Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
mu'amalarta da mutane, kusan du motsin Anmy a tafin hannayensa yake
Tun tana karama ta samu farin jinni a anguwa saboda tsarin halitarta har ya zamo mutan anguwa kowa na cewa ya kama irin abin wasan nan da ake yiwa yara, sai da mahaifinta ya nuna baya so sai aka daina, ama masu burin hakan nada abinsu a rai lokaci suke jira
TALYAT ta fi sauran yan uwanta kulafurcin uba, sannu a hankali girmanta na karruwa tana janyewa daga shi sakamakon irin yadda idannuwanta ke gannin yadda yake tafe da mahaifiyarta , hakan ya sa lokaci daya karfin soyayar mahaifiyarta ya rinjayi komai ya tafi da komai, danma mahaifiyar Tata ke katse wasu abubuwan tabas da abin ya fi haka karfi......
yannayin TALYAT da yan magangannun dake kwacewa daga bakinta wasu lokutan ya sa mahaifiyarta saka mata ido sosai, dan kuwa ita da kanta ta san yarinyar na dauke da wani lamari mai girman gaske
Ajiyar zuciya Hajia ta sauke a nutse ta mike ta fice dan bin dakunnansu saboda ba zata iya barci ba in bata je ta yiwa kowane adu'a ba, su rai bakwai kennan yan matan, an yiwa daya aure ba zaunaniyar garin bace, kuma daya bayan daya kowa da dakinsa a bangaren yaran gidan, mazan ne ke ta cen bari daban falo ya raba tsakani domin suma zuwa yanzu du sun tasa sosai , danma girman mace da namiji ne da bambanci
Gidan Elhaji bangare hudu ne, nasa, na matansa mai dauke da part hudu wato koda hali zai bada ya jera su ya shirya, sai na yayansa wanda aka jera dakunna kamar na yan makaranta kowane da nasa da gadonsa da komai masha ALLAH
A lokacin da ta zo dakin Karima bata buga ba ta shige, dan tsai ta yi sakamakon kamar idannuwanta sun ga hasken waya
Hannunta ta kai ta kunna fitilar dakin tana sake zubawa Karima ido, wace ta yi wani irin kwonci da sauri ta kifu a saman cikinta, wato rub da ciki
A nutse ta karasa kusa da gadonta ta dan duka tana bin inda hannun Karimar yake, wato cikin sket dinta yake
A tausashe ta dan shafa gefen fuskarta a hankali ta ce" Karima, ke Karima"
Idannuwanta dake dan marmar ta bude tana kallon maman nasu ta yi kamar barci take yi
Hajia ta ce" Wannan wani irin kwonciya ne kika yi haka? kuma me yasa hannun ki ke cikin sket din ki? wace irin dabi'a ce haka?"
Hannun ta ciro tana juyar da kwonciyarta ta koma saman hannunta na dama tana sake dane filonta dan kar wayar da ta boye ta falasata, a hankali ta mayar da idannuwanta bayan ta ce" mama barci nake ji"
Tsai Hajia ta sake yi, kafin ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta yi mata adu'a sannan ta mike ta fice bayan ta kashe mata fitila
Wata irin ajiyar zuciya ta sauke ta diro daga saman gadon ta je ta saka kunnenta ta saurara har ta ji maman na kule bangaren nasu sannan ta koma ta dane saman gadonta ta zarro wayarta tana sake sakin ajiyar zuciya na tsoro, da yau an kama wayar nan bata san ko zata kwana da ranta ba
dariya ta yi bayan ta bude grup dinta da take posting din littafin da take rubutawa, tun posting din da ta musu yau a makaranta ne suke ta cmmnt, sai zuzuta bangaren da star din littafin suka hadu a matsayin innuwa daya suke yi, ta yi murmushi ta fito ta shiga msg din da aka yi mata a pc ta shiga karantawa, fita ta yi ta koma na wace ke neman shawarta na matsalar da mijinta ke fama da shi a harkar jima'i, gyara zama ta yi tana yi mata tambayoyi ita kuwa sai amsa take bata har fayyace mata take yi komai da komai ita kuma tamkar wace ta sani tana ta bata shawarar yadda zata kula da harkar nan tamkar wace ta san kan abin a gasken gaske, har sai da karfe biyun dare yayi sannan ta kashe sai langi take ta boye wayar ta kwonta barci, dan kuwa da an jima za'a tashe su karatun asubahi, idan suka yi sai sun yi sallar asubahi suke dawowa bangaren kuma su yi shirin zuwa makaranta wace suke da ta boko ko ta islamiyya.
