Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
yau dinma a kan wace ta fi kowa kusanci da zuciyar tasa ya sake kawar da kan, ya sake daukan hakurin da komai da komai a kansa ya juya zai tafi da dacin zuciya a kan lamarin
A hankali Nana Hamza ya ce" AL'WALED......, zo"
AL'WALED ya juyo yana kallonsa a hankali ya dawo ya sake dukawar a gabansa
A hankali baba Hamza ya dago fuskarsa yana kallonsa a tausashe ya ce" Ka yi hakuri ka ji? Na yafe mata, na jima da yafewar....., ina ji a raina ne kamar ba zan iya ganninta ba....., Ama in sha Allah zan yi kokarin yin hakan....., ka je ka sameta ka yi mata biyayya ka so ta......., a baya na taba ce maka ko abu ta baka kar ka ci ko?, to ka ci......, na tabbata a yanzu ita da kanta tana taka tsantsan da rayuwa ba zata cutar da kai ba."
Hannayen nasa ya sake hadewa ya rasa bakin magana sai wata irin ajiyar zuciya da yake saukewa, yana ta murza hannayen na baba a jikin fuskarsa......., sai kuma ya mike da sauri ya fice a dakin wanda hakan ya sa suka kalli junna , kaka b da sauri ta sauko ta duka gaban dan tsohon mijinsu dan su rarashi abinsu a daka bakinsu alekum.
Ko da ya iso bude masa kawai ake yi har ya zo inda zai bude da kansa ya bude ya shige yana kokarin neman hawa sama dan isketa dakinta domin a tunaninsa tana dakinta ne. ....sai ya sameta a falonta ta dantsatsa uwar kwsalya cikin shiga mai kyau da alfarma ga kanshi na tashi a jikinta, tana jiran shigowarsa ne.....domin yana shigowar ta mike tana murmushi, sai dai kunya ta hannata zuwa ta rungume shi kamar yadda ta tsarawa kanta tunda ta raka kurma dakinta ta yi barci ta yi mata addu'a ta je nata dakin ta yi wanka da shiryawar nan dan ta tarbe shi, wanda ta sakawa ranta cewar zata yi haka dan ta sake kusanta kanta da zuciyarsa ne........................
A hankali ya karaso inda take tsaye, sai kuma ya saka hannu ya janyota jikinsa ya rungumeta tsammmmm a cikin kirjinsa........, Muryarsa ta fito a hankali ya ce" Baba ne......, yace ina iya zuwa in ga Mama......, Hajia karamahhhhhhhh.............da gaske yake ya yafewa Mama"
Da sauri ta dago fuskarta tana kallon tasa, sam ya ki a kalli idannuwansa saboda irin halin da yake ciki mai girman gaske ne........, da wani irin farin ciki ta ce" Alhamdulilah, papah litle alhamdulilah......, plz mu tafi.....mu tafi yanzu plz....."
49
07/12/2024, 17:38 - samiraharounayacouba: Murmushi ya saki mai tafe da wani irin ajiyar zuciya sannan ya kai zaune da ita a jikinsa a hankali ya ce" idan muka je ta yiwu ta kwana bata rintsa ba....kuma kin ga bata da lafiya....., in sha Allah zamu tafi da asubahi domin ina gama sallar aubah zan dauke ki mu tafi....."
Khadeeja ta kwontar da kanta a saman kirjinsa a tausashe ta ce" Allah ya nuna mana rohi....., bari in kawo maka abincinka nan"
Mikewa ta yi, shima sai ya mike din yana kallon ta yana fadin" Mu je in taya ki dauka mu ci a dakina....."
Hakan ne ya faru, sun ci a dakinsa bayan nan sun yi bruch suka kwonta ya rungumeta a jikinsa yana dan shafa jikinta a hankali har barci ya dauketa
A nutse ya zubawa fuskarta ido , du wani tunanin zuwan alkhairin duniyarsa idan yayi sai ya ga tana shigowa hakan ya same shi...., irin yadda du motsinta cikin hikima take jefo maganar maman nasa kuwa ya ringa bashi mamaki da mamakinta da tunanin kamar wace ta wuce shekarunta......., sai dai hakane, mata Allah na halittarsu ne da hikima , sai wace ta zubar da nata ne zata auri wata rayuwar daban....................
