Chapter 37 Reading ZAZZAFAN SO COMPLETE HAUSA NOVELS BY KARIMA TIJJANI MANSUR.txt Arewa Novels

ZAZZAFAN SO COMPLETE HAUSA NOVELS BY KARIMA TIJJANI MANSUR.txt

Author :  KARIMA TIJJANI MANSUR Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   37 / 40

108K to 111K   out of 119.4K words

din kuwa.
Ta d'an kara takowa ta matso ya gama karanta raunin da take ciki.
"Ka zauna don Allah kaji..
Ya danyi jim, sai kuma
baiyi magana ba ya nufi kujerun itama ta bishi suka zauna kusan tare.

Wannan karon shiya fara magana. "To me kuma kike so Hafsah ko baki hak'ura bane."?
Murya a dashe ta sauke numfashi sannan tace, "I'm sorry please wallahi ni bansan..."
Sai kuma tayi shuru.
"Baki san me ba."?
Sai ta kama bakinta don zancen bashi da k'arashe. Ce mishi zatayi batasan an bashi ita ba ko me."?
"Kiyi magana mana."
Tayi shuru don bata da abin cewa.
Shuru ya mamaye gurin sai shi ya zuba mata ido.
"Bai zaci zata iya mishi abinda ta mishi ba, kuma yanxu yaji tana bashi hakuri to me hakan ke nufi."?

Ya katse shurun da dan yin gyaran murya.

"Me yasa kikayi shuru uhum.."? Bai jira cewarta ba shima ya shiga fad'ar abinda ke ranshi.

"Ni ina tunanin kamar mun zama daya ne, zan iya fad'a miki ra'ayi na a kanki."
Ya zubo mata idanu.. "Ba dole nayi niyyar miki ba Shawara na baki.. nima fa ina da k'anne mata Hafsah wallahi bazan aureki na cutar dake ba ki fad'a min duk wasu burikan ki in sha Allah zanyi kokari wajen ganin cikarsu..amma fa har ga Allah zan kara fad'a miki banason aikin gidan TV."

Kanta na kasa bata d'ago ba tace.. "Kayi hakuri.."
Ya kalleta da mamaki.
"Meyasa kike bani hak'uri ne."? Ai ra'ayinki kika nuna ba fa laifi kikai ba."

Ya tausasa murya don ya lura neman kuka take amma yana mamakinta.. _kamar ba itace ta mishi fada a waya ba to mene dalilin rauninta a yanzu.?_

A hankali ta kara bude baki zatayi magana sai kuma ta fasa.
Cikin sanyi shima yace "To kiyi hakuri kema na aibata miki k'awaye.!!
Ta rasa abin cewa sai tayi murmurshin jin kunya tana kawar dakai.

Suka k'ara yin shuru..ita tana matuk'ar son ta cire mishi shakku akanta amma kuma ta kasa ta yadda zatayi ta mishi bayani.

A yadda ta karance shi har yanzu abinda tayi mishi yana ranshi kuma tabbas ya saka ayar tambaya akanta.

So take ta kalleshi don ta k'ara fahimtar shi don haka ta dago da idonta sosai a sanyaye suka had'a ido ta kauda ido gefe.
Daidai da mik'ewarshi.. "Zan tafi," yace da ita.
Tayi shuru babu magana bata son ya tafi bata fahimtar dashi wani abu ba amma kuma ta kasa.

Sai ta lura da wani abu da yake mik'o mata, ita kuma tana can tunani.
Tayi sauri tasa hannu biyu ta amsa babu musu duk da tana shakkun karb'a.
"Ki gaida su mama."
Yace da ita tare da fara takun shi don barin gurin.

Sukaci karo da Bashir a tsakiyar gidan daidai lokacin shigowar shi kenan.
Bashir ya fad'ad'a murmurshi suka yi musabiha. Ukhashatu ne ya fara magana.. ya akayi mutumina baka tafin ba ne."?

Wallahi gobe nake shirin d'agawa.
Suka fara takowa zuwa inda Hafsah take, bisa dole tabar wajen.

Suka zauna suna fuskantar juna.. Ukhashatu yace "zamuyi missing dinka fa aboki."
Basheer yayi murmurshi, "Sosai fa especially mutuniyar taka.!!
Ukhashatu ya zubo mishi ido da wani kalar murmurshi akan fuskarshi wanda ke bayyana zallar shauk'i.

"Hmm to zamu hanaka tafiya."
Sukayi daria a tare..

