Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

Author :  Sajida Nijar Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 64

54K to 57K   out of 190.8K words

in gani"

Ran Mama ya riga ya kai kololuwar ษ“aci, a nutse ta karaso inda yake tsaye ta dube shi cikin ido, furfura du ta gama kansa ama sai fitina, a kausashe ta ce" Baka isa ka kashe rayuwar y'ata ba, bayan ka gama kashe tawa, baka isa ka yi ikon nan da y'ata ba, Ni na gama salwantar maka da komai, na gama malaka maka kuruciyata ka lalata son ranka, bari ka ji ta Anmy sai inda karfina ya kare, zata kawo wanda take so a aura mata, zata je ta yi rayuwar jin dadi, Elhaji a kan Anmy komai na iya faruwa, a kanta zaka san wace Useina!, ka janye kudirin ka tun kafin in tabbatar maka rashin karfinka a kanmu a aikace Dan walahi a irin wannan lokacin na gama gane babu komai a cikin ido sai ruwa, zan kuma ganar da kai shayi ruwa ne!"

Tsananin tashin hankali ne ya cinye bambami da masifar Elhaji? ko tarin mamakin Mama ne ya nemi tsayar da bugun numfashin sa?, ya samu kansa a wani yannayi mai karfin gaske da ya daskarar da shi Har mama ta gama ta nufi dakinta , sai da ta rufo da karar rufo kofar ya ankara har ya zabura kamar kofar fuskarsa ta daka


A lokacin da ake wannan dauki ba Dadin a tsakanin Mama da Aba, a falon su Mama rigima ce ta kacame a daidai lokacin da Aba ya bada baya mama ta bi shi Lubna da idannuwanta ke waje ta dubi Khadija dake kallon coridor kamar an saka mata abinda ya tsayar da numfashinta , domin kamar bata numfashi bale motsi a yannayinta

Luba ce ta fara tabota bayan ta dubi samarin da suma du suka zarro ido suka kali KHADIJA

A firgice ta kalle su, daya bayan daya ta kalle su, sai kuwa ta ja uban tsaki tana mikewa ta ce" Kai dilla ku daina kallona ba fa da Ni yake ba"

Garin mikewar ne ta bige Karima dake kukan tashin hankalin da ta jefa kanta a ciki, dan ta sani in dai Aba ya duba wayar cen ta gama kadewa
ta dago a rikice dan tsoro ta ji kar aje Aban ne ya dawo, sai ta ga Khadija ce ta tureta

Mikewa ta yi rai bace ta tura khadijar tana fadin" Ke dan ubanki bakya gani ne zaki ture ni? ban son iskanci fa!"

Khadija ta yi dan tangal tangal ta rike kanta ta dawo da karfi ta ture Karima sai da ta kifa rai bace ta ce" kar ki ja in maida Yan watannin da kika bani gefe in nada maki dukan tsiya a gidan nan, banza da bata jin maganar babanta, gashi zaki ja mana masifa muna zaman mu, ki zauna addu'ar Allah ya sa khadijar gidan kawun kauye baba ke nufi, dan in ni khadijar larabawa ce sai na daidaita maki hakoran bakinki , sakarya ko ki gudu ki je gidan uban wa? banza mai bakin yan iska!"

Nan fa fada ya kaure, domin itama Karimar bata kyaleta ba , duk da ta san irin yadda take wahala a hannun khadija in ta hado su, haka ta dawo suka shiga dambe a falon nan amarya na gefe tana kallo, sauran yan uwan sunna ta kokarin rabawa ama abin na neman sake rikicewa har sai da mamanta ta ga zata ilatata ta shiga tsakiya rai bace ta ce" Ke kam inaga a halayar uwarki babu abinda kika baro, bayan kin shiga tsakaninta da ubanta ya baki mijin da ya zaba mata kuma so kike ki raunatata? shegiya mai karfin yan dambe to ahir dinki, Karima ma nan gidan ubanta ne baki da yadda zaki yi da ita y'ar bakin ciki"

Khadija da kukanta na iya shege, dan sai ta gama cutarka ta fashe da kuka ta ce" mama kin ga dai Mammana ta hanna ni sa'in sa da baba, ama gaskiya ko daina zaginta dan ba zan jure ba, kuma aure ba da Ni ake nufi ba, da khadijar kauye ake nufi!"

Tana gama fada ta yi ciki tana kukan nan na iya shege ta nufi wajen mamanta, sai dai me, tana tunkarowa ta ga babanta tsaye a kofar , shi bai buga ba, shi bai yi baya ba

Da sanda ta juya dan kar ya ganta ta koma coridor din nan ta tsaya tana jira ya bar wajen sai ta je su shawarta da Mama, dan ta tabbata Maman ma ita take jira ta fada mata ba fa da ita ake wannan tatsuniyar ba .

