Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   2 / 64

3K to 6K   out of 190.8K words

ta biyo su a wata motar da direba tana tsaye tamkar zata fashe, sai dai bata da halin nuna damuwarta,

Da kyar babar likitar dake aiki ta sake dannar likitocin tana fadin su yi hakuri abokiyar aikinsu ce su fara dubata first, hakan ya sa suka dukufa kanta ba ji ba gani har suka gano aikin da aka kawo masu ba nasu bane, na likitar haihuwa ne, ama kuma a dole suka daidaita abin suka tsayar da jinnin suka yi mata allura sannan suka kaita dakin hoton ciki suka yi mata suka kuma dawo da ita dakin hutu bayan sun kimtsata bisa hadin kai irin na likitoci sannan babar likitar ta bashi damar shigowa shi da Amaryarsa

Da kula sosai Docter Zalika ta sake gaishe shi
07/12/2024, 14:40 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na biyu (2)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*


*META FORCE*

*menene meta force*

business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force

*shidai meta force crypto currency* ne

kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency

akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba

yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai

*TACTILE*

1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars

hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira

*Spillover*da*over flow*

wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu

to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*

*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja



LABARI

Da kula sosai docter Zalika ta sake gaishe shi, shima ya amsa yana bin Hajia da kallo wace ke kwonce tana sauke numfashi a hankali a hankali

Numfashi ya sauke ya ce" Likita bari ne ta yi ko? likita wani abin ta sha ta zubar min da ciki dan tarin kiyaya ko menene?"

Da mamaki docter Zalika ke kallonsa, kwarai takan ji bayanin mutun ne mai tsatsauran ra'ayi da wuyar zama a wajen wasu abokan aikinsu domin da kyar da jibin goshi ya yarda da aikin nan na Hajia , a yanzu haka su da kansu sukan zamo shedun wasu rigingimun dake faruwa tsakaninta da shi saboda aikin, domin shi irin mutanen nan ne da basu san boye bacin rai ko yin karra idan ransu ya ɓaci ba, duk inda ta kama gwada hali yake yi baya shaƙar kowa ko komai baya bari su je gida su yi a dakinsu, shi yasa ake yi masa take a wannan gari shine mai kudi uban kowa sannan kowa banza, ama bata taɓa tunanin zai dubi babar mutun mai tarin daraja, babar likita malamar likitoci ya yi furucin ta zubar masa da ciki ba, sai dai bata da hurumin nuna masa bacin ranta, sai ta tausasa murya a nutse ta ce" A'a Elhaji, babu abinda ta sha ko ta matsa da zai haifar mata da zubar jinnin nan, ka ga dukkan abinda ya dace mu yi mun yi kafin ka shigo, jinninta ne ya hau sosai shi yasa cikin bai zauna ba, zata kwana a wajen mu zuwa gobe in sha Allah mu ga yadda jikinta ya bada sai ta je gida, Allah ya bada lafiya"

Tana gama fada ta fita daga dakin ta nufi wajen ma'aikatansu suka zauna suka ci gaba da aiki

Ya jima yana kallonta da tunanika kala kala a cikin zuciyarsa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kalli amaryarsa ya ce" Ni zan wuce gida sai da safe"

Mikewa ta yi da sauri tana fadin" Mu je, Allah ya bata lafiya"

dakatawa ya yi ya juyo yana kallonta ya ce" Ban gane mu tafi ba, waye zai zauna a wajen ta? ko so kike in sanar da gidansu dan bata da lafiya bayan gaki y'ar uwarta? ki koma ki kula da ita shi ya fi alkhairi idan kin bi Ni gidanma babu abinda zaki min, yarana dama ba ke kike kula da su ba bale in ce in ba ke wa zai kular min!" Yana gama fada ya fice ya nufi bakar motarsa ya shiga ya nufi gida ko takalmi babu a kafafuwansa dan har zuwa lokacin hankalinsa a tashe yake sosai

Sosai hakan ya sosa mata rai, ta ki komawa dakin dan gaskiya babu ƙatuwar da zata yi jinya haka kawai, kuma ba zai yiwu ba sai an bata kwananta da ake son cinyewa dan ita shi ya fi damunta.

