Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
gida
Sunna zuwa suka tarar an gyara bangaren da su Hajia suke, dama bangare bangare ne a appartement din, wanda suke bangare biyar ne harda na baba, su Hajia kuwa su uku ne , baba bai yi ta hudu ba, sai kawai aka sakata a dayan bangaren, su Hajiya Binta suka tarbeta aka turo Hajiya Inna itama harda ita a yan tarbar Tata, cike da tausayawa yannayin da ta dawo, domin da farko buya ta ringa yi a bayansa tana cimuimuye rigarsa tana leko su ta jikinsa tana faman fadin a sanar musu bata kashe mijinta ba, ba zata kuma ba, idan ma ya dawo ba zata kashe shi ba kuma, sai a hankali ta yarda ta fito, harma ta saki jiki a hankali da su har ya zamo ta zauna cikin su, kuma yanzu da suke gidan ya yi iya yinsa har ta fahimci cewar yanzu yana nan tare da ita zai je yayi wanka ya dan huta ne sai ya dawo, harma ta yarda ita da kanta ta ringa masa byby tana rike da hannun kurma har ya tafi sannan ta sake yin tsuru tana kallon su Hajiya dake kokarin ganin ta ɗan sake da su , su dinma.
A lokacin da suka wuce dakin Khadeeja yana cire tufafin jikinsa domin ya sanar mata ta shirya su je gida, za'a yi daurin auren sisters dinta, du irin yadda take cikin zumudi sai ta boye a hankali ta rungume shi ta baya ta yi shiruuuuuu
Irin yadda kirjinta ke bugawa a hankali a hankali ya saka shi juyo da ita ta gabansa ya rungumeta sosai a kirjinsa yana dan sauke ajiyar zuciya
Murya a tausashe ta ce" In sha Allah, mama zata samu lafiya, kar ka saka damuwa a ranka plz"
AL'WALED ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce" Kamar mama ta samu.....kamar ta samu tabuwar hankali.....Hajiya karama ko jinnin mahaifina ne yak..."
"Bata kashe shi ba, wanda ya kashe shin ai yana gidan yari har yanzu, kowace mace da irin yadda take tafiyar da kishinta, kar ka yi mamaki akoy wace ko mahaifiyar mutun tana iya yin kishi da ita......, laifinta daya ne kuma wanda ta yiwa ya yafe mata....su waye mu da zamu dubeta da shi? Mama bata kashe aba ba, ba ita ta kashe shi ba Aban litle" ta fada a tausashe tana sake shiga jikinsa....., shi kuwa yana ta sauke ajiyar zuciya kamar wanda dama abinda yake jira ya ji kennan kamar bai san abin ba, kamar wanda fadin abin magani ne a wata cutarsa
A hankali ya dago habarta ya kura mata ido, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi kasa kasa ya ce" Ina son ki....."
Khadeeja ta lumshe idannuwanta tsigar jikinta na tashi
A hankali ya sake furta" Ina son ki Rohi"
Yanzu kam har sai da ta jimke hannayenta a jikinsa da dan karfi
A tausashe ya ce" Idan kina haka....., ba zamu iya zuwa wajen daurin auren ba fa....., sake gwadawa zan yi ko ma samu ciki "
Yanzu kam sai kawai ta dake shi da gudu ta yi bayi tana dan ihun jin kunya, wanda ya saka shi sakin murmushi ya bita da kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya yana jin zuciyarsa na sakewa sosai da sosai sannan ya fice ya je nasa dakin shima dan ya shirya
Kusan sallar magariba suka fito daga gidan suka dauki hanya, a dole suka dakata dan yayi Sallah a masallaci, dan ya dauke mata kewa Sai kawai ya kamo mata tiktok ya bude mata data ya fice tare da direba
Kallo ta shiga yi hankali kwonce, lokaci daya kuma msg na shigowa a WhatsApp dinsa , msg din kuma na numba daya ya fi shigowa yana karawa harda callll kamar jira ake yi ya bude datar
Har ta share wani call din ya sake shigowa, a lokacin ta gyara zata dauki hoto da wayar ne cikin tsadadan lesss dinta mai ruwan Golding, sai kawai ta shige msg din dan tace zai bada amsa idan ya dawo, Sai gannin voice note ta yi rututu, da hoto da kuma missss callll da rubutacen sako
Abinka da wayar da ba'a saita mata harkar bude hoto ba, tana shiga hoton ya bude da kansa ne , kuma abinda ta gani a hoton shi ya nemi dauke ganninta hadi da jinta lokaci guda, har ya zamo kura nasa idon da ta yi bata san cewa an fito daga masallaci ba har direba ya bude ya shigo, har sai da ya bude shima zai shigo ya ganta a gefen da take, wato bayan direba take zaune kasa kasa ya ce" Madame dan matsa , ba zaki zauna a bayansa ba, ko ya baki in ja ne?"