Ta kusa minti ashirin a nan, bata san abinda ake yi ba, bata koma falo ba, bata shiga ciki ba, sai gannin mahaifiyarta ta yi ta fito janye da akwati ta nufo hanyar falo, da hijabinta, yannayin tafiyarta kuwa. fusace
ne

Da sauri ta bi bayanta dan wuceta ta yi bata ce da ita ufan ba,

Tana fitowa falon bata dubi kowa ba ta nufi hanyar filin gidan

Kusan kaf yaran dake zaune sunna musu tsakaninsu a tsorace suka mike, hankalin kowane a tashe suka bi bayan Khadija dake aikin kiran Mama, Mama lafiya? Mama ina zaki je da akwati?

Har ta zo fita ta dakata ta juyo a fusace saboda Muhammad ya rike akwatin gam tana ja yana ja yana faman kiran sunnanta

Da karfi ta fizge akwatin bayan ta zabga masa harara murya a kausashe ta ce" Zaka sakar min ko ba zaka saki ba? sa'arka ce Ni? sake min akwatina nace!

Gaba daya suka zo suka mamayeta, su dukansu suka daneta , Du girmansu suka saka mata kuka, a rikice suke , hankalinsu a tashe yake, tamkar za'a raba su da wani sashi ne na jikinsu, du rikice suke
Muhammad ya fashe da kuka yana rike da jakar ya ce" A'a mama, ke ba sa'ata bace, ama idan na sakar maki jakar ina zaki je ki barmu?"

Anmy lokaci daya abun ke neman girmamar kwakwaluwarta, ita dai ta sani addu'ar barin mahaifiyarta a gidan mahaifinta tana daya daga cikin adu'o'in da bata bari in dai ta yi sallah, sai gashi yau abin ya samu ama kuma ta kasa tantance a wani hali take ciki, hankalinta ya gama kaiwa kololuwar tashi, tsaye take ama kamar a kife take jinta, a hankali ta sake gusawa ta ba Lubna waje wace ta karra rukunkume Mama tana kuka itama ta ce" Mama, to in kika tafi ina zamu saka ranmu?"


Wannan furuci na Lubna ya sa Khadija rintse idannuwanta ta sake budewa a kansa baki dayansu

A hankali ta juya ta dauki hanyar da ita da kanta bata gane nan take bi ba ta nufi wajen da zuciyarta ta aiketa kanta tsaye

Mama murya a raunane bayan ta raka khadija da kallo ta yi kokarin ciro Lubna daga jikinta a tausashe ta ce" Haba Lubna, a yanzu ko dokar daji ne ai zan iya kai ku , ku rayu, ku yi zaman ku a gidan Babanku, nima yau lokacin in je namu gidan ya yi kun ji?"

A tunaninta idan ta fadi haka ta samu su saketa, sai abin ya nunku, suka naniketa suka ki barinta, karshe sai da ta musu jan ido suka saketa ta sakar musu jakar ta juya ta kama hanyarta ta fito ta tsayar da dan taxi tana masa kwatancen gidan Hajiar Larabawa yaran suka bude taxi din suka shige gaba dayansu, har daya kan daya suka yi dan ta musu kadan, hakan ya sa Mama zuba musu ido zuciyarta na tsintsinkewa......., lokaci daya kwakwaluwarta da zuciyarta na son su cenza mata tunani, sai dai ta fi karfinsu ta shige motar , bayan direba ya saka akwatinta a baya da mutun biyu a bayan suka daga suka yi gidan Hajiar Larabawan tare

Sunna isowa daidai da kannin Mama ya fito daga motarsa, daga wajen aiki yake shima likitan ne, ya karaso yana mamakin tsatsakuwar da suka yi a motar da kuma yannayin auntyn tasa

Yana kokarin tambayar lafiya? Mama ta yi ciki ta barshi tsaye da su Sadik , su Lubna kuwa tuni suka bi bayanta suka shige

Sadik ya dube shi bayan sun gaisa ya ce" Baba karami mun kauro nan ne da mamanmu, ka biya mai taxi din dan bamu da ko sisi mu"

Da mamaki yake kallon yan samarin, daya bayan daya kafin ya ciro jaka biyar daga aljihunsa ya mikawa mai taxi dake jira sannan suka dugunzuma suka yi ciki su dukansu

Sunna shiga suka samu Mama kwonce saman shinfidar Hajiar Larabawa, kuka take yi sosai da sosai tana fadin ita kam ba zata koma gidan Elhaji ba, ta gama da zama da shi, kuma ba zai yiwa y'arta auren hadi ba, ba zata yarda ba, in me yake takama da shi ta shirya sai su yi fito na fito da shi, ba tsoronsa take ji ba

Hajiar Larabawa a zaune hankalinta tashe tana kallon ta, idan ta kalleta sai ta juyo ta kalli ฦดaฦดanta da kanninta da yayi tsaye yana kallon ikon Allah

Lubna dake kukan itama tana rike da hannun mamansu ta ce" Mama daina kuka kin ji? shikenan ai mun bar masa gidansa ya huta, kuma ba zai yiwa Anmy auren ba, sai mu kai shi kotu ai, ga yaya Sadik lauya ne shi zai rufe shi kowama ya huta!"

