Author : Sajida Nijar Category : Romantic Hausa Novels
fita, khadija kuwa ta nufi bayi, ita kuwa y'ar uwar tasu wato Ummu ta nufi dakinta dan a bude ta barshi da nufin dauko dardumarta sannan ta rufo
KARIMA jikinta a mugun mace yake, ta dubi Lubna a hankali ta ce" Lubna, ina cikin wani hali, Lubna ina cikin wasu tunanika da suka cinkushe min kwakwaluwa, Lubna anya kuwa zan ga da kyau? idan ina gaban Mama zuciyata na cika da kaunarta, da tausayinta, da begen ta tamkar wace ta haifeni, saboda a tare da ita bana gannin wani bakin hali ko bakin ciki a kaina, idan kuma na bar inda take na je gidan su Mama sai a ringa ganar da Ni wani abin daban..........gaba daya an hade min lissafin rayuwa"
Lubna na dubanta, a hankali ta ce" Ban san me ake fada maki ba, ban san girman zugar mahaifi a kan ya'yansa ba, dan Ni tawa mahaifiyar a kulun nuna min take yi tunda Mama ta ci kashina da fitsarina uwata ce har a gaban Allah, idan na saba mata Allah ne zai saka mata, Karima ke ba mahaukaciya bace, zan so ki yiwa kanki adalci, ki yiwa Mama, abu daya na sani Mama haihuwarmu ce kawai bata yi, walahi du wanda yayi mata butulci sai Allah ya saka mata.., kina kallon iri........"
Shiru ta yi saboda tahowar Khadeeja, domin idan Khadeeja ta ji yanzu wasan zai watse, koda wasa ka fadi wani abu a kan mama ta rikeka kennan, in babu yadda zata yi da kai zata kai karar ka wajen Allah ne, idan kuwa tana iya dira ta rike maka kwalar riga an gama, wasan ya tashi dan walahi sai inda karfinta ya kare, dan sun sha fito na fito da Karima idan ta ga Mama ta yi musu fada Karima ta yi gaba tana turo baki, takan ce mata ke kam kamar y'ar iska, Mama ai uwarki ce, shikenan ta kirkiro hanyar da zasu daku da KARIMA, kuma yawancin lokuta Karima na kuka ake amsarta dan idan ta daneta sai an kwaceta
Sallar ta kabbarta , ta yi isha'i sannan ta yi shafa'i da wutir, ta je ta kwonta a shinfidar Mama ta lumshe idannuwanta, ta afka duniyar tunani mai girman gaske....., gaba daya gani take yi ne an gama dukanta sannaan an hannata kuka, gani take yi an gama kashe mata rayuwa ita kam sai ceton Ubangiji, a irin mazan da Aba ke zabowa mutun fa harda wanda baya ra'ayin a yi karatu?, idannuwanta ta rintse a cen kasan zuciyarta ta ayana' Ya Allah, baki da mafaka, bani da matsera sai wajenka, gashi maganar aure ake yi sunnan mafi soyuwa a wajenka, ya Ubangiji Ni din ban isa in take ko in ki yiwa iyayena biyaya ba domin ina fatan samun rabauta a wajenka, ya Allah ka sa ko wanene alkhairina ne, ya Ubangiji ka sa ba'a bani mai kudi ba, domin na riga na sarewa auren mai kudi a rayuwa, ya Allah ka bani wanda zamu fahimci junna, zamu yi wasa da dariya, idan ta kama sai na toya kosai dan mu samu abin ci in dai da kwonciyar hankali zan toya, ya Allah ka sa mijin da babana ya bani mai sanyin hali ne, Allah ka bani ikon yiwa iyayena biyayya.......
Tana jin lokacin da ake ta yi mata magana dan ta tashi su ci abinci ta yi likimo ta ki tashin , Mama tace su kyaleta su ci su kwonta , tana yi tana duba lokaci, gidan an ragu sosai sai iya su da Mama fateema da kuma kannen amarya domin a lokacin da suka so tafiya da suka fuskanci Mama fateema a nan zata kwana shine suma suka ce ai a gidan zasu kwana, ita dai Mama fateema bata shige dakin Khadeeja da nufin kwonciya ba sai da ta gama aikace aikacen da ya dace tasss sannan ta shige ta rufe ta yi kwonciyarta, dan a lokacin karfe takwas ta wuce na dare
SU ABA
Tunda ya sa suka yi shiga ta manyan mutane ya fito da su daga gaban Mama ya zamo a tsorace suke , domin koda suka zo gidan bawan Allahn nan wanda sarai habubacar ya gane gidan su Mudansir ne su Dukansu a tsoracen suke , kuma sun kama kansu kowane da abinda yake ayanawa a cikin zuciyarsa
Tsakin da Aba ya yi a zaunen nan ya fi cikin kwondo, ya tambayi lokaci a wajen Mubarack ya fi a irga, wanda ke rike da wayoyinsa, yana yi yana sake duban wajen da aka basu abin zama da lemu ya ja wani uban tsaki ya dubi Muhammad ya ce" Muhammadu ka ga Ni aka sauke da lemu a wajen nan, sai kace dan yinwa? to wai an sanar masa sakona na jiya kuwa?"
