Chapter 15 Reading AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt Arewa Novels

AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt

Author :  Aisha Bagudu Category :  Old Hausa Novels

Chapter   15 / 123

42K to 45K   out of 366.6K words

gidansu dan dauka kayanta dazata saka .
wanda ta manta bata hadu dashi ba cikin kaya .
,tafe take tana sauri . yayinda su ya faruk da abonkan DEENi ke tsaye duk cikin shirinsu na zuwa daurin aure .
amman banda DEENi wanda dagani shi suke Jira .
Wani irin kunya ce taji takamata dan haka ta dan janyo gefen mayafinta ta rufe fuskarta ,tana jin yaya faruk nacewa amaryamu ki bude idanunta kada ki fadi mana .
amman ina ko waiwayo batayi ba tacigaba da tafiyarta ta kofar baya tabi yauma.
tashigo dogon parlour'nsu ta baya kennan tasoma jiyo kamshin turarensa kafin tayi kokarin bude fuskarta taji sunyi karo da mutun .
da sauri takarasa bude fuskarta "yaya DEENi ne wanda zai fito har wayar dake hannushi ta fadi .
,gabanta ne yayi wani irin faduwa dan har wani juya juya ta dinga ji da sauri ta tsugunna dan miko masa shima ya tsugunna da zai dauka a tare hannunsu yakai kan wayar ,wani irin shock ne yajata " wanda baita kadai ba har shi DEENi yaji abinda taji.

Wani iri shima yaji ajikinsa tamkar an jona masa lantarkin .
. Shine yasoma kokarin janye hannushi daga kan nata ,ahankali ta Miko masa wayar batare da ta mike ba hade da cewa kayi hakuri dan Allah .

komai Bai iya cewa ba baya ga amsar wayar da Yayi ya barta nan tsugunne.

Bayansa tabi da kallo yayi matukar yi mata kyau har batasan yadda zata misalta ba sanye yake cikin shadda fara kal sai kamshin yake zubawa .
gabadaya kamshin turarensa ya gyaraye dogon parlour'n .
Ahankali zuciyarta tasoma bugawa tamkar zata basa kirjinta ..
girgiza kai kawai tayi dan batasan wani irin aure take shirin yi ba haka ta juya cikin sanyi jiki tabar gurin tana shiga ciki.m mutane akama kiranta da amarya amarya kinsha kamshi ita dai bata iya cewa komai ba dan gabadaya jikinta a sanyaye yake .






MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Page 27-28

Part din cike yake da abonkan arzikin da en'uwa ,Ummi
Jikinta a sanyaye ta dinga ratsa mutane dake ,zaune a parlour ' har ta iso dakin ummi , da idanun take bin en dakin da kallo .
kozata ga ummi ganin bata alamunta bane , yasa tmbye matar uncle din Inda ummi take.
tace yanzu tashiga bathroom .
Ahankali ta fidda numfashi tare sauke ajiyar zuciya .
cikin haka ummi ta fito tana ganin zeenat din.
ta bata fuskarta "ta zauna tana dubanta"

gefen ummi zeenat tasamu ta zauna fuskarta dauke da murmushi wanda da Gani na karfin hali ne .

Cikin kasa da murya ummi tace yana ganki haka ina kayanki ?

Cikin sanyi jiki zeenat tace shi nazo dauka .

,ummi tace ke dai kin cika shiririta wlh "
komai baza kiyi shi cikin sauri da kazar kazar ba kin dinga jan jiki kennan ,kmr wata mage .

Alhalin kin san halin wanda zaki aura " dan oya oya ne .

jin haka yasa jikin zeenat din sake yin sanye, tare jin wata irin faduwar gaba " zuciyar ta dinga dokawa da sauri tamkar baso kirjinta.
ahankali tasa hannuta ta kamo na ummi
cikin nata jikinta har rawa yake hade da rage murya tamkar mai shirin zubda kwalla tace dan Allah ummi kiyi hakuri kinji karkiyi fushi dani ,zan canza inshallahu Amman " kimin addu'a .
wlh tun sanda aka samo shirin bikin nan nake jin faduwar gaba wanda narasa dalili .
ummi ta tayi shr tare da zuba mata idanu kawai tana kallonta .
tausayinta ne ya sake kamata , ,duk sai taga takara ramewa ba kmr kwanaki ba hakan yasa taji ba dadi aranta.
, ahankali ummi ta mike tare da riko hannuta tayi cikin , bedroom daita. En dakin suka bisu da kallon sha'awa duk da basu ji maganarsu ba Amman sun birgesu .

