Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   40 / 64

117K to 120K   out of 190.8K words

nufar dakin shara da kwondon shara ya dauki wayar yana gannin sunnan kaka B, wato Hajia Binta ne ya daga a tausashe yayi salama

Hajia Binta ta amsa sannan ta ɗora da fadin" Ranka ya dade ina ka buya haka ka bar amaryar tamu ita kadai gata ta zo da zazabi kuma mun rasa docter Maryama sai docter Najeeb muka samu muna ta nema mu ji ya shiga ya dubata ne ko mu kaita asibiti?"

Dan jim yayi, sai kuma ya bude motar ya fita da ky din a tausashe ya ce" Na shigo gidan, ina zuwa"

Daga haka ya kashe kiran ya nufin bangaren nasa a nutse yana dan dagawa masu yi masa sannu da zuwa hannu har ya shige bayan mai tsaron babar kofar ta bude

Karasawa yayi bangaren baki , domin har zuwa lokacin sunna nan da Docter a zaune

Hannu ya ba Docter yana duban aunty shareefat da Hajia Binta ya ce" Uman AL'WALID baki yi barci ba?"

Aunty shareefat ta ce" Ina zan iya yin barci d'an shareefat yarinyana ba lafiya kuma ko abincin da na kai bata ci ba? , waiya nake gannin hannunka ba komai? ina yar ledar nan baka da ake shigowa da ita? Docter gane min hanya?"

AL'WALID ya dan yi murmushin dariyar da Docter yayi ya ce" Gaskiya sir ya muke ganninka hakaa?"

Ya girgiza kai kawai ya nufi hanyar sama yana fadin" Bari in yi mata magana"

Su kam ci gaba suka yi da fadin ba fa zai yiwu ba a yi mata maganar ba laifi ama kuma a fitoma a ganar da su maganar hannu sumul ba leda mai dauke da zukul hamama.


A hankali ya bude dakin da yake kyautata zaton shine nata bayan ya buga sau biyu a hankali ba'a bude ba

Fitilar dake kashe ya saka hannu ya kunna ya shiga neman inda zai ga mutun

A kwonce take ta ba kofar baya, kwonciyar Tata ta dage rigar abayar nan dake damunta har kusan cinyoyinta, ta saki gashin kanta dake daure ta rungume filow, wato saman filo din ta hayar da kirjinta hakan ya sa gashin kan nata bazuwa a wuya da gefen kafadunta zuwa saman shinfidar

Idannuwansa ya dan dauke a hankali ya kalli kasa, sai dai cikin ikon Allah idannuwan nasa suka sake dauko duban nasa suka mayar saman wace ke kwonce, wace ya ringa jin wani dan abu na ratsa jikinsa kamar wanda yake jin sanyi haka dai.....


A hankali ya karaso wajen gadon yana kallon abin maganin dake ajiye

Dukawa yayi ya dauka ya karanta maganin, kil fevr ne, sai ya ajiye ya sake dubanta da tunanin yaya zai tashe ta?, gata da sunnan da bai san ko bakinsa zai iya kamawa tashi daya ba


A hankali ya dan bunbuga gefen filon ya bude baki zai fadi sunnanta da ke tashi mana, ta yi wata irin juyowa tana fitar da idannuwanta waje, lokaci daya kuma ta gwara goshinta da goshinsa sai kuma ta koma ta yi wani zama tana fitar da ido hadi da murza gaban goshinta

Kallonta yake yi bayan ya bude idannuwansa da ya rintse, a hankali a hankali kamanin mai jifa suka dawo tarrr a idannuwansa Duda wasi wasin da ya shiga ransa domin wannan sai ta cika idannuwansa sosai