Docter Zalika na hankalce da su, tana gannin ya tafi, itama matar ta samu waje ta yi zamanta tana faman amsa waya sai ta mike ta koma dakin ita ta yi zamanta a gefenta sannan ta sa aka yi kiran kanwar Hajiar aka sanar mata abinda ake ciki da sanar mata cewar da sauki sosai ba sai ta zo ba, ama ta nuna a'a gatanan zuwa ta yi ta masu godiya da suka sanar mata,

Ba bata lokaci ta sanarwa mijinta ta dauki abin bukata ta tafi bayan ta bar salahun kar a sanarwa mahaifiyarsu Maganar.


Tunda duku duku ta ringa bude idannuwanta a hankali tana buɗe bakinta tana yin addu'ar farkawa a barci hadi da dan yunkurin tashi kamar yadda ta saba, sai dai jin wani irin suka a mararta ya sakata dakatawa a hankali tana bin dakin da take kwonce da kallo da kuma hannunta dake dauke da abun karrin ruwa

Idannuwanta ta kai wajen da ta ji alamun motsi, sauka idannuwan nata suka yi a kan kanwarta da ta bude kofa ta bada hanya tana gaisar da wanda ya shigo

Da sauri ta mayar da idannuwanta ta rufe tana jin muryarsa sama sama a dan dakile yana tambayar mai jikin , ya karaso inda take kwonce ya dan tsaya jim sannan ya juya
Har ya fita ya juyo yana duban Fatima ya ce" Fatima yaushe kika zo? sai da nace kar a sanar maki bari ne fa ta yi Fatima cikin ya bare"

Fatima ta yi murmushi bata tana jajanta masa da adu'ar samun wanda zai zauna mai albarka

Ya amsata da kula dan ba laifi sunna ganewa junna da Fatima daga ya fice a dakin ba tare da ya nemi amaryarsa ba dan a tunaninsa tana bayi kuma ba zai koma da ita yanzu ba dole zata yi jinyar Hajia

yana tafiya Hajia ta bude idannuwanta da suka yi mata nauyi , sannan suka cika da hawaye ta zubawa acn dakin asibitin ido kirjinta na sake cinkushewa

karasowa Fatima ta yi ta zauna daf da ita tana kallonta a hankali ta ce" kin farka? yaya jikin naki Hajia?"

idannuwanta ta maido kanta, a hankali ta dan mata alamun da sauki sai kuma ta kama da nufin tashi

kamata ta yi ta tashe ta da kyau sannan ta shige bayi ta dauko kwanon wanke baki da ruwa a buta ta dawo ta bare bruch din da docter ta miko masu tun kafin ta tafi gida ta matsa mata abin wanke bakinta ta bata ta kuskure bakinta da kyau sannan ta wanke idannuwanta da yan ruwa masu dan dumi sannan ta kai bayin ta zubar ta wanke abin tasss ta ajiye ta dawo ta dauko mata ruwa masu dan dumi ta dawo bakin gadon tana ta kallon fuskarta da yannayinta ta ce" Sannu, da ciwon har yanzu ba? nake gannin fuskarki ba dadi? dan sha ruwan nan kafin a jima a kawo kunnu daga gida"

Ruwan ta amsa a hannunta, ama ta kasa sha
A hankali ta sauke ajiyar zuciya muryarta cen ciki ta ce" Anya kuwa idan na mutu a wannan halin ban kashe kaina a banza ba?"

Da sauri Fatima ta dubeta ta ce" Subahanallah, wace irin magana ce wannan kuma?"

Fuskarta mai cike da datako ta dan yamutsa, a nutse ta ce" Eh mana, abinda nake son sani, anya akoy lada a wannan ibadar? idan zama ya.ki dadi aka nace sai an zauna saboda dalilin y'aya , ya'yan da ɗaya ce kwal tawa, ita dinma ta kai mizanin kula da kanta anya hakan ya dace a yi kuwa? ina nufin dama ya'yan nan da kake zaune kana cin kashi saboda su kana da ikon hanna abinda Allah ya dora masu ko ka sa su zama wani abin da babu shi tsarin zanen kadarar rayuwarsu ba? , da ake cewa mace na haifa dole na jure dan ita......sauran da iyayensu suka fita suka bar su me ya same su?"

