Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   32 / 64

93K to 96K   out of 190.8K words

kunna pampo a jikinta, jikinta rawa yake yi kamar ba nata ba, gaba daya hankalinta ba a jikinta ba, gaba daya daf take da fita a hayacinta, domin wannan abu dake faruwa da ita shine abinda ake yi a gidansu idan za'a saka mace a lalle, wato kunshin amarya, wannan abin ne ake yi,to wai jama'a haukacewa suka yi ko kawunnansu sun bugo ne sun hadeta da Karima? bafa ita bace amaryar Karima ce!

A tausashe Hajiar Larabawa ta dubi gefen da su Mama suke zaune cikin shiga ta alfarma, wato du bidirin nan da ake ciki ya'yan Mama ne kawai basu shirya ba, sunne basu san wainar da ake toyawa ba, a cikin gidan Mama lamari yayi nisa tuni su sai yanzu aka saka kowace shiryawa, mazan kuwa dama sunna tare da mahaifinsu tun dazun ya ce su je neman aure zasu tafi.

A tausashe Hajiar Larabawa ta ce" Kun yi mata dukkan abinda ya dace? kun sanar da ita dukkan abinda ke jiranta?"

Mama ta sada kai a hankali ta ce" Bata san komai ba hajia"

Hajia ta yi mata kallon mamaki, ta dubi amarya wace ke zaune itama cikin uwar kwaliya ta ce" Hajia baku sanar da y'ar taku cewa aurenta jibin nan ne ba?"

Amarya ta yi dan murmushi a hankali ta ce" Ai bamu samu zama ba hajia"

Hajia ta ta gyada kai, ta dubi inda aka rufe khadija a tausashe ta ce" Khadija , ashe baki san ke amarya bace, kai wannan ango namu Ni na san dama nice zai zaba kawai"

Wajen ya dauki dariyar barkonci, yan uwanta kuwa suka kalli junna a zabure sannan suka kalli inda take

A tausashe Hajiar Larabawa ta ce" Masha Allah, bismillah ku sakata a lalle"

Lokaci daya masu kira suka dauki gudar da ta saka su Lubna fashewa da kuka da gudu suka karaso inda Khadija take suka duka suka rukunkumeta tamkar ana yin bankwana ne ta dindindin

Rashin sani ne? firgici ne? abin dai ba karami bane da ya gigita yan matan nan har suka idasa gigita khadija , wace ta fashe da kukan itama jikinta na mugun rawa, bale a lokacin da iya ta bude fuskarta aka dauko lallenmu na Hausa aka shiga shafa mata, kanta, kirjinta, hannayenta, kaffafuwanta, ana yi ana wankewa da ruwa ana shafa turare sannan ana gogewa da sabuwar atampar nan

Ana gamawa Khadeeja dake zaune ita daya a tsakiya, yan uwanta zagaye da ita sai kukan nan take yi kamar ranta zai fita, haka summa kukan suke yi sosai da sosai, ana daukan vidio ne dan ajiyewa tarihi

Khajida ta juyo da sauri ta rukunkume su Lubna a raunane ta ce" Me yake faruwa? Lubna aure za'a min? to da wa wai?"

Sai kuma ta sake su ta rarafa da sauri ta rukunkume Hajiar Larabawa ta ɗora kanta a saman kirjinta ta fashe da wani kukan da ya sa Hajia share kwallah a hankali ta ɗora hannunta saman lebenta kasa kasa ta furta" Shiiiiiiit, kar in ji maganar ki a nan"
Ta mika hannu ta amshi sabuwar atampar nan ta lulubeta da ita a tausashe ta ce" Allah ya miki albarka Takwarraty, Allah ya sa gidan zamanki ne na alkhairi, Fatima a hanna daukan vidion nan hakanan, kama min ita kaita daki ta huta"

Mama Fatima ta kamata a hankali ta mikar da ita sannan ta nufi coridor da ita, inda yan uwanta suka bi bayansu da sauri har kamar zasu doke junna dan tashin hankali

A hankali Mama ta dauke idannuwanta daga hanyar da suka bi, ta kakaro murmushi tana duban mutane,

Ba'a jima ba Hajiar Larabawa ta ce a kirayi baba Umar ya mayar da ita gida, dama yana kofa yana jira


Kamata suka yi , da Mama da Mama Fatima suka mikar da ita sannan suka taka da ita a hankali suka fito da ita har inda uncle Umaru yake dan shi zai karasa da ita motar su tafi

