Chapter 94 Reading AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt Arewa Novels

AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt

Author :  Aisha Bagudu Category :  Old Hausa Novels

Chapter   94 / 123

279K to 282K   out of 366.6K words

zeenat ya sake baci sosai Amman ta share tacigaba da hirarta da kawarta.

Byn suhaila ta wuce nablah ta sauko .
zeenat ta Kalleta ta Kalli ummi kana tace wlh ummi yarinyar nan makirci take son Kawo mana akan wayan nan shegun yayan nan nata.
da zarar taga anyi baki lokacin tsalle tsallenta ke tashi sbd tasan jarabar yaran bata tashi sai bata gurin salon mutane su gano. ummi dake zaune ta dago idanunta ahankali tace karki ce hk manana yaran ne suke da kulafuci uwa Bari ma junior duk yafisu naci bakiga yanzu su haidar da anan Sun daina wannan kukan ba .sun saba dake.
Allah ummi har da iskancin wanna makirar yarinyar takarasa fadar hk cike da takaici.
duk da nabla najinta Amman tayi shr domin ita yanzu har tafi tausayin kanta akan yaran tazo wucewa hannuta rike da plate din abinci junior da ke faman binta yana kuka .
Tasan may be yunwa yake ji shine ma dalilin saukowarta Kasa sbd kukanshi da yayi yawa aiko zeenat ta sanya mata kafa ta kifa saman junior kadan ya rage bata danneshi ba tayi saurin rungumoshi jikinta yaron yashiga kuka sosai sbd ya tsorata.
itama batasan sanda hawaye yashiga Bin kuncinta ba tana kuka gwanin ban tausayi deeni da fitowarsa Kennan daga daki sannan hkn ya faru akan idanunshi ya zabura yakaraso gurin a sukwane ya rungumesu gabadaya ajikinsa yana jin wani irin radadi a zuciyarsa .
shafa cikin jikin nablah yayi a boye batare da hankalin kowa yakai gurin ba yace bakiji ciwo ba? Kai kawai ta iya daga masa sbd har lokacin deeni ne kadai Yasan nablah tana dauke da ciki wata Shida batare da sanin kowa ba .
shi ne kawai yasan da zamansa..

ummi ma tana zaune tana ganin abinda ke faruwa haushin zeenat ya rufeta Amman batayi mgn ba .

tashin deeni yayi kmr wani zaki yayo kan zeent tana ganin hk tayi byn ummi da sauri ta boye Amman ya fuxgota da karfi wani irin Maruka yasakar mata ajere guda hudu sannan ya Barta .
suman wucin gadi tayi.tana kallonsa hankalinta atashe.

ummi ganin irin abinda deeni yayiwa zeenat ya matukar bata ranta sosai jikinta har rawa yake sbd bacin rai zeenat kuwa cewa da deeni tayi akan wannan yar iska karuwar tsintacciyar mage yar aikin banza zaka mareni ?
Wallahi sai tabar gidan nan yau wani irin kallo yayi mata idan kika km kiranta da karuwa zan Kara miki wani Marin yarinyar data rufa miki asiri a lokacin dakike bukata hkn .
why not kema ki dinga Tausaya mata.talauci fa ba hauka bane hk arziki bame daurewa bane.
wanna karuwar zan tausayawa ya daga hannu zai sauke mata wani Marin ummi ta mike a fusace ta rike masa hannu,gam Ta daukeshi da wani gigitaccen Mari .
gabadaya kowa dake gurin yayi tsit aka shiga kallon kallo daga deeni har zeenat da nablah sautin muryar ummi ya karade parlour yau shine Karo na farko km na karshe da Zaka km Marin zeenat akan wata kana haukani ne ko bawar ubanka ce ita?giyar wake kasha ko me?
yayi shr yakasa cewa komai tmbyrka Nike?
still yaki mgn yarinya tazo har bayana Amman bbu shakka ko kunyata ka fixgota ka mareta .wlh
karka km ta nuna sa da yatsanta kuskureni tayi ni kaina shirin daukar mataki nike akan abinda tayi Amman bata hanyar daka biyo ba.
Tana Gama fadar hk ta damki hannu zeenat tayi dakinta daita tana kuka zeenat na kuka kiyi hakuri kinji mamana sosai take kuka ummi na rarrashinta kiyi hkr duk ke kika jawo komai .
alamarin gabadaya ya cukudewa zeenat da ummi..
Daren ranar dole ummi tasaka deeni agaba da kuka km dole yabawa zeenat hakuri byn tayi masa fada sosai ya fita daga dakin itama nabla jikinta a sanyaye tashigo dakin ta durkusa har kasa tabawa ummi da zeenat hkr inda ummi tace mata yakamata tabasu yaran takama gabanta sbd zamanta a gidan babu abinda yaje jawowa sai fitina yake hadasawa kullun .
nablah ta fashe da kuka ummi na amince zan bar muku yaran ni kaina ina son barin gidan nan Amman nasan matsawar ina son tafiya dole nabarsu.
wlh na hakura dasu gara na barsu naje na cigaba da rayuwarta.
ta Mike tana kuka takoma dakinta ta rungume dukka yaran ajikinta tana kuka suma sunayi.

