Chapter 8 Reading AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt Arewa Novels

AUREN SIRRI Book 2 Complete by Aisha Bagudu.txt

Author :  Aisha Bagudu Category :  Old Hausa Novels

Chapter   8 / 123

21K to 24K   out of 366.6K words

yace yanzu me kika gani idan kin amince , magana zata wuce gurin big dady kai tsaye batare da bata lokacin ba .
ta tabe bakinta kmr batayi murna dajin zance ba , sannan tace gaskiya kagaya masa kawai yayi hakuri dan ni narigada na tsaida wanda zan aura ,.

fk yace waye shi km a ina yake km kin kai maganar wajen big dady ne ? Duk alokaci yajero mata tambayar ,tace Ko daya muna dai shirin yin haka fk yace yace shi din wanene tace wani ne acikin family dinmu yake humm yace inbaki shawara ta daga masa kanta" zan so ki dakatar da koma waye.
dan kowa zaki aura ina tabbatar miki ba zai taba kai kmr DEENI ba .

ke kanki kinsa samun irin su DEENi sai an tona. zakiyi alfahari samun mijin kmr sa "mata dayawa suna ,sonshi ban sani ba kodan sun fahimci qualities dinsa ne .
sai km yace amman bazan takura miki ba in kinga bakison shi Shikenan .
ta kalleshi a shashance hade da wani irin salo sannan tace nifa bance maka bana son shi ba na dai kawai kace masa na tsaida wanda zan aura .
Kaga yanzu idan na canza raayina da sauri haka shi saurayin nawa bazai dadi ba .
ka dai bashi hakuri Allah ya hada kowa da rabonsa na alkhari .

fk yayi shiru yana cizan yatsa hankalinsa yasoma tashi "karfa yarinyar nan ta kwafsa masa yazaci yana mata zance zata amsa da murna ya fadi haka a kasan ranshi.
can km yace to ni yanzu mekike son nace masa ?

Ta sake tabe baki yace Kafada masa gaskiya kawai , yace ba za kiyi tunani akai ba kafin ki yanke hukunci ,ko km kuje kisamu wanda kika san kin amince mata km tasan deeni din sosai tabaki shawara akai, Zeenat tace naji zanyi tunanin .

Fk Yace Shikenan zan sake nemeki zuwa gobe naji abinda kika yanke akai , tace badamuwa .

Byn ya tafi, ne tashiga dakin ummi tana murna cike da farincikin burinta yakusan cika ,fitowar ummi kennan daga bathroom aiko tana ganin yanayinta da alamun tace musu ta amince ,take ta sake daure fuskarta , ta rufeta ta fada, ai gashi nan saboda baisan darajarki ,da kimarki ba sannan bai dauke ki da mahimmanci ba ,yakasa zuwa da kansa sai abokinsa ya turo miki nasan jikinki na rawa kika amincewa ko ?.

Zeenat taaba fuska tamkar zata saki kuka tace nifa ba wani rawar jikin danayi .
ummi tace wlh kiyiwa kanki fada, akan sakarcin da kikeyi ke kmr ba macce ba .
sam bawani jan aji irin na sauran mata .
Zeenat ta sake bata rai sosai .
ummi tace gaki nan ga deeni ,inda shine nabarki dashi ya isheki wando da riga .


A waya DEENi yaji duk yadda sukayi ya dinga mamaki wai wannan yar yarinyar ce zata ce sai tayi shawara to dawa zatayi ? Km ita ce wa ?

Fk yace itace mace deeni yace dan Allah malam imin shiru shiya sa fa kaga bazan iya kai kaina gareta da sunan Ina sonta ba bare tamin salo . Nan km yau zazzagawa fk maseefa yana Ai shi yaja masa duk wulakancin da'aka masa fk yace kwanta da hankalinka kavarni daita kawai nasan zata yarda ma kawai dai itama so take ta nuna mana itama macce .
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO


Page 19-20



Shiyasa kaga bazan iya kai" kaina gareta ba da sunan Ina sonta , bare tamin salo .

Nan km yayi ta zazzagawa Fk maseefa hade da cewa ai shi yaja masa duk wulakancin da'aka masa .

Fk yace kwantar da hankalinka kabarni daita kawai ,nasan zata yarda ma ,.
kawai dai itama so take ta nuna mana ,itama macece , nasan jan aji ne kawai na mata Amman ita din wa dazatace bata sonka ,Ina rai inshallahu zamuyi nasara.

Cikin fushi da jin haushi deeni Yace in taki yarda ka kyaleta kawai , yarinya sai kace wata gold sai wani yawo akamin da hankali akanta, yaja tsaki hade da kashe wayar batare daya sake jin abinda fk zai ce ba .