,Har suka shigo bedroom din Ummi na rike da hannuta Ta zauna daita tana rarrashita kan ta kwantar da hankalinta fargaban aurene kawai ke sata jin faduwar gaba Amman bbu abinda zai faru inshallahu "
Ummi da kanta ta shirya diyatata cikin wata arniyarta geziner ligth blue sai daukar ido take da kamshi tare da fesheta da turaruka kala kala masu sanyi kamshin take zeenat ta fito amarya sak .tayi kyau sosai
Ummi ,ta dauki waya tayi mata hotuna sannan takira Maryam tace tazo ta tafi daita din .



Kwanciyar tayi flat a kan gadon su shemah tana kallo da sauraran duk abinda ke faruwa .
a cikin dakin dake cike da en mata da kawaye

abinka ga mai yawan kawaye " da mutane kala daban daban " yasa dayawa wayan dake cikin dakin kawayen zeenat din ne .
gyara kwanciyarta tayi idanunta na kallon celling dakin hannuwanta duk rungume da kirjinta yayainda zuciyarta ke cigaba tsalle tamkar zata fasa kirjinta ta fito waje.

ahankali ta runtse idanunta sanyi taji yana ratsa koina a jikinta duk da tarin fargaban dake tattare daita hakan bai hanata jin jikinta yayi mata nauyi ba .
Tana ji ajikinta burinta da dokin son auren DEENi .
duk babu shi ahalin yanzu sakamakon fargaba da tsoron kasancewa tare dashi a muhalli daya .
Ta dauki lokacin mai tsawo kwance yayinda ta dinga jin wani iri ajikinta .
Bugun zuciyata na sake karuwa.
ta dinga kokarin ganinta ta cire damuwar dake damunta wanda a zahirance ita ta daurawa kanta .
har yanzu da take kwance jikinta a sanyaye yake takasa tabuka komai.
idanunta ta runtse tana cigaba da sauraron hirar dasuke sama sama .



10:30


Karfe goma da rabi daidai na ranar lahadi Allah ya cika alkawarinsa domin dimbin, jama'a sun shaida daurin auren NASURULDEENI ALIYU BELLO da MUZEENAT HABIB BELLO" daurin auren daya tara manya attajirai da kusoshin gwanati hade da maikata
bakaramin farinciki family din muhd bello suka yi ba ganin sun kara karfafa zumunci a atsakaninsu, .
dan haka farincikisu ya sake karuwa takoina ka juya , family din murna ne cunkushe a fuskokinsu



Zeenat dake kwance har lokacin tana saka da warwara still jikinta a sanyaye yake takasa kwakwaran motse .
zuciyarta fall da fargaba musamman lokacin da taji hayaniyar mutane ta cika gidan alamun an daura aure, en'uwa nata shigowa ana gaisawa , ajiyar zuciya dumin hawaye taji yana bin kuncinta shikennan ta faru takare tana matukar son deeni Amman tana jin tsoron zama dashi hayaniyar mutane take sake jiyowa hakan yasa jikinta ya dauki kirma,kirrrrrr... sam ko kadan bbu wanda ya lura da yanayinta.
Sai ma tashi sukayi suka fita waje km har sanda suka fito tsakar gidan suna ta daukar hotuna bbu wanda ya lura da yanayin da suka barta .
" Maryam ce data karaso wajensu taga suna ta hotuna bbu ita yasa tashiga dakin dan dubota dan kusan tana lura daita tun jiya tamkar mara lfy .

kwance ta tadda ita tana fidda numfashi sama sama .
Da sauri ta karasa inda take bbu abinda jikinta keyi sai fidda hucin zafi, a rude ta dinga takiran sunanta zeenat ... zeenat daman bakida lfy ne?

Kai kawai ta iya girgiza mata alamun eh da sauri Maryam ta mike ta nufi part din ummi tasanar mata .
tare suka dawo gurinta da wasu en'uwa ummi guda biyu .
zuwa yanzu jikinta ya tsananta zafi tare da karkarwa .
ban da salati bbu abinda ummi keyi da sauri takarasa kusa da zeenat din ta zauna tare da riko hannuta" may zan Gani , haka ni fadeela ?
, zeenat kina son ki kashe min kanki ne ?
Ko yaya ,
Alhalin kinsa ke kadai gareni duk duniyan nan km ke kadai debimin kewar er'uwarta dana rasa , bazan iya jurar rashinki ba dan Allah ki tausayi min mamana.
sai km hawaye shar shar daga idanun ummi sosai Ummi ke zubda kwallar tausayi diyarta ganin yadda ta fita haiyacinta cikin lokaci daya .
Ummi tace zahra kamama min ita dan Allah .
su aunty suka mata zeenat sukayi part din Ummi daita .


kai tsaye dakin DEENi ummi tabada umarnin a wuce daita.batare da bata lokaci ba ummi
takira family doctor dinsu .
sannan takira DEENi tace yasameta a dakinshi yanzu yanzu .


