Author : KARIMA TIJJANI MANSUR Category : Romantic Hausa Novels
gama mama."
"Kiyi sauri kizo kiyi break dai."
Ta gyada kai.
Gani nan mama."
Maman ta juya itama ta fita.
Ukhashatu, tsahon ranar yinin farin ciki yayi, jiyake babu wanda ya kaishi farin ciki a yau. Godiya yake kawai ga Allah don shi ya mallaka mishi ita. Zuciyar shi cike take fal da tsare tsaren yadda rayuwar su zata kasance shida ita.
Bai iya jurewa ba, har sai da kira wayarta da azahar amma Hafsah taki d'agawa, ji take bazata iya mishi magana a yau ba.
Yayi murmushi lokacin da kiran ya yanke.
Kawai sai ya zana mata _text messages_
_"Hmm, dole kik'i daga waya mana dama, kin rikita bawan Allah, kin barshi a rikice kuma.!!_
Text d`in dariya ya bata, ta dinga yinta, har abokiyar aikinta na tambayarta "meke faruwa."?
Sai kuma ta dinga jin kamar da ita yake, domin itace a rikice ai, tun safiyar yau."
Don ta kare kanta ta aika mishi da, _lots of work dear, let's phone to night.!!_
Sanda ya ida karantawa, sai da ya maimaita kalmar _Dear_ a fili.
Ya dinga murmushi shi kad'ai shima, yana fatan daren yayi da sauri.
Amma murnarshi ta koma ciki, daya tuna yana da meeting da daddaren..
π
*HAJEEEYAH KHAREEMERH*
[17/03, 2:48 p.m.] UMAIMA BASHEER: β₯οΈβ₯οΈβ₯οΈβ₯οΈ
*ZAZZAFAN SO*
(Masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so (Guba ne)*
ππ
*By*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Khareemerh)*
*Dedicated to unique in your love heart*
π *57*
____________________
Bai samu ya kuma kiranta ba a ranar, itama kuma sai taji tana da jiran kiranshi, amma bai kirata ba, haka ta hakura har zuwan lokacin baccinta.
Tana mamakin dalilin daya tare shi ga barin kiran nata.
Ranar data biyo baya, sukayi waya, dole ta saki jiki da shi, saboda salon shi, gareta. Duk wani abu da ukhasha zaiyi ya tabbatar mata da son da yake mata yayi shi, wani ta mayar mishi wani kuma ta bishi da murmushi ko tayi shuru, don yanzu ta gama fahimtar dawa take tare. _Wato shi mutum ne daya k'ware a ko ina, yana matuk'ar son yaga ya sakata farinciki kuma._
Daga k'arshe yake rok'onta akan ta barshi ya k'ara zuwa ya ganta.
Da take tambayar shi, yaushe yake so ce mata yayi.
Ko yaushe kika ce nazo zaki ganni."
Tayi dariya Kawai sannan tace, Aa dai mu bari sai k'arshen sati."
"Babu musu ya amince.
Allah ya kaimu lokacin."
Amiin tace mishi.
___________________
Shiri sosai Hafsah ta dinga yi ranar da ya kama zai zo d`in.
Har tunani ta shiga yi, me ya dace tayi mishi na tarbarshi."
Ta kasa tunana komai, k'arshe ta yanke shawarar bashi lemo da snacks kawai tunda suna da shi.
Shiri tayi alwashin yi sosai akan zuwan na shi. Ba su kara yin waya ba tun bayan wayar da sukayi, da rana.
Wani abu da ya da ya wargazawa Hafsah shiri, wanda badon zuwan Ukhasha ba babu abinda zatayi farinciki dashi kamar shi, amma sai zuciyarta ta kasu biyu gefe na jin dad`in hakan gefe kuma naga tunanin gudun samun matsala. Wato abin ba komai bane fa ce zuwan _Jamila_ a ranar.
Misalin k'arfe uku da rabi daidai na yamma, lokacin Hafsah na cikin toilet, don tayi alwashin shiryawa da wuri, ba zata b'ata mishi lokaci ba, sannan tayi alwashin zata nuna mishi soyayya daidai gwargwado yadda zai fahimci tana son shi itama.
