Author : KARIMA TIJJANI MANSUR Category : Romantic Hausa Novels
Auntie.'
"Um, game nakeyi"
'Auntie tayi murmushi.'
To kada ki k'ara d'aukar mata waya.'
"To"
"Ta dafa kafad'arta.'
Tashi maza ki deb'o kayanki kinji, gida na zaki je, tun da yanzu bakya zuwa makaranta.'
'Hafsah bataji dad'in hakan ba, ta mik'e babu k'wari ta fara debo kayan daga cikin drawer.'
'Shaf ta manta da ledar nan ta Yusuf, aiko tana dakko wasu kaya, ledar ta fad'o.'
'Mama tayi saurin d'aukar ledar cikin rud'ewa ta ke cewa Auntie kin gani koh, ai mai hali baya fasa halinshi."
'Auntie ta karb'i ledar ta bud'e, sai taci karo da kwalin wayar mai tsadar gaske wato, 'IPhone' a ciki, sai wani tsadadden agogo, sai turare mai tsadar gaske, sai kuma, 'Greeting card'
'Auntie ta mayar da kulle ledar dama rubi biyu ce.'
'Hafsa ta gama shirya kayan sannan ta kulle akwatin, tasa hijabi, suka fito dukansu.'
'Auntie tace maza ki kai kayan cikin mota.'
'Ta ja akwatin tayi waje inda drivern auntie take.'
'Auntie ta kalli Mama bayan fitar Hafsah, "Ki bar komai a hannuna, ba wani abin tashin hankali bane ina zatan kyauta aka kuma bata, in sha Allah komai zai yi daidai.'
'Mama tace "Toh"
Ina wayarki kira Abbanta zanyi mishi bayani da kaina.'
'Mama ta danna kiran, bayan ya d'aga "Hello, barka da rana, ya aiki."
"Alhamdulillah, aiki yasani gaba."
"Allah sarki to "Sannu da k'okari."
"Yawwa."
"Dama, Auntie Nafisa ce tazo tana son kuyi magana ne."
"Okay to bata wayar."
"Sun gaisa sannan ta ce, nazo ne kuma sai Amina keyi min k'orafi akan Hafsa, to shine ina so abani ita don Allah in tafi da ita tayi koda sati ne a wajena."
'Abba bashi da matsala da ita, kuma yasan ta macece jajirtacciya,kuma
babba ce, don haka yace, "babu komai ai, yayi kyau wallahi, na gode sosai."
"Sai dai Don Allah kada a barta ta kula duk wanda yazo wajenta, kuma kada ta dinga yawo."
"To in sha Allah, na gane babu komai ai."
"Yawwa, wani yaro ne yake son wargaza mata lissafi."
"Auntie tace
"Eh na fahimta, yaran yanzu ne babu abinda suka sani sai soyayya."
"Wallahi kuwa, Allah ya kyauta ya shige mana gaba."
"Ami'n inji Abba, to nagode fa, agaida alhajin."
"To zaiji in sha Allah."
'Ta, kashe wayar ta mik'awa mama.'
"Ki dinga yi mata addu,a, amma wannan ba wata matsala ba ce Babba, kinga shi baban nata ai ya fahimci komai."
"To auntie, nagode."
"To bari mu wuce."
'Auntie tace sanda Hafsah ta shigo.'
'Mama ta taka musu zuwa bakin gate.'
"Mama mun tafi."
'Inji hafsah.'
'Maman ta saki fuska sosai to hafsah in kuma auntie ta rik'e ki shikenan sai ki zama bak'uwa."
"Hafsah tayi murmushi, taji dad'in sakin fuskar da mama tayi."
'Suka shiga mota suna daga wa mama hannu. Driver yaja suka tafi.'
'Hafsah taji kamar tayi kuka, bata tab'a yin tafiyar data wuce kwana biyu, shima gidan Hajiyah take zuwa, amma taji auntie tace wai sati biyu zata yi..'
'Gaskiya zatayi kewar jama,ah da dama..
'Amma haka dai, zata hak'ura.'