Sunyi hira mai tsaho wacce yawancinta ta zancen makarantar da Bashir yake yi ne. Ukhasha yake kwatanta mishi wani abokinshi wanda yake matsayin HOD a makarantar Bashir bai gane shi ba don haka suka rufe zancen da cewa..zan mishi nuni da kai ince qanina ne yana da kirki mutumin.
Bashir ya amsa da "Toh nagode Yaya.
Ukhashatu ya duba agogonshi. "Bari na wuce kaji."
Bashir ya mik'e suna takawa har qofar gida in da yabar motarshi.. _HONDA ACCORD._ motar da Hafsah bata ma san ya na da ita ba.

Sukayi musabiha bayan Ukhashatu ya shiga mota. "To qanina Allah ya kiyaye hanya kaji."
"Amiin, inji Bashir.
Ya motsa da niyyar juyawa Ukhashatu ya kirashi. "Bashir na manta Ungo wannan."
Bashir zaton shi sak'on Hafsah ne don haka ya mik'a hannu. Ukhashatu ya mik'o mishi kudin. Bashir yayi jimm, "karbi mana." Inji Ukhashatu.
Bashir ya amsa yana kallonshi da neman k'arin bayani.
"Ka kara guzuri dashi nagode ka gaida su Abba.

Bashir yayi jimm jiki a sanyaye yana buda baki zai ce mishi "angode" ya ga har ya fara tada motar duk da haka sai da ya fada "angode."
Ukhasha ya d'aga mishi hannu kafin ya ja motar ya wuce..
__________________
A palour ta fada kan kujera sanda ta koma cikin gida. Mufeedah ce da amira a palourn babu Zainab suna ganinta suka maida hankalinsu kanta da alama tana cikin damuwa.

Kamar ta rusa ihu haka take ji.. ya akayi tayi sakaci har ya tafi bata wanke kanta ba a wajen shi."?

Ta bata mintuna a daskare hankalinta na can ga tunani, sai da mufida ta kirata.
Yaya baki tab'a nuna min ya Ukhashatu ba aunty Ameera ce kawai ta sanshi.
Da zata share ta sai kuma ta bude baki a hankali tace.. Idan ya qara zuwa zan kiraku ku gaisa."
Cike da fara'a Mufeedah tace "Yaushe zai k'ara xuwa eh yaya."?
"I don't know! ta fada a kufule.
Mufida ta kama kanta don taga kamar a sama yayar tasu take.

Kamar an tsikare ta yi zumbur ta duba gefenta inda ta ajye ledar data shigo da ita.
Ta dauka da sauri cikin zakuwa take son taga menene aciki.

Da sauri ta zaro abinda taci karo da shi..wani dan box (akwatu) ne shima ta buda shi da sauri ta zaro zoben da ta gani ciki sai shek'i yake.

A hankali ta zame zoben hannunta.. wanda idan zata tuna shine na Yusuf daya kawo mata dake ba sashi take ba sai lokaci zuwa lokaci saboda haka yana nan kar kasancewar shi _Gold_ shima na yanxun gold ne mai matuk'ar kyau. Ai kuwa tana zame shi tayi cilli dashi. Idanun qannenta tun dazu akanta don haka tana yarwa mufeedah tayi zaraf ta samu. Har suna fada da Zainab.
Yadda take zura zoben a hannunta a hankali ta kuma wani irin shauk'i tana jin wata iriyar k'auna na shigar ta.

Yayi mata kyau matuka a a hannunta tana gamawa ta maida akwatun cikin ledar sai ta lura da wata yar takarda a ciki da sauri ta dakko ta a dan nannad'e take don haka ta yi saurin bude ta yar qarama ce sosai. Da rubutun biro kuma da hannu (handwriting) me kyau taga an rubuta _"I love you.."_
Ta ja wata doguwar ajiyar zuciya da tunanin dalilin kyautan haka a halin da suke ciki..

Zainab da mufida har yanzu basu daina sa'insa ba akan zoben yayin da Hafsah ta kulle bakinta kawai taki ta kanta musu bare ta raba gardama.
Mama ta fito daga d'akinta.
Ku lafiya meye haka."?
Mufida ta mayar da jawabi "Maman wai aunty Hafsah ne ta cillar da zoben ta shine na tsinta wai ya Amira sai na bata.
Mama bata bi ta kansu ba sai ta kalli Hafsah da ta jingina kanta jikin kujera. Yaushe kika dawo."?
Ahankali tace yanzu.
Wanne zoben kika yar suke fada akai."?
Mufida tayi zaraf ta nuna mata "Kinganshi wai ya Ukhashatu ne ya bata wani.."