Da asubah bayan Hajia ta tashe su, gaba daya sun tafi bangaren mahaifinsu, du kusan kawunnansu daya dan kuwa ba wani girman junna suka yi da yawa ba kowa da mamansa ne aure kusa da aure haihuwa a wata daya ko wata mai bima wata,
A bangaren nasa suke yin karatun sai ta koma dakinta ta shige wanka
Bayan ta fito ta shirya jikinta sosai ta dauki carbinta ta zauna tana ta ja, saboda ba sallah take yi ba abin barin da ta yi.
ta yi nisa a salatin Annabi kunnayenta suka ringa jiyo mata ihun yaran da kukansu
Gabanta ya yanke ya fadi, ta dago da sauri ta dubi agogon bangon dakinta, tana gannin har an dawo daga masallaci ta mike da sauri ta zura silifasss dinta a saman safarta ta fita ta nufi bangaren Elhaji
Tana shigowa filin karatun idannuwanta suka sauka a kansa, rike da dorina yana zane yaran,domin sun cure waje daya sai ihu suke da kuka yana zane su, gefe daya matarsa tsaye rike da litafinta tana kallonsu
Tana shigowa yaran da gudu suka nufeta sunna kuka da kiran Mama
Tangal tangal ta yi kamar zata kifa sai kuma ta tsaya kan kaffafuwanta ta saka idannuwanta cikin nasa a lokacin da ya daga bulalar ya nufe su suka cimuimuyeta sunna ihu masha ALLAH zaratan samari da yan mata har haka ama har yanzu bai daina daga musu bulala ya zane su ba
Rai bace yace" Bani su nan, kin ga baki da lafiya kar shafi ta shafe ki, bani yan iska na wulakanta musu fata"
A tsayen da take ta tausasa ainun ta ce" Ka yi hakuri tunda sun zo nan, sun tuba ka yafe musu ba zasu kuma ba"
" Karya kike usaina, karya kike , zasu sake, dan ubansu ba na fada musu ba idan wani yayi wani abu suka boye min gaba daya sai jikinsu ya fada musu ba? laifinsu ne saboda Khadija ba zata ringa abu kai sake ba , laifinsu ne su suke kyaleta tana yi, wai ace ambu mai tebur Ni zai kalla yace ya ga iri a gidana? ama Allah ya isa Ni da ambu safiya na yi zan kai shi wajen sarki ya mana tsakani dan iska kawai, ke kuwa khadija idan kika kuma zuwa hanyar da yake sai na cicira maki fata, du laifinki ne Usaina Ni kam aurenki tashin hankali kawai yake sakani, gwara in sauki in huta" Ya karashe rai bace yana harowa Hajia wace ta sake zubawa fuskarsa ido, hakama Khadija dake bayanta ta yi wani irin dakatawa kirjinta na dokawa ta dago tana duban mahaifinsu da duka kaf ya'yan nasa
A hankali Hajia ta ce" Daga wannan maganar sai kace gwara ka sakeni? koda ban ci arzikin zama na yau da gobe ba ai na ci na zama da yayanka!"
Amaryarsa ta tabe baki tana sakin murmushi, shi kuwa ya ninke bulalarsa cike da jin haushin ta hanna shi yiwa yaran nan dukan mutuwa yace" *YA'YA SU TASHI A TASHA* ba damuwarki bace, ko yayanki ne Ni wannan balakin?"
Yana gama fada ya nufi bangarensa amaryarsa ta yi yar dariya kasa kasa ta ce" wai shisshigi ba gindin zama, dadina da Elhaji wannan bata kai shi!"
