Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
sannan ta yi kiran Aba ta sanar masa, domin nakudar bayan sallar asubahi ta sakota gaba, ta rufe bakinta Allah ya taimaketa har ya bar gidan bata nuna ba, sai kusan karfe daya na rana ta nuna , saima da ta kama hanya ta sanarwar mama fateema suka hade a asibitin.....komai ya kankama ta samu lafiya, harma ta yi awa hudu bisa kulawar likitoci sannan suka dawo gida ne ta sanar masa a lokacin kuwa yama ta yi sun baza tabarmu a kofar shago sunna tattaunawa, aba na sauraron baba Hamza dake fadan ya dawo da matarsa sintirinta ita da iyayenta ya ishe shi hakanan, Gimbiya da kanta sau uku tana masa zancen, idan ma horo ne ya isa hakanan, shi kuwa ya wani dauke kai ya bashi keya yana kada kafa, a lokacin al Walid ya karaso majalisar ya zauna shima saboda har sun saba da zaman yamar nan, in dai sunna gari to kuwa da shi ake yinsa shima, shine kira ya shigo ya kuwa daga yana murmushi ya ce" Gimbiya sarautar mata, Gimbiya mai Ni , ya aka yi? Yanzu ubana ke batun in maki kishiya danma na bijire masa.....ya aka yi ko in zo?"
AL'WALED ya sunne kai kawai yana murmushi a lokacin da kukan jariri ya karade wajen saboda handsfree da ya maka
Ido ya zarro ya ciro wayar yana dubawa ya ce" Ke yanzu asibitin kika je bayan su da kansu sun ce an baki juyin haihuwa? Haba Gimbiya wai menenene Ni kike so mu yi balaki iyeah? Kina jan kafa da kyar kika je amsar haihuwar wata idan ta daka maki kafa a rumbu kuma ace min me????"
Mama ta yi murmushi a tausashe ta ce" Ka dai ga kawai idan ka tashi sai ka zo gida, na sauka fa"
Baba Hamza ya dan zarro ido, hakama Aba, AL'WALED kuwa ya dago da sauri , dan kuwa bayanin cikin Gimbiya ai aba ya gama sanar da suruki sala sala
Aba ya ce" Daga ina kika sauko din? Innalilahi kar dai ace haihuwa kika yi Gimbiya? Na shiga uku wannan kukan ai na gardi ne, wai Gimbiya kin haihu? Namiji????"
Mama fateema na dariya ta karbi wayar saboda mama sai murmushi kawai take yi abinta ta karra a kunne ta ce"
😫 Yana mana bankwana ka dai yafe mana😁😁😁😁 farkon gannin idona😍😍😍😍
54.......
07/12/2024, 17:39 - samiraharounayacouba: Ta ce" Wallahi yaya ta sauka gamu a gida, gayanan boy yana ta tsala kuka wai wanka Hajiya iya ke masa"
Aba ya yi wuuuuuu ya zabura yana fadin" La'ila ha ilalahu, kai Gimbiya an yi yar bakin ciki yanzu bata bari na Kaita ba?, hahaha Baba Hamza ta sama min? Allah ya miki albarka Gimbiya kin haifo min ubana, ganinan zuwa gidan dama na san abinda ke cikin nan dan ubansa namiji ne"
Baba Hamza baki har kunne faman fadin alhamdulilah yake yi shima yana kokarin tashi, AL'WALED kuma sai murmushi yake yi yana kallon su
Baba Hamza ya ce" Mun tafi sai yadda ta yiwu kuma"
AL'WALED yayi dariya yana girgiza kai ya furta" Allah ya raya mana, zan zo in dauke ka da dare ko?"