A tausashe Hajiar Larabawa ta ce" Usaina, ki kula da yarinyar nan, ki barwa Fatima bakin ki tarda yaran nan, Usaina ki ja abinki a jiki, ki yi kokari ki nusar da ita, Usaina ki kula, ki saka mata girman mahaifinta a zuciyarta da idannuwanta, Usaina ke kin san me nake nufi, kuma sarai a furucin y'ayanki kin fahimci sunna da wani abu mai nauyi a zuciyarsu dangane da mahaifinsu, na sani mutun shi yake janyowa kansa komai tunda har suka iya kwasa suka bi ki suka bar mahaifinsu, kin rike su ya'ya, ama kuma mijinki uba ne cikake wanda a kusa kusan nan yayanmu suka rasa irinsa, ki yi hakuri Usaina, ki yi hakuri, na san kina gannin jarabawa mai girman gaske a rayuwa, kuma ki sani a tsaye nake a kanki da addu'a ba dare ba rana, sai dai tunda ina raye har yanzun, dole nice zan taro abinda zaki so kaucewa saboda bacin rai koda Ni dinma bana son ganninki a irin wannan yannayin, ga kudaden da Anmy ta je da su ranar da kuka yi yaji, Allah ya karra hakurin zama, a karra jurewa a ci gaba da biyaya, in sha Allah mahakurci mawadaci ne Usaina, zaki tsinci abinki tun a duniya sannan ki tarda kyakkyawan sakamako gobe kiyama, Allah ya yi albarka, ya sakata dakinta lafiya, kar a manta wunin gobe ko kofa kar ta fito, sannan a kula da dukkan abubuwan tsari , a kiyaye komai, Allah ya tsare"



Da amen suke amsawa gaba dayansu

A tausashe Mama ta ce" Hajia Ni ba zan amshi kudin kawarki ba, dama abinku naku ne ai"

Nanma suka yi dariya

Hajiar Larabawa ta yi murmushi ta ce" Su takwarraty sai na je gidanta ma hade ko Usaina? ko kuwa sai na zo daurin auren? haka fa tace in na yarda aka yi mata auren dole zan iya rasata in shiga uku, gashi an hadu da Ni za'a ci amanar ta"

Mama ta sada kai tana murmushi, mama Fatima ta ce" Hajia ki yi zamanki ki huta muna nan ai, ita da zata dauke abinta, ai kin ji cewa take yi in ta yi aure zata tara kudi ta maki ginin larabawa sai ta kai ki tana siyar da kosai tana siyo maki kayan shayi, Anmy kennan manyan gari"

Du suka saka dariya, sannan ya kamata suka tafi a hankali , su kuwa sunna tsaye sunna kallonsu har suka shige mota uncle Umar ya tayar, mai gadi Ya bude musu suka wuce

Ajiyar zuciya Mama Fatima ta sauke a hankali ta ce" Ki je wajen su Anmy, ki zauna a wajenta, dan Allah aunty banda fada da jan warning, ki yi hakuri da ita ki kuma nusar da ita, bana son amaryar gidan nan ta fahimci komai, kin dai ga irin abinda suke yi ita da yan uwanta so suke yi a kula su, iya tsohuwa tace kar wanda ya kula su, ta fadawa matan anguwar nan kar ta ji kar ta gani, kin ga kuma sun ji gasucen aikace aikacen su suke yi, sun ce zasu yi safiya su je kasuwa siyan kayan miya gobe "

Mama ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" To shikenan Fatima, ama a nan zaki kwana? malan fa?"

Mama fateema ta yi gaba tana fadin" Na ce masa sai bayan sati biyu"

Mama ta zarro ido tana dariya ta ce" Kin isama, yarinya mu je dai in gama samun nutsuwa ki wuce ki je dakinki, zaki yi bayani ne na kusa fara maki irin na Hajiar Larabawa"

Haka suka shige sunna dan barkwancinsu


Mama fateema ta yi wajen baki ita kuwa Mama ta shige bayan ta yafito iya tsohuwa dan kar su nemeta su ga bata nan, ta sanar mata zata je ta rarashi y'ar dakin nata , iya kuwa tana dariya ta ce" Je ki rarasheta, ai na ga ta tsorata kamar ba da ita muke koyar surfen tsakar gida idan mai gida na nan kalarsa daban da wanda baya gida, sai kuka take rusawa yar ashata"

Mama ta kama baki kasa kasa ta ce" Iya, wai Anmyn ce take abin nan?"