Daga nan ta bi bayansa, ya rage mama da yaran gaba daya da jikinsu yayi mugun sanyi
A hankali take biye da su bayan ta tisa su a gaba har suka shiga baban falon su
Sunna shiga ta nufi dakinta da sauri ta shige, tana shiga ta saki kukan da ya danne mata zuciya
Ashe tana shiga Khadija ta bi bayanta, haka sauran sunna gannin haka suka rufa mata baya sai ji ta yi sun rungumeta sunna kukan summa
Dif ta dauke kukanta ta zuba musu ido, murya a raunane ta ce"
07/12/2024, 14:40 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*🇳🇪
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na huɗu (4)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
*META FORCE*
*menene meta force*
business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force
*shidai meta force crypto currency* ne
kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency
akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba
yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai
*TACTILE*
1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars
hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira
*Spillover*da*over flow*
wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu
to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*
*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja
LABARI
Dif ta dauke kukan nata ta zuba musu ido murya a raunane ta ce" Kai, me kuke yi haka? da girmanku? ku daina mana, Kai sidiku harda kai ko?"
Sidiku na kuka tamkar karamin yaro, domin har cikin zuciyarsa yake jin tausayin wannan baiwar Allah , ta same su da haƙoransu a bakinsu, ta karra runguma ya zamo a yanzu basu da wajen fakewa su ji sanyi sai a jikinta , a raunane ya ce" Mama dan Allah ki yi hakuri kin ji? in sha Allah baba ba zai sake sake ki ba, in kuwa ya sake ki walahi mu dukanmu bin ki zamu yi gidan Hajiar Larabawa mu yi zamanmu"
Murmushi ya hau kan lebenta, wannan shine salamarta, irin yadda suke shiga damuwa da damuwarta Duda sun girma, sun kuma san ba fa ita ta haife su ba ama kuma sunna matukar girmama lamarin ta tamkar yadda take girmama nasu, shi yasa lokuta da yawa take ji a ranta eh tana iya cin kashin nan saboda su
Salamarsu ta yi bayan ta nuna masu ba komai su je su shirya
Khadija ce a baya, har ta fara tafiya ta dakata ta juyo ta dawo ta duka tana kallon kaffafuwan mahaifiyarta, a hankali ta ce" Idan ya sake kin sai me Anmi?, ba yace mu tashi a tasha ba to mu tashin mana shi ya haife mu ai, sai mu zame masa balakin da ba zai iya ba, kuma umma tsohuwa tace Allah wadaran namijin dake wulakanta matarsa......."
"innalilahi ke Anmi, subahanallah ke a ina kika jiyo maganganu irin haka?" Mama ta katseta da karfi tana hannata ci gaba da magana dan har ga Allah sai da ta ji tsoro ya kamata
Ta ɗora da fadin" Wato ke bakinki bakya koya masa maganar da ta dace a yiwa baba ko karami da kuma kwabarsa ko? ina ruwanki da maganata da Babanku ne Ni? au abinda kike koyowa a gidan umma tsohuwar kennan? to shikenan na gode tashi ki tafi ama kar na kuma jinki a gidan umma tsohuwa tunda lamarin ya koma *BADAKALAR HARSHE*"
Kai ta sada tana jin irin yadda kirjinta ke zafi, a cen kasan zuciyarta take ayana' yaya za'a yi in yi aure? yaya za'a yi in auri namijin da zai min abinda Aba ke yiwa mahaifiyata in zauna? ta yaya? ama aba da mama dama cen sun tsani junna ko? yanzu Abdul karim yana iya yi min haka wata rana? to walahi idan ya min haka sai na zabga masa mari, sannan ya sake Ni, Ni ba zan zauna dan yayansa ba koda yana da su walahi!' A bayane kuwa sai tace" Ki yi hakuri mama, dan Allah ki yi hakuri ba zan kuma ba"
Hajia dake kallon yannayinta a tausashe ta ce" Zo nan"
Mikewa ta yi ta je ta zauna daf da ita sosai
Ta zuba mata ido, kalaman bakin Khadija tamkar ba na shekarunta ba, lamarin nan na bata tsoro lokuta da dama, harta girman jikinta ba na shekarunta bane haka kalaman bakinta, tana da zafi Khadija, tana da fada, shi yasa take son zama a gefenta dan ta ganar da ita baki da fari ta kuma tabatar mata rayuwar yau fa haka ta gada, koda Allah zai hadata da mai baudaden hali ta yi ibada da zuciya daya sai idan ya gagara ne zata dubeta, domin ita ta yiwa kanta alkawarin in sha Allah ba zata tafiyar da y'arta irin yadda Hajiar Larabawa ta tafiyar da ita ba, idan zai yiwu a yi, in ba zai yiwu ba kuwa a hakura ne saboda rai daya ne jal, daga bakin lokacin da ba zai anfani mai shi ba bashi da wani anfani.