'Sai kuma kalaman yusuf a text to kenan Abba ya kirashi,?? To me yake nufi da ita, da yake cewa wai tafad'awa abba koh..??
'Lallai ma Yusuf,
Allah yaso ta sa number a blacklist, bayan shigowar text d'in saboda tsoron kada ya kira Mama.'
'Ta jingina jikin kujera, tana tunano ya zata kasance idan Yusuf ya guje ta...
Shikuma driver sai gudu yake kan titi har suka isa unguwar Kabuga, inada gidan Auntie yake..'ππΌππΌππΌ
*TO ALHAMDULILLAHI READERS, FANS, ANAN MUKA GAMA KASHI NA D'AYA NA WANNAN LITTAFI SAI KU JIRA KASHI NA BIYU, DOMIN JIN YA RAYUWAR HAFSAH DA YUSUF ZATA KASANCE.'??*
*A cikin..*ππΌππΌππΌ
β₯β₯β₯β₯
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin Kwarai)
ππ
ππΌππΌππΌππΌ
*'Jikar waziri Ahmadu dai..!!*ππΌ
*(HAJEEYAH KAREEMER)*
β₯β₯β₯β₯
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin K'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
ππ
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members*
π *36*
*BAYAN SHEKARU SHIDDA.*
*Katafaren* d'akin, taron 'Meena event center,' ya k'awatu sosai, an cika ana jiran shigowar ango da amarya da ango.
'Tana zaune a nasu table d'in.. Ita da sauran k'awayenta.. Babu jima wa ango da amarya suka shigo tare da rakiyar k'awaye da abokai..'
'Alokacin ne kuma biki ya kankama, aka fara lik'i da rawa."
'Tunda tazo wajen bataci komai ba..
tayi kyau cikin ankon bikin na atamfa da peace d'in head.'
'A can b'angaren abokan ango kuma.. rawa suke casa, kasancewar Mc, ya basu fagen.'
'Kana ganinsu kaga wayayyu maza ajin farko, sam basu da hayaniya, rawar ma ba wani yinta suke bilhak'k'i, ba. Sai kudad'e 'yan dubu dubu, da suke ta yin ruwan su.'
'Ahankali angon ya jawo wani daga cikin su, ya dafa kafad'ar shi, yai mishi rad'a a kunne,
"Mene haka ne please ka saki ranka don Allah kada wannan abin ya b'ata maka rai.'
'Ya lumshe idonshi a hankali ya bud'e.'
"Ok, but kasan dole ne fa abin ya dameni, matar nan fa taci mutunci na.'
"Na sani amma ka share please kada ka damu kaji? Kaje ka zauna ka sami nutsuwa."
"Ok.
"Baya ya wuce yana duba 'sit' d'in da babu mutane sosai, amma ko ina da jama,a, gashi tsarin duk na mata da maza aka cakud'a a kowanne table '
'Yaja siririn tsaki lokacin da ya isa daf da table d'in da Hafsa take, bai wani lura da su wanene akan table d'in ba, amma yasan dai matane su uku kawai.'
"Tunda ya zauna ya dafe kanshi da hannunshi.'
'Sauran 'yan matan ne su biyu suka mik'e, don jin cewa, an buk'aci k'awayen amarya na school da su fito suma.'
'Itama Hafsa mik'ewa tayi ta bisu tana cewa,
"Anisa, bari nima na biku, nayi lik'i.
'Sai da suka fara tafiya sannan ya d'ago kanshi.'
'Ya sauke ajiyar zuciya, yana kiran sunan Allah a zuciyarshi, a hankali ya fara jin nutsuwa na saukar mishi.'
'Sai lokacin ya tuna rabonshi da abinci tun safe, gashi yanzu har k'arfe shida saura kwata.'
'Hafsah tayi wa amarya lik'i tare da yi mata fatan alkhairi, sannan ta nemi da su Nabila su taho su koma wajen zamansu. 'Amma sukace mata ai su sai sun ca she.'
'Dama bikin wata 'yar ajinsu ne da suka yi degree tare da ita.'
"No nidai gaskiya i can't dance cikin wad'annan gayyar mazan kawai ni na tafi, ku sameni acan.'