Tana cikin band'akin taji sallama daga palourn mama kamar anyi bak'uwa. Bata damu ba take wankan ta a tsanake.
A falon kuma, mama ce zaune ita da mufida, tana mata tausa a k'afa, sukaji anyi sallama da wata iriyar muryar da ta sakasu juyawa duka, don basu gane wanene mai muryar ba.
Mama wata hamshak'iyar babbar mace ta gani, a cikin falonta, wacce ita a ganinta tafi mata kama da irin mata 'yan siyasa.
Mufida kuwa idonta ne yayi wani harr, sai da mai sallamar ta k'aras Shigowa sannan ta gane ta, don sun ganta Kwanaki ita da su yaya Hafsah.
Mama ce tace mata, "sannu da zuwa, zauna mana."
Ta tsuguna ta gaida maman kafin ta zauna a kujerar da aka bata.
Abun ya bawa mama mamaki matuk'a, kafin ta kai ga tambayarta wacece, ita taji tanacewa.
Mama, Hafsah na nan."?
Eh tana nan inji mama, tana k'ara kallon Jamila.
Sannan ta kalli mufida, "Jeki ki kira Hafsan."
Maman taga alamun kamar mufida tasan bak'uwar, amma babu damar ta tambaye ta, sannan da taji wajen Hafsah tazo, sai tafi alak'antata da abokan aikin Hafsah. Amma kuma taji kamar tasan muryar, amma ta manta a ina."?
Sanda mufida ta shigo d'akin hafsah na shirin fitowa daga toilet d`in, don haka ta d'an jirata ta fito.
"Yaya kinyi bak'uwa.
Hafsah na tsane ruwan jikinta da wani towel d`in banda wanda ta d'aura, ta kalli mufida. "Bak'uwa kuma."?
"Eh, Wannan da muka gani a park dinnan ce.!
Gaban Hafsah yayi wata iriyar bugawa.
"Toh, jamila!!
Ta fad'a a hankali.
Sannan ta goge fuskarta kafin ta kuma cewa, "Kice ina zuwa bari na shirya."
Tunda aka, fad'a mata zuwan bak'uwar taji jikinta yayi sanyi.
Da kyar ta tattaro nutsuwa, ta shafa mai sannan ta dakko kayan da tayi niyyar sakawa tasa.
Bata tsaya shafa ko da powder ba, shima kafin ta k'arasa sai da mama ta leko ta.
"Hafsah kiyi sauri mana kin barta tana jiranki."?
"Mama gani nan, yanzu zan fito." Ta bada amsa da haka.
Maman ta k'ara kallonta sannan ta juya ta fita.
Leshin ya amshe ta sosai, tayi kyau duk da bata shafa komai ba, d'an kunne da agogo kawai ta saka, sannan ta fito palourn bayan tayi amfani da turarukan ta.
A palourn sunyi shuru, duka, sai Jamila da jefi jefi take kallon wasu shashi na palourn.
Gidan ya chanja sosai ba kamar yadda tasan shi da ba, an sami cigaba a tsarin gidan da komai ma.
Mama ce ta gaji da hasashen son gano wacece, don haka ta kalli Jamila tana murmushi tace, "Um kema wajen aikin naku d'aya da Hafasan ne."?
Jamila tayi yar dariya sannan tace, Aa, mama baki ganeni ba koh."?
Mama ta jinjina kai, naga kamar na san fuskar koh kina zuwa gidan ne.
Babu jiran komai Jamila tace, "Mama Jamila ce fah."
Tana murmushi.
Mama kallonta ta tsayi sosai, kallon mamaki da tambayoyi, da k'yar ta d`auke ido, tace tana 'yar dariya.
Laa, ai ban ganeki ba sam, ashe kece."
Daga nan ta rufe bakinta.
A Kofar shigowa daga waje ta palourn, Basheer ne ya shigo da sallama.
Mama ta amsa mishi, ya k'araso ciki, daidai lokacin kuma Hafsah itama ta fito daga d'akinta tana takowa zuwa cikin palourn.