Iya ta yi dariya ta ce" Ke dai hade min ta wajena tsaf mikata daki, sauran abubuwan ma ji da shi innar ya'yan Ya'u"

Murmushi Mama ta yi ta nufi cikin, a ranta tana ayana' o, gidan nan ba iya ina son jin me suke aikatawa kuma yanzu ina tsoron kar in juyowa kaina fitina, harda wani surfen tsakar gida na gaban mai gida? Allah na tuba ya'yan yanzu tafe suke da fitinu, Allah ya sa itama Anmyn ba tafiyarsu daya da Karimar ba , dan kuwa lamarin abin tsoro ne '

Dakin ta bude a lokacin da Khadija ta kwonce , kanta a saman cinyar Karima tana magana muryarta cen ciki ta ce" Ba zaku gane ba, Ni na san mutuwa zan yi, ashe har haka babanmu ya tsane mu?, me yasa ba zai bamu lafiya mu yi rayuwarmu bane a gidansa ? aure ai yi zamu yi in lokaci yayi ko? ama ace dole sai an yi mana auren hadi? an daukowa Karima wanda bai yi mata ba ta bijire Ni yanzu ba'a bani damar in ga wanda za'a banin Bama , Allah idan dai fitinar nan ta ki mutuwa Allah ka zabi daya ka dauka kawai, ko Ni din ko uban nawa dan ka fi kowa son'mu "

KARIMA ta dungure mata kai ta ce" Ke walahi in baki daina addu'ar nan ba zan ci ubanki!"

Da sauri Lubna ta ce" Ta sakamu gaba sai kuka take sakamu, kuma yanzu tana neman mu da fitina, Anmy salon mu taba lafiyarki jiki ya haye maki ko? ba laifi , dan so dama ai babanmu baya son'mu mun sani, ki daina kukan hakanan mana, kin san dai Mama zata tayamu yakarsa ko? zata tsaya mana, zamu kai makiyi kass tabass!"

Kan mama sai da ya fara sarawa, sun tsundumu a duniyar tashin hankali basu san ta jima a tsaye a kansu ba suke magangannun da suka san ba zata taba lamunce musu yi mata shi ba

Hankalinta yayi kololuwar tashi da jin furucin bakin yan ƴaƴanta

A hankali ta karasa cikinsu ta yi zaman da bata shirya ba tana cire hijabin dake jikinta dan tsabar shiga wani hali na matsuwar zuciya

"Innalilahi mama yaushe kila shigo?"
Lubna ta fada tana zabura zata matsa dan ta sani in dai Mama ta jiyo furucin bakinsu tabas dakan danyar kubewa zata musu a dakin nan ba ruwanta da amarya ko yayun amarya gaskiya

A zabure Anmy ta mike zaune tana buɗe idannuwanta ta ce" Ke dilla Mama kuma?".....
Ai kuwa sai gannin Maman ta yi a zaune tare da su, da sauri ta rika neman hijabinta ta ce" Mama, sannu da zuwa yaushe kika zo?, innalilahi Allah ga Anmy, Allah ka ji kaina ba dan na mutu ba..."



Mama dake kallonsu, murya a raunane sosai ta langwabar da kanta tana dubansu ta ce" waye yace muku baya son ku? waye yace muku zai muku zabin tumun dare?, kun san Allah a kusa kusan nan ban ga mai son yaya irin mahaifinku ba, kuma ba zai taba yi muku zabin tumun dare ba, ko waye yace muku ku je ku zauna da shi ku je, ina da yakinin sai kun yi masa godiya....."

Ta ajiye maganar tana dubansu, idannuwanta na cika da kwallah ta ce" Ku barshi da fadansa, da dukansa, bayan wannan me yake muku? ya tsare muku ci, sha, sutura, ya muku ginni mai kyau ya kilace ku, ya tsaya kan ilimin ku na addini da na boko, idan kana son gannin bacin ransa a tabo ku, me kuke nema da uba sama da haka?, Mahaifinku uba ne tsayaye , tsaurinsa ya samo asali daga irin yadda aka raine shi shima, yanzu haka kuke zama kunna zagin min shi?".........Sai kawai hawayen nan suka bale mata, saboda bata da baban firgici sama da wannan, ita fa tana girmama yadda yake tafe da ya'yansa, wasu furucin nasa ne ke daga mata hankali wa'inda take addu'ar ya daina a kan ya'yansa saboda rayuwa, ama ace ya'yan nan su zasu yiwa rashin mutunci har haka? fisabililahi me suka yi musu da zafi har haka?

(Uhum' Hajia mama kennan, ke dai Allah ya baki hakuri ama kam ai abubuwa kam mijinki na yi sai dai a yafe masa kawai🚶🏿‍♀️🚶🏿‍♀️🚶🏿‍♀️)




*ALLAH, KA SA CIKIN YAN KUNGIYAR BATI DA AKE FITARWA NOVEL DIN NAN A SAMU MASU SIYA YA RAB, AMEN AMEN AMEN KU TAYANI DA AMSAWA AMEN*
07/12/2024, 15:11 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da shida (26)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*


https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
👉0912 262 1080





LABARI



A tsorace du suka dubeta, dama kawunnansu a kasa tunda ta fara maganar, jin gargadar murya ya saka du suka dago a tsorace

Hannu Khadeeja ta ɗora a kai ta ce" Innalilahi, kuka kuma?"

