye, Karima? tana daki fa tun dazu"

Umma ta girgiza kai ta ce" A'a, karya take yanzu na wuce su da mahaifiyarta da wani saurayi cen baya yake , yaron Bama ya jin magana ko kadan yaron, babu wanda yake girmamawa a anguwa, dan ubansa nada dukiya yake tunanin dai-dai yake da kowa, gaskiya ki san mafita"

Mama ta sauke ajiyar zuciya da mamaki ta ce" To shikenan umma, in sha Allah zan yiwa tufkar hanci, Allah ya kyauta"

Daga haka suka yi salama mama ta koma cikin gida ta zauna yaran na aikinsu tana kula, ama kuma zuciyarta ta tafi wani tunani daban........

Ta kasa gane me hakan yake nufi kuma? bale irin yadda Karima har ta iya fita daga gidan nan ta dawo ta zauna ta gila karyar a daki take bata gane ba hakan ba? tun yaushe ake irin haka? me yasa ake boyewar? ba wai mahaifiyar Karima bata isa ta ga y'arta bane, a'a, ko daya, hasalima ta fi kowa iko da abinta ciki kuwa harda ubanta, matsalar ɗaya ce Karima a karkashin kulawar Hajiar take, tarbiyyarta da komai a hannun hajiyar yake, idan har an jima ana irin haka anya wani abu ne mai kyau kuwa?

A nutse ta kalli Karima ta dan zuba mata ido tana kallon ta, normal dai yadda suke da haka ne yanzunma, dan abinda ba za'a rasa ba na yaron da baka haifa ba tana gani lokaci zuwa lokaci, ama ta riga da ta san cewa haka na iya faruwa, sai ta ba kanta lafiya bata tsaurarawa, idan hakan ya samu takan yi uzuri ta bada lokaci, cikin ikon Allah yaran da kansu suke dawowa su bata hakuri a ci gaba da zama, D'AN YAU ka haife shi ma ai baka haifi halinsa ba bale wanda ba kai ka haifa ba .......koda yake zata bi komai a hankali in sha Allah har ta gane abinda yake faruwa
Daga nan ta kawar da maganar daga cikin zuciyarta ta ci gaba da yan kaye kayenta har suka gama komai da komai ta raba kamar yadda ta saba ta cire na mahaifinsu ta kai da kanta bangarensa sannan ta ware nasu da na yaran maza nasu daban, na matan daban sannan suka tatare suka kai komai Muhallinsa sannan kowa ya nufi dakinsa dan yin wanka da cenza tufafin da aka yi girki da shi bisa koyarwar mamansu , itama hajiyar ta nufi nata dakin

Khadija na shiga dakinta bayan ta tube ta daura tawul ta nufi wanka tana tunanin yau fa kwana shida cif bata je wajen zaman da suke yi a gidan Umma ba, kai gaskiya ta yi asarar abu da yawa ta sani ne, ama in sha Allah gobe zata je dan kuwa fashin zuwa gidan umma asara ne mai girman gaske a wajenta

Karima kuwa maimakun ta fada wankan tana shiga dakinta sai ta lalubo wayarta ta kunna ta shige bayi ta zauna saman wc ta shiga whatsup dinta tana ta dakon msg dinsa

Ai kuwa ba jimawa msg din ya shigo, ta bi numbar da kallo sannan ta bude dp dinsa

Wani murmushi ta saki mai kyan gaske tana zooming din fuskar da kyau har wajen jajayen idannuwansa da sigari da shisha ce suka rinar da su ba komai ba

Wani murmushin ta yi tana talabe habarta a hankali ta furta" Tabas jajayen idannuwa gare shi, Tabas na yi dace in na same shi, hariji ne da ganninsa, zai biya min dukkan bukatuna......., wayo Allahna mamana kin gama taimakona kin gama birgeni....gashi maai kudi, ga kyau, ga jan ido kihuuuuuuu"

Sai kuma ta dafe bakinta ta rufe tana dan zarro ido ta kashe wayar ta ajiye da nufin idan ta gama wanka zata dauke, sai dare yayi in wancen y'ar balakin ta gama yi musu addu'a ta rufe zata kunna wayar su yi waya da abin sonta, tabas gaskiyar mamanta ce, matar babansu ba zata taba sinsu ba, ba zata taba yin abu dan ci gabansu ba, gashi dai kiri kiri so take yi ta hanna a basu damar yin zance, wai karatu suke yi, wato ita in suka rasa mazan aure ai ba damuwarta bane, ita dai ba zata yarda ba gaskiya, cen ta yi iko da y'arta mana ai ta haifa , ama zata wani fake tana neman hannawa mutane rawar gaban hantsi ita da ta fi kowa Sannin abinda ya kamata, aikin banza!