Sai da Basheer yazo Tsakiyar palourn sannan yaga fuskar bak'uwar don kujerar da take kai cikin falon take kallowa, sai kuma yaga Hafsah ta fito tana fara,a cikin shigar da tafi kama data fita, badon bata saka mayafi ba, sannan yaji cikin fara,a tana ambaton sunan Jamila.
"Ah, Jamila Sannu da zuwa ashe kece.!!
Maganar data saka Basheer, juyawa ya kalli Jamila sosai.
Ta ganshi itama. Amma basu yiwa juna magana ba, ya nemi guri a kujera 1 _seater_ ya zauna.
Yana bin Hafsah da wani kallo na tuhuma lokacin da take cewaJamila, "shigo ciki mana."
Jamila ta mik'e ta bita. Mama bata ce musu komai ba sai kallo da tabi Jamila da shi, sannan ta k'ara sauke kallon akan Basheer.
Suna nesa dasu, bakin Basheer ya bude rai a b'ace yace, "Mama wai meyasa Yaya zata dinga yin irin haka ne."
Mama ta gane akan me yake magana, amma sai ta cigaba da kallonshi don neman k'arin bayani.
Meyasa dole tace sai ta kula waccan, bata ganin yanzu ba da bace, kinga ta gayyato mana ita gida koh."?
Mama ta danyi murmushi sannan tace, "Haba Basheer ai ba,a gudun mutum a duk halin da yake ciki, kuma ni yarinyar shekarunta nawa rabon da ka ganta a nan gidan, tun sanda akace _tabar gidansu fah._ Ba yawo sukayi da yayarka ba bare kace janta take suna fita."
Basheer ya sake bata rai, "Nidai mama bana son tana kulata bare har ta dinga zuwar mana gida, dama na sani tun ranar da muka ganta a park, Yaya ta wani rikice data ganta, saida taje sukayi magana sannan taji dad`i, shine fa sukayi exchange numbers"
Mama ta d'anyi shuru kafin tace, "Ba fad'a ya dace kayi ba, bayani zakayi mata yadda zata fahimta, amma ka fara zuba ido kaga tunda ai yau ka fara ganin tazo gidan koh."? Kuma ko babu komai Hafsah fa yayarka ce dole ka bi ta a hankali."
Basheer yayi shuru yana had'e rai, _shidai sam bai gamsu da zuwan Jamila ba, kuma har su shige daki ita da yayarshi._
A cikin d'akin kuma, suna shiga Hafsah cikin farin ciki, ta nunawa Jamila gefen gado, "Zauna mana."
Jamila tayi murmushi sannan ta nemi guri ta zauna.
Hafsah cikin rawar jiki ta fito don nemawa Jamila ruwa.
Tana fitowa palourn kai tsaye hanyar kitchen tayi. Basheer ya bita da kallon Takaici, ta zubo mata snacks da dambun nama da basa rabo dashi a, ta had'o da lemo da ruwa. Sai da tazo zata wuce su Bashir yayi mata magana murya a dak'ile.
"Yaya.!
Bata amsa ba ta juyo.
"Yanzu sai da kika gayyato wannan gidannan koh..."?
Jin abinda yake fitowa daga bakin shi ya sata yin gaba, don bata son ma ta saurare shi.
Basheer ya cije leb'e don matuk'a ta bata mishi rai, ya zabura zai mik'e ya bi bayanta amma mama ta hana shi.
Ta daga mishi hannu, "Bari Basheer kada ka bita."
Ranshi ya k'ara b'aci ya zauna shuru ya jingina sosai jikin kujera, bai fi minti d'aya ba, ya mik'e yayi waje mama ta bishi da kallo.
Niyyar ficewa yayi daga gidan gaba d'aya don haka ya nufi hanyar waje kai tsaye.
Yana bud'e k'ofar gate d`in wani Napep na tsayawa a k'ofar gidan nasu.
Bashir na k'arasa fita yaga kamar ana d'ago mishi hannu ta ciki. Don haka ya dan dakata har mutumin ya fito, me Napep yayi gaba, shi kuma mutumin ya nufo wajen Basheer.