Khadeeja ta dago da sauri saboda sai a lokacin ta ji mutun, kuma ta ji Muryarsa
Irin kallon da ta masa ya saka shi ɗan dubanta da kula ya furta" Are You ok?"
Ama khadeeja ta kasa ce masa uffan, sai matsawa da ta yi tana kashe hasken wayar kirjinta na wata irin masifafiyar bugawa kamar zai balo ya fito daga kirjinta
Gaba daya jikinta rawa yake yi, gumi na neman wanke mata jiki, du kuma sanyin acn cikin motar sai ta ji kamar iska ta yi mata kadan, kamar ana zafin balaki
Du irin yadda ya ringa tambayar ko lafiya? Khadeeja ta kasa amsa shi sai farcen karamar yatsarta da ta saka a bakinta tana ta faman cirewa har ta fara cizon yatsar
Kasancewar sun kusa gidan ne aka fara kiran sallar da wuri suka iso, sunna isowa bata tsaya ta saurari riko hannunta da yayi ba sai kawai ta fice tana ajiye masa wayar a nan saman kujerar ta yi ciki kamar zata kifa, ko kula bata yi da Aba dake kokarin fitowa da kunnu a baban faranti na baba da aka gama yanzu yanzu ba
Da sauri ya bude motar zai fita, sai kuma ya dakata ya dauki wayar yana kallonta da tunanin me kenan?, yanzu yanzu fa yana magana da matarsa lafiya kalau Allah ma kuwa...., me yake faruwa me aka yi? Me ya rikitata? Ko bata jin dadin jikinta ne?
Aba kuwa har zai dura ashar ya gane wace dan haka ya wani saki murmushi ya ce" Ke anmy ya zaki wuce babanki a kan hanya? Dawo mu gaisa yaushe rabona da ke yar albarkana tun fa jiya ko? Dama ina so mu yi zance na uba da y'a in ji in komai kalau bari in ba tsohon cen kunnunsa in zo kafin yan daurin auren su karaso saboda cewa na yi a daura idan aka fito daga sallar isha'i"
Khadeeja dake haki bata iya cewa komai ba sai gyada kai da take yi, wani irin jirri na dibanta da jin karnin kunnun aba har cikin kwakwalwarta da kirjinta, bayan ta gyadawa Aban kai sai kawai ta shige tana rufe fuskarta da sauri ta bi ta bayan gida ta nufi ciki ta baya , tana shiga ta shige dakin Mama ta banko kofar ta cire mayafinta ta yar a nan , ta cire dan kwalin ta yar ta ringa haki kamar mai kamun athsma ta ɗora hannu a kai zata fasa ihu mama dake tsaye da dan kwali zata daura shigowar khadeejan ya sa ta dakatar da mamaki tana binta da kallo da sauri ta ce" Subahanalah, ke? Lafiyarki???"