Muhammad ya sada kai ya kasa bashi amsa, shi kuwa ya dube shi shekeke kafin ya dauke kai ya ce" Yan buro'uba ya'yan gimbiya du baku da isashiyar tarbiya, ina magana kana wani sune kai kamar da gaske, bayan a cikinku aka samu mai son mai jan ido"
Su dai Allah ne ya kawo su wannan lokaci sun sani, kuma shine zai raba su lafiya da shi wannan ma sun sani, sunna fatan Allah ya raba su lafiya tun kafin ya sauke haushinsa a kansu, su basu san me suka zo nema nan din ba, kuma ance mai gidan na nan, ama a kala sun dauki sama da awa a zaune, cikin ikon Allah mai gidan bai fito ba, sun rasa abinda yake faruwa ,sunna fatan ko menene Allah ya kawo musu shi da sauki
An sake daukan kusan minti goma, Har Aba ya mike fuuuuuu yana baza babar riga zai kama hanyar fita aka yi salama daga kofar shigowa ta cikin gidan aka shigo
Elhaji Umaru Musa ne ya shigo da farar jalabiyarsa , bayansa kusa Mudansir ne da ya'yan Mudansir din da kuma kanninsa biyu, suka karaso suka zauna kusa da su Abubakar, shi kuwa Elhaji Umaru din ya tarbi Aba da ya dakata ya mika masa hannu yana fadin" Asalamu alaikum Elhajin Allah, Barka da dare, a yi hakuri, a yi hakuri ban san kai bane a lokacin da Madame ta sanar min na yi bako an kawo min abinci ne, sai da na kamala na fito mun zauna zamu yi shawara da yara aka sanar min bakon fa kaine kuma kana nan"
Aba ya amshi hannun nasa suka gaisa yayi murmushi bai ce da shi komai ba ya koma ya zauna
Bayan sun zauna Elhaji Umaru ya ce" Elhajin Allah maman yara ke cewa bakon na Mudansir ne? ina fata lafiya?"
Aba ya dubi Mudansir dake sine kai, shi walahi yaron sai yake masa kama da yan daudu, kuma jan ido kam eh gaskiya jan ido gareshi ama shi fa bai ga jan ido na dakankan namiji, kardai aje dan shanye shaye ne Karima da uwarta suke so?, ji yake kamar ya janyo shi ya ci ubansa, inama ace fada ya kaure a nan ya hada shi da ubansa ya musu dukan tsiya su Sidik su kama masa, dan walahi dai a yadda yake gannin uban Mudansir din nan shima ba wani abun kirki zai yi ba
Kai ya dauke ya fuskanci Elhaji Umar ya ce" Kwarai Elhaji, tafiya ce ta dole ta kawo Ni gidanka, a kan yaran nan na zamani, yarinyar wajena na yiwa miji, ta bi dare ta bi yaron wajenka gayanan, karshe dai na tsinci abubuwa mararsa dadi a wayar da ba Ni na bata ba, shine ya bata ba da izinina ba, shine na zo in SAMEKA dan mu san yadda za'a yiwa tufkar hanci"
Elhaji Umar ya dubi yaron nasa cike da jin haushin shima zai yi abinda yayansa ya musu kennan? ya ce" Mudansir? kaima sahun da Lukman ya bine ne zaka tono? kaima y'ar mutane kake son lalatawa? Mudansir an yiwa yarinyar miji shine zaka je ka dauketa daga gidansu? wannan din ai bai dace ba, kan me yasa kuke haka ne ya'yan nan?""
Aba yayi tsurutsuru yana kallon uban, a hankali ya ce" Elhaji yi hakuri, ama waye Lukman din?"
Elhaji Umar ya ce" Yayansa ne ai, haka yaron nan ya je ya samu y'ar mutane ya hure mata kunne ya janyo mana masifa kala kala a gidan nan, dan haihuwarsa biyu da yarinyar karshe dai aka aura masa ita suke zaune gayanan kana ganninsa yara basu tafasa Bama suke konewa?"
