Author : KARIMA TIJJANI MANSUR Category : Romantic Hausa Novels
gun, yaji tace, "Don Allah ka karb'a.
Baya son su tsawaita, Allah ne ma ya rufa mishi asiri abba baya nan.
"Ya mik'a mata hannu, ya amsa.
Cikin k'osawa ya mata alama, _kije gida, kije gida._ yace da ita.
Yana k'ara kallon shigarta, riga da skirt na atamfa matsatstsu, sai siririn mayafi.
Tayi Jim tana kallon shi. Shima wani tunani yayi.
_Za,a iya zargin shi fa, musamman ma,aikatan gidan._
Allah yaso a iya nan suka tsaya.
Wuce muje yace mata, don yaga kallon da take mishi yayi yawa.
Don gwara agansu tare d'in.
Sai da suka zo bakin gate d`in fita, yace mata, _"Maza kije gida na gode ki gaida mama kinji."_
Tana murmushi ta d'aga mishi hannu. Ya juya ya koma ciki da ledar a hannu.
Yana shiga yayi wurgi da kayan, a k'asa, suka zubo daga cikin ledar, memo ne, me photonta ajiki, sai tarkacen su snacks.
Lallai dole yasan abinyi, tun kafin abubuwa suyi nisa , ai baisan yarinyar haka take ba.
Sai daya kintaci taje gida ya kirata.
"Ke ya akayi kika san gidanmu."
"Um da dama na sani fah."
"To ke a ina kike."
"Can gaba da layin ku."
"Kada ki k'ara min haka, kada ki sake zuwa gidan mu."
Ya fad'a cikin kaushin murya.
Sai ta fara kuka, tana fadar wasu maganganu da bai bi takansu ba, wai ita sonshi take, ta gaji kwana biyu bata ganinshi, kuma don tazo gidan su shine yake mata fada haka."?
Shidai ya katse wayar yana, takaici. Ya zama wajibi ya yanke alak'arsu dama ya gaji.
Tun lokcin duk wani block yayi amma, chanja layi take, kamar me aiki a companin _SIM card_ da yayi block zata chanja number ta kirashi, har ya gaji ya daina, idan ta kira ya share, amma haka zatayi ta kira kamar bata da aikin yi sai kiranshi, ala dole yake d`agawa ko dan ta barshi yayi aikinshi sosai. Ya gaji da abubuwan, shine ya d`auki matakin tunda yarinya ce, bara ya bita ta yadda kwakwalwarta zata iya d'auka. "Ya kirata da kanshi wata rana yace, za,a bashi mata a gidansu.
Amma ga mamakinshi bata nuna alamun damuwa ba tace, "Ta ji yayi ta biyu da ita zata jira shi.!!
Gaba-d`aya lamuran yarinyar sun dame shi, shi ba abin ya sauya number shi ba, yana da abubuwan da suke da matuk'ar muhimmanci akan number, Misali account d'inshi na banki, da sauransu.
Wasa-wasa watansu shidda shida ita, ana fama, Allah yaso babu wanda yasan da ita idan ba Fadwa ba, itama saboda ta ganta rannan ne.!
_Sometimes yarinyar na bashi tausayi, wani lokacin ta bashi haushi, yau dai tausayinta ne yafi yawa saboda shima ya fara bin layin da take bi yaji ya akeji.._ 😂
____________
Abisa dole