"Alright"
'Inji Nabila tana tsokanarta ke kin fiya kunya wallahi.'
'Bata kula su ba ta wuce ta dawo wajen zamansu.'
'Tun da take takowa yake kallonta ita kuma sai taji kamar ta sauya waje saboda su kad'ai kenan zasu zauna a table d'in.'
'Zata wuce shi kenan taji yace a hankali,
"Nop, ki zo wajenki ki zauna babu matsala."
"A hankali batare da ta kalleshi ba ta zauna a kujera dama da shi amma tabar tazarar kujera d'aya a tsakaninsu.'
"I hope ban tsare miki guri ba."
'Ya fad'a cikin taushin muryar da taji sanyin ta har cikin ranta.'
"Ta girgiza mishi kai ahankali kawai."
'Su kayi shiru na d'an wani lokaci yayin da shi yake aikin kallonta.'
"Ita kuma duk bata jin d'adin zaman wajen so take kawai ta tashi."
'Gashi karo na wajen uku kenan tana jin ringing d'in wayar shi amma a yadda ta lura ko kalla bai yi ba bare ya d'aga.'
'Wasu maza ta gani wajen su biyar cikin abokan ango sun nufo su.'
'Suna k'arasowa da'ya ya zagaya bayanshi ya dafa shi, sannan ya fara yi mishi magana.'
"Please ukasha ka share abin nan don Allah, meye zaka sawa ranka damuwa.? Please feel free mana."
'Shiru shi dai baiyi magana ba.'
"Daya daga cikin su ne yace " ka bari a gama harkar bikin nan, zata gane kuranta, amma ya zaka zauna wata mace tasa ka maka damuwa.."
'D'ayan ne yai dariya har da tafa hannaye, "Ku kuna abinku, yayi muku banza ba kuga shi hankalinshi ba ya wajenku ba, no wonder ma haushinku yakeji, yana tad'in shi kunzo kun dame shi.'
"Ko ba haka ba ne UK"?
'Ya fad'a tare da dukar mishi baya.'
"Murmushi yayi shi dai kawai."
'Ita dai Hafsah Allah Allah take dukan su su tashi subar mata wajen saboda gaba d'ayan su sun dameta, gata ita kad'aice mace duk mazaa sun zo sun baibaye ta.'
'Wanda tun da suka zo baiyi magana ba, shine ya kalleta yace,
"Kinga please k'anwata ki dan miqo mishi wannan abincin ko zai ci."
'Tab, inji Hafsah acikin zuciyarta, a wanne dalilin zasu sata wani aiki kan wani mai ji da kanshi sai wani cika yake kamar ita ta mishi abinda akai mishi.'
'Ta kalli wanda yai mata maganar, sannan ta mik'e tare da cewa "Excuse me please"
'Ta rab'a ta gefensu ta, bar musu wajen.'
'Dukkansu suka bi bayanta da kallo har da shi d'in ma.'
"Wanda yai mata maganar shi ya fara yin magana.'
"Tab, lallai Yarinyar nan 'yar zafin kai ce, wato ba zatayi magana ba ma shine ta mik'e ta bar mana wajen kenan.?"
"Muna da aurenmu, bare taja mana aji wannan UK ta, yarfa ai."
'D'ayan yace Allah yaso bani ta yarfa ba.'
'Da bazan iya ha'kuri ba wallahi.'
'Sai yanzu wanda suka taru danshi d'in yai magana, bayan yayi ajiyar zuciya,
"To kada ka hak'ura d'in."
'Su rasa ma abinda za suyi mishi sukayi, sai kawai suka shek'e mishi da dariya.'
'Wanda ya mata magana, ya fara jawo hannunshi, "Wallahi sai ka taso kuwa mun tafi, duk hada hadar nan sai anyi dakai."
"Mubarak ka barshi yasha ko da ruwa ne mana."
'Take ya girgiza kai shima, "No bazan iya sha ba.'
'Ya mik'e ya bisu, a hankali take fad'o mishi a cikin ranshi, sai ya dinga jin damuwar shi gaba d'aya ta gushe, sai ma damuwar, tafiyar da tayi, ke damun ranshi.'