Aba ya yi wani irin kama an wanka masa mari ya turo hula gaba, ya mayar da ita baya, ya sake turota gaba, kai karshe ya cireta yana fifita ya ce" Shikenan, an gama da Ni, innalilahi wa inna ilaihi raj'une abin yayi nisa ashe nake neman bakin zaren, kannin dan iska ai dan iska ne, kai bayan tarin sakwanin daren farkon ku ka ga daren ko baka gani ba?"
Wata irin kunya ta sa samarin ya'yan b
aba kasa kallonsa, shi kuwa Aba gannin ya'yan Elhaji Umar sai wani shanshan kanshi suke ya samu ya yi tsalan albarka ya riki Mudansir kafin ubansa ya mike ya sakar masa rankwashi a tsakiyar kai ya jijiga shi yace" Dan ubanka amsa daya nake so, ka ga daren farkon nan da y'ata ko a gaba?"
"Subahanallah Elhaji ya da haka, sake shi dan Allah sake min yaro, tunda nake ban taba saka hannuna a kan y'ayana ba, Ni bana dukan yarana, dukan yaran me yake haifarwa banda kiyaya tsakanin ya'yan da iyayensu? sake shi, ko me ya yiwa yarinyar ka ai ana iya samun masalaha, ko me kake so sai a duba a gani idan zai yiwu ama ya zaka rike min yaro haka sake shi Elhaji kar abin ya kai mu da gannin bakin junna dan a kan y'ayana Ni sai in kai karar ka kuma a zo ana cewa na kai karar makoci" mahaifin Mudansir dake kiriniyar amsar Mudansir ke fadan haka da karfi ko Aba zai ji shi
Aba ya sake riΖe Mudansir da kyau ya ki saki rai bace ya ce" Da ikon, da d'an naka , da yan anguwar masu gulma uwarku ta ci uwa tarrrrrrr! waye kai! wa ya tsaya maka a nan duniya? me ka tanada ? ka jima baka rufeni ba a kan y'ayana sai inda karfina ya kare, kai zaka daina langwui ka fada min ka ga daren farkon da y'ata ko sai na murde banzan abin uban kowa ya huta da mugun iri d'an yan iska?"
Da sauri Lukman ya nufo da karfinsa yana fadin" Kai Elhaji ka sake shi mana, ai ba'a taba yin d'an iska daya ba, idan kana kiransa d'an iska ita y'ar taka mecece? ai ba da karfi ya dauko ta yayi iskancin da ita ba idanma yayin, ka sake shi walahi kar in........"
A haukace Sidik ya dago, kafin Lukman ya kai karshen aya ya dauke shi da gigitacen mari , sannan ya ja zai kai masa naushi Muhammad ya rigaye shi, Sarkin fada kuwa dama tuni ya tare dayan yace" Kai, kar ka shiga harkar manya "
Rai bace Sidik ya ce" Kar ka yarda, kar ka saki ka zagi ubanmu, ka barsu su yi magana, ka barsu su ganewa junna, ba ruwanka, idan kuwa kace da ruwanka ba laifi ka gwada walahi sai mun fitini rayuwarka !, kuma ai kunna da y'an mata a gidanku na rantse da wanda raina ke hannunsa in dai Ni jinnin Elhaji Ya'u ne sai na nuna muku shegantaka biki ce!"
Aba ido yake zarrowa, yana kallon samarin ya'yansa a tsaye, haka kuma haba habar mutane ta fara yawaita yan bayar da hakuri da rabiyar fadan
Baban kamili da ya shigo ne ya karaso inda su Aba suka sarke junna ya saka hannayensa yana fadin" Subahanallah, subahanallah subahanallah, ku saku, ku saku, subahanallah, haba haba jama'a da girmanku da mutuncinku kuke irin haka? haba dan Allah idan yara sun hada rikici ai zama ake yi a sasanta bale ya'yan nan namu na yanzu idan muka ce su zamu biya sai mun rasa wanda zamu gaisa da shi a titi"
Tsakiyar su ya shiga, Aba yana haki ya dubi Sidik ya ce" Daukon hulata mu je, Elhaji Umar zan nuna maka mu irin namu son ya'yan ba irin naku bane, domin sonsu bai sa mun gaza tsawatar musu ba, kuma ka sani zan je in binciki y'ata idan har ya ga farkon daren nan da ita kafin daren yayi alkur'an sai na masa dandatsa, yaro kana da gaskiya ba'a dan iska daya, biyu ne, Ni na ga kattttt, ku wuce mu je , da neman aure muka zo tunda ta wulakantamu ta watsa mana kasa a ido ta nuna shi take so, sai dai ashe girman na jiki ne kawai Allah ya kawo da furfura , yaro kuwa kannin d'an iska ah d'an iska ne, mu je!"
