Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   29 / 64

84K to 87K   out of 190.8K words

NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da huΙ—u (24)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*


https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ
πŸ‘‰0912 262 1080





LABARI



Tunda ta taho kallo daya ya yi mata ya dauke dubansa ya samu kansa da waigawa ta wajen madubin motar yana hangen mutanen dake wajen mai gadin, domin mai gadin yaro ne , saurayi ne kuma irin samarin nan na zamani yan shan kida, hakan ya sa koda yaushe yana tare da abokansa ne sunna shan kade kadensu daga cikin gidan

Idannuwansa da suke kara rinewar bacin rai ya bude ya dora a kanta a lokacin da ta bude motar ta shigo ta karyar da murya sosai ta furta" Bab....."


Ido ya dan zubawa fuskarta yana tunani mai nisan gaske......., haka dabi'unta suke fa, kuma ba ruwanta a gaban kowa tana iya fitowa haka ba tare da ta riko wani abin da zai rufe jikinta ba
Da ace Mufeeda da dan abi yarima a sha kida take tare ya tabbata da shafa fatihar kawai yi ne za'a yi saboda kar y'an ya'ya su zo a haka, domin da ace zai nuna wani abu yake so a wajenta bashi zata yi komai girman abin....., ita bata san cewa a yanzu fitar da tsiraici ya zama kauyanci ba? ita bata san cewa sunnansa ke yawo a tare da ita bane? , ita bata san cewa mace yake so mai daraja wace zata daukaka darajarsa , ta mutunta shi, ta girmama shi, ta bashi kula, ta kare mutuncinsa ta so ahalinsa ta so kurma, ta ba kurma tarbiya, ta ba kurma kula, ta zamo uwa abar koyi na dabi'u da dukkan wani abun alkhairi na kurma ba? mace yake so wace zai huce radadin shekarun da ya rasa matarsa, mace yake so wace zasu yi soyaya cikin nutsuwa da kwonciyar hankali, shi yasa ya yi hakuri har ya yarda da soyayar da take yi masa kafin a ya ji a ransa yana iya aurenta, sai dai gashi wata magana ta fito mai girman gaske, kuma ga wata fitina da yake son ganewa a bayane a idannuwansa a kan lamarin ta, dan a baya bayan nan da kuma jiya sai yake gannin wasu dabi'u daban da wa'inda yake tunanin nata ne ita Mufeeda.

Wayarsa ya ajiye ya dan sake kallonta a nutse ya ce" Kin yi sallah ma kuwa?"

ido ta dan zarro , sai kuma ta dan kikifta ido, 'Sallah kuma? wace ma wai tukunan? Ni ai tun ta jiya da na yi ban yi ba, to raina a bacen ina zan iya yin sallah' Ta ringa anbatar magangannun nan a cikin zuciyarta

A bayane kuwa sai ta ce" Eh na yi, da na yi ne na kwonta"

"Ok, je ki sako hijab ki dawo mu yi magana" Ya fada ya sake dauke kansa a kanta

Bayan ta yi gajartacen tunani a kan ta je ko kar ta je ta yanke shawarar kira a miko mata, sai kawai ta yi kiran kanwarta ta ce" Baby ki dauko min wani abin da zan rufe jikina, da turare" Domin ita da kanta a yanzu da ta shigo motarsa kanshin turaren motar da na jikinsa sun saka ta ji kunyar nata yannayin, dan bata kanshin turare gaskiya, hasalima jikinta irin jikin nan ne da in dai ta yarda ta dauki dan lokaci bata saka turare ba take fara wari, haka jikinta yake, gashi yau wankan nema bata yi ba fa, tana cikin gadonta ne a nanade idanma ta ji hamatarta na son damunta sai kawai ta sa bargon ta goge jikin nata da kyau dan bata yi niyar yin wanka da wuri ba, so ta yi sai bayan magariba ta yi wanka ta shirya ta koma gidan , ta tabbata zuwa lokacin baba Hamza ya masa magana ya sauko, sai gashi ya zo

Ido kawai ya zuba mata, a nan kusan motar ta saka abayar da kanwar ta kawo mata, sannan ta yiwa jikinta wanka da turare ta bude motar ta dawo ta saka shi gaba, kanwar Tata kuwa ko gaisar da shi bata yi ba ta koma, dama haka suke yan uwanta basu iya gannin mutun su gaishe shi ba ko waye shi, idan ka ga sun yi maka magana wata bukatar su ce ta kawo su.

"Bab, ya na ga kamar ranka a bace ne? me yake faruwa ne?" Ta fada tana sake dubansa da kyau

Dubansa ya sake saukewa a kan fuskarsa da kyar ya iya ba kansa hakuri ya jure sosai yana kallonta ya ce" Me ya sa bakya jin magana? Sau nawa zan yi maki maganar suturce jikinki ne?"