Khadeeja ta juyo da karfi, dan wallahi bata zata, zata samu wani a dakin ba, a hankali take girgiza kai, sai kawai ta duke a nan ta fasa kukan da take ji zai kashe ta idan bata yi ba
A tsorace mama ta furta" innalilahi wa Inna ilaihi raj'une anmy lafiya? Me yake faruwa? Me ya damu mijin naki? Ina babanki? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, me yake faruwa??????"
A tsorace mama ta nufi kofar dan a gaskiya tsoro ya kamata mai karfin gaske, har sai da Khadeeja ta dago tana kukan nan ta ce" Mama sunna waje, innalilahi mama wallahi hotonsa ne da wannan wace akace budurwarsa ce, mama ya rike habarta, wallahi ya rike habarta innalilahi wayo Allahna zan mutu na shiga uku na lalace"
Mama ta juyo da karfi ta yi turus tana kallonta, daidai nan lubna ta shigo bayan ta buga da salama zata yi magana itama ta ja ta tsaya haka kuma da sauri ta maida kofar ta rufe ta shigo da kyau tana fadin" Subahanalah, mama lafiya? Me ta yi kika doke ta?"
Mama ta gyada kai, cike da takaici ta yi kyaftu ta nuno su da yatsa ta ce" A'a yankata na yi, nace yankata na yi Lubna, kin ga na rantse idan ta yi wasa da Ni dukanta zan yi a gidan nan, Ni zaki kashe ina ta kaina ki fasa min kukan iskanci kukan jin dadi a kan kishin miji? Ke yanzu dan kin ga hoton mijinki da budurwa ne kike yin wannan? To ai gwarama ki daina saboda namiji ai ba dan ke kadai aka halicce shi ba, idan ma kika saka haka a Tanko ai wahalar da kanki zaki yi, in ba iya shege irin naki ba ke ubanki nawa yayi? Kenan dai ba zaki nutsu ba ko?, ai na zata kin nutsu anmy, na zata kin nutsu fa, ashe da sauran ki ko? Ki yi aniya ki daga min hankali in nada maki na jaki a gidan nan!"
Mama na gamq fada ta daura dan kwalinta ta dauki hijabinta ta zumbula ta fice tana mako musu kofar
Da sauri Lubna ta karasa ta kama Khadeeja tana mikar da ita a tausashe ta ce" Anmy, shigowa da kula kuma? Waye ya taba min ke?"
Khadeeja ta RINGA shasheka ta ce" Yaya za'a hannani kuka? Kin kuwa ga hoton? Kin kuwa san wacece ita a duniyarsa? Ana ta dauki ba dadi da shi a kanta fa, yaya za'a yi ba zan damu ba?, kin san a yaya na ga hoton? Jikinsa da nata a hade, jikin Aban litle mai daraja ya hade min da nata? Shikenan an cuceni, an gama da Ni, an gama cutata, shikenan an wulakantani, wayo zan mutu, taba kirjina ki ji inaga shikenan lokacin yayi......."
Lubna ta dubeta shekeke kafin ta nuna mata yatsa ta ce" ke da kaniya ban hannaki kuka a kan namiji ba?"
Khadeeja da tarin takaici ta ce" To ai sai ku kashe Ni ku huta, an gaya miki baban litle namiji ne?"
Lubna ta dubeta da mamaki ta ce" na bani, kamar ya????"