Mudansir a tsaye yake, jikinsa a mugun mace, gaba daya hankalinsa a tashe, yana kallo suka bar gidan, ya juya da sauri yayi ciki wajen mamansu ya saka mata kuka
Hankali tashe take tambayar abinda yake faruwa? , a rikice ya ce" Mama, mahaifin Karima ne suka dawo ai, maimakun a bishi a laluma a kashe fitinar dake faruwa a sasanta a bani aurenta shikenan dan ya shakeni shine baba ya fada masa magana, Mama walahi kin ga mutumen nan ba zai taba bani Karima ba, kuma in fada maki sai ya saka bana a uku a cikin garin nan, dan kuwa du inda baba yake tunanin rigimar mutumen nan ya wuce nan!"
"ina yake d'an naki? yana ina? Ni kam ya'yan nan sune zasu yi sanadiyata a duniyar nan, kai kuwa du ya'yan dake cike a garin nan ka rasa d'an wanda zaka bi sai ta wannan dan balakin? me take da shi da zai sa ka janyowa ubanka masifa? ka san waye shi? ka janyo bamu yi maganar fahimta ba ya bar gidan nan , ka san cewa shi a daku bata ce masa komai? wannan wace irin masifa ce?" Elhaji Umar Musa ke fada rai bace
Hajia rukaya ta girgiza kai, rai bace itama ta ce" To ai kare ne ya take sawun kura, kaima wa'inda kake bin ai ba na rufin asirin bane, Ni dai zaku kashe ba kowa ba, Allah ya sa bai hadata da ciki ba dan walahi ba ruwana sai dai ku karata, na fada muku, kai da ka ji kunne baku da gaskiya ai sai ka bi hanyar da ta dace a samu masalaha, d'an naka yace yana son yarinyar, sai ka san yadda zaka yi ka daidaita rigimar" Daga haka ta yi wucewarta ciki, domin alkawarin da ta daukarwa kanta shine ba zata taba bari tashin hankalinsu ya taba lafiyarta ba.
(Wannan kennan)
Tuki Aba yake yi cikin shiru da tashin hankali, ya'yansa kuwa tunda suka shigo mota ya bi su da kallo yana karrawa babu wanda yace masa komai har suka karaso kofar gidansa , Sidik ya fita daga motar ya karasa a Ζafarsa, Aban ya bi shi da kallo ya ga irin yadda ya'yan nasa suka zama samari, sai da wani abu ya dan tsirga a zuciyarsa
Kai ya dauke ya shigar da motar ya fice ya bar sauran da wani irin sauri bangaren su Hajia
A HANKALI Muhammad ya ce" Kai wai ina akwatin Mama ne? da aka dawo da mu ba nace maka mu barta a kusa ba ta yiwu mu kuma yin yajin kwana kusa ba?"
Dariya yayi yana hangen hanyar ya ce" Ko mun je maido mu za'a yi, Ni kam bari in boye dan na san yau ko wa yake gidan nan ba zai hanna gidan nan kamawa da wutar balaki ba, Allah ya sanyayawa Mamanmu baiwar Allah KARIMA sai janyo mata masifa take yi, ama ka san Allah, Elhajin nan da ya'yansa sai sun ga rashin mutunci, mu za'a tabawa uba?"
Muhammad ya yi murmushi ya fita shima ya ce" Barsu, Wadinnan ai daidai muke da su, ku zo mu yi gyaran kofar nan tun yanzu dan gobe da wahala mu samu time, ina sauran samarin gidan ne?"
Sidik daga ciki ya ce" kai ku bari a gama haya hayar cen, idan bai sakar mana uwa ba ma gyara masa gidan in kuwa ya koreta sai mu kara gaba, walahi idan Karima ta sake janyowa mama wata fitinar sai na zane banza marar hankali!"
Haka dai suka yi zamansu sunna tataunawa kafin sauran su dawo daga aiken da Mama ta musu.
A tsiyace Aba ya shigo yana ihun fadin"
07/12/2024, 15:13 - samiraharounayacouba: πΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊ
*FARKON GANIN IDONA*
πΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*π³πͺ
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you π*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ΖAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAΖIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da takwas(28)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
π0912 262 1080
LABARI
A tsiyace Aba ya shigo yana ihun fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, innalilahi