Hajiar Larabawa ta zubawa Lubna ido, sannan ta dubi sauran ta ga kowane yayi amana da furucin Lubna, haka kuma kunnayenta na sauraron karfin kukan Mama na raguwa, wanda ta tabbata furucin y'ar Tata ne ya sa haka,, sai ta dauke kanta tana duban kofa a hankali ta ce" To ke, kin zo kina ta kuka a gaban yayanki, baki yi shiru Bama bale mu san abinda ya dace a yi, ina takwarar take ne? ina Khadijar ne?"

Sai a lokacin Mama ta dago da sauri ta ringa bin yaran da kallo, haka suma suka dubi junna, Lukman mai saurin zagi a cikinsu ne ya tafa hannu ya ce" Kai, ina wannan shegiyar take kar dai mun manceta a cen yayi kulli kullin kubura da ita?"

Da sauri Muhammad ya buge shi yana fadin" Kai mai sunnan Hajiar Larabawan kake zagi?"

Yana fada yana mikewa ne ya ce" Ku tashi mu je mu zo da ita"

Basu wani jira ba du suka mike, suka kuma kama hanyar fita,

Da sauri Mama ta mike tana fadin" Baba karami ka kirawo min su, idan suka koma walahi Dukansu zai yi bana nan, su kyaleta ita ba zai daketa ba, kirawo min yarana kar ya wulakanta min su"

Da sauri ya bi bayansu, yana fita mama ta dubi Hajiar Larabawa suka yi ido hudu, sai ta juyar da kai tana sake hade fuska dan kuwa a shirye tsaf ta zowa Hajia yau.

Hajia ta yi murmushi ta juyar da kanta ta yi kiran mai aikinta

tana zuwa ta duka gaban Hajiar, itama datijuwa ce

Hajia ta dubeta da kula ta ce" Baba salamatu, a gyarawa ya'yan Usaina daki samarin su sauka a cen, yan matan kuwa sai mu hadu a nan mu zauna, yaji suka yiyo ita da ya'yanta"

Baba salamatu ta dubi Mama da mamaki, sai dai yannayin da maman take ciki ya sa bata ce komai ba ta mike a hankali ta nufi aikin da aka sakata zuciyarta cike da tunani, ama kuma ko menene zasu jira mutuniyar ta saku da kanta a zauna, yaji kuma? masha Allah da girmanta da komai? ai yanzu ko ANMY aka sa dakin miji ta fi karfin yaji bale Mamanta.



A gidan Aba


Kofar dakin khadija ta murda ta shiga , idannuwanta a kan wanda take son ganni, har ta hange shi zaune saman kujera , hannunsa na hagu a saman gaban goshinsa, gefensa kuwa magani ne a ajiye a bude, sha ne zai yi? ko ya sha din? wannan shi kadai ya sani sai Allah.


Bata kula da abubuwan nan ba, fatanta ta karasa gabansa, Sai da ta karasa ta duka a daf da kaffafuwansa sannan ta dago kanta ta kalli fuskarsa wace ya dago shima yana kallonta

A sanyaye sosai ta ce" Aba, Mama baba ce da akwati, wai ta tafi gidan Hajiar Larabawa, sakinta ka yi ne itama?"

A hankali ya sake zuba idannuwansa a kan KHADIJA, a bayane ya gane bata cikin hayacinta yarinyar, domin ya sani da a cikin hayacinta take ba zata taba daukan wannan baban risk din na zuwa gabansa a irin wannan lokacin, har ta yi masa magana a haka ba, magana kanta tsaye da furuci irin wannan ba

A tausashe ya girgiza kai ya ce" A'a, ban saketa ba, cewa ta yi ban isa in yi iko da ke ba Hajia karama, kuma a haka dinma ban ce mata komai ba ta tafi"
Ya ajiye maganar a hankali yana dan rintse idannuwansa sanadiyar sarawar da kansa yake yi

Tunda Allah ya haliceta bata taษ“a gannin mahaifinta a irin wannan yannayin ba, duk rintsi baya sada muryarsa irin haka, hakan ya sa ta shiga dawowa hayacinta har ta kafe fuskarsa da ido tana kallonsa

A hankali ta ce" Baka da lafiya ne Aba?"