Sai da ya gama yiwa Allah godiya da bashi wace ta maye gurbin iyalinsa mai albarka mai kula, mai hankali da tarin ilimi....mai addini, tabbas ya san ya more, jiran da yayi ya ci ribarsa.
Alwallah ya dauro ya haye salaya dan baya jin in zai iya rintsawa a yau, gaba daya farin cikinsa ya sa ji yake yi kamar ya yi ta ihun murna hadi da kuka wiwi irin na wanda aka yiwa mugun duka...., sai dai hakan ba zai samu ba sai wani irin farin ciki da annashuwa dake tasowa tun daga cikin zuciyarsa
Kwana yayi yana ibada, bayan ya wuce masallaci da asubahi a yau hatta yan anguwa sun karra sannin yau rana ce ta musamman a duniyar bawan Allahn nan mai yawan kyauta, domin kyauta ta bajinta du Wanda ya fito dan yin ibada ya sameta a wannan safiya.
Da wuri ya wuce bangarensa bayan ya gama da bangaren hajia Inna, ya damu wani abin farin cikin , domin tuni sun shirya, uwa uba an fitar da girki cewar Mama din za'a kaiwa, sai kawai yake gannin abin bako a duniyarsa,
Da wuri wuri ya gama shiryawar shima ya sauko ya karasa bangaren hajia Inna dan sun tafi cen din
Ya yi shiga ne ta dakakiyar shada da hula, kanshi turaransa kuwa shi ke sanar da isowarsa waje da zarar ya doso wajen
Samunsu yayi sunna zaune sunna fira dakin hajia innar a cike domin du wa'inda ke gidan sunna nan
Sake gaisawa suka yi a dan tsaitsaye ya juya bayan ya furta" Sai mun dawo"
Da sauri kaka z ta mike tana fadin" ai kuwa mu je da wuri wuri saboda a samu a tattauna sosai a gidan"
Du kallon ta suka yi, domin su Dukansu sun tashi da niyar binsa, baba Hamza ne Yace a'a yau dai a barshi su tafi shi da matarsa da y'arsa sai aunty shareefat, itama cewa yayi da zarar ta ga komai ya daidaita ta samu ta silale ta zo ta fara shirin tafiya saboda mijinta yayi kira ta tarda shi Niamey , shine hajia z zata yi kamar bata ji ba tace bari su yi su tashi su tafi?
Khaleesat kallon mahaifiyarta take yi a zuciyarta tana ayyana ' ina tsoron wasu abubuwan idan na ga kina yi mama, bayan kin min alkarin cewa ba ke ba ire Iren abubuwan nan tun ranar da kuka fito ke da kawarki daga ɓangaren big son, ke da kanki kika min alwarin nan bayan na yi maki dogon bayani da tuni da hannunka mai sanda a kan lamarin da ya shafi big son da duniyar baba Hamza......, sai dai gashi nan a yanzu ma kamar baki gane ba mama....dan Allah ki rufa min asiri mama , kar ki ja abinda baba Hamza zai tsane ki a duniyarsa da Ni baki daya'
Kaka b ce ta ce" A'a, ki zauna kawai......, jikale tashi y'ar albarka ku je mota, bari ki ga in taya maman naku kula da masu saka kayayyakin da aka fitar din, Allah ya muku albarka, mu ma je daga baya in sha Allah"
Kaka z ta dan dubi hajia b sannan ta zauna tana jin gwuiwarta na sacewa, a ranta kuwa tunani take yi anya ba SHAREEFA bace ta fadawa mahaifiyarta wani abu dangane da comportement dinta ?, a kwanakin nan wasu abubuwan saima an yi an gama take sani, bayan a da ko menene ana ƙoƙarin sanar mata itama dan a fita hakinta......, a yanzu kuwa sai abinda ba za'a rasa ba in ya zama wajibi ta ji take ji, nan fa suka gama yiwa baba Hamza fushi ita Bama ta da labari, koda yake ko a lokacin da hajia Inna keda dan karfi karfi haka suke yi sai ace wai a hade masa kai, ita kam bata biye musu dan bata ga dalili ba, su suke yin hakanan har su yi su gama ita tana cencanar dan tsohon ta...., to ama ai bata isa ta raba tsakaninta da big son ba wallahi, sai dai kowa yayi ta kansa a lamarinsa.