Basheer yaso gane shi, sannan yana mamakin irin murmushin da yake mishi.
Yana k'arasowa ya k'ara fad'ad'a murmushinshi, sannan ya mik'wa Basheer hannu suka gaisa.
Cikin fara,a yace mishi, Allah ya sake had'amu koh."?
Basheer yayi murmushi tana kallon shi da mamaki.
Kafin yace, "Ai ni sai yanzu na gano ka."
Shima murmushin ya mayar mishi.
Bashir dai kallonshi yake da buk'atar k'arin bayani, kuma yaga kamar bai da niyyar k'ara cewa komai. Don haka yayi gajen hakuri yace. "Ka kira number ta baka samu ba koh."?
"Hmm, kai dai bari nasha wahala fah,
Ya dafa kafad'ar Basheer, yana murmushi, "Ka wahalar dani abokina, meya faru ne."? Cewar Ukhasha.
Bashir ya taya shi murmushin,
"Wallah a ranar aka d`auke min waya."
Ayya Allah ya kikaye gaba. Ukhasha ya fad'a cike da alhini.
"Amiin inji Bashir, sannan cikin son tabbatar wa yace, "Naga kamar nan gidan kazo koh."?
Ukhashatu yayi murmushi mai sauti, sannan yace, "Eh."
"Nan na zo."!!
Bashir ya mishi kallon mamaki kafin yace, "Gurin abbanmu,? kar dai ka sanshi dama."
Ukhasha yayi 'yar dariya, sannan yace, kai tsaye, "A,a gurin Hafsah nazo.!!
Bashir najin haka ya fad'ad'a murmushi sannan ya mishi nuni, "Aa shigo, zo mu shiga ciki don inason k'arin bayani.
Sukayi dariya dukkansu, sannan yabi Bashir suka samu kujeru suka zauna, Bashir ya bude baki zaiyi magana Ukhasha ya dakatar dashi.
"Eh dama na santa, na ganta wajen bikin aboki na, so ta hanyar shi na sami contact d'inta a wajen matarshi, bayan na kasa samunka a waya."
Tare suka sheke da dariya, don yanayin amsar tashi ya baiwa Basheer dariya.
"Ai nasan abinda zaka tambaya kenan a ina na santa koh."?
Cewar Ukhasha.
Basheer ya jinjina kai "Yes.!
Basheer nason yi mishi k'arin tambayoyi amma baya son ya dameshi.
Da kanshi ya kuma cewa, "Ai nazo wajenta fiye da sati d'aya daya wuce, kawai dai bamu had'u da kai bane."
Bashir yace, "Hakane, sai yau Allah yayi.
Sosai Basheer yake yi mishi wata fara,a ta musamman domin har cikin ranshi murna yake kuma yana godiya ga Allah da Hafsah ta samu Ukhasha a matsayin mai sonta, don komai ya had'a, kudi, kyau, ga ilimi.
Bari naje na kira maka ita koh."?
Inji Bashir.
Ukhasha yayi murmushi, "Nagode dama na kira number ta tun kafin na sauka ba,ayi picking ba.
Bashir yayi shuru yadai mik'e, amma a zuciyar shi yana cewa, _"Ya zaayi tayi picking tana tare da wannan banzar kawar tata.?_
Ya nufi ciki Ukhasha ya bishi da kallo, gaba-d`aya yaron yayi mishi kuma yaji ya k'ara samun nutsuwa da Hafsah dama gidansu da komai nata..
Allah-Allah yake kawai ta fito ya k'ara ganinta yaji sanyi a ranshi, don tunda ta tabbatar mishi ta amshi soyayyarshi, yake jin wani irin abu na musamman game da ita fiye da na da..
________________________
A cikin gidan kuwa, komawar Hafsah d'akin kenan ta ajyewa Jamila kayan data kawo mata tana murmushi take ce mata, "Ga ruwa fah."
Jamila tayi murmushi, ta k'ara bin Hafsah da kallon da take ta bin ta dashi tun zuwanta gidan.