Mama ta kalleta da kyau sai Hafsah taji yar kunya.
Ta zaro zoben a hankali ta dakko box din ta mik'a wa mama. Maman ta amsa tana murmushi wani irin farin ciki takeji. Angode tace sannan ta mik'a mata.
Hafsah ta amsa cike da kunya, bata mayar dashi hannunta ba saboda mama dake wajen.

Mama na shirin zama Bashir ya shigo da fara'a ya nufi mama. A takaice yake mata bayani yadda zai zata fuskanci shi.
Mama ya Ukhasha ne ya ban wannan.
Ya mik'a mata kudin yana k'ara mata bayanin yadda akayi kudin suka zo hanunshi.
Mama tayi murmurshi masha Allah an gode."

Hafsah ta mik'e zumbur ta bar musu palour Bashir ma ya tashi ya bita aka bar mama na zaman shari'ar zobe.

____________________________
Yaya Allah mutumin nan naki akwai kirki.
Inji Bashir.
Hmm tace mishi ta nemi waje cikin drawer tana adana zoben ta.

Allah yaso lokacin muna hutu za'ayi bikin ku da wallahi ko babu hutun sai nazo gida nayi two weeks.

Hafsah ta bishi da kallo kawai.
Kinga 5k ya bani and yace zai had'ani da friend dinshi wani HOD a school din mu.
Sai yanxu tayi magana Okey good.

Bashir ya gyara zama..
Yaya baki fad'a min yadda zanyi da yarinyar nan ta school dinmu ba fa.. Allah ni itace damuwata.
'Ka daina sakar mata fuska!!
Ta fad'a a takaice.
Kuma fa haka za'ayi.
Sannan ya gangaro kan hirar abinda yafi damun shi.
Yaya me da me zamu tsara a bikin naki ne.. nafison ayi shagali sosai wanda ba'a taba yi ba.
Hafsah tayi murmurshin da babu shiri. Wannan wane irin zumudi ne Basheer keji da shi, bama shi kadai ba duka kannen nata haka.

"Hmm.. kai sai kace abin ya zo daf."
Yazo mana Yaya ni tun yanxu zan tsara saboda bana nan xa'ayi tsare tsaren kada yaran can suyi ma shirme.
To ka je kuyi tsare tsarenku da su Zainab ni ku daina sa ni a ciki."
Bashir ya sheke da dariya hmm au na manta fa "Yaya ashe ke amarya ce dole kiji kunya."
Hafsah ta kai mishi duka ya mike da sauri yana cewa bari naje kitchen Zainab nayi min baking cake in taya ta tunda kin koreni.. _Amaryar Ukhasha_
Tayi murmushi taji dadi sosai sunan nan daya kirata da shi.
Fitar shi ya bata damar baje tunanin dake ranta. Menene ma'anar zoben daya bata da kuma wannan takardar mai jaddada soyayyar shi."?
Hakan na nufin babu sauran fushinta a zuciyarshi ko kuma me."?
Ya akayi ma ta kasa fahimtar dashi komai.
Ta tuhumi kanta tare da jin haushin kanta sosai har daga k'arshe ta bige da buda wayar ta ko zataci karo da sak'on k'arin bayani akai.
Babu wani text message daya shigo. Data buda data kuma bai online kwata-kwata sai dai wani abu daya dauki hankalinta..wato chanjawar profile dinshi zuwa photon shi da yayi matuk'ar kyau.

Ta bata mintuna tana k'are mishi kallo tare da kissima abubuwa da dama cikin zuciyarta ciki harda tsananin soyayya da jin kishin shi mai zafi ya tsarga a zuciyarta. _Allah ne kadai yasan iya adadin yan matan da yayi soyayya dasu kafin ya iso gareta._
________________
Da komawar Ukhashatu gida ya kara amsa kiran Abban shi.
Ya gurfana gabanshi cikin ladabi, bayan ya gaida shi abba ya fara kwaro jawabi.

Kaga saura kwanaki uku su fara bikin Maryam so nake yi ana gama bikin a fara shirin naka kuma ma'ana ka fara shirin gyaran gida da sauransu.
Nasan dai baka da matsalar masu yi maka aikin haka kayan aikin kasan masu inganci sai dai kada a saka shiririta aciki don Allah idan akayi kammala gyaran kaga anrage aiki sai a fara kuma shirin had'a lefen koh.
Ukhashatu ya gyada kai hakane Abba.
Yawwa Malam zan tura maka kud'i sai a fara shirin.
Ukhashatu ya dago kai Aa Abba za'ayi hidimar biki fa, in sha Allah ina da abinda zai isa.
Take fuskar Abban ta chanja ya fara magana fad'a fad'a, nasan ba zasu ishe ka kayi komai ba nima kuma nasan kana dashi din kuma na baka to ka karba kawai.
To angode Abba Allah ya kara girma Allah ya saka da alkairi."
Yawwa ko kaifa."?
Tashi kaje kayi shawara dai da yayan naka.
"Toh Abba a huta lafiya.
_________________________
Hafsah ta tsumayi kiranshi har zuwa washe gari amma shuru babu ko da text..