Da sauri ya dauke idannuwansa ya mike a nutse ya furta" Sorry, Ba ke nake nema ba, ina sister din naki......, ya Salam, ina zuwa" Sai kawai ya kama hanya ya nufi waje dan komawa ya tambayi wa'inda suka kawo yarinyar inda suka ajiyeta suka bar kanwarta a dakin da yake kyautata zaton nan ne zasu saka amaryar tunda shine dakin dake jikin nasa, kuma ya san dai da wahala ace koda kanninta zasu kwana a gidan nan yau sun kwana daki daya, ai an jima da daina wannan lamari, sai dai kuma ta yiwu haka din ne, ta yiwu mai jifar ce tace sai a dakin amaryar zata kwana tunda kamar ai rigima gareta yarinyar


Baki bude Anmy ta bi bayansa da kallo, lokaci daya ta zabura ta mike tsaye ta furta" Innalilahi, sak irin masu ƙarfin nan na Indiya sai dai shi saje gare shi, to waye wannan? ga dare ya latsa gani Ni kadai ko dai aljanni ne? innalilahi bari in yafa rufar nan in nemi cikin jama'a in shige kar a kashe Ni a yiwa Mama asara abu daya jal kamar rai ????"

Da sauri ta diro ta dauki rufar da aka yi mata ta amare ta dan yafa ta saka slifas dinta da aka kawota da shi ta juyo da dan sauri ta kama hanyar fita


Tunda ya dawo ya tambayi a wani amaryar take suka sanar masa dakin dake jikin nasa, yayi tambayar ok tare da kanwarta take ne? aka sanar masa a'a ita daya ai aka kawo tana kwonce da bak'ar abaya sai ya samu kansa da dan zuba musu ido, sai kuma ya juyo wajen Hajia dake tambayar ko jikin yayi tsanani ne kawai su haye sama da Docter?


Docter din ya juya ya kalla, lokaci daya kuma suka juya inda suke jin tafiya, saukowar Anmy, mayafin kanta na sauka daga jikinta tana dube dube da tunanin inda zata auka a guje dan samun tsira

Idannuwansa ya lumshe sakamakon bayyanar baki sidik din gashin kanta fili, a irin wajen da ba kowa ya dace ace ya gani ba, duba da ita din ta dauki daraja mai girman gaske a yau , wace ta amsa sunnan tasa!, kuma ya zama wajibi a kiyaye hakan ba dan kishi ko wani abu mai zafi ba, a'a, sai kawai dan a kare hakkin addini........, hakan ya sa ya dan dubi aunty shareefat kasa kasa ya ce" Zamu kaita asibiti"

Daga haka ya mika hannu ya kashe fitilun falukan gaba daya saboda ragewa idon da ya kurawa y'ar mutane ganni, domin docterma kallon y'ar mutane ne yake yi bayan kamar hakan shiga gagarumin hurumin addini ne


Bayanuwar duhun nan ya saka Anmy kamewa, sai kuma ta bude baki sama sama ta furta" Kai, innahu mine sulaimana wa innahu bismillahi rahamanin rahim, ko dakin abin na fado gaba daya ne?'''"


Aunty shareefat da mahaukacin mamaki da wani farin ciki suka lulube zuciyarta na abinda ya faru, da kashe fitilar tasa da maganar cewa sa je asibiti da itan ta mike a hankali ta ce" Mu je Hajia, docter bismillah"

Hajia ta yi mirsisi ta ki tashi ta ce" A'a shareefat, wai me ya samu wutar ne? ya zamu je haska cen wajen Muryar yarinyar nan fa nake ji , ga wayata haska in gani"

A hankali bayan ya rike wayar ta hajia ya ce" Uman AL'WALID mana"

Da sauri Aunty shareefat ta kama hannun Hajia dariya na kubce mata ta ce"
07/12/2024, 15:14 - samiraharounayacouba: *FARKON GANIN IDONA*


PAGE 34

TALLAH TALLAH TALLAH TALLAH

*Zumar 3in1 zumace ingantacciya mekyau megyara jiki sosai zatasaka kayi bulbul breast sugyaru hips yafito kiyi yar duma duma hajiya bazakigane abundanake fadaba dai kinshata zakigane*
*08030861857*
*Zumar breast Zumar hips duk munadasu masu inganci sosai da sosai*