Khadeeja ta ce" Ina nufin wallahi ba banzan namijin da ba za'a yi masa kuka bane, to in ban yi masa kuka ba in yi me? Wallahi mijina ya isa a masa kuka, kuma sai na nemo ta dan ubanta na daki banza, wayo Ni wayo kaina"
"Eh lalle bari mu sake dukawa a yi mana auren nan, dan wallahi wannan lamari da ya gigita Anmy ba karami bane, gwara dai a mana auren nan mu tafi mumaa" Lubna ta fada tana dauke kanta hadi da dan girgiza kai
Khadeeja ta yi sororo tana kallonta ta ce" Ama dai kin san Ni ba y'ar bace kar ki fasarani mana"
Lubna ta tabe baki ta mike tana isa wajen kayan mama ta dauko turarukan da mama ta tanadarwa khadeejar tana fadin" Sai dai kar a kuma , su anmy ai an gama shiga gari, ga dai kayan karin gyaran zaman auren nan, kin ga kayan nan wallahi makudan kudade mama ta kashe ta siya maki su , wasu muka hada maki da kanmu, wallahi ki kula da kyau ki yi anfani da su yadda ya dace, idan sun kare kuma sai ku kawo kudin ku a muku wasu dan ba zamu tsaya muna muka bati ba"
Khadeeja ta dubeta tana janyo hannunta ta ce" Lubna, dan Allah ki zauna ki kwontar min da hankalina, walahi ban nuna masa komai ba fa, kuka ne na yi dan in huce da"
Lubna ta dubeta da kyau ta ce" Kin tabata baki yi a gabansa ba???"
Khadeeja ta gyada kai tana kallonta
Lubna ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Haba kema, anmy a gabanmu sau nawa idan aba ya fara neman aure irin yadda mama ke yi?????, shikenan ke da bama neman auren ne yake yi ba sai ki gigice haka? Ina amfanin kokarin da mamanmu ke yi dan ta jure ta cije ta yi watsi da komai zai je a wajenki ????, kina gani aure aba zai yi Ama a kulun darajar mama daban take, a gabanki ai irin hidimar da zai yiwa mama ma daban ce, ke shaida ce ko hudubar da yake yi idan ya hade mu da sabuwar matarsa da mama a kan tsakanin matarsa da mama ma daban ce....., ke yanzu a ganninki da mama zuwa ta yi du auren da zai yi ta ringa iface iface ta ringa biye masa da ta kawo warhaka cikin hayacinta?....., wallahi da tuni ya fitar da ita a hayacinta inma wai tana gidan nan....., dan kuwa tsaf zai masheta birin wasa in dai Abanmu ne...., kuma ba shi kadai ba, in fada maki kaf maza haka suke, abinda kika san baki isa ki iya Hanna su ba gwara ki hade ki yi watsi da abin ki yi sabgar gabanki ina mai tabbatar maki sai kin fi kima da daraja a duniyarsu fiye da wace suka gano din suka auro din, kuma in aka yi rashin dace ta shigo da rawar kai wallahi dai ta zama kamar tinkiya a gaban nasu fa"
Khadeeja ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Ni da so samu na yi, karma yayi yan matan"
Lubna ta yi murmushi tana rike hannayenta a tausashe ta ce" Ba zan so ki fara da haka ba, dan zaki wahalar da kanki, ki wahalar da iyayenmu, sannan ki wahalar da mu....., kin ga du abinda ake zumudi ba dare ba rana bako ne, idan ya riga ya zama na yau da kullum anfani ake yi da shi ɗan abu ne da ya zama dole a yi amfanin da shi a rayuwa........, anmy misali abinci.....du ranar da kika ga sabo yaya kike ji a ranki? Ama idan kika jera kwanaki kina anfani da shi fa? Wani lokacin zaki cenza shi har na kwanaki kafin kuma ki ji ya mugun biyo maki a rai......, to ki dauka haka.......du kyan mace, du takamarta ana wayar gari mijinta ya so wace bata kama farcenta a komai ba....., zaki ga wani auren idan namiji yayi ana cewa ikon Allah wai kin ga Amaryar? Saboda