Baba Hamza ya ce" In sha Allah, bari in je in ga takwara, ka sanar da yan gidan "
Shi dai yana kallo , ba ya Hanna aba tuka su ba yau aba ya fitar masa da lasisin tukinsa ya masa karatu sala sala, sai kawai ya bi su da adu'a ya ci gaba da jiran sallar magariba, yana burin ya shige ya sanar da tasa mai tsohuwar ajiyar itama dan ya ga murnarta, a yanzu take da wata bakwai Ama Tata ajiyar ma ta turo sosai ana nan ana ja sai fatan rabuwa lafiya, yanzu haka sunna nan ita da y'ar sunna soye soyen yama ......, wani murmushin ya saki, idan ya tuna irin yadda yanzu litle ke farin cikin kasancewar Khadeeja mamanta farin ciki da kwanciyar hankali ke mamaye kirjinsa, ko watan da ya wuce sai da ta kaita wajen kakarta ta wajen uwa ta sanar masa da sunna callll, sannan ta nuna normal ne ta yi haka a matsayinta na uwa a wajen kurma, tana da yancin daukan décision din da ta dace da y'arta in har ba zata cutar da ita ba, sannan ta nuna cewa kwana biyu zata yi, zata je ta dauko abinta, sai kawai ya bita da kallo irin yadda ta wani daure fuska ta dauke kai........Anmy....... Khadeeja.......kwarai yana tare da mace daya tamkar dubu.................. Allah ya karra lafiya .
Bayan sallar magariba ya shigar musu da wannan abin farin cikin wanda ya sa Khadeeja ta nemi daka tsalle abinta na murna sai da mama khadeeja ta yi gaggawar rikota tana dariya ta ce" ki rufa min asiri takwara ke yanzu ai idan murna ta wuce ta dariya daga zaune a yi hakuri a yafe maki ita"
Hajiya Inna me zata yi banda dariya a hankali tana dan motsa kaffafuwanta da sandunnanta biyu, dama motsin ne suke yi na dole wanda idan ba'a yi ba Anmy bata bata lafiya shi yasa itama da ta ga lokacin a motsa jikin yayi sai ta yi iya yinta su shiga motsawar kuma cikin ikon Allah kullum karra gannin sauki ake yi
AL'WALED ya zauna saman kujera yana murmushi , kurma ta zauna daf da shi tana sake tambayar a ina ne wai aka samu babyn? , yana murmushi ya kwatanta mata cewar ai kakarta mai kiranta kishiyale ce ta kawo baby....., ai kuwa yarinya ta wuce bangarensu tuni bayan ta sanar cewa ita kam zata hada kayanta sai gidan kakan kurma
Al' Walid ya mike yana fadin " Anmyn litle dauko hijabinki mu je mu dauko baba sannan mu gano baby, idan ya so kwa je ku wuni gobe in sha Allah"
Sosai kurma ta ɗora musu rigimar ita fa sai ta je da kaya, da kyar suka mata wayo ta dauki kala biyu suka kama hanyar gidan Aba
Da suka karaso sun samu samarin gidan a kofar gida sunna firarsu da dariya sama sama
Saukowar kurma ya sa habubakar sakin murmushi ya mika mata hannu yana fadin" Ga y'ar Habu ta iso, zo nan yarinyana, "
Muhammad yayi dariya ya ce" wallahi Sadik sai son girman tsiya, idan ya ga amu ya ringa wani budewa shi mai y'a, Ni so nake yi a bamu ita, ka ga fa yanzu gidan nan ba mace itama mama maimakun ta karro mana wace zata maye gurbin su Anmy sai ta karro mana gardi , mu KENNAN babu mai mana sangarta a gida du yah baba ya kawar da su? Allah ni ina son girl"
Sidik ya tabe baki ya mike yana rike da hannun litle dake faman ihun wai an kawo baby? Ita fa ta kauro gidan nan tunda an kawo baby, ya ce" ai sai ka yi, abinda auren kawai dai sunnan an kai su ne, ita wannan bini bini an kawota, ita Karima dama ta auri mijin tace dan iskanci lokacin da ta yi niya zai kawota ta ga babarta, ita Ummi ai ta fi uban kowa kaniya saboda rainon cikin a nan take yi , Lubna kanta in ba dan aba ya bi su da gudu ba kai ka san da kullum tana kan hanyar Nijar to Nijeriya, shine zaka ce basa nan? Ni ai kallonsu nake yi ina shiryawa saboda idan na yi aure babu y'ar da zata mayar da Ni mijin Hajiya!"