*Akwai pills na 3in1 shima aikinsu Daya da zumar 3in1 gawayanda basashan zumane mukayi daminsu*
*08030861857*
*Infection flusher Ingantacce maganine mai magance dukwata matsalar mara Kai harda rashin haihuwa yanayi banahaufi akai don angwada angani mace indai rashin niima ne na cutar sanyi yararaketa kuraje kaikayi dattin mara zonabaki infection flusher kisha mamaki yar uwa Insha Allah zakigodemin*

*Kayanmu guarantee ne sai angwada akansan nakwarai location gombe munaturawa koinah Insha Allah* *08030861857* Kira KO WhatsApp Insha Allah



LABARI




Da sauri Aunty shareefat ta kama hannun Hajia dariya na din kubce mata ta ce" Hajia mu tafi mana"

Hajia ta mike du ta shiga tunanin abinda yake faruwa dan ita bata gane komai ba, haka kuma kukan yarinyar kasa kasa na tashi hankalinta na son tashi, haka dai suka bi bayan shareefat din ita da Docter Najeeb


Sai da ya ga rufowar kofarsu sannan ya mika hannunsa a nutse ya kunna wutar ya shigo falon ya ja ya tsaya yana kallonta

Da sauri ta dago kanta da ta cusa cikin kaffafuwanta tana mururai ta zuba masa ido

Shima kallon nata yake yi, ya ki yayi magana yana hankalce da yannayinta, farko addu'a take yi sai ta dan faki idonsa ta tofo masa, sai kuma ta karra sada kai, har ya zamo yar ido da ido ne take tofa masa addu'ar, ta mike ta nufi inda yake ta miko dan hannunta da nufin taba kirjinsa da shi dan so take yi ta tabbatar cewa mutun din ne

Gocewa yayi ya shiga tafiya a hankali ya ce" Kar ki taba Ni!, kin wani yada mayafinki a wajen da ba kowa ne yake muharaminki ba, ke bakya tunani ne?"

Khadeeja ta zuba masa ido, ta ga ya nufi inda abin rufarta yake, sai ta samu kanta da furta" Allah dai ya sa ba kai ne ake nufin wai an bani ba"

Daga ita din, da furucin bakin nata sai da suka sake dukansa a inda bai shirya ba, kai ku ji da fitina, an bata? ko an bashi?

Tsayuwar yayi yanzunma ya harde hannayensa yana kallon wace ke magana

Khadeeja ta dafe gaban goshinta, ta rintse idannu, a hankali ta ce" Dan Allah ka yi hakuri ka bani amsa, dan Allah kai ne? to ai ganganci kennan haihuwa da damuna, Ni din banza zan zauna da mai kyau? Hau ya fada min hala da zan zauna da mai kyau kuma mai kudi, inaga lokaci yayi da za'a yi abinda ya dace, in sha Allah daga nan sai in yi waje dama na kula kayana kala uku kawai aka sako min, an ba babanmu idan ya fito kasuwa inma ba'a bani ba na yafe , ah kai ina"

Ba wai da karfi kalaman ta ke fita ba, hasalima ta karkatar da kai yadda ka san tana kukan tashin hankali domin harta muryarta a tausashe sosai take furucin da ita, sai hannunta dake murza gefen wuyanta , gashin kan nata kuwa ya zubu gefen da ta karkatar da kan

Sake juyawa ya yi a nutse ya shiga haurawa da mayafin nata a hannunsa

Ido ta dan zarro, lokaci daya ta shiga tunanin to ko dai baya jin Hausa? kar dai aje Balarabe ne? da an ga balaki to ita a larabcin nan banda dajajatun me ta gama fahimta? ta san dai ba zata ce da shi anstun ba, ta'alll kuwa yayi tsauri a miji ko? ya Allah, lokacin a bani Yaren nan a harshena yayi, gaba daya ta manta dazu fa yayi mata tambaya kuma da Hausar yayi magana, sai ta shiga haurawa da dan gudu gudu ta wani lankwashe murya tana karewa tsayinsa kallo ta ce" Ji mana, am, AM, asalamu alaikum ya ustaz, inni an.............."