Da sauri Lubna ta sauka kasa daf da kafar maman ta mika hannu tana janyo sauran, du suka sauko suka duka kawunnansu a ƙasa

Murya a raunane Lubna ta ce" Mama, kuka kuma dan Allah kar ki mana kuka mu fada fushin Ubangiji, ki yi hakuri ba zamu kuma ba"

A hankali Khadeeja ta sake dago idannuwanta ta dubi fuskar mama, zuciyarta ta shiga babalewa, a hankali ta mike ta fada jikin Maman muryarta na rawa sosai ta ce" Ko da wasa ba zamu so gannin hawayenki ba, bale da gaske, dan Allah ki yi hakuri, in sha Allah ba zamu kuma ba "

Mama ta lumshe idannuwanta tana yiwa Allah godiya da ya yi mata arzikin da idan ta nuna bacin ranta ko menene sun barshi kennan

A tausashe bayan ta zaunar da Khadeeja ta kuma zaunar da yan uwanta ta dube su ta ce" Ku gane, dole a yi muku fada, dole a dake ku idan ta kama, wannan shine baban gatan da zamu yi maku, saboda rayuwa babu kwaba, babu hannawa ai ba rayuwa bace"

KARIMA na duban Mama, tunaninta na rabuwa waje waje, ba zata manta ba du idan suka yi laifi aka musu duka da fada mahaifiyarta na fadin babu ubanda ta haifawa da za'a kashe mata, ta sha cewa idan ta dawo gidansu zata hanna mahaifinsu dukansu dan bai isa ya dakesu tana tsaye ba, takan ce na anfanin a saka yaro a gaba a yi ta zagi ana duka? me yasa za'a yi ta Dukansu? takan ce du mai dukan ya'yansa baya sonsa, gwara a kyale yaro da kansa zai gane in laifi yake yi ya daina, takan ce da ita mamansu itace ke ziga babansu ya dake su, a gabansu ta nuna ba haka ba, ama itace ke hada su

Mama ta ce" Ku sani, Ni da kuke tunanin wai zan yi muku yaki da shi ba abokin gabana bane, na fada muku ba abokin gabana bane, kuma ban fi karfin mijina ba, biyayya nake yi masa dan aljannata tana karkashin kaffafuwansa, Mahaifinku bashi da wata riba da zai ci dan kun lalace ko wani abin ya same ku, shine wanda zai fi kowa shiga tashin hankali idan wani abu ya same ku a rayuwa, mahaifinku shi ya fi kowa son gannin kun zama wani abu na alfahari a duniya, a mizanin da kuka kai kuwa kun isa aure, auren da za'a yi muku shine baban rufin asirinku , darajar ku, a gidan duniya dan ya samo muku mijin aure shine alkhairin da zai yi muku mafi girma a rayuwa......., ku sani walahi da ace Karima tunda farko ta nuna min bata son mijin da aka samo mata da ba'a samu matsalar da aka samu ba domin ko yayane zamu samu mafitar da ta dacewa damuwar , muna zama da shi, muna shawarar abinda ya dace da ku, ba daba bane shi da kuke gani kuma zai fi kowa son ganninku cikin farin ciki, kun fahimta?"

Su kawai suke ganewa, Karima gaba daya kwakwaluwarta ta cushe, Maman take kallo tana sauraron kalamanta, ta shiga cikin yannayin fashin baki da don lalle a yannayin Mama da kalaman Mama sai ta tono munafurcin da mahaifiyarta ke fadar tana yi musu a rayuwa, hakan ya gagara

A hankali Mama ta ce" Ku yi masa biyaya shine kawai abinda zaku yi dan ku birge shi, ku yi mana biyaya shine abinda Allah ya umarce ku da shi muddin ba abinda ya sabawa Allah muka zo muku da shi ba, yana da niyar aurar da kowace a wannan shekarar dan haka ku shirya, a wajena baku da wata mafaka da ta wuce mu yi masa biyaya, in sha Allah zamu ci riba baki daya kun fahimta? maza ku biyu da kuke sallah ku tashi ku dauro alwallah ku yi, ke kuwa Lubna ke da Karima ku gyara muku wajen kwonciya, bari in je in gyara muku abinda zaku ci in zo"

Mikewa mama ta yi ta

32 / 64