Wuce su Khadeeja ta yi da gaggawa ta fara shigewa falon zata wuce ciki tana tura tulun cikinta
Aba ya kalli baba Hamza da sauri ya kalli inda ta wuce din, kasa kasa ya ce" Ji y'ar nan yadda take tafe da kadarar mutane, ya dace in ci ubanta yau"
Baba Hamza ya girgiza masa kai yana sake rungume jariri ya ce" ka ga, wallahi ka kiyayi matar AL'WALED, idan ya kyale mu furfurar karya ke habata, ka ga murmushin nan da yake yi? Na munafurci ne kadan muka taba masa mata zai kai ya rufe a yi abinda za'a yi, ba kunya gare shi ba fa a kan matarsa, kana ganni ai idonka na gane maka, sai ka yi aniya ka taba masa mata harda ciki ka ga aiki da cikawa "
Aba yayi tsuru yana kallonsa lokacin ne kuma AL'WALED ya karaso tare da su Sadik da ya dakatar suka gaisa da kurma wace ta nufi wajen baba Hamza direct tana buɗe babyn farin ciki kamar ta yi me
Aba ya gyada kai kasa kasa ya ce" Ni abinda ke bani mamaki da suke kai mace gari wai su yi jiranta, sai kace wace ta shanyeka? Ta isama yo Ni an isa ma???"
AL'WALED yayi kiskirim yana sauraron su saboda irin yadda ake magana kasa kasa ya tabbata hali ake yi, wato gulmarsa
Baba Hamza ya ce" Kai ka ji tsoron Allah, kai da kake kwana a kofar asibiti fa an gaya maka ban gane ka ba? Ko so kake yi a yi a bayyane kowa ya ji?"
Aba ya zarro ido harda zabura yana kallon baba Hamza kafin ya dauke kai yana mikewa ya kama hannun kurma ya dawo da ita daf da shi yana fadin" Zo, a nan ke kadai ce ta Allah, meye a jakar in gani???"
AL'WALED na murmushi ya ce" Wai tufafi ta kwaso, tana jin ance an samu karuwar nan ta rikice mana da kyar ta yarda aka dauko biyu, banma san ta inda zan yi mata wayo mu juya ba"
Aba ya ce" Elhaji karami ku juya ina? Inace sun shiga baban hutu kuma dama ba yau ba nake ce maka tunda ka kwace uwata ka bani jikata mana? In ba'a bani ita gaba daya ba a bani na dan lokaci mana dan Allah dan Annabi iyeah? Ni menenene ya sa ake son daga min hankali ne???"
AL'WALED ya dan zarro ido sai kuma ya kalli baba Hamza wanda ya dage kafadu yana sake taba hancin Hamza karami
AL'WALED ya yi murmushi ya ce" Shikenan Aba in Allah ya yarda gobe sai maman nata ta zo mata da wasu kayan sai ta yi hutu "
Aba ya saki murmushi ya ce" Allah dai ya maka albarka ya karra daukaka da dukiya masu yawa yadda zaka kara aure ka yi ta zubo min su, yauwa batun zuwa ka ga ka iya ce mata a'a fa, kar a fi karfin ka a gidanka, idan tace abu kace ke an ki ba'a yi gidana ne ko na waye, kana iya tsayawa ka hade fuska ka ce sai ka zane mutun ka zane banza, ko kuwa ka samu ka zane din ai Anmy kanwarka ce ka girme ta idan ka zaneta babu abinda za'a yi human right din sun ci ubansu "
Habubakar ya furta" La'ila ha ilalahu " yana zarro ido hadi da kame baki
Aba ya Dube shi ya ce" Kaima ka ci ubanka , to me kake nufi? Ba za'a ɗora mutun a hanyar da ta dace ba? Kai ji karma ku turon matanku gidan nan ku rike abinku ranar sunnaa hade , duda Gimbiya tace ba'a taro ama sai na yi tunda ba shege bane , ita ke kunya to Ni Allah na tuba ai babu wanda zai ce min ya haka wai wani ta aurar da su anmy ace tana yi sunna yi? To sai me? In dai da lafiya badi ma in sha Allah ina fatan Gimbiya ta haihu ko baba??"