Da kanta tayi wa kanta fad'a _ai itace a k'asa kuma itace mai laifi_ don haka ita ya dace ta neme shi ko dan ta nuna mishi jin dadin kyautar shi.

Kiran da ta mishi bai dauka ba sam..sai ta kara shiga damuwa don haka a lokacin ta tura mishi da _"Thnks my luv"_
Cike da zak'uwar ganin reply dinshi amma har bayan awa d'aya shuru..

Sun raka Basheer inda zai hau mota cike da rashin jin dadi musamman ga Hafsah don zata rasa abokin hira. Sannan ga tunanin idan ya sake dawowa basu da wannan damar sosai kamar tayi kuka takeji. Haka ta yini sukuku babu kuzari ga damuwar Ukhasha _anya ba matakin kuntata mata ya dauka ba."_

Tana wannan tunanen tunanen taji k'arar shigowar sms a wayarta
_You deserve more my dear!_
Ta lumshe Idonta tana murmushin jin dadi don gaskiya ya sham shammace ta, sai kuma taji tana son suyi waya dashi amma sai ta share tunda shima bai kirata ba..

Hidima ta yiwa Ukhashatu yawa har takai yau kwana uku kenan bai kira Hafsah a waya ba. Shirye shirye yake na abubuwa da dama kamar su lefen sa, wanda yawanci yayarsu ce dake abuja zata had'o sai kuma shi da duk sanda zai wuce wani shagon sai da kayan mata baya rasa abin shiga ya dakko mata.

Sai kuma hidimar fara aikin gidan da kuma harkokin da suka shiga shida yayanshi ga bikin Maryam wanda shima ya bada tashi gudunmawar shiyasa yake mamakin Abbanshi yadda ya bashi kudi a irin wannan lokacin. Baya samun zama sam sai dare kullum cikin zirga-zirga ga zuwa wajen aiki, lokaci d'aya yayi yar wata 'ra ma' sannan kuma yayi duhu.

Suna hirar Hafsah da hajiyarshi idan ya shigo wajen Hajiyar. Ya nuna mata ita kuma tayi fatan alkhairi sai dai shima tayi mishi magana kan idan sunyi aure yayi k'okarin chanja mata wajen aiki, ya gyada kai to hajiya in sha Allah.
Yawwa kaga hakan zai fi ko."?
Hakane Hajiya in sha Allah za'ayi hakan.


Hafsah ta kissima abubuwa da yawa a ranta na yadda Ukhashatu yayi watsi da ita har kwana uku, zuciyarta har ta fara inkarin soyayyar da yake cewa yana mata sannan dad'in dad'awa ta gano wato ramuwa yake. _"Shi kalar tashi ramuwar kenan."_ Ta fad'a a zuciyarta cike da neman abinyi. Bata jin zata kirashi dai amma zata k'ara mishi kwanaki.

Har dare sannan wani abin mamaki ya faru...

_Sanda take zaune tana sak'e-sak'en ta wani yaro da yake musu yan aikace- aikace ya shigo ga mamakin ta yace mata aunty ana kiranki bata tambayi ko wanene ba ta kimtsa fuskarta ta fita._

Bata ga kowa ba a harabar gidan, ta d'an tsaya waige-waige sai ga yaron ya fito daga cikin gida da plask d'in abincin shi a hannu.
"Jamil Ina yake ne."?
Ta tambaye shi.
Yana waje aunty bai shigo ciki ba ai."
Ta d'anyi jimm kafin ta fara tafiya.
_Wato bashi da niyyar shigowa ciki ma kenan."_
Mota ce mai matuk'ar kyau a 'fa ke' a kofar gidan..akwai haske ta ciki n kwayayen da sukayi wa bangon gidan ado a tsakanin fulawowi da kuma bangon sun haska wajen yayi kyau yadda zaka iya ganin mutum sosai.


Motar mai bak'in glass ce Hafsah bata iya gano na ciki ba sai dai ta tsargu da bata lokacin da yayi bai sauke glass din motar ba.

Shiko dama ya samu ya k'are mata kallon kewa cike da wani irin shauk'i tare da tuno abubuwan baya masu yawa ji yake yi kamar ya maida hannun agogo baya.