A hankali ta ce" Bab na ga a cikin gida ne, kuma tare da kai ne?"

Da haushin da yake ta rikewa baya son ta ga yannayinsa idan ransa a bace ya dubeta ya ce" Dan Allah ki yi shiru, idan har kin san maganar da zaki fadi bata da wani tsari gwara ki yi shiru, kina ganin a gida ne a gidan wadincen muharamanki ne? ko Ni muharaminki ne?"

Hankalinta ne ya fara tashi dan irin yadda ta fuskanci ransa a bace yake sosai

A hankali ta ce" To ka yi hakuri"

Ya dauke kansa yana murza gaban goshinsa sannan ya sake dubanta ya ce" Mufeeda, zaki iya fitowa ki fada min abinda yake faruwa tsakanin ki da dangina?"

Gabanta sai da ya fadi, ta yi tsuru tsuru tana kallonsa, hankalinta ya yi kololuwar tashi, cikin inda inda ta ce" Me suka ce na yi kuma?"


Ya tsareta da kallon da ya sa ta sada nata idannuwan, domin du iya shegenta ta sani bata kawo masa garaje ko a yannayin dadi bale a irin wannan yannayin da ransa ke bace

A nutse ya ce" Sai sun fada min wani abin zan tambayeki? kamar wasu abubuwa na rashin girmamawa nake gani a tsakani, wa'inda ba zan so ace haka din ne ba!"

Mufeeda ta girgiza kai da sauri ta ce" Ni dai bayan wanda suka fada jiya ba komai, shima kuma dan sunna zagina ne nake yi musu haka dan kar in ringa kyale su su cuta min, dan Allah ka yi hakuri"

Idannuwansa ya dauke a kanta ya zuba kan sitiyarin motar, ya kasa gane daga ina wata babbar baraka ta fito wace baba Hamza ya ki sanar masa ya biyo ta wannan hanyar , wato yi masa aure da yarinya yar kankanuwa wace sam bai hangi haka a rayuwarsa ba, Duda ya nuna bayan auren da dan lokaci za'a yi na Mufeedan, wace yake kyautata zaton zata iya rainon kurma, saboda idan sun koma gidansu ba zai iya barin kurma a nan ba, idan har yana da rabon samun wasu ya'yan a duniya zai so ace su tashi tsintsiya madaurinki daya su da kurma, ba wai kurma kadai ba harta Hajia inna ba barinta zai yi ba, ba dan ya raina abinda ake yi mata a nan ba, no, yana sonta daf da shi, yana son ganninta kusa da shi


Idannuwansa ya lumshe ya Kwontar da bayansa a jikin motar a hankali ya ce" Mufeeda, ban san abinda yake faruwa ba, ban san me ya faru ba, abinda na sani shine shi baba baya yanke hukunci cikin duhu, kuma a duk sanda zai yanke hukunci yana yi ne cikin kiyayewa da kare hakkin kowa, yana cewa ne yana tsoron tsayuwar sa a gaban Allah, sannan yana tsoron cutar da d'an wani ko dan kar a cuci nasa.........., You see wannan abin yana iya sakani a wani hali na bacin rai da batawar tsarin rayuwa, becaus Ni da na yarda zan yi da ke saboda na yarda da soyayarki, na kuma yarda zaki rike min litle da Hajia ................"

Ya ajiye maganar a hankali, ita kuwa gaba daya hankalinta a kansa, har zuwa maganarsa ta karshe, sai ya zamo farko farkon da ta fara fahimta kamar baya cikin nutsuwarsa ne ya shafe ta shiga tunani a zuciyarta kamar haka' Hum, Ni jaka ko? haka kawai in shafe shekarun ina jiran babar rana irin wannan, yanzu lokaci yayi ka hadani da wace zan ringa ruri a cikin gida ina ihu ina rubuce rubuce da kwatance kafin ta gane abinda nake son fada mata da kuma dangin yawu gidan zarnin fitsari da karnin tsufa? Allah ya sawaka zaka dawo hayacinka ne idan na shafe su a duniyar mu, ita da kanta tsohuwar nan ai dan ba kasar turawa bane da tuni sun maka mata allurar da zata dauke numfashinta dan tarin kauna da su barta a wannan yannayin, bale kurmar nan ai kaita zasu yi makarantar kwana ta kurame cen su karata, Ni kai nake so ba yan banzan danginka ba gaskiya, ina!"

AL'WALID ya dube ta ya ga kallonsa dai take yi bata ce komai bayan ya dace ace ta furta wani abin ko menene

A hankali ya ce" baki da abin cewa?"