Da AL'WALED din, da Sadik din sai suka mike a tare har sunna kallon junna kafin su kama hanyar waje, Aba ya kame haba ya ce" Ni suka bari ina zuba kamar mai sakin danyan magana?"
Baba Hamza ya Dube shi da harare ya ce" Kai dai Allah ya shirye ka, baka jin magana sam, wato idan kana tsoron dakar masa mata kar a rufe ka shine zaka koya masa ya daka shi ko? Ai shima rufe shin za'a yi, wato kai kana lalaba taka a daki a waje kana hargagin karya kake so a ringa musu? Ba ruwana du Wanda ya janyo rigimarsa Ni yanzu sai dai in ce Allah ya kyauta dan in ya yarda ya daga mata hankali ta masa fushi ba zan bata hakuri ba, Ni yanzu abinda ya fi damuna ma takwara, kar aje ka ringa masa ihu ka gigita shi wallahi "
Aba ya Dube su daga shi har takwran kafin ya mike yana kama hannun litle ya ce" Mu je, tashi mu yi tafiyarmu mu barsu da bakin halinsu, in ba dan ba dan ba ai da sai ka je da takwaran naka ku karata, matsalar shayarwa ne kawai zai hanna, Ama gardi kam ai ya fado da kafar dama ubansa zai ci wallahi!"
Yayi tafiyarsa abinda, baba Hamza kuwa na dariya kawai yana girgiza kai
A dakin mama kuwa tunda yan matan suka hade ta hade fuska tana tambayar me suka zo yi yau kuma? Sai suka ki cewa komai saboda lamarin mama sai ita, karshema sai ta ja warning tana fadin" Bana son shashanci har an ce mun saka muku ido kowani motsi kunna gida, kar na kuma gannin kaffafuwanku a gidan nan sai na neme ku, kun dai ji na fada muku"
Karima ta shagwabe fuska ta ce" Mama Ama ai yanzu dalili ne ko mama, kuma ai dole ma zo mu yi shirye shiryen biki da ranar bikin"
Mama ta sakar mata harare ta ce" Karima ki kiyayeni ban saka ku ba, Ni babu bikin da zan yi , ku tashi maza ku je ku yi abinda ya dace dare na sake yi kun wani zo kun sakani a gaba!"
Ai kuwa bata wani sauraresu ba ta Kore su sai fada take yi da famar fadin Bari babansu ya shigo babu mai mata taron sunna haba shekarunta nawa yanzu? Kawai ya shafa fatiharsa a masallaci a rabar da naman wa makota shikenan , baba kuwa Allah ya raya .
Ba shiri kowace ta bi mijinta suka juya gida
Sunna zuwa ta nufi bangarenta ta kimtsa kamar yadda ta saba, domin kokari take yi sosai da sosai , sam bata bari ta jibge ba, hakan ya sa take samun dadin jikinta sosai da sosai
Tana cikin saka turaran wuta a dakinsa ya shigo yana murmushi da wayarsa ya hasko mata Aunty SHAREEFA da ta yi masa VIDIO call
Ai kuwa ta gyara rigar rijinta da kyau ta zauna tana amsa kiran , shi kuwa ya zauna daf da ita yana kallon yadda suke fira har suka gama suka yi salama sannan ya kashe kiran ya mikar da ita ya nufi wajen bed da ita yana kokarin cire mata rigar nan ya ce" Mu je in murza miki kaffafuwanki kin gaji sosai maman litle"
Khadeeja ta yi murmushi tana rike hannunsa ta ce" Fisabililahi Ni nace na gaji?"