Tunda ummi tayiwa deeni mgnr tafiyar nablah hankalinsa ya tashin matuka yashiga damuwa ya dinga bawa ummi hakuri.
kiyi hakuri first love kada kirabani daita ki Bari asanarwa zeenat da komai wlh bazan iya rabuwa daita ba first kinsan ina ..ina.. sonta.ya karasa fadar hk bakinsa na rawa Ai sbd nasan kana son nan ta ne yasa nace ka saketa aboye kmr yadda ka aureta a boye batare da sanin kowa ba.
domin koda angayawa zeenat din ma ba adalci zakayi atsakanisu ba,.
meyasa bakason zeenat kmr yadda Kake son yarinyar nan ? Me nablah tafita kyau gata kome?
jikinsa na rawa yace ummi bazaki taba ganewa ba km ni yaushe nace bana son zeenat ko baka fada ba nasani tun ba yau ba deeni .
shiyasa naki amincewa na baka aurenta tun farko dan nasan zalintata zakayi .

ni ummi wani irin zalinci ne baa min ba dan kawai ni banida gata banida ME shigarmi banida ME tausaya min.
ya miki tsaye jikinsa na cigaba da rawa yace ni dai ummi ina son matata km wlh bazan iyawa rabuwa rabuwa daita ba gara kawai ki sanarwa zeenat da komai km kice kece kika shirya komai game da aurena da nablah dan ni ban shiryawa kaina yin AURRIN SIRRI.... da kowace mace ba .sai da tsarinki yakoma ya durkusa har kasa ya tsuguna gaban ummi ummi kiyiwa Allah kiyi hkr ki gafarceni dan Allah nima bayin kaina bane... Hawaye ya zubowa ummi yayi saurin tarewa please ummina ki tausayamin kar ki zubda hawayenki akaina maseeface me girma gareni.
nidai kibarni nacigaba da rayuwa da matana duka km kowace tasan matsayinta....

Shine banaso ai the different is clear Kai ma Kasaan da hk.
km hkn ba me yuwa bane zeenat batason zama da kishiya km bazan cigaba da danne hakkin yarinyar nan nablah ba .
ka saketa kawai. gabadaya ya rude ya marairaice ya dawo wani iri ya daura hannuwansa duka bisa kafafun ummi muryarsa na rawa yace first love nabla wani ciki gareta.... Ummi tayi wani irin zabura ta mike tsaye dafe da kirji tashiga salati tana juya kai.
ta tsura masa ido tana kallonsa ciki fa kace deeni? Ya kada mata kai tmkr wani kadangare ta sake rudewa ummi tashiga damuwa da tashin hankali tashiga zariya a dakin ta kai kawo ya nufo gareta ta tsaida shi da hannuta kada ka karaso gareni deeni hk mukayi da Kai yace kiyi hakuri firfirst lov.
amsa kawai Zaka bani.
yace a,a OK yanzu ban isa nace ga abinda nake son kayi ba.
wallahi ba hk bane ni din banza har yau ban isa na ja da mgnrki ba Amman bazan iya rabuwa da nablah ba.
Da kyar da taimakon Allah yasamu ya shawo kan ummi ta zauna ya dinga bata hkr har ta sauko aka sake kira zeenat ummi tabata hkr shima ya bata hakuri Amman takasa sanar mata da matsayin nablah a gurin deeni wanda daga karshe ta fashe da kuka. Atare deeni da zeenat suke bata hkr.



adaren komai ya wuce tare suka kwana daita. Amman ummi bata Yi wani bacci kirki ba yadda taga rana hk taga dare har zuwa washegari ranar. Ckin damuwa take da daasani.