Idannuwa Fatima ta sada gabanta na faduwa, yannayin da yar uwarta ke magana na daf da sakata ta fashe da kuka, shi yasa ta zabi sada dubanta fiye da komai

A hankali Hajia ta sake bude dubanta sosai tana kallonta ta ce" A takaice, zan iya ce maki na yi dogon nazari na rasa a wani bigiri zan ajiye mutumen nan, gashi dai mahardacin Alkur'ani , ama tamkar jahili, Allah ya masa wadatar da shi kansa a yanzu ba zai fadi ga adadin dukiyarsa ba, ama kamar kasurgumin talakan da ya kasa dangana da hakuri da lamarin Ubangiji, wai shin Fatima iyaye gida nawa suka kasu? a tunanina wasu iyayen maza sunna bakin kokarinsu na gannin sun ciyar, sun tufatar, sun bada tarbiyya, har Allah ya raraba lafiya, wasu sukan ɗora ya'yan a hanyar da ta dace, wasun haihuwar ya'yan kawai suka sani Babu ruwansu da wannan dawainiyar......ama shi nasa halayar uban ya'yan nan a bayane yake yana bayar da tarbiyyar kwarai , ama kuma shine shugaban lalatawa ta hanyar da ba zaki iya ganewa ba"

A birkice Fatima ta ce" Wani irin lalatawa innalilahi Wa inna ilaihi raj'une, me yake faruwa"

Da sauri Hajia ta katseta ta hanyar fadin" Ba fa abinda kike tunani nake nufi ba, lalatawar ta hanyar nuna masu wasu halayar da ko a gobe suka yi koyi da shi sun shiga uku, ba kamar matan cikinsu.....Fatima ban taba gannin uban da yake ikirarin son ya'ya a duniya ama a aikace ya zamo halaka a gurin ya'yansa ba sai uban ya'yan nan, da ace yau wani a waje zai taba daya a cikinsu zaki ga tarin tashin hankali harda kalar da baki taba gani ba tunda Allah ya halice ki, ama fa ace zaki ga irin abinda zai yiwa ƙaramar cikinsu saboda dan laifin da bai taka karra ya karya ba, rashin ji dai da kowani yaro mai rai da lafiya ke aikatawa ana masa uzuri idan ya yi ƙamari a tsawatar, to irinsa ne idan ya kama tamkar zai kashe, walahi talahi Fatima na tsane shi...................."
A hankali ta dora kanta a gefen kafadar Fatima hawaye ya shiga zubar mata tamkar an bude pampo

hankalin Fatima a matukar tashe take murza hannun yar uwarta wanda ta cire karin ruwan tuni a sanyaye murya na rawa ta ce" Dan Allah ki yi hakuri, dan Allah ki daina kuka, kema wulakantakin yake yi ko?"

Da dan takaici hawayenta na zuba ta dago dubanta tana dubanta ta ce" Kina tunanin a duniyar da nake neman mafita ido rufe dan abinda na haifa da shi har zan kula wani wulakantarwar da yake yi min? ai idan kina neman wanda taken mai kudi ya haukata kika zo kansa ki dasa aya, wulakanta mace shine abinda ya fi kwarewa a duniya, kuma nan da kike ganina a yanzu dai ba ta wannan nake ba, bai dameni ya darajani ko ya wulakanta Ni ba, abinda ya fi dadani da kassss shine na fice a gidansa na kama gabana, abinda ya fi daga min hankali rashin bada goyon bayan iyayena, yau da ace zasu bani goyon baya da na jima da barin gidansa, Fatima da ace zasu amince min da na kama haya koda ba zasu iya rikeni ba, yau koda bani da aikin yi na gwamnati na iya nema, da wata wahalar gwara wata, ko kosai zan siyar in ciyar da kaina, a shekaruna talatin da tara ina cikin ta arba'in inaga ya dace ace zuwa yanzu na wuce wulakancin d'a namiji, sai dai gashi a kulun abu ke shiga raina irin sai kace nawa iyayenma basa kaunata ko gani suke yi na yi girman da rabuwa da aurena zai zame musu abin kunya ne? shin sai an basu gawata ne zasu yarda ina cikin taskun rayuwa?"