Juyowar da yayi ya saka ta ja da karfi abin tiles ya j kafar

Gaba daya ta salama, t rintse ido ta riga ta ganta a kakarye kasa , sai kuma ta ji an yi mata wani irin janyowa an dan cirata sannan an hade bayanta da jikin kofar da ya so budewa ya shiga

Da sauri ta bude idannuwanta, kuma a tsorace tana kallonsa

Idannuwansa ya dauke daga fuskarta a hankali ya ce" Mema sunnanki?"

Anmy dake zarro ido a hankali ta ce" kha.... Khadeeja"

Idannuwan nasa ya maido kan fuskarta da lebenta da ya ambaci sunan nan

A hankali ya ce" Bayan shi, baki da wani sunnan?""

Khadijah ta rintse ido gumi na taruwa a gaban goshinta a hankali ta ce" Sunna ce min Mama, ko Anmy"

Dan buda ido yayi kadan a kan fuskarta sai kuma ya dan rage masu girma kadan ya ce" Ni baki haifeni ba, "

Sai kuma ya dan matsa kadan daga matse mata wajen da yayi kasa kasa sosai ya ce" Ki shiga ki saka hijab baba mu je asibiti"

Khadijah ta rasa ina zata tsoma ranta, ta dube shi ya fi a irga, da kyar bayan ta dan motsa ta ce" Me zamu yi a cen?"

A kasan zuciyarsa aya ringa ayana' In dai wannan mai jifar ce ai kya yi abinda ya fi haka, fisabililahi ke bakuwa kece zaki sakani a gaba da tambayoyin nan? Ni kam baba me ya faru da kai ka hadani da aiki?'

Yana dubanta da duban da ya sakata kasa yi masa wata tambayar Sai hannayenta da ta dan watsa a raunane ta ce" An hada min komai fa, yanzu na sha maganin , idan an jima in na ji da fever din zan yi allura"

Bai san dalilin da ya sa du in ta yi magana yake bin bakinta da kallo ba, bayan Hausa dai ce take yi ba wani bakon Yaren ba

Hanya ya bata da ido ya yi mata alamun ta je dakin nata

hannunta take murzawa bakinta na motsi kadan kadan , sai ta dan yi tafiya sai ya juyo tana son cewa a bata abar kuma wani irin shayinsa ya darsun mata a zuciya

Kasa kasa ya samu kansa da furta" Banda addu'ar in karye, banda jifa ta baya, kin ga ai ban maki komai ba"

Da sauri ta ja ta tsaya, ta juyo da wani irin sauri ta zuba masa ido, bakinta na dan rawa ta ce" Kai ne?"

Murmushi kawai ya yi ya bude nasa dakin ya shige da zannin nata, hakan ya sa Khadeeja daskarewa a waje daya lisafinta na neman kuncewa
Sai kuma ta juya da sauri ta nufi dakinta ta bude ta shiga ta rufe ta karasa bakin bed ta zauna a hankali ta ringa sauke ajiyar zuciya.......

Ba zata taba mantawa ba ranar da ta yi addu'ar nan a kan kunnen mutumen da aka kawo zai auri Karima
Ana nufin wannan ne? ya salam Karima dama basaja aka yi maki dan a ga ko zaki amince da irin zabin da kike so? KARIMA shine irin mafarkinki ba nawa ba, Karima kin sakani a wani hali na yaya zan yi, ina zan kai mutun irin wannan? ina zan kai shi? KARIMA kece daidai da shi, ke ce kika dace da shi...Ya Allah.....Da sauri ta rungume hannayenta a kirjinta sakamakon wani irin bugawa da zuciyarta ke yi mai tsananin gaske, zazzabin da ta ji saukinsa ya nemi sake rufo mata, a dole ta ja abin rufa ta kudundune jikinta a ciki tana addu'a dan samun saukin wannan abu da bata taba jinsa a rayuwarta ba sai yau.