"Thank you! tace mata, sannan ta d'ora "Nayi missing dambun nama nan naku da snacks d'innan."
Jamila mamaki ta bawa Hafsah, amma sai tayi, murmushin yak'e kawai tanajin ciwon abin cikin zuciyarta.
"An kira wayarki fah." Jamila ta fad'a sanda ta debo dambun nama zataci.
Hafsah ta d`auki wayar tana dubawa,
sai taga sunan Ukhasha, ta tsaya jimm, da zata bi kiran amma sai ta fasa. Don tana da yak'inin zai sake kira kuma bata son katse hirar su, kuma bata son tayi waya dashi a gaban Jamila.
"Kinsan da agidanmu aka bani abubuwan nan bazan ci ba.."? Ta dan tsaya, Hafsah kuma ta zubo mata ido.
"Nan ma don na mugun yarda da ke neh."!!
Inji Jamila tana wani irin murmushi.
Lamarin daya bawa Hafsah matuk'ar mamaki ta kalli Jamila da neman k'arin bayani.
Jamila ta jinjina kai. "Yes, ba komai ake bani a ko'ina nake ci ba musamman ma idan nazo gidanmu, don zan iya ce miki rabona da ko da ruwan gidanmu ne za,ayi shekara biyar ko shidda."
Hafsah ta zaro ido, lamarin ya ba ta mamaki, mamakin dalilin Jamila na kin yarda da abincin gidansu. _Wannan wacce irin jaraba ce!!_
Ta fad'a a zuciyarta.
Kafin tayi magana, Jamila tace, _"Saboda zasu iya min kiranye ni kuma ban shirya komawa gidan ba.!!_
Hafsah ta dan zaro ido, abin yafi k'arfinta. Ashe duk abinda take tunani mafarki ne kawai, Jamila bata da tunanin sauyawa. Saitaji tana shakkar yi mata wasu tambayoyi da, da tayi niyyar duk randa jamilar tazo zatayi mata su. Don a ganinta Jamila Itace dai wacce ta sani a da, kuma tafi kowa sanin ta, sannan tana ganin ta isa da ita da har zata yi mata kowacce irin tambaya.
Ashe ba haka bane, tunaninta ne ita a haka, Jamila tayi nisa kuma ta riga ta chanja tsarin rayuwa.....
π
*HAJEEEYAH KHAREEMERH*
[17/03, 2:53 p.m.] UMAIMA BASHEER: β₯οΈβ₯οΈβ₯οΈβ₯οΈ
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
ππ
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh )*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*
*HELLO FANS KU K'ARA HAKURI DANI BISA RASHIN POSTING... IN SHA ALLAH, ZAN TAK'AITA LITTAFIN*
_BANA SAMUN LOKACIN TYPING NE SOSAI._ππΌππΌ
*NOT EDITED*βοΈ
π *58*
*Suka* shuru ita da Jamila na dan wani lokaci kafin Jamila ta k'ara kallon Hafsah.
"H. hameeed, naga kamar shirin fita kike yi koh."?
Hafsah ta d'anyi jimm, kafin tace, "Eh akwai wanda zan gani ne."
Jamila ta kafe ta da ido tana mata wani irin kallo, "Hmm kice an kusa mu fara shiri."
Hafsah ta d'anyi wani d'an murmushi. "Hmm Jamila kenan ina fah.."? Wannan _manager_ inda nake aiki ne, zaizo zamuyi wata magana."
Sanin Hafsah bata k'arya yasa Jamila yarda da zancenta.
Kafin daga bisani Jamila tace, "To gaskiya kiyi kwalliya a fuskar ki don naga bakiyi kwalliya ba."
You know mazaa akwai rainin hankali, musamman manyan ma,aikatan nan."
Abin ya bawa Hafsah dariya.
Yes nake fad'a miki, inji Jamila tana zuge jakarta ta dakko wata powder.
Ta mik'e tana cewa, "ungo shafa ko in shafa miki."!!