'Babu laifi ya saki ranshi aka sha hidima sosai da shi, sai dai kuma tun da Hafsah tabar wajensu, har aka tashi bai k'ara ganinta ba, lamarin daya d'an tashi hankalinshi kenan.'
'Misalin k'arfe takwas kenan na na dare aka tashi daga gurin bikin, kai tsaye shi gida ya nufa, bai tsaya wani hada hadar d'iban mutane ba saboda kiran da Baffa yai mishi tun yamma, yace ko k'arfe nawa ne idan ya gama yazo yana nemanshi.'
'D'aya daga cikin drivers (Direbobi) na gidan ya kira a waya, yace yazo ya kaishi gadon k'aya.'
'Yasan ba zai nutsu yayi tuk'i ba, saboda fargarbar abinda baffan zai fad'a mishi.'
'Driver yana fito wa ya nufi motar ya bud'e mishi ya fito, sannan ya gaishe shi..
'Ya koma gidan baya, yayin da drivern ya zauna a mazaunin driver ya bawa motar wuta.'
'Mintuna kad'an ya kaisu unguwar, inda sukayi parking a dai dai, k'ofar wani madaidaicin gida, driver ya fito ya bud'e mishi k'ofar sannan ya fito, ya fara takawa zuwa cikin gidan.'
'Kai tsaye sit room d'in gidan ya nufa don ya ganshi a bud'e.'
'Yai sallama aka amsa, sannan baffan yai mishi izini daya shigo.'
'Shida Hajiya ne a sit room d'in.'
'Cikin nutsuwa ya durk'usa ya gaida su, suka amsa tare da tambayar shi ya mutanen gidan.'
'Hajiyar ce ta mik'e ta nufi cikin gidan da dama ta sit room d'in zaka iya shigowa ko kuma ta k'ofar dake gefe.'
'Baffa ya kira sunanshi, "Ukashatu"
Cikin ladabi ya amsa,
"Na,am baffa"?
Kasan dalilin kiran nan naka?
'Ya girgiza kai,
"A,a baffa."
'Yad'anyi murmushi sannan, yace, to zancen mu ne dai dai da aka saba shi."
'Ukasha ya gyara zama, har wani zufa yaji ya keto mishi, baya son ayi mishi zancen nan, bayan kuma gashi yau gaba d'aya ma ranshi a b'ace yake.'
'Cikin tunanin shi yaji yo, Baffan na mishi magana babu alamun wasa a tattare da shi.'
"Ya ake ciki to, kasan dai tun tini lokacin da muka baka ya cika koh"?
"Ya gyad'a kai, nasani baffa."
"To ya banji bayani ba har sai da na kirawo ka"?
'Ya muskuta, sannan ya fara magana
, "Ai baffa ba,a samu ba ne.'
.
"Nan take baffan ya rufe shi da fad'a,
"Wato ka maida mu abokan wasan ka koh?.. Ka d'auki zancen da wasa koh??
"Shikenan to yayi kyau abinda kayi, amma ka san bazamu zuba maka ido ba koh"?
'Tun da ya fara mishi fad'an ya sunkuyar da kanshi k'asa, sai da ya dire zancen shi sannan ya kwantar da murya yana bada hak'uri.'
'Ayi ha'kuri baffa, Allah ya huci zuciyarka, bani da burin in b'ata muku rai wallahi ayi hak'uri dai."
'Shima baffan sakkowa yayi, saboda wani tunani da yazo cikin zuciyarshi.'
"Wato ya dace su mishi uzuri, basu san dalilinshi nayin hakan ba, ga kuma larura irin ta jinnu da dai sauransu.'
'Don haka yace,
Ukashatu, ba muna matsa maka bane amma kasani aure shine cikar mutum, kuma, muna ganin ka kai munzalin da ya dace ace kaima kana da iyalinka, duba kaga shekarunka yanxu a k'alla sun kai talatin da shida, fa, to me kake jira, tunda kana da rufin asirinka, ka k'aninka ya gaji da jiranka har yana da 'yarshi?