A bangarensa kuwa yana shiga dakinsa ya samu waje ya zauna da zanninta a hannunsa yana sauke wani murmushi da ya tsaya a saman lebensa

Ba komai ke saka shi jin dariya a ransa ba sai irin yadda wai ta yi tsaye take Larabci, uwa uba ko ya salameta ko me? To ta je ina? ai ko babu ran baba tsoho a yiwa kushewa, ko jaki ya daure a gidan nan an bashi ruwa bale mutun, mutun dinma y'ar kakan kurma? uhum, lalle yarinyar nan ta zo da bidi'a mai karfin gaske, zai yi mata addu'ar samun linzami a harshe da kuma ikon yiwa uban kurma biyaya saboda rayuwa ai ana yin biyayar auren nan dan Allah ne ba dan wani ba, in ba abin yarinyar nan Bama shima ai irin na kakaninsa aka yi masa, jeka daki ga matarka cen, bai san inda aka jefa shi ba sai hali ya bada damar karantar hali a zama irin na yau da gobe mai binciko da boyayan sirri komai girmansa

Mikewa yayi ya bar komai nan saboda yayi abinda ya saba kafin ya kwonta, gashi yau ko su Hajia bai leka ba, irin wannan lokacin ya san ta yi barci daga ita har Litle

Bayan ya gama komai ya zo ya kwonta ya dauki wayarsa yana dubawa, nan ya samu misss call din Mufeeda birjik a wayar

Ya dan jima yana dubawa kafin ya fita a nutse ya dana wajen wanda ke kula da harkar sirinsa ya yi msg kamar haka " Ina son bincike a kan dukkan abinda ya shafi Mufeeda nan da sati Daya"

Daga haka ya sauke connexion din ya lumshe idannuwansa yana neman barci, Duda wata zuciyarsa na yi masa maganar ya leka dakin mai jifa ya ga jikinta? sai wata ta yi hanni da hakan ta nuna masa zai leka idan an jima ai, ta yiwu yanzu ta jima da kwontawar harma ta samu barci



A gidan malan Abdullahi


Karfe goma sha biyu harda minti arba'in da wani abu , ama gidan babu wanda keda alamun kwonciya saboda fitinar dake faruwa wace ta same su rana tsaka, to rana tsaka zasu kirayi abin mana tunda basu saba gannin haka ba, tun daga Elhaji Maiga har autar gidansa ne a gidan nasu, domin tunda ya koma a birkice ya Sa aka basu salama bayan likita ya duba shi ya sanar masa Elhaji Ya'u bai fasa masa molon kai ba sai ya sa aka salami Mufeeda dake cikin aikata musu hauka tubran tunda kanwarta ta tabatar mata aure fa an daurawa AL'WALID shi a yau, ita dinma take ihun a salameta dan kuwa aiki ne ja a gabanta, ta yi rantsuwa ta maya ta ci alwashin ko ita ko wace AL'WALID ya aura, ba zata taba yafewa yarinyar ba, uwa uba idan wani sashi na zuciyarta ya hasaso mata shi da yarinyar da ya aura sai zuciyarta ta yi kamar zata daina aiki, tabasss yannayinta abin tausayi ne domin shi so bai bar kowa ba, idan ka cire furucin bakinta dake sakawa a daina jin tausayinta sauran lamarin komai ya shigo ne a daidai lokacin da ba lalle zuciya ta amince ba


Duban Malan suke yi su biyar dake zaune a saman shinfidar tabarmar da aka shinfida ya gama yiwa Mufeeda tofi ko Ayar Allah zata sa ta nutsu, a nan ne mahaifinta ya fitar da rikitaciyar maganar da shi dai ya yi masa kallon ashe Maiga baka da hankali? ama kuma ya kasa furta koda A ne yana duban kasa, sai matarsa dake kallonsa kirjinta na dokawa dan wannan abu kam ba zata taba bari mijinta ya aikata ba

Elhaji Maiga ya ce" Abdullahi kai fa nake sauraro, ka duba ka ga halin da y'arka yake ciki, ya dace ka

40 / 64