Doctor bai dauki wani lokacin ba" sai gashi yana zuwa yasoma duddubata tare dabata taimakon gaggawa .

ummi ta dubi doctor hankalinta a tashe tace doctor meke damunta ?

doctor yace bawani abu bane damuwace kawai tayi mata yawa "amman inshallahu zata. dawo daidai .

A gaugauce DEENi yashigo byn amsa kiran Ummi .
yana shigowa dakin mutane suka dan ragu .

ahankali yakaraso kusa da Ummi ya tsaya yana tmbyrta abinda ke faru sai data ja numfashi sannan ta nuna masa inda zeenat din ke kwance tace zeenat ce ba lfy sai lokacin idanunshi suka kai gareta kwance take akan bed dinshi an lullubeta da bangon rufarsa.
shr yayi tare da zuba mata rikitattun idanunshi.

Daddaden kamshin turarensa tasoma juyowa may matukar sanyi ahankali ta dan lumshe idanunta .

Taku daya zuwa biyu yayi yaja ya sake ya tsaya" sannan ya dubi inda ummi ke tsaye yace me doctor din yace yana damunta?
, doctor din still ya sake mashi bayani kmr dai yadda yayiwa ummi . ahankali ya sake mai idanushin kanta yana cigaba da kallonta wannan shine karo na farko daya tsaya ya Kare mata ,
, sosai kamshin turarensa ke sake kaiwa hancinta farmaki tare da susuta mata duk wata gaba dake jikinta .
.
jikinta da zuciyata suka dauki rawa wani zazzabi mai zafi yayi nasarar sake rufeta sakamakon idanushi dake yawo a gangar jikinta .

Da sauri doctor ya nufo inda take" deeni yasa hannu ya dakatar dashi alamun kada yakarasa gareta" dan wani abu yaji yana taso masa sanda doctor ke masa bayanin abinda ke damunta , tamkar ya auna doctor waje dan takaicin abinda ke cin zuciyarsa.
ganin haka yasa doctor din yace a samo ruwa da towel a goge mata jiki dashi dan tazo daya dubata yaji yadda jikinta ya dau zafi yace zai je ya dauko magani ya dawo cikin sauri ya fice dakin .

A ranta tace doctor dama kayi zamanka dan maganinka kadai ba zai taba min maganin damuwarta ba .

dan ita kadai tasan abinda ke cin ranta .
Wanda tun daga cikin zuciyarta take jin yake taso mata .
tare da haddasa mata tsoro da faduwar gaba.


Tsaye yake har yanzu sai suke hanuwanshi duka da Yayi cikin aljihun wandonsa.

ahankali yasoma takowa zuwa bakin gadon km idanushi akanta.
cikin sanyi ya yaye bargon da aka lullube mata jiki dashi. idanunshi fes akan fuskarta dake lumshe tayi fayu sannan km takara rame sosai ahankali ya daura hannushi saman goshinta .
jin yadda goshinta ya dau zafi da yadda take fidda numfashi sama sama yasanyashi kai hannushi da sauri jikinta.
take yaji abinda ya sake frigitashi .
zafin dake jikinta ya ratsa tafin hannushi" wanda bai san sanda tausayinta ya lullubet shi ba ya dinga jin wani abu na tsigar wa ajikinsa , ya juyo tsaitin Maryam yana harararta yace tsayuwar me kike anan da sauri ta fice daga dakin bata fi minti uku ba Sai gata ta dawo da ruwan ahanunta jikinta na rawa.
azaton zeenat ummi ce ko auntyta zasu goge mata jiki ,amman sai taga DEENi yakarbi robar ruwan a hannu maryam .
Gabadaya suka fita daga dakin har ummi "tare da kulle masu dakin .

Cikin sanyi jiki ya tashi ya dawo gabanta har yanzu sanye yake cikin shadda fara tas sai kamshin turarensa ke tashi a dakin .