Elhaji ya mayar da kansa ya jingine yayi shiru

Cen ya budi baki ya ce" Kalau nake Anmy, in sha Allah rigimar mamanki ba zata kasheni ba, aure ne na rantse sai na daura maki shi da wannan bawan Allahn, mutun ne mai daraja sosai, mutun ne da idan na bashi y'a na san na saka a hannu mai kyau, kuma na fada zan kuma fada na isa da ku ke da mahaifiyarki , zan yi iko da ku, idan har Usaina ta min garaje zan daura aurenki a yau kowama ya huta"

Cikinta sai da ya juya, ta kawo hannunta ta rafka tagumi ,

Babu abinda kirjinta ke yi sai dokawa, so take yi ta kwonta ta yi burgima a nan ta sanar da shi bafa zai yiwu ba, ama a yanzu ta dawo hayacinta ta san idan ta yi haka sumar da ita zai yi ya mata auren ya kaita a summe, gwara ta bi bayansu a dauki matakin da ya dace a kansa, aure zai yi mata ita? na dole? aaa aaa aaaa ai Elhaji bai gane ba, gaskiya bai wani isa da su ba, da ace Mama ce ta mata mijin nan lafiya lau zara yi biyayya ama ba wai shi ba, inama hadi yo Allah mun tuba?

Mikewa ta yi bata ce masa komai ba , har ta fara tafiya ta dawo ta duka ta ce" Aba ka bani kudin taxi in tarda su, sun tafi fa"

Yannayinta kawai yake kallo, sai kuma ya mike ya je wajen da yake ajiyar kudi ya bude ya ciro kudin ya dawo ya bata ta juya ta tafi sannan ya koma ya zauna yana dafe kansa da hannayensa biyu

Shi dai ba yaro karami bane, a yanzu zai iya cewa soyayya da ita da babu uwasu daya ubansu daya, baya tunanin akoy abinda zai taba shi wanda bai taba shi a da ba, sai dai tafiyar Usaina, tafiyar Usaina wani abu ne baba a cikin manyan abubuwan da suke iya gigita shi.....gefen kansa yake ji yana wani irin ciwo, da kuma kirjinsa da ya yi masa nauyi

Mikewa yayi ya koma saman kujera ya shiga shiga wayar Karima ya shiga bincike
Karatu in dai da Hausa ne, zai iya yi maka shi, da kuma larabci, turanci ne kawai bai iya ba, abin mamaki kuwa abubuwan ta du da Hausa ne

A hankali ya ringa shiga msg dinta na cikin whatsup dinta

Tun bai yi nisa ba numfashinsa ya ringa yi masa nauyi, zufa ta ringa keto masa, mijirya ta ringa kama kaffafuwansa da jikinsa baki daya

Msg din da ya shiga nata da Mudansir kadai ya fitar da shi a hayacinsa, irin kalaman da suke yi na batsa tsantsa da alkawarurukan bayan aurensu irin zaman da zasu yi ya sa ya ringa kokowa da numfashinsa , wayar ya saki dan dole ya mike da kyar yana bin layi ya fito dan neman agaji, domin idan bai nemi agajin nan da gagawa ba tabas maganar Hajia zata tabbata, d'an yau zai gila abinda zai dauke numfashinsa dan firgici gashi shi kadai ne a dakin, ga yana cikin yannayin fada da kowa amarya ba zata taba nufo dakinsa a irin wannan lokacin ba, wace ke tunkararsa duk wuya duk rintsi din kuwa ta bar masa gidan da ita da ya'yansa baki daya.........


A mugun jigace ya fito yana kiran masu gadi

Su ne suka talabeshi a rikice suka yi asibiti da shi bayan sun sanarwa amarya ta fito suka rankaya tare..........( Wannan kennan)








WANNAN SHINE FARKON LABARINA...................A YANZU ZAMU NAUSA CIKIN LABARI GADAN GADAN,

YAYA WANNAN RIGIMAR ZATA KAYA?

ANMY, WACECE ANMY? ME ZATA ZO MAKU DA SHI A LABARIN NAN?

URS SIR AL'WALID .....WANENE SHI? YAYA TASA RAYUWAR TAKE?


MUFEEDA FA?


YAYA ZAMANTAKEWAR GIDAN ELHAJI ZATA KOMA? HAJIA TA BAR MASA GIDANSA KENNAN?


TABASSS ZAKU SAMU FADAKARWA, ABIN TAUSAYI, ABIN NISHADI A WANNAN LABARIN..........KU TAHO KU BIYA KUDIN KARATUNKU NAIRA DARI BIYAR DAN KU RINGA SAMUN SABBIN UPDATE DA ZARAR NA SAKI......NI CE TAKU, SAJIDA NIJAR 93811618


Karshen free page๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐Ÿ˜
07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba: ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ
*FARKON GANIN IDONA*
๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐Ÿ˜*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦŠAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦ˜IN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na sha shida (16)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*


https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI

19 / 64