A tausashe ta yi mata nasihar da ta saba yi mata sannan ta umarceta da ta je ta shirya zuwa makaranta kar su yi lati, idan direba ya fito kuma wasu basu fito ba ba zai yi jiran kowa ba tafiya zai yi hakan kuma na nufin wani tashin hankalin a wajen Elhaji.
Sai da Yaren suka tafi kaf dinsu sannan ta koma dakinta a nutse ta kwonta, sai a lokacin zafin magangannunsa suka karra kona mata zuciya, ta tashi ta yi zaune abin na tukarta
Firgit ta mike ta fito, tana daf da nufar hanyar da zata kaita inda yake ya shigo dauke da jakar kudinsa , dama dakinta zai je ya karra gannin jikinta sannan ya wuce, bayansa kuwa jelar tasa ke biye da shi
Tsayawa yayi yana kallon yannayinta , dan kuwa fuskarta a hade take sosai ta dube shi cikin idoda tarin balaki ta ce" Kana tunanin zaune da nake a gidanka saboda wani abin ne? soyaya ko kudin da kake gannin ka take su zaka take wanda ka ga dama a lokacin da ka ga dama? Kana tunanin idan ka sakeni ba zan rayu ba? a yanzu da Ni nawa sawun ya kai inda ba zan moru ba ai ba namiji ke gabana ba ka san da haka, a haka har ake mangarina a waje? a haka har ake zagina da kalaman na malakeka kana ta auri saki kafina, haka kuma bayana sai aurowa kake yi kana saki Ni ce ka ki saki dan na malakeka? Allah ka jarabi du wace ke burin shigowa gidan nan ta zo ta maye gurbina, ina kuma dakon ranar da zaka sakeni, dan walahi na saku har gaban abada! "
Ido ya dan zarro yana kallonta kafin yace" to yanzu kuma me aka yi zaki min rashin kunya? sai kace kamar wace lafiyarki kalau walahi, ke da baki da lafiya kike fada kina dagawa aljanarki murya me aka yi ne gimbiya waye ya bata maki rai kuma?"
Takaici ya shake mata wuya, so ta yi ya maimaita maganarsa ta dazu wa bilahilazi ta nuna masa itama danyan kai ce, rai bace ta ce" Ko me kake tunani a kai ka maida hankali, akoy ranar kin dilaci, idan kana abinka kuma ka guji idannuwan yaran ka dan ina mai tabbatar maka idan girmanka da mutuncinka ya idasa zubewa a idannuwansu ka kade,, Wadinnan din da kake gannin ba komai bane sunne gatanka, walahi sunne gatanka dan ko Ni ban jin zan iya da kayan tsufa! idan kuwa ka yi wasa su zasu fitineka su fitini duniyar ka, babu arzikin da ya kai maka su a duniya, ka dage ka kakarya su daya bayan daya , anan zaka gane su ba gado bane da za'a kawo kafinta ya gyara ba, a nan kuma zaka gane madara suke idan fa suka zube walahi ba zasu kwasu da dadi ba, igiyar aurena kuma in yau kake son tsinkewa ka bani dalilin