ahankali ya cire farar hular shi ya ajiye gefe sannan yasa hannushi duka ya tattarota jikinsa yaja zip din rigar kasa ya zare rigar jikinta ya ajiye gefe ,take jikinta ya sake daukar kirma gabanta yacigaba da faduwa .
tsoro da mamaki suka taru cika zuciyarta. aranta tace wayyo nashiga uku me yaya ke nufi da cire min riga ? yana nufin shi ,zai goge min jiki .
tana ji tana Gani ya cire mata kayan jikinta tsab har bra dinta .
ta rage daga ita sai zani iya cibiya ,sannan ya zauna tare daurata a saman cinyarsa" ya juyo daita suna facing juna taso tasa hannu ta Kare kirjinta amman kasancewar jikinta bbu kwari yasa takasa aiwatar da komai "dan haka ta runtse idanunta gam.
tana jiran taji ruwa ajikinta Amman sai taji shr ahankali ta dan bude idanunta ,DEENi zaune idanunshi kyam akan kirjinta .
da sauri ta maida idanunta ta rufe dan frigice da tsoro ya dauko towel din ya matse sannan yasoma goge mata saman jikinta zuwa kirjinta da fuskarta , ya dimauce da ganin halitatta kirjinta ,hakan yasa yafi goge mata gurin a tare suka dinga sauke ajiyar zuciya .

can yaji ana nouking din dakin yayi sauri ya mayar mata da rigarta sannan yabada izinin shigowa.
doctor ne yashigo da ledar magunguna ahannushi Yace abata abinci taci tukun sannan tasha maganin.
byn tafiyar doctor DEENI yakira ummi Yace akawo tea, en'uwa dayawa suka shigo dakin "ummi da matar uncle din zeenat ,Maryam har ma da shemah . suka dinga jero mata sannu.

byn sun fita ne taji tamkar kar su fita dan bata son abarta daga ita Sai shi.
hakan na sake frigita zuciyarta .
kadan tasha tea din tace takoshi bai wani takurata ba ,ya ballo magani ya Mike mata ba musu tasa hannu ta karba tasha ,dan tasan halinsa ciwonta bazai hana ya jibgeta ba .
Shiya gabadaya a tsorace take dashi.


MMN SUDAIS
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO



Page 29-30


Byn tasha magani . komawa tayi ta kwanta lomo ajikinsa' tana sakin numfashi sama sama wani iri taji ajikinta lokacin data tsinci kanta kwance kan tattausan jikinsa .
ga kamshin turaren jikinsa gyaraye dana dakin sun buwayi hancinta .
ji take tamkar sukasance haka har abada.
, ahankali tasoma lumshe idanunta har ta rufe su rufff..
bacci ne may nauyi Yayi nasarar daukarta acikin mintina da basu wuce goma ba .


Kyawawan idanushi masu matukar haske da daukar hankali ya zuba mata.
Tare da Kare mata kallo wani zirrrrrrrr ya dinga ji ajikinsa" lokacin daya jita lefe a saman kirjinsa .
da kyar yake jawo numfashin yana fesarwa.
hannushi ya sake kaiwa wuyanta har lokacin jikinta da sauran hucin zafi.
janyota jikinsa ya sake yi .
Tare da ,yasanya hannuwansa duka ya rungume tsam tsam ajikinsa "yana fidda numfashi .
tare da fatan samun saukin zugin da zuciyarsa ke masa wanda shi kansa yarasa dalilin haka.
" Har lokacin bacci take rungume ajikinsa suna musayar numfashin juna mutuwar da jikinsa yayi ne yasashi sake zuba mata rikitattun idanunshi tsawon lokaci yana kallonta
Da kyar yasamu yayo control din kansa cikin sanyi jiki ya zareta daga jikinsa ya kwantar daita ya sake lullube ta da blanket ,sannan ya Mike tsaye yana karkabe jikinsa.

,rigar jikinsa yasoma cirewa ya saura daga shi Sai farar single da wanda shadda.

Wordrob dinsa ya bude ya dauke wasu kayan da zai canza " tare da yashigewa bathroom .


Dakin ya sake dawo byn yagama shirya kansa , cikin farin yadin voyal may matukar taushi da daukar hankali.
Agabanta ya tsaya yana makale links din gaban rigarsa yayinda idanushi ke kanta yana cigaba da kallon fuskarta.

Ahankali ya dinga jin reaction din jikinsa na sauyawa ,yayinda zuciyarsa ke beating tana tsalle tamkar zata bafa masa kirji . wanda shi kansa yarasa dalilin dayasa shi jin haka.
Ahankali ya dauke idanushi a kanta sakamakon
, ji yayi "ana nouking din dakin "yabada umarnin ashigo batare daya tmbyi kowaye ba .
Maryam ce tashigo da sallmarta .
ta gaidashi ya amsa mata a dake .
Cikin sanyi nan nasa
Yakarasa gaban mirrow ya dauki agogon ya daura a tsintsiyar hannushi tare daukar kwalbar turaren ya feshe ilahirin jikinsa ta cikin mirrow din yake wa Maryam magana cikin dakakiyyar " muryasa ki kula daita idan ta farka .idan kika ji zazzabi

15 / 123