Cikin Kwanaki duk inda nablah tayi da idanu ummi take binta tana mamakin wai wani cikin gareta har hawaye take zubdawa aboye ta goge Tana tunanin yadda zata bulowa da zeenat da zance ita kanta tsoron lamarin take da tasan hk komai zai cukude musu wlh dabata kawo wannan shawarar ba gashi komai na neman ruftawa dasu.

A wata safiyar byn deeni yagama shirinsa na zuwa Aiki yaso kwarai yashiga dakin nablah yaga halin da take ciki tunda yana tare da yaransa alokacin Amman kememe zeenat ta kasa ta tsare har sai dataga fitarsa sannan ta nufi dakin ummi byn kmr minti goma shabiyar sai ga kiran deeni yashigo wayarta ta dauka cike yauki muryarsa cike da sanyi kmr koda yaushe yace taje dakinsa akwai wanI file din daya Bari a saman gadonsa ga Mathew nan zuwa zai karbar masa.
ta Mike tsaye tana karasa jin abinda yace ta nufi dakinsa kmr yadda yace mata tana shiga taga file din ta dauko ta kira labara ta mika mata kije ki tsaya waje akwai wanda zai zo yanzu kimika masa wanna ta juyo cike da yauki madadin takoma nata dakin sai ta sake koma dakinsa tayi kwanciyarta saman bed dinshi Tana fida numfashi ahankali tana shakar daddande kamshin turarensa ahankali tasoma juyi akan makake gadonsa tana Jin wani irin feelings dinsa can km ta mike zaune ta tsurawa tangamemen hotonsa dake manne a bangon dakin ido tana kallon tsantsar kyawun halitar mijinta.
ahankali ta Mike tsaye jikinta a matukar sanyaye ta tsaya gaban hoton Tana kallonsa tmkr inda an kirasa zai amsa.
Tasa hanuta tana shafa fuskarsa tsawon lokaci ta dauka tana kallonsa tana Kara jin tsantsar kaunar mijinta da kishinsa acikin zuciyarta kafin daga baya ta nufi jikin mirror ta tsaya tana karewa kanta kallo tasa hannu ta dauki turarensa ta fesawa jikinta akan wanda ta fesa haka kawai taji gabanta yayi wani irin mummunar faduwa har sai da zuciyarta ta amsa wasu file file ta hango ta cikin mirrow daga lungu bedside dinsa alamun xubewa sukayi jikinta a mace sannan km zuciyarta na tsananta bugawa takarasa tasa hannu tazaro su duka ta zauna kan bed tana shiryasu daya byn daya cikin hk idanunta ya sauka akan wani farar takarda .
tasoma warwareWanna ahankali cike da matsanancin faduwar gaba Tana dubawa rassss gabanta yayi wani irin mugun bugawa da karfi ta zaro idanunta waje sosai tana sake kallon takardar da kyau tana juyawa tana sake karantawa gwajin ciki ne dauke da Sunan nablah ajikin taksrdar ta mike tsaye jikinta na kirmmma.
take wani irin gume ya rufeta tashiga tunanin yadda akayi takarda gwajin ciki dake dauke da sunan nablah dakin mijinta .
ahankali komai yashiga zuwa mata daki daki kwalkwaluwarta ta dauki caji tundaga zuwan yarinyar gidan matsayin me aiki har zuwa cikinta na farko da yaranta da kamaninsu da mijinta. sosai jikinta ke rawa gume ya rufeta sosai tashiga tsiyaya wani irin razananniyar ihu tasaka kardai deeni kwana yake da yar mutane agidan batare dasanin kowa ba idan dai abinda take tunani hk ne zina Kennan yake daita komai?
take ta fito daga dakin a haukace ta nufi dakin nablah.. Tana shiga dakin ta sameta kwance jikinta sanye da Wando three Guater da riga whit harmless ta shan iska kanta babu komai gashinta kwance ya zubo har gadon bayanta cike da natsuwa Take shirya kayanta na barin gidan .
yaranta zagaye daita sunata zuba mata surutu irin nasu na yara.amman banda junior wanda yayi shr yana kallonta dominshi fitinanne miskili ne sak ubansa har halinsa babu abinda yabari.
bata tsaya wata wata ba tayi kanta nablah naganin yanayinta hankalinta ya tashi ya Mike tsaye da sauri tana kokarin daukar hijab dinta.
zeenat ta fixge a haukace ta damki wuyanta tayo waje daita kiiiiiiiiii tasoma janta Dan ubanki sai kin gayamin ubanwa yayi miki ciki ?