"Ki daina wannan furucin, ki yi hakuri ki daina wannan furucin....., tabas babu abinda ya kai zama da namiji mai mugun hali tashin hankali, domin komai na duniyar na iya fice maka a rai, da yawa ta haka suke haduwa da ciwon da zai zama sanadiyar su, babu abinda baya faruwa, ama kuma babu abinda hakuri da addu'a baya magani, na sani zaki ce nima bani da tunani, na yarda na dauka , ama ki sani babu wanda zai ji ciwon damuwarki sama da iyayenmu a duniyar nan sai mu y'an uwanki, kawai dai rayuwa ce ta Hausawa da nake kasa fasarawa, ta yiwu haka muka gama gane musuluncin ta yiwu kuma daidan kennan , Ace ya zamo malan bahaushe ba zai taba yarda yaronsa ya baro gidan miji sai idan kilu ta janyo bau, wato duk wahala duk tashin hankali zai fi so duniya ta shaida y'arsa na dakinta, na rasa kunyar ace y'ar ta fito ne ke saka malan bahaushe murje ido da toka ya mayar da yarinyar gidan da shi da kansa ya san cewa tana zaune ne dan biyayyar aure da ta iyaye ko mijin baya bukatar ta , ko tsabar biyayya wa Musulunci ne? abinda na sani shine akoy cutuwa mai girman gaske wace zata ja gagarumin tsaiko a gobe kiyama, Hajia ki yi hakuri, ki yi hakuri, ki sake hakuri, mu yi ta addu'a Allah ya zaba maki abinda ya fi zama alkhairi a rayuwarki, in sha Allah na tabata ko wahalarsa da kika sha a baya ta tsaya a yau Allah zai dube ki ya dubi bayanki, Allah ya shiryar mana da zuri'a ya sa mu samu dace duniya da kiyama "

Shigowar mai gidan Fatimar ne ya saka su yin shiru da maganar hannayensa dauke da abin kari niki niki..............................................


"Malan Ambu, idan har da amana ina iya zuwa wajen nan in dauki abu kyauta in ci , yanzu dan kudin nan basa amsuwa sai ka ki saida min?" Khadija ta fada cikin yannayin maganarta mai sauka a hankali , ama izar furucin mai tafe da tarin yanga

murmushi ya yi yana kallonta, ya dauko ledar cingam din gaba daya ya ce" Hajia khadija, da ace zaki yarda da soyayata cingan din me? , darin ce bata amsuwa ai kin san tunda aka fitar da ta takarda aka hanna amsar ta kwondala, amshi darin ki, ga cingan din"

Dan jim ta yi tana kallonsa , ikon Allah soyaya kuma? malan Ambu fa zai kai sa'an babansu in bai shi ba, ta yiwu idan mamanta na yi mata fadan ta kiyaye harkar maza da irinsa take nufi, in ba mutuwar zuciya ba ina ita ina shi? lalle bai san daga inda ta fito ba da bai tarki yi mata wannan furucin ba, dan kawai tana siyan abu wajensa sai wannan maganar? lalle, ita a rayuwa bata tunanin zata iya auren mai shekaru, a yanzu shekarunta goma sha takwas soyayar jinta take yi ama a irin yadda ake maganar soyayar idan sunna tare da kawayensu ta riga ta sakawa ranta gwara ta samu yaro su girma tare

"Karbi kudin ki wuce mu tafi" Muryar Abdul karim ta sakata juyowa da sauri ta kalle shi, sai kuma ta sune kai ta mika hannu ta amshi kudinta sum sum sum ta yi

2 / 64