an raina yannayinta duba da uwar gidan yadda take, wannan kuwa ba wani abin mamaki bane ai Anmy, yannayin namijin kenan, abinda ku baku gani ba shi ai ya gama kanowa, wato bakon gida, bakon wuri, sabon waje, shine zaki ga da an kwana biyu kuma komai ya daidaita kun dawo kun zama daya sai kuma a koma kan maganar wace ta fi iya hakuri, iya tafiyar da shi, iya girki da tatali da komai ta fi kwatar zuciyarsa......., to kin ga kuwa mutanen da Allah ya basu irin wannan baiwar mai zafi zaki ce ki saka damuwarsu a ranki, tabasssss zaki halaka kanki a banza saboda su ba wannan ne damuwarsu ba, idan suka riga suka hango ki kame kanki ki yi ta addu'a shi ya fi alkhairi, ba sai kin zubar da darajar ki, ki bari ya gama gane ki ba, daga baya ki ce zaki wani ja zare...., wani zaren? Wanda kika gama tsinkawa a gabansa! Ai kin gama bude masa komai ya gane cewar sai da shi zaki rayu, in wata ta rabe shi kina iya mutuwa meye kuma zaki birge shi da shi....., Ni Bama zan yarda ya gane kishina a kansa ba Allah kuwa"
Khadeeja ta ringa samun kwarin gwuiwa, har ta ji zata yi masa uzuri ta ji me hoton ke nufi idan har ya yi mata maganar....saboda ta kula Aban litle yana da kula sosai da tausasawa........
A hankali ta ce" Ke wai ya aka yi tumbin gimbiya na ga ya karu? Ita da bata da tumbi?"
Lubna ta zarro ido ta mike tana fadin" bari in yi kiran su Karima su kauro nan mu hadu, dan Ni kadai ba zan iya da lamarin ki ba, ke kam kin kunna yanzu kuma kin tashi daga rikicin da kika shigo da shi zaki janyo mana ruwan da ya fi karfin mu? Matar elhaji dai ai kin san ta fi karfin mu daga ita har mijinta....ya maki kyau"
Khadeeja ta ringa tafa hannu tana tunanin magana dai da babansu ya ringa fadi ta tabbata kenan? La'ila ha ilalahu ashe dai ba ita bace auta? Eh lalle duniya........
A kofar gida
Bayan sun gama gaisawa da mutanen dake nan ya samu waje ya zauna dan nesa da baba Hamza da d'ansa ya shiga wayarsa saboda gaba daya tunaninsa ya gama bashi cenjin mood dinta ya shafi wayar nan, duda a dogon nazarinsa ya kasa gano mahadin abin, sai dai da ya gama tunanin ya idasa gane cewar ta yiwu ko an samu rashin Sa'a wani abu ya zo wayarsa ko kuwa wani kira ta samu? Sai kawai ya shiga wayar gadan gadan
A cikin whatsup fada, yana shiga ya samu msg din dake ciki
Kirjinsa sai da buga a lokacin da ya ga hoton dake ciki, da voice note din yaronsa da msg da kuma tarin missss callll
Kai ya dago a hankali ya sauke dubansa a kan baba dake shan kunnu yana ta baje baki......., ga elhaji ya'u sai amsa waya yake yana karra tabbatarwa jama'a ai yanzu za'a daura da yardar Allah sai kawai ya samu zuciyarsa da ayyana masa abu kamar haka' oh my god........., hoton nan.....yaushe aka dauke shi?..... Yaushe ya faru......., ya Salam.....shi ta gani? ......a haka ta gani???......ya rab kar dai ta yi tunanin cewa Nine na dauki hoton nan da manufar da ake so a cikin hoton.......'
A nutse ya danna wajen voice note din ya shiga saurara kamar haka......
52
07/12/2024, 17:39 - samiraharounayacouba: Bayanan dake cikin voice note din suka saka shi turawa yaron nasa kira ya dan yi shiru
Daga dayan bangaren tana fara RINGIN ya daga yayi salama hadi da gaisar da AL'WALED din
AL'WALED ya amsa a nutse kafin ya ce" Wani mataki ka dauka? Dan ban gama sauraro ba"
A nutse ya ce" mun yi gaggawar sakawa an rufe mata account din