wani cikin a gidana ummi
Takwallawa ummi kira tana jan nablah da iyakancin karfinta wlh sai kingaya uban da yayi miki ciki ?gabadaya yaran suka rikece suma sukaga binta suna kuka
daidai wannan lokacin motocin deeni dana escort dinsa sungama danno kai cikin estate har sun faka motocinsu wani daga cikin escort dinsa ya fito da sauri ya bude masa motor ya fito da kyar tare da alamun gajiya ataredashi yana tsaye yaji gabansa ya fadi yashiga duka uku uku .duk esoct dinsa da derebobinsa zagaye dashi yasoma takunsa cike da natsuwa suna biye dashi wanda kaida ne sai sun Dan ganashi da kofar shiga gdansa suke juyawa .
zeenat wacce idanuta suka gama rufewa da tsabar tashin hankali ta bude kofa da karfi ummi dake saukowa takara hanzarta saurinta tana dakatar daita da kiran sunanta da tmbayarta abinda ke faruwa Amman ina zeenat batama san abinda ummi ke fadiba .
ta hankada nablah habar gidan da iyakacin karfinta shi km deeni ya kawo kai sai saman fadadden kirjinshi yaran sukayo gurin deeni da nablah suna kuka..............fitar min daga gida daga ke har yaranki bana son yaran ki kwashi tsiyarki ki fita daga gidan........







mmn sudais ce
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—
AUREN SIRRI
πŸ’–πŸ’–πŸ’–
πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—πŸ’—




AYSHA A BAGUDO


Dedicated to
Hauwa A usaman
Jiddar



🌈Kainuwa writers association


Page 104


Jin furuncin zeenat dake shiga cikin kunneta yasa tasoma yin Kasa kasa daga jikin deeni kadan ya rage bata zame ba yayi sautin tarota Amman ki yarda ta tsaya bisa kafafunta dole tasa,shima ya bita yana sake rungumeta ajikinshi
yaranta gabadaya suka sake yowa kanta suka kamkameta suna kuka .
ummi najin abinda zeenat ke faman fada tana kuruwa da zunduma ihu..... gabanta ya yanke yayi wani irin mummunar faduwa ta karasa fitowa waje da saurin maseefa.wanda har hankalin jama'ar dake cikin estate din yafara yowa kansu dan wasu daga cikinsu MA har Sun fara lekowa ta balcony suna kallonsu.
Idanun ummi suka sauka akan deeni dake durkushe rungume da nablah ajikinshi ....
kallo daya zaka masa Kasan hankalinsa a matukar tashe yake .
Sanann km take zaka gane yana cikin tsaka ME wuya.
ahankali ya dago rikitattun idanunshi ya zubawa ummi yana kallon da mamaki A saman fuskarshi .
suka hada ido da ummi wace yanayinTa kawai mutun zai kalla ya gane irin kallar tashin hankalin datake ciki.
Kallonta yacigaba dayi yana zafi cikin zuciyatsa da gangar jikinsa Wato Tana kallon zeenat ke shirin Yi masa aika aika agida batare data ta tsawarta mata ba ....
ya runtse rikitattun idanunshi yana me jin tsantsar takaicin abinda umminsa kema masa ahalin yanzu..
dakewa kawai ummi tayi tamkar bataji duk abinda ke faruwa ba tare da Nemo jarumta ta sanyawa jikinta ta dauke idanunta akan deeni kana muryarta na shaking tace zee..zeenat lafiya meke faruwa ne?