Mota uku suka fita da ita saboda irin yadda baba ya da a cika kayan tsarabar da ya shafi abinci kala kala a motoci biyun nan, bai san cewa a gidanta tun kafin store ya kai rabi ake sake sake shi, koda yake datako ne irin na manya masu daraja da suka san ana ungo koda a wajen da ake da shi ne ya sa ya yi wannan motsin......, hakan kuwa ya matukar birge jikan nasa dake Hakimce a bayan mota hannunsa rike da hannun anmy dake gefensa, a gaban motar kuwa aunty SHAREEFA ce rike da litle tana saman cinyarta zaune ta cika motar da Yaren bebencinta sai ihun murnar nan take yi tana dake tambayar shikenan itama yau zata je ta ga maman nan da aka hannata maganar ta? Ashe dai zata ga maman babanta ??????, farin ciki zallah take cikinsa , kuma babu wanda ya hannata dan kuwa kowa zuciyarsa cike da tunanin wannan rana yake
Sunna isowa mai gadin ya karaso har wajen motocin ya duba da kyau, ai kuwa yana gannin wanda ke motar ya je da gudu ya bude idannuwansa waje cike da wani irin farin farin ciki marar misaltawa saboda a gidan nan daga masu aikinta da mai gadin ta babu wanda bai san labarin gudaliya da abinda ya faru ba, dan su har tunani suke yi ko ta zauce ne? Zuwa take yi ta zauna kawai ta yi ta yi musu labarin gudalinta, shi yasa mai gadin ya ringa amsa mata taimako na dangana a wajen mahaifinsa baban malamin addini, da adu'o'i masu daraja wa'inda ke saka mata nutsuwa da sake kusantar kanta da Allah.
Tunda motocin nan suka tsaya masu aikin suka fara lekowa dan gannin su wanenen a mota fiye da daya a gidan nasu yau????, domin babu mai kawo musu ziyara sama da yaron uban gidan nasu....., shi kuwa bai taba zuwa da mota sama da daya ba......, sai dai sunna cikin wannan tunanin uwar gidan nasu da yauma ta tashi da begen yaron nata tana ta dakon karfe goma ta yi ta yi kiran numbar matar yaron nata kamar yadda yanzu ta mayar da haka kamar ibada, saboda lokacin na yi take kira ta yi ta fira da ita, itama yarinyar ya zamo idan bata yi kiran Bama itace ke kiranta tun daga lokacin da suka yi waya da daren nan shakuwa ta shiga tsakanin su mai girman gaske, a yanzu itama ta fito dan gannin su wanene a motoci sama da daya, a lokacin ne kuma su aunty shareefat suka fito, sunna kallon ta , haka shima ya bude bangaren nasa Ama kaffafuwansa sun kasa daukarsa, idannuwansa a kanta daga inda yake zaune , dan shi yana hangota rasssss, a fili a wajen da ba wani shamaki, duda yakan ganta a ire Iren lokutan rashin lafiya idan tana cikin daki yakan tsaya daga jikin madubi ya kalleta son ransa, ko idan ta tada rikicin sai ta ganshi yakan je inda take daga nesa ya zauna yana hangenta, sai gashi yau yana kallon ta a kusa da kusan da babu wani shamaki a tsakani