Ya k'ara sassauta murya, sannan yace,
'Kodai baka da lafiya ne, baka fad'a mana ba"?
'Abinda ya ba ukasha dariya kenan har yayi dariya mai sauti, sannan yayi saurin toshe bakin shi, tuna wa da yayi baffan ba abokin wasan shi ba ne.'
'Baffan ma murmusawa yayi, sannan yace cikin sigar yi mishi, wayo ko dan idan yana da larurar ma ya sanar da shi.'
"Ka daina jin kunya, ko 'shi' yana nufin ('Abban ukashan') idan ka b'oye mishi ai ni bazaka b'oye min ba, kuma larura ai daga Allah take, wannan ba abu bane da zaka b'oyemana, sai ka fada mana koda a waya ne sai a nema maka magani koh"?
"Amma asani na, da yadda sa,anninka na nan gidan ma suke fad'a ba,a tab'a jin kayi lissafin aure cikin sha,anin ka ba sam."
'Ya d'an gyara murya sannan yace,
"Baffa in sha Allahu na kusa kawo muku ita, a dinga yi mana addu,a dai Allah ya taya mu zab'i na gari."
"Ami'n, ami'n, inji kawu daya saki murmushin jin dad'in furucin, sannan ya d'ora da cewa,
"Kuma kaima ka dage da addu,a saboda da akwai shed'anun aljanu masu cutar da d'an adam."
"Hakane Baffa na gode sosai, Allah ya k'ara girma."
Ami'n, baffa ya fad'a yana mik'a mishi hannu alamar suyi 'musabaha' (Abisa al,adar kawun idan zasu yi bankwana da koda jinkansa ne.')
'Ukasha ya mik'a hannu sukayi musabiha, sannan ya mik'e.'
"To na barka lafiya baffa."
"Masha Allah, a gaida mutanen gidan, Allah yai muku albarka."
"Ami'n baffa ya fito yana, ajiyar zuciya, don yaga alamun sassauci a b'angaren K'anin mahaifin nasashi.'
'Ya nufi gate, ya tarar da driver ya d'an kwanta cikin motar yana jiran shi.'
'Yana ganinshi yayi saurin fitowa zai bud'e mishi gidan baya.'
Ya dakatar da shi, "A,a ka gaba zan zauna ina son zamuyi hira ne.'
'Driver yayi murmushin jin dad'in hakan, duk da suna gaisuwar mutunci amma yayi mamakin cewa hira da Ukasha yace zaiyi da shi, saboda yasan shi ba ma,abocin yawan magana ba ne da yawa, amma sam ba,za,a ce yana da wulak'anci ba saboda halin gidansu gaba d'aya na karamci ne, domin sun gaji girma da karamci.'
'Ya bud'e mishi gaban, sannan ya zagayo, shima ya zauna ya kunna motar sannan suka hau bisa titi.'
'Sai da suka fara tafiya sannan ya kalle driver yace,
"Malam najib, ina son tambayarka ne, amma don Allah ka Fad'amin gaskiya."
"To in sha Allahu, mai gida zan fad'a maka iya abinda na sani."
"Yawwa to, am nasan dai ak'alla zan baka shekaru kamar hud'u, amma ina son sanin wani abu ne tun da kai kana da aure, kuma, yanzu 'ya'yanka biyu kace koh."?
'Ya gyad'a kai, "Hakane mai gida, yanzu na uku ake shirin haifowa."
"Yai murmushi, Masha Allah."
'Sannan ya saita muryarshi,
"Aganinka me yasa su baffa suka takura min da sai nayi aure."?
'Najib driver yayi dariya sannan yace,
Ai mai gida, bama sai an tambaya ba ka isa munzali tun yaushe, kuma, tunda ba wani abu ake jira na shiri ba (Kud'i) ai ya dace dai ace zuwa yanzu an mallaki iyali. Sannan hankalinsu zaifi kwanciya idan har kana da auren"
"Wane irin kwanciyar hankali kuma"?
"Najib yai 'yar dariya, sannan yace a zuciyarshi, "Bari na bi dashi ta yadda zai fi fahimta."