Mufeeda ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Bab, ka daina fushin nan, ka ga ko a gida idan ka ga na yi fada an tabani ne, kuma su sun yi aiki da gannin Hajia zainab baba ce ko me ta fada maka zaka yarda, shine ta zo ta fada maka, kula Allah yana gani da ce basu tabani ba ba zan taba biye musu ba, ka yi hakuri ka ji?"

Kallonta kawai yake yi, yana mamakin wani abu a cen kasan zuciyarsa, irin yadda take nunin Hajiar ma shari ta yi mata ko menene?

Rasa abin cewa ya yi kawai ya dauke kansa ya ce" Ok, kina iya tafiya"

Dubansa ta yi da sauri tana fadin " Bab in tafi kuma? bamu gama firar ba fa"

Ya juyo zai bata amsa aka dan kwonkwasa gefen da take zaune

Zuge glasss din motar ta yi tana kallon kanwarta, zata tambayeta lafiya? kanwar ta bata waya tana fadin" Dady ne"

Amsa ta yi ta karra a kunnenta ta ce" Hello dad"

Mahaifinta bai wani tsaya sun yi doguwar magana ba ya ce" Mofi kina jina?, na yi kiran direbobinku da masu tsaron ku, zaku taso yanzu yanzu ku kwana a kwani sai ku karaso Niamey gobe"

Da mamaki ta dubi wayar ta mayar kunnenta ta ce" Dady yanzu fa ka ce? to yaya za'a yi in koma yanzu bayan shi yana garin bai tafi ba fa, lafiya dai ko?"

Uban ya ce" Shi din ubanki ne? nace yanzu yanzu zaku taso kar ki yarda ki bata min rai kin ji na fada maki!"

Mahaifiyarta ce ta amshi wayar da sauri tana fadin" Hello Mofi ? ke me yasa kike da gardama ne? ance ku taso yau yau kina neman wata maganar? ku taso akace in kun zo ko menene ai kya ji ko?"

Rai bace ta ce" Momy, wai wani irin mu taso yau? yaya zan cewa bab yau zan koma? kin san ai ban taba barinsa shi kadai a garin nan ba ko? haba dan Allah ko meye ai sai a fada min a wayar ko? bana kin akoy abinda zai sa ku tasoni haka tunda gaki kina magana da ranki haka shima dady ko?"

Rai bace uwar ta ce" Ok, ya maki kyau, ke ba bakya jin magana ba? ya yi maki kyau ki zauna din du abinda ya biyo baya ke kika gano!" Kitttt ta katse kiran tana fadin" Walahi yarinyar nan sam bata da hankali, ban san abinda ke cikin kwakwaluwarta ba, ta san dai idan akace ta taso yanzu yanzu ba banza ba ko?"

Elhaji Maiga ya dubeta ya ce" Me tace? ba zasu taso ba ko?"

Hajia maimuna ta ce" Ka san ai ba zasu taso ba, ka dan halinta ka kyaleta idan dai har maganar auren nan da gaske ne in aka daura sai ta tataro ta dawo, ba yau ba nake fada maka ya dace yarinyar nan ta koyi kama kanta ta iya kama mutuncin kanta, ka nuna min babu abinda y'arka zata aikata ka yarda da ita, kuma dan ta nunawa wanda take so kulawa ai ba laifi bane, gashinan, babu abinda zubar da kai ke janyowa ai dama sai wulakanci, nan ka tashi ka je wajen kakansa ka yi rokon kudi a lokacin da la shiga matsalar nan, babu irin abinda ban nuna maka ba ka nuna ai kun zama daya, da waye kuka zama dayan? kai da waye? yau ko Mufeeda yake aure ai ba zaka yi haka ba bale Elhaji kana mantawa soyaya ce! soyayarma wace taka y'ar ta fi so din fiye da shi!"

" Ok, madallah da ke, nace madallah da ke Hajia maimuna, kennan yanzu ne lokacin ki ringa min wasu zaceceku? na je na tambayar da ban tambaya din ba da yanzu muna cikin wani hali a tunaninki?, na fada maki zan kama hanya jibin in sha Allah zan je garin idan ta zo na fada mata na rarasheta zan je da kaina in gani, , ba zan kyaleta din ba, so kike yi in kyaleta ta ji maganar nan a gari ta samu paralyse ko?"

Sake aika kira yayi a wayar Mufeedan, a lokacin kuwa Mufeeda a gaban AL'WALID ta ringa dauki ba dadi da kanwarta tana faman fadin babu inda zata je in su zasu tafi su tafi

Mamaki ke neman kashe shi a zaune, na irin yadda take magana haka bayan sakon daga iyayenta ne

Gannin kiran ya sa ta daga ta karra a kunnenta tana sauraro

Rai bace uban ya ce" Mufeeda, in nace ki taso ke kin san baban dalili ne zai sa in ce ki taso kai tsaye haka ko?, ki taso ku taho "

MUFEEDA ta ce" Dady, Ni fa ba zan zo ba tunda bai tafi ba, dady baka san yan matan garin nan bane gaskiya ba zan zo ba, gayanan zaune fa muna tare yanzu haka, ka bari in na ji yaushe zai tafi sai in taho"

Uban ya yi dan shiru yana jin maganar gayanan zaune ya ce" Waye yake zaunen?"