AL'WALED ya sake riƙe mata hannun ya karra nufar gadon da ita yana murmushi shima ya sabule rigar
Khadeeja da mamakinsa ta ce" wai Aban litle da wannan tulun cikin me yake jan ra'ayinka????"
AL'WALED ya dubeta yana jin dokin jikinsa na sake murdewa a tausashe ya shiga neman rikitata kasa kasa ya ce" Kin fi kyau a haka....., kuma Allah ya taimakeni mai hannani ihu ta je wajen kakanta..... Anmy......... Zo mu bashi madara ko ya karra karfi yayi ya fito ko?????"
Murmushi kawai ta yi, du irin yadda cikinta ya girma haka take jurewa ta bashi hadin kai, danma tunda cikin ya kai haka shi da kansa sai yake daga mata kafa, Ama fa idan ya tara abin baya ji baya gani sai ya amayar, bale yau da litle ta tafi ai ita ta kawowa aiki dan kuwa babanta sai ya baje kolinsa a duk inda hali ya bada.
Washe gari bayan sun karya tana zaune kaffafuwanta saman cinyarsa yana amsa waya da abokinsa da zai shigo garin kan harkar kasuwancinsa ita kuwa sunna faman chating ta whatsup da yan uwanta har ya gama wayar ya ajiye itama ta ajiye tana dubansa saboda maganar da ya fara
A nutse ya ce" Bab a ina kike son haihuwa? Wace kasa zamu je?"
Khadeeja ta Dube shi da dan mamaki ta ce" Maleek khalbi, wace kasa zamu je kuwa da ta wuce nan?"
Ya ɗan sake duban ta da kulawa ya ce" Bakya so mu je wani wajen?"
Khadeeja ta girgiza kai a hankali ta ce" Na fi so a nan, kusa da su Hajiya , hankalina zai fi kwonciya, ka ga daga baya sai mu tafi idan da rai da lafiya"
Murmushi kawai yayi yana ji a ransa anya a yanzu zai iya yin wata tafiyar kuwa? Baya jin in har zai iya yi, saboda ba zai taba lamunta nakuda ta taso mata baya kusa ba, yana addu'a ba dare ba rana kar Allah ya sake nuna masa ranar da ya nuna masa a kan maman litle, ranar da ya kawo matarsa haihuwa ta haihu aka bashi jaririyar a hannunsa mahaifiyarta kuwa aka lulubeta aka yi mutuware da ita, tabasss ya shiga halin tashin hankali mai wuyar fasara, yana fatan Allah ya jikanta sannan ya sauke duk wata mai junna biyu lafiya.
Sannu a hankali ta ci gaba da rainon cikinta, a gidan aba kuwa sai da yayi taronsa Ama ba mai yawan nan ba, dan kuwa ita mama bata yi Bama sai yan anguwa da suka ringa lekowa ana sake yi mata Barka da ban gajiya har aka gama aka watse, sannan ta Hanna su Khadeeja zuwa sai zamansu suka yi, ita kunya take ji, ya'yan nan kaf dinsu wata kama ce da su kawai sai su zo su jeru? A'a Allah ya kiyaye ba zata kwashi abin kunyar nan ba gaskiya
Kwonci tashi asarar mai rai, a lokacin da cikin Khadeeja ya kai haihuwa ya zamo hatta baba Hamza baya wuni bai lekota ba, bini bini zaka ga wani ya leko yace dan a gaisa ne, ita abin har dariya yake bata, irin kulawar kuwa da mijinta ke bata ya fi komai kwontar mata da hankali da saka mata nutsuwa , ya zamo bata wani fargaban haihuwar , ta gama fawalawa Allah komai tana jiran lokaci
Yau asabar, sun tashi da karfe daya na rana da nufin sauka kasa dan su ci abinci, a lokacin da ta zo saukowa daga gadon bayanta ya rike mata, wata irin rikewar da bata taba jin irinta ba kafin ya sakar mata tauna mai zafin gaske da radadi
Du yadda ta gwanance wajen boye masa nakudar