'Don ya fahimci, ba wai ukasha ya damu da auren bane, idan ya fahimta ma shi zancen ma baso yake ana yi mishi shi ba.'
'Sai ya kada baki yace,
"Mai gida, sai kawai ayi hak'uri tun da manya sun nuna suna so sai a yi k'okari ko don biyayya.'
'Sannan shi aure yana sa a dinga ganin k'imar mutum ta musammaman.'
'Ya kalleshi,
"To yanzu idan na fahimta wata tawaya ce kenan saboda bani da aure koh."?
"A,a mai gida, kawai shi aure yana cika darajar mutum ne."
"Yai murmushi, sannan ya gimtse, sannan yace,
"Bana son wulak'anci ne irin na mata."
"Alhaji ai ba kalar ku ake wukak'antawa ba gaskiya.'
"Hmm, haka kace, amma kada in maka shishshigi da sai ince, tsakaninka da Allah matar ka bata maka wulak'anci."?
"Kasan ni shine abinda na tsana a gurin mace."
'Ya fad'a yana yatsina fuska.'
"Eh to, wallahi mai gida batayi gata da sanin yakamata, ga tsafta, sai dai kawai kasan mata ba,a rabasu da jan aji wani lokacin."
"Yai murmushi sannan ya jingina jikin kujerar motar,
'Jin daga an tab'o matar shi ya fara zuba.'
"Ahankali yace Allah sarki, tunda haka ne, in sha Allah nima zanyi k'okari ko dan farin cikin su Abba.'
'Driver ya ce "Toh Allah ya zab'a ta gari, mai gida."
"Ami'n"
'Dai dai lokacin sunzo wajen wani store mai kyau, yayi mishi alamar da yayi parking a wajen.'
'Sai da suka tsaya, sannan ya kalle shi,
"Muje kad'an sama mata kayan gayu, madam d'in taka tunda kace 'yar gayu ce, sai ka had'a harda na jaririn koh? "
'Driver ya hau fara,a "Godiya nake alhaji."
"Tare suka shiga, kantin.'
'Kaya ake siyar wa na madaidaitan kud'i, amma sai kyau."
B'angaren atamfofi ya zab'ar mata uku masu kyau, amma ya mishi alamar daya k'ara, ya dad'a guda biyu saboda kada ya zak'e da yawa, babu abinda bai sashi ya d'aukar mata ba tun daga kan mayafai takalma, sark'oki da turare, da sauransu.'
'Sai kuma kayan Baby, sai takalman yara da yace ya d'aukarwa ya'yan nashi.'
'Shidai Najib har kasa godiya yayi, yasan kawai Allah ne yayi mishi katari, ayau d'in, don yana shirin fitowa ya nufi gida, Ukashan ya kirashi, kira yake kawai,
"Allah ya k'ara arziki, yasa a gama lafiya, Allah ya k'arawa alhaji nisan kwana."
"Ami'n yake cewa shi dai,
'Ya mik'a katinshi aka zara wajen dubu abba'in da wani abin.'
abinka da kud'in yanzu ba wuya kiji sun taru akan k'aramar siyayya bare kuma siyayya irin wannan.'
'Sai da suka fito yace mishi, to adinga taya mu da addu,a muma, Allah ya bamu nagari."
"Ami'n Ami'n, mai gida addu,a dama kullum muna saka ku a cikinta."
"Sun isa gida, ya sauke shi, sannan ya deb'e kayan shi ya nufi gida cike da jin dad'in yadda matarshi zatayi farin ciki da kayan, saboda yana yabonta sosai.'
"Ukasha kuwa, yana shiga cikin gidan yaji wata masifaffiyar yunwa, nan ya tuna rabonshi da abinci tun safe, lokaci guda kuma ya tuno da wannan Yarinyar ta d'azu a wajen biki, take yaji wata mummunar fad'uwar gaba, daya tuna bai ma san yaushe tabar wajen ba."
"A shagwaba irin tashi ne, ya nufi d'akin k'anwarshi yana buga mata k'ofa, saboda sanyi ne duk sunyi