Kawai sai ta hau shafawa Hafsan. Haka kawai Hafsah taji tana d'ard'ar d`in hakan, taji tana kyankyamin Jamila ta tab'a ta amma babu yadda zatayi.
_Powder ce mai tsada Jamila ta shafa mata wacce a k'alla kud'inta zai kai 5k, ta kuwa amshi fuskar Hafsah sosai, dama ta farare ce, tunda Jamila ta zama fara sosai itama duk da dama can tana da hasken fata._
Jamila ta ajye powder a gefe, ta kwance daurin d'ankwalin kan Hafsah, bak'in gashin ta mai tsaho ya bayyana.
Jamila ta yarfe dan kwalin tana cewa, "Gashin nan dai na nan yadda na sanshi sai baki daya k'ara.!!
Hafsah tayi dariya, sosai.
Jamila kenan, kina son gashin nan, gashin da naki ma yafi shi yawa "?
"Ta fara zarga mata d'auri tana cewa, Hmm ai nawa fushi ne dashi gashi ba gaba-d`aya ya tafi ba wani yafi wani tsaho."
Ganin suna hira haka ya bawa Hafsah k'warin guiwa wajen yin tambayar data dami zuciyarta. Dama bata son had'a ido da Jamila tayi mata ne, yanzu kuwa tana mata d'auri.
"Jamila wa zaki raka Dubai please."
Hafsah ta dake murya ta tambaye ta.
Jamila tayi murmushi.
"Hmm, H hameeed kenan."
________________________________
A parlour, Basheer ne ya shigo, har yanzu mama na zaune a parlourn, ita kanta ji take bata aminta da shigewar Hafsah da Jamila d'aki ba. Tunda bata san me Jamilan zata fad'a mata ba.
Sallama Basheer kawai yayi ya nufi inda d'akin Hafsah yake.
Mama ta kira sunan shi, "Basheer."?
Ya dakata, sannan ya juyo, "Naam mama."?
"Me zaka shiga d'akin kayi."?
Ya dan shagwabe murya, Kai mama babu komai fah, Ya Hafsah ce tayi bak'o zan fad'a mata."
"Hmm, da gaske."?
Ya saki murya.
"Allah mama.!
Mama ta maimaita, Bak'o."? "Jeka fad'a mata toh.
Mama a ranta itama bata so bakon Hafsah yaga Jamila ba.
Basheer ya wuce, ya nufi k'ofar d'akin.
_____________________________
"Ai Hafsah badon kina da abinyi ba akwai labari.. Cikin muryar tausayi ta cigaba.
"Bansan ya akayi na yada ke ba, amma cikin in sha Allah idan na dawo daga tafiyar nan zanzo zamu tattauna don ke kad'ai ce zan fadawa magana ki yarda kuma ki bani Shawara tsakani da Allah."
Hafsah tayi shuru tana sauraron ta jikinta ya k'ara sanyi.
Ita har yanzu Jamila bata bata amsar abinda take son ji ba.
Sai ta ji Jamila na cewa,
"Aunty zan raka, Kinsan yanzu duk duniya bata da kamata Nima bani da ya ita sai dai akwai Matsala guda d'aya nida ita.."!!
Ji sukayi an turo k'ofar babu ko sallama.
Jamila ta juyo, Hafsah kuma ta d'ago.
Yaya."?
Kira sunanta rai a cunkushe.
Ran Hafsah ya b'aci.
Mene."?
Tace mishi.
Ita kuma Jamila ta cigaba da gyara mata d'aurin.
"To kizo kiji mana."
Inji Bashir.
Hafsah ta bude baki cikin fushi.
Bazan zo ba, Basheer ni kake disgracing koh agaban kawata koh ni kake wa haka."?
Muryata tayi rauni, "Shikenan bazan zo ba, ko ma mene bazan zo ba inyaso ka rufe ni da duka.."
Bashir yasan hali don haka ya k'araso cikin d'akin.
Lokacin Jamila ta k'arasa mata d'aurin ta zauna.
"Am sorry my yaya, ba abin zafi bane, kiranki ake a waje."
"Shine Bazaka fadamin ba kake kirana kamar nice