Mufeeda ta ce" Bab din"

Elhaji Maiga ya ce" Kina nufin Elhaji AL'WALID din ne a wajenki ko ke kike gidansu?"

Mufeeda ta ce" A'a shi ya zo, gayanan a mota a zaune"

Tunanin mahaifinta ya kasu kashi biyu, ya rasa amsar da zai ba kansa shi da kansa ya kusa kasa gaskata cewa AL'WALID ne ya zo, dan bai ga dalilin zuwan ba tunda ance zai yi aure ai, dan haka ya ce" Bani shi"

Mufeeda ta karyar da wuya ta ce" Aya dad, dan Allah kar ka sa yace in taho ka san idan ya ji cewa zai yi sai na taho, plz ka barni har ya tafi mana"

Gannin ba bashi shi zata yi ba sai kawai ya kashe kiran ya shiga neman layin AL'WALID din da fatan Allah ya sa ya fita da wayarsa

Ta dan jima tana ringin, idannuwansa a lumshen nan da suke bayan ta dawo cikin motar sunna hakanan bai daga su ba , bai kuma rufe su ba, gaba daya mamakinta na neman goge masa harda

Wayar ya daga ya karra a kunnensa ya yi salama cen kasan makoshinsa

Amsawa Elhaji Maiga ya yi sannan ya ce" Barka da hutawa Elhaji, ina fatan komai lafiya"

AL'WALID ya furta" Alhamdulilah Aba, ya aiki"

Elhaji Maiga ya furta" Alhamdulilah"

Sai kuma ya dan dakata sannan ya ce" Dazu yayana ya kirayeni yake fada min wata magana, cewar su Elhaji baba Hamza sun same shi da wani batu, shine na so ta taho ita dan ka san komai na iya faruwa, to kuma sai tace wai kunna tare, ko dai ba haka abin yake ba?"

AL'WALID ya bude idannuwansa da kyau dan jin wai Baba ya je ya fadi sakon nan, eh lalle da gaske baba yake, hummmm

A nutse ya ce" Sakon da aka bayar, haka abin yake" Daga haka ya yi shiru yana sauraron irin yadda Elhaji Maiga ke faman fadin Innalilahi wa inna ilaihi raj'une



Da kyar Elhaji Maiga ya ce" Me ya faru tsakaninku ne? wani laifi ta yi?, kuma na ga tace gakanan a wajenta ko ta sani ne?"

AL'WALID ya dage girarakinsa sannan ya dubi Mufeeda da ta kasa kunne tana sauraronsa, ga kanwarta a tsaye tana jira ta ji yaya zasu wuce din ne su je su shirya kayansu ko kuwa?

A nutse ya ce" Ba abinda ta yi"

"Bab, wai lafiya?" Mufeeda ta fada a hankali cike da marairaicewa ba kamar yadda ta gama yiwa iyayenta tsayaya ba

Mahaifinta ya yi gagawar fadin" Kana ji? dan Allah kar ka sanar mata, ka saka ta taho gida kawai, idan yaso ko menene ma ji daga baya, in ta ki kuwa bari Ni in taso dan na san halinta a kanka, ina so in zo Ni dinma mu yi magana saboda abin nan ya sakani a duhu, ko me ta yi ai sai a yi magana a yi mata magana ba in ji magana haka daga sama ba, dan Allah ka saka ta taho yau , yanzu yanzu"

AL'WALID ya fitar da dan huci sannan ya dubi Mufeeda

Har ga Allah zuwan nan da ya yi ya so ace ya samu amsoshin da yake so, wa'inda daga nan idan ya je gida zai samu Baba tsoho a kan maganar bai ki maganar auren zabinsa ba, ama kuma a hade da Mufeeda a daura, gaba daya sai ta ringa bashi wasu amsoshin da suka saka shi sake shawara da dogon tunani, domin ba zai taba yarda ya yi gigin aikata aikin nan ba

" Dan Allah ka ji? kar ka kashe yi mata maganar ina ji, ta amsaka ina jinta, dan Ni tace ta kiya wai" Mahaifinta ya fada a hankali, kana jin muryarsa a yannayin damuwa yake ciki

A hankali AL'WALID ya sake dubanta, tarin mamakin iyayenta da kuma ita din kanta na damunsa, ya san ya sha yi mata kashedin

29 / 64