Da sauri ta sauko daga matakala ukun dake hanyar ta karaso tana kallon aunty SHAREEFA da fuskarta ta bayyana da fafadan murmushi ta yi iya yinta ta cire duk wani rashin jituwa da ya faru tana duban matar d'an uwanta da fuskar da ta fi sauki a lamarin tana mamakin lokaci da damuwa irin yadda suka iya motsar da mutun su saukar masa da tsufa , duda ba laifi a yanzu ta kai shekara hamsin ko kusan hakan a duniya......Ama kuma bai kai ta yi irin tsufan nan da ya bayyana a tare da ita ba.....,
A hankali ta ɗan daga hannunta sai kuma ta mayar jikinta a hankali ta ce" Kamar Shareefat?....., anya ? Shareefat ai ba zata taba zuwa inda nake ba, shareefat fushi take yi da Ni itama...., maman gudaliya fushi take yi da Ni itama"
A hankali shareefat ta ɗan mayar da kanta gefe cike da tausayin gannin kamar matar yayan nata ta ɗan samu matsala a ƙwaƙwalwa ta ce" Ni ce auntyna, ni ce Na zo, "
A hankali a hankali kuka ya bale mata tana shashekar kukan nan masu aikinta suka karaso sunna kokarin hannata kukan ta Kiya tana kallon aunty SHAREEFA ta kama hannunta ta ce" SHAREEFA, nice na kashe shi akace ko? Wallahi ba kashe shi na je yi ba, kin ga yaya za'a yi Ni khadeeja in kashe Muhammad? Haba dai Ni khadeeja ba zan iya kashe mumu dina ba, wallahi na nemi maganin nan dan in masa kadawar madara in shanye na rasa.....kin kawo min maganin ne? Kin kawo? Ina gudalinki? Ina gudali? Ki fada masa Allah kuwa ba zan iya kashe mahaifinsa ba...."
Da sauri aunty shareefat ta kamata hawaye na bale mata , kurma kuwa ta ja baya tana kallon su, a hankali ta ce" Ku sake ta "
Masu aikin nan suka saki mama khadeeja
Aunty shareefat tana dubanta ta ce" ki daina kukan haka auntyna, kin kuwa ga waye ya zo maki yau? Zo ki ga gudalinki, taho ki ga gudalinki "
Tana fada tana rikota da kyau ta nufi bayan motar a hankali da ita , ita kuwa jikinta nan da nan ya dauki rawa, sunna karasawa bayan motar suka same su, khadeeja na rike da hannunsa tana murzawa a tausashe tana fadin ya fito, ya gyada mata kai ama ya kasa fitar, sai ganninsu suka yi sun karaso daf da daf da ƙafarsa daya da ya fitar waje
Jikinta na mugun rawa ta saki hannayen aunty SHAREEFA ta riko damtsen hannunsa guda, sai kuma ta saki ta kama fuskarsa, ga saki ta rike hannayensa......
A hankali ta ringa shidewa tana kokarin har kama sunnansa a lokacin da ya rike hannayenta ya zubawa fuskarta ido hawayen da yake ta tunanin a inda zai same su suka shiga bin kumatunsa ba tare da ya san fitarsu ba, murya a raunane sosai ta saka dariya hadi da fashe da kuka mai tsananin gaske kafin ta rukunkume shi da runguma mai matukar shiga jiki, kukanta hadi da hailalarta suka saka saka gaba daya mutanen dake wajen nan kuka, shi kuwa hancinsa a jikin tufafinta yana rike da ita tsam a jikinsa , da kyar ya iya samun amon Muryarsa ya furta" Maman gudaliya....."