Da wannan ta shiga kimtsawar itama zuciyarta cike da sake sake kala kala


Hajia bata nufi bangaren Elhaji ba sai da ta gama da Yaran gaba daya sannan ta tafi

A hanyar zuwanta yadda bawa ke addu'ar Allah ya tsare shi da dukkan wani abu na ki haka take adu'ar Allah ya sa har ta je ta dawo da asubahi babu wani abin da zai daga mata hankali, ita da kanta sai da ta yi hakan ta samu kanta da yin murmushi a ranta ta ayana' Elhaji kennan, mai abin mamaki, ka ji da rigimarsa, ka ji da ta matan da yake aurowa, ka ji da ta mutanen gari masu zagin kai ka kanainaye komai nasa, sannan yanzu ga dukkan alamu lokacin ka ji da wata fitinar ta ya'yansa ta gabato? ya Allah ka san zuciyata, ka san da wace zuciya nake zaune da yaran nan, ya Ubangiji kar ka basu damar wulakanta irin tarbiyyar da nake basu, ko me zai faru ka basu ikon jin tsoronka da kiyaye hakokin ka ya Allah '

Da wannan ta shiga falon ta karasa ta zauna saman kujera ta same shi yana amsa waya

Gannin wayar ta dan ja ya sa ta mike ta shiga sauko masa kayan abinci daya bayan daya tana jerawa

sai da ta gama ta zauna ta shiga zabawa dai-dai ya gama amsa wayar ya dubeta da kula ya ce" Gimbiya sannu da hidima, Allah dai ya maki albarka"

Mama ta dan yi tsai, sai kuma ta amsa bayan ta zuba masa

Elhaji ya wani dan yi murmushi ya ce" To mu ci mana"

Mama ta ce" Ka san ai na ci nawa , ban iya cin abinci a irin wannan lokacin ba"

Elhaji ya gyada kai ya ce" Hakane kuma y'ar gayuta"

Mama ta yi murmushi kawai bata ce komai, ita abin du wani iri take ji, doguwar fira da shi in ba ta balaki ba ko dadi bata yi, du sai ta ga kamar munafuntarta ake yi a lamarin

Shima jin ta yi shiru ya dan sake dubanta dai ya ga tana kallon tv bai ce komai ba, ya ci gaba da cin abincinsa har sai da ya gama ta kwashe komai ta dawo ta zauna

Jim kadan ya budi baki bayan ya yi dan gyaran murya ya ce" Ni kam akoy maganar da nake so mu yi gimbiya"

Mama ta dago tana kallonsa a ranta ta ayana' An zo wajen'

Baba ya ci gaba da fadin" Ya'yan nan naki nake cewa, kin ga ya'ya mata ne, a lamarin musulunci tun daga bakin lokacin da yarinya ta fara gannin jinji sakata a dakinta shine ya fi zama alkhairi, kin ga kuwa ai Karima yanzu ta kai shekara goma sha takwas ko? shine na yi mata miji"

Tsai ta yi tana dubansa, kafin ta yi dan murmushi a hankali ta ce" masha ALLAH, yaushe ta fara zance ne y'ar tawa?"

Baba ya ce" Zance fa, a'a bata fara zance ba, a gaba dai zai zo su gana su aminta da junna shikenan sai a yi"

Mama ta karra fuskantarsa ta ce" Kana nufin dai auren hadi zaka yi mata ne babansu?"

Baba ya fuskance ta shima yana dan hade fuska ya ce" Auren dace dai ba na hadi ba, kin san da bambanci , auren da Allah yace mu yiwa yayanmu , wato mazan farko ko mamansu?"

Mama ta yi murmushi tana dauke dubanta daga cikin nasa ta ce" Hakane, sai dai zamani da ya'yan zamani a barsu su kawo zabin nasu a auna a gani idan har ya cencenta daga halaya da addini sai a bashi su je su cencana rayuwa ya fi, domin auren soyayar kansa yana zama wani abin a yau bale auren hadi babansu"

Baba ya hade fuska nan take, yana dubanta ya ce" Wannan Yaren masu ta'amali da magangannun yahudu da nasara kennan, mu abinda Allah yace a yi zamu yi ai ta hakan zamu fi gannin yayi kyau, auren soyayar me Allah na tuba, miji mai mutunci ai ya fi komai , y'ar ta kai sha takwas kwarata zan yi in cinye ko me kike nufi"

Hajia ta dan dafe baki tana dubansa gannin yadda nan da nan har hali ya dawo, a haden nan itama ta ce" Hakane kuma, auren soyayar a yanzu shi yake rikicewa ya zama na kiyaya, nima shaida ce, dama shiru muka yi aka yi mana je ki ga mijinki da ba haka ba, yarinya kuwa ai ta kai

6 / 64