A haukace muryar zeenat na rawa jikinta na wani irin tsuma tace ummi wannan yarinyace ta km yin ciki a gidan nan har na tsawon wata shida ummi idan da ance kb NE to yanzu cikin uban waye ajikinta ? Tunda dai kb yabar gidan nan.....


banda kuka babu abinda nablah da yaranta ke faman yi .
yaran kuwa sai faman tsallara kuka suke ganin uwar su afrigice tana kuka yayinda deeni dake rungume daita yasake kamkameta tsam ajikinsa yana shafa bayanta da tafin hannushi gabadaya ji yayi sararin samaniyya da inda yake durkushe na jujjuyawa dashi.yarasa wace irin masseefa da tashin hankali ke tattare da zeenat ....
Yarasa wani irin kishin hauka gareta .
sanadinta yarasa abubuwa dayawa. Yarasa kulawar mahaifiyarsa da soyayyarta yarasa farincikinsa yarasa jin dadin duniya duk wani farincikinsa kokari take taga tadagushe masa . yayinda kwata kwata batada wani amfani agareshi yarasa abinda take nufi dashin ? Farincikinsa ta haifa masa ya'ya takasa wanda yasamu km tana neman ganin bynsu tare da sabautasu ummi na zaune tana kallo ta daure mata Gindi .
yaya ake son yayi darayuwarsa ?
Tsuma kawai yake jikinsa na kirrrma yana jin tamkar ya Mike ya sabauta mata jiki da mahaukacin duka ko zai ragewa kanshi takaicinta....

itako nablah gabanta ne ya sake yin wani irin matsanancin faduwa da karfi .
Wani irin bugawa kirjinta keyi da sauri da sauri yayinda zuciyarta ke suya da harbawa...ganin kuka bazai fishsheta ba yasa ta tasaka iyakacin karfinta ta fexge jikinta daga jikin deeni .......

jikinta na kirrrrrma ta dubi zeenat ta furta kalmar ciki.

Ciki fa kika aunty ? Meye hadina da ciki km ahalin yanzu?
takarasa mgnr tana kuka ta girgiza Kai.

Eh munafukar Allah ciki ne dake km wallahi sai Kin sanar Dani uban da dayake dirka miki ciki a gidan nan batare da saninmu ba .

deeni ya Mike tsaye da kyar jikinsa a sanyaye Tare da cire long sleeve din dake sanye ajikinshi ya sanyawa nablah.
har ya saka mata rigar hankalinta bai jikinta burinta kawai taji duk abinda ke fitowa daga bakin zeenat yazamto karyane ba gaskiya ba.ya tareta sosai da fadadden kirjinshi ta yadda bbu me ganinta kana
yasoma aikawa escort dinsa da derebobinsa da securities din da suka dan taso domin ganin tashin hankalin dake faruwa.
da wani irin kallon kasa kasa me kama da tsayuwar uwar me suke masa agurin tare da nuna musu hanyar biiiiiiii da yatsansa ...... dan kwata kwata takaicin wulakancin abinda zeenat tayi masa ya hanasa furta daidai da kalma daya ce .......
aiko take suka juya gabadayansu km bbu wanda ya sake juyowa acikinsu..
hankali nablah a matukar Tashe ta nufi
Gurin wannan takardar da zeenat ta jefar ta dauka jikinta na kirrrrma Tasoma karantawa tabbas sunanta ne rubuce cikin farar takardar dauke da ciki har na tsawon 6 months.
innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai nablah ke maimaitawa ta juyo da sauri tana duban deeni dake tsaye still yana kareta daita da jikinshi.. tsuru tayi masa da ido kawai tana kallonsa hawaye na tsiyaya daga idanunta kafin daga baya ta juya tana kallon zeenta da ummi wasu tsiraran hawaye Masu dumi suka shiga kokuwar biyo kuncinta ta dawo tamkar wata mutun mutumi atsaye a gurin.

ahankali km ta daga idanunta sama Tana kallon sararin samaniya alamun son tuno wani abu dangane da rayuwarta .. sai lokacin komai ya dawo mata....

94 / 123