Kwana deeni yayi da tunanin hade da zullumi halin da zai tsinci kansa idan yarinyar nan taki yarda dashi, duk shi Gani yake ba sonta yake ba. zai dai yi aure ne kawai saboda umarnin umminsa, bugu da Kari ma, bazai iya kaskantar da kansa wajen mace ba ballanantana har ya kai shi ga furta kalmar so.

Har zuwa wayewar garin ya cigaban mamakinta ganinta yake , tamkar yau aka haifeta, sannan har zuwa yanzu kallon karamar yarinya yake mata, ashe tasan abinda take yi ,uhmmmm uhmmmm ahankali ya dinga sauke ajiyar zuciya, wai zatayi tunani akai ya sake tunawa da kalmar data fadawa fk to da ko da uban wa zatayi tunani ya furta hakan a kasan rashi .


kwance take akan bed din ummi Amman ba bacci takeyi ba ,hannuta rike da wani English novel mai suna ,mumy why sanye take cikin kananan kaya, pencil jeans da riga iya gwiwa a natse take karatunta dan tana jin dadi labarin yarinyar ciki litattafin ta birgeta kwaira ,ta yadda take kokarin kwatarwa kanta enci saboda mahaifiyarta ta hanata auren saurayin da take son ..
Cikin isa da kasaita yashigo dakin , tana jin motsen bude kofa Amman tashare dan batason abinda zai katse mata karatunta .

Jin kamshin turarensa yasa ta dan dago idanunta suka sauka akansa , ganinsa yasa ta dan mike daga kwanciyar datayi, tasha jinin jikinta bata san meke sata jin yawan faduwar gaba ba, a duk sanda taga yaya DEENi .
ta gaidashi batare daya kalli inda take ba , ya amsa mata a ciki ,km cikin isa da takama sannan a takaice , tamkar dai yadda yasaba dan baya son duk abinda zai sa magana tayi tsawo atsakaninsu .
sai dai ita kam tsintar kanta tayi da zuba masa idanunta, tana binsa da wani irin mayyen kallo , cikakken namiji ne sosai mai ji da kansa , ko a tafiyarsa zaka shida haka. gabadaya bbu wata alamun ragwanta atare dashi .kana ganinsa zakaji ya birgeka ,daman aikin da yakace shi kennan wato jami'in tsaro .

Har suka gaisa da ummi dake tsaye fitowarta kennan daga bathroom ya juya da niyar barin dakin, idanun Zeenat na kansa tamkar zata ya dawo ya zauna kada ya fita saboda tsoron masu farautarsa ,takasa dauke idanunta daga kallonsa take taji wani irin masefaffen kishinsa ya diram mata zuciyarta ta dinga rawa bata idanunta a kansa ba sai data daina ganinsa .

Ummi tabita da kallo tausayi tace inkin gama kallon nashi sai ki tashi ki hado masa abinsa ko kawai soyayya aka iya ba'asan tattali ba , Zeenat ta dan turo baki tace ni dai ummi kwanan bansa abinda na miki ba komai nayi sai kin min fada, ki dinga ganin laifina , nifa bashi nake kallo ba , ummi tace eh ai nasan bashi kike kallo ba kuruwarsa kike kallo jairar yarinya kawai ni tashi ban guri .

Washegari

Zeenat tarasa dawa zatayi zance yaya DEENi taji dadi kuma yaba shawara tamkar yadda zuciyarta ta aminta dashi ,ganinta duk wanda ta nufa da maganar baza tasamu goyon baya ba ,kmr dai yadda ummi tayi ,
Maryam ce ta fado mata a rai ,dan haka tashirya taje har part din su.

Tana shiga part din idanunta sukaci karo da fuskar data tsana a halin yanzun arayuwarta ,kmr ta juya ta koma haka taji , shemah ta hango zaune akan three site suna hira da Maryam take taji wani iri abu ya caki zuciyarta .


ganinta yasa taji tamkar an soka mata kibiya ne a kahon zuciya taja ta tsaya takasa karasawa inda suke dan baza juri zama a duk inda take ba , ganin haka yasa itama shemah ta mike ta fice Tama bar part din gabadaya . Da kallo Maryam tabi kowanne su
Ahankali Zeenat takaraso tasamu waje kusa da Maryam din ta zauna zuciyarta a cunkushe , tsawon lokacin takasa cewa komai , Maryam tace wai yana ganki haka ne ? Cikin nishadi Maryam ta soma janta hira har Zeenat ta sake Sosai
Daga nan ta labarta mata duk halin da'ake ciki ,.