Mama khadeeja ta karra fashewa da wani kukan wanda da kyar aka samu ya lafa mata, sai dai ta ki sakinsa a haka dole ya sauko da ita a jikinsa a rike kankam suka nufi falon nata sai tambayoyi take tana ta rike kuncinsa tana
Ta faman tambayoyi da neman afuwa , suka zauna a kujera yana rike da hannayenta a hankali yana bata amsoshinta, du idan tace masa ya san dai ba zata kashe babansa ba da gangan ko? Sai ya rike hannayenta ya gyada mata kai , da kyar dai suka samu ta dan lafa , har ta iya gannin khadeeja da kurma , wace ke lafe a jikin khadeeja , nanma farin cikinta ya karu , Sai godiya take yiwa su khadeeja da aunty SHAREEFA, sai tambayar su hajia Inna take da su baba da su hajia Binta, kai du wani da ta sani sai ta tambaye su shi, su kuwa sunna bin yannayinta a hankali da tausayawa sunna bata amsa, hatta abincin da suka zo da shi nan aka zuba , AL'WALED ya sauka saman cafet, ta kuwa sauko itama ta zauna a nan din tana rike da hannunsa guda, ya ringa saka mata abincin nan a bakinta yana yi mata murmushin da Allah kadai ya san irin farin cikin dake lulube a cikin murmushin, inda khadeeja hankalinta ke matukar kwonce ta samu wata irin nutsuwa ta ratsa mata zuciya, du idan ta dago suka hada ido sai ya faki ido ya sakar mata murmushi ko kuwa ya wani lumshe mata ido , ya zamo daga dan nesan da suke yana bata kulawarta itama..............
(Allah ka yafe mana, Allah ka sa a kadarar rayuwarmu babu ta rai, ya Ubangiji ka sanyaya mana zanen kadarar rayuwar mu)
A gidan baba tsoho kusan karfe takwassss su Aba suka same shi a falon hajia Inna shi da malan Abdullahi suke sanar masa duka abinda ya faru, cewar a jiya dai an daura auren Karima, sauran kuwa yau da yama za'a daura da komai da komai
Baba Hamza ya ringa mamakin lamarin maman Karima da irin abinda ta so saka y'arta, cike da mamaki ya ce" To wai mutane a me suka dauki duniya ne?, dama yaya na auren mijin kanwa da rai da komai?, yarinyar nan ko dai ta samu matsala a kwakwalwarta ba'a sani ba? Ka san wani lokacin fa ba'a gane mutun hauka yake yi sai tafiya ta yi nisa"
A tausashe malan Abdullahi ya ce" Hum, ai kam haka dai na yi tunani da yarinyar nan ta wajen maiga, ka san cewa wai hannunta ta yanka irin abin nan da ake yi dan a kashe kai? Kai dai Allah ya rufa asiri aka ganta da wuri ba rabon a yi baban tabewar , wato a kashe kai, maganar da nake maka yanzu haka sunna waje ita da maman nata da mahaifin nata wai an Kaita asibitin waje , sun ce ana yi mata séance na thérapie dai a yadda Muhammadu ke fada min, yarinyar ta zama bata cewa um bale um um, da na kwatantawa uban ya dace a fuskanceta a tsaga mata gaskiya a kuma dawo da ita hayacinta a yi kokarin sake dorata a turbar gaskiya sai cewa yayi shi bai sabawa ya'yansa haka ba, in barshi zai daidaita abinsa a hankali, abinda dai ya sani shine in dai ya samu yadda yake so Bama zasu dawo rayuwar Nijar ba bale har ta ringa tuna Elhaji, to kuwa ka ga ai ba'a nemi sauki ba, Kai da zaka rungumi addu'a da tsarkake zuciyarka ka kusanta kanka da Allah ko ka samu sauki sai ka karra dauko wani abin ai dole zuciya ta ki samun sukuni "
Baba Hamza ya girgiza kai cike da alhini ya ce" Ikon Allah, wai kenan shi sai kace rainon faransa?"
Aba ya tabe baki yana sake baje goron dake gabansa yana Kasafi dan karma tsohon nan ya cuci matansa da kansa yake rabon nan ya dago zai yi magana hajia zainab ta shigo tana fadin" Ki shigo mana na ce maki a nan yake elhajin ai, shigo mana"
Maman Karima dake dizgar kuka rike da huhun