Tunawa da yayi zata iya juyawa ta barshi, yasa shi cikin sauri ya dan zuge glass din motar sannan ya bude da sauri ya fito.

Lokacin Hafsah ta fara waige-waige tana son gane ko dai ba shi ya aika kiranta ba.

Sanye cikin K'ananan kaya ya k'ara k'iba kadan da haske gami da k'aruwar goge wa.

Juyowar Hafsah kenan idonta ya gane mata shi ta d'an so tsorata kad'an.

Yana ida fitowa daga motar ya nufe ta kai tsaye ya tsaya daf da ita ita kuma ta d'an matsa.

Ya d'an kalleta na seconni cikin muryarshi mai bayyana matuk'ar rauni daga k'asan zuciya yace.
Assalamu alaikum."
Bakinta ya kulle gam ta ma kasa motsa shi bare ta amsa sai ma kallon gefe da tayi taga idan da hanyar wucewa.

Ya d'an fahimci manufar ta don haka ya buda baki ya fara magana da muryarshi wacce ba zata tab'a mantawa ba _har yanzu Hausar shi a juye take."_

Hafsah please help me and forgive me Don Allah wallahi na rantse I regretted all what I did to you..shedan ne yasani..plz"
Cikin sauri ta motsa da niyyar barin wajen ya maraice yace.
Don Allah karki tafi ki tsaya badon ni ba."

Ta kuwa tsaya d'in aranta babu dad'i tanajin zafin shi amma kuma tana mamakin yadda abin ke faruwa kamar a mafarki duk wani wanda ya gujeta ma yanzu suke dawowa me yasa."? Sam bata so ya riske kamar da ba ( _babu aure_) gani take kamar zaiga zaman jiranshi ne yasa.

Amma sai kuma tayi saurin ture wannan tunanin bisa wata ankararwa da wani bangare na zuciyar ta yayi mata.
_Hafsah kada kiyiwa Allah butulci hak'ika rayuwarki gaba-taci ba baya ba. Kuma yanzu you're engaged kin yiwa Yusuf nisa._

Ta daga kanta ta kalleshi ya kuwa k'ura mata ido kallon ta na tuno mishi abubuwa da dama.

Me ya kawo ka wajena."?
Ta fad'a da kaushin murya.
Bani da hanyar contacting dinki ina miki magana kina share ni kiyi hakuri, na zo ne na baki hak'uri... ya d'anyi shuru kafin yace _and to tell you that my father had died._

Tayi jimm sai yanxu taji d'an tausayin shi saboda a yadda tasan Yusuf da yadda yakeson iyayenshi kuma suma suke son shi.

"Ahankali tace Allah ya jik'anshi."
Yayi wani bushashshen murmurshi ta kuma lura da kwallar data taru a idanunshi.
"Amiin ya amsa sannan ya dora cikin sanyin muryar.

Please Hafsah ki yarda muyi aure mana wallahi na daina duk.."

Ta daga mishi hannu cike da b'acin rai.
Nooo never.!! Kada ka kara mini wannan zancen and kada ka kara zuwa wajena.."

Tana shirin juyawa gida taji cikin daga sauti yace...
Don Allah ki taimakeni Nasan kina sona fah Basma ne ta rabamu kuma nayi regret abinda ya faru..please Hafsah I lost my dad kada na rasa ki kema.."
Ga mamakin ta sai taga yana share hawaye ta tsaya jimm cikin takaicin abubuwan wacce kaddara ce ma tasa ya dawo gareta..ita ta manta dashi ta manta duk wata rayuwar da sukayi a baya imma dad'in ta da wahalar ta duk ta manta. To kuma me zaisa ya dawo mata da wannan zancen gani takeyi ma k'arya yake lokacin yayi tsaho ace da ragowar son ta a zuciyar shi..

Ko ita da tayi sha fama _Zazzafan son_ shi ta warke kuma ta manta bare kuma shi da take da yak'inin wasu abubuwa ne game da ita ke tafiya dashi bawai zallar sonta bane.

Tana tsaye har wata motar ta zo ta dallare ta har sai da ta kare idanunta da hannu motar ta zo gefenta tayi parking sannan aka zuge Glass din ta hango na ciki.

Gabanta ya yanke ya fad'i taji kamar ta sume don fargaba..meyasa abubuwa suke zuwar mata a haka ne."?

Babu shiri ta nemi hanyar barin wajen yayin da Yusuf ya biyo ta yana kira "please Hafsah.!!
Rasa inda zata dosa tayi wurinshi ko kuma gida sai ta

37 / 40