Maryam ta zaro idanu waje tana mamaki tace kai da gaske kike ,to Ina girman kan nasa km?
Zeenat tace yana nan bai je koina ba" sai ma abinda yakaru ,

Maryam tace in fada miki gaskiya,zeenat ta daga mata kai alamun eh "ki amince kawai" karkiyi wasa da damarki domin mata dayawa suna can suna neman miji irin yaya DEENi
basu samu ba.

amman idan kin yi saken da kika tsaya yauki ,wai ke jan aji ,kya zo daga baya kina nadama dan irinsu tsada ne dasu ,.
kin dai san halinsa da maseefar zuciyar tsiya.
maryam takarasa zance da
Uhmmmm .. Ina ma ni Yace yana so ......

jin haka yasa take Zeenat ta hade fuskarta tamau , hade da zabgawa Maryam din wata uwar harara tace kefa Yar wulakanci ce bangane dama ke yace yana so ba Maryam tace ke nifa da wasa nake dan baga kmr kin fara hassala Zeenat tace ,wani irin wasa wannan, nifa banson shirme bazan.
Ko kema zaki shiga layin shemah ne?

Maryam tayi murmushi tace bada dai Ai tsakaninmu bbu haka yauwa naji ance ma kunyi fada da shemah Kwanaki ?

wai may ya hadaku fada ne , Zeenat ta tabe baki tana sauke ajiyar zuciya sannan tace shirme tamin irin naki .
nan dai ta zaiyanewa Maryam komai ,suka tafa suna kyalkyale dariya Maryam tace kai tawan kina wuta , Zeenat tace Ai ni bata wasa bace ban daukar raini tuni nagama daita duk da batasan abinda tamin ba har yanzu.

Maryam ta sake bata hannu suka taba, tace baki da kyau fa" sai dai idan ba'a tabo ki ba.
Maryam tacigaba tawan ki Amince kawai da auren nan musha biki amman fa zakisha fama da wannan miskililin ,Zeenat ta sake yin murmushi tace indai zai cigaba da sona kmr yadda yake yi yanzu Ina ruwana da wani miskilancinsa can yakarata , ai abinda yafi ma birgeni dashi kennan.
Amman nasan wuyarta dai ayi auren da sannu zai rage duk wannan jin kan nasa .


Zeena ta kagu dare yayi saboda cewar da yaya faruk yayi zai dawo .
,tun tana Jiran zuwansa har ta fida tsammani dan tara tayi gabadaya hankalinta a matukar tashe yake,t unaninta kar dai ya deeni ya hakura daita kmr yadda tace abashi hakuri.

zuciyar tashiga rawa tamkar zata tsinke ta mike tsaye cikin sanyi jiki tasoma zariya duk dai ummi biye daita da kallo can Ganin goma tayi yasa ta nufi dakin ummi tana shiga ta fada kan gadon tana zubda kwalla,.
ahankali tace Allah Allah kasa ba hakura yaya DEENi yayi ba ,.
dako na cuci kaina da kaina tashiga zubda hawaye baji ba Gani tana jin zuciyarta na neman taewatsewa tace Allah ka tausayin ka jin kai na ka mallakamin abin kaunarta deeni ina sonka deeni tunda ka furta kana sona nakasa samun sukuni dan karkace ka fasa kuka take sosai hade da sambatu ,,.

Shadaya daidai ummi tashigo ta dubi inda Zeenat take kwance taga alamun kmr bata jin dadi karasowa yayi tace ke lafiyarki kuwa da kyar Zeenat ta iya bude bakinta,t ace kaina ke min ciwo ummi tace shine zaki zauna kina kuka ,tayi mata sannu taje takawo mata magani .

Wasa wasa sai da Zeenat tayi kwana biyar cur batare da taga zuwan yaya faruk ba.h hakan yasa hankalinta sake tashi fiyye da koda yaushe .
cikin lokacin kadan ta zabge ta sake ragewa zazzabi may zafi ya rufeta, jikinta ya dauki zafi gwau , hankalin ummi yatashi , da Ganin halin da Zeenat take ciki kmr zatayi kuka.
Ummi ta kira likitan dake duba su, wato family doctor dinsu , byn yazo ne yasoma aikinsa cikin sauri ganin yadda Zeenat din takeyi taki magana sai zubda hawaye kawai take ga zuciyarta na buguwa da sauri da sauri Ganin haka yasa doctor din ya dauko abin awo ,ya auna BP dinta ,cikin mintina da basu wace ashirin ba ya gano abinda yake damunta sannan ya daura ma drip hade da sanya allurar bacci ciki take ko bacci yayi awon gaba daita .

Gabadaya hankalin Ummi ya sake tashi wani irin tsoro ne yashigeta lokacin daya ,da sauri tace doctor meke damunta ?
doctor yayi shiru yana nazarin abinda zai cewa Ummi kafin daga bisani ya numfasa ,sannan Yace akwai abinda tasa aranta wanda shine yayi dalilin haddasa mata damuwa har takai jinita ya hau sosai , Ummi ta sake maimaita abinda doctor yace , doctor yace Amman inshallahu bbu da damuwa zata samu lfy da zarar ta tashi komai zai yi dade, ummi tace to doctor na gode yayi mata sallama tare da gayamata yadda zata bata magani.duk wannan drama da akeyi deeni bai sani ba dan ko yashiga gaida Ummi baya damuwa daita ballantana yasan ko bata da lfy ne ,ita Kuma da haushi taki sanar masa Ai shi ba makaho bane

Kwata kwata Fk bai samu damar zuwa ba sai acikon kwana na bakwai tukun yazo ,yasamu Zeenat din bayadda take yayi mamakin , yadda DEENi bai sanar masa ba gashi kusan kullum sai sun hadu .
byn sun gaisa da ummi ne ,ya fita Yace Zeenat din ta same shi a parlour .

Cikin tsanyi jiki ta mike tasoma daga karta da kyar, cikin gimtsewar fuska ummi tace Ina km zaki kefa bakida lfy ?
Zeenat tabata fuska dan kada ummi ta hanata zuwa tace ummi sako zan karbo gurin Yaya faruk ,yanzu zan dawo , Ummi ta bita da idanu kawai Zeenat tace ummi sai nadawo cikin jin haushi da akaici Ummi tace kada ma ki dawo ki kwana a can .


Da sallamarta tashigo parlour "Zaune ta same yaya faruk din suka gaisa ya sake yi mata ya jiki sannan Yace sister kiyi hakuri dan girman da rashin zuwana kmr yadda nace, wasu abubuwa ne suka sha kaina wlh, dan haka yanzun naxo naji abinda kika yanke,zeenat ta danyi shr kmr mai nazari Yace kada ki damu idan har baki son shi , kisanar dani ,danshi yace idan baki amince ba, kada atakura miki shi ya hakura, a dan frigice tace Ai yaya kaima kasan bazan iya cewa banason shi ba, ko dan ummi dan haka kace masa kawai na amince .


Fk ya saki murmushi murna yayi hamdala a zuciyarsa hade da godiyar cin nasara yace Shikenan ni zan wuce sai kin jimu .

A ranar ummi ta nemi ciwon Zeenat ,tarasa duk tana zargin ciwan nata bazai wuce akan DEENi bane ,da daddare har nafila Zeenat tayi dan Mika godiyar ga Allah. ummi tayi murmushi tace yau km ibadar ce ta motsa har da sallar dare ?

Zeenat tayi mata banza kmr bataji ba tacigaba da sallarta, Ummi ta sake cewa Allah yasa a dore in km nasamun NASURULDEENI ne nasan daga yau Shikenan .

Abinda ke sake bawa Zeenat mamaki bai wuce Ganin yadda kullum yaya DEENi ke nuna ko in kula akanta ba gabadaya ma Gani take kmr baisan da zamanta ba .
ko magana ta fatar baki bata hadu su, idan ma yana guri kennan ita kanta batason zama in da yake yanzu ,Allah Allah take tabar wanje dan juriyarta takusan karewa .


Fk bai samu ganin deeni ba, sakamakon wani aiki daya taso masa ,Amman Yace masa yabari zuwa weekend ,ya same shi a gida .sai da fk yakirasa a waya ya tabbatar masa da yana gida sannan yazo .
zaune suke cikin parlour deeni byn sun gaisa fk yayi masa bayani duk yadda suka yi da Zeenat a boye DEENi ya sauke ajiyar zuciya ,sannan Yace ta taimaki kanta da kanta , kennan , fk yabishi da wani irin kallo sannan yace kai fa dan rainin wayo ne abinda yakamata kace kennan, deeni Yace nifa bawai na matsu dole sai ta amince da aurena bane .
asalima ita din ba irin kalar type dina bace zan dai aureta ne kawai ,a rashi samun choice dina fk ya saki baki yana kallon deeni ,Yace Amman friend kasan itama tana kyawunta daidaina , sai da ya dauki lokacin sannan yace ni nace maka dan kyawunta zan aureta?
Ai bata da kyawun da zai rudeni ,km wlh har ga Allah da bata amince ba na hakura , har zuwa sanda zansamu type dina.

MMN SUDAIS CE
💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗



AYSHA A BAGUDO



Page 21-22



Wani irin kallon mamaki fk yake masa , ,gabadaya ya zamo tamkar mutun mutimi a zaune a gurin ,

Yarasa meke damun brain din DEENi , mutun Sai girman kan tsiya da nuna isa " wai shi DEENi wani irin bahagon mutun ne ?
Shi sam bbu ruwan shi da fadar duk magana da tazo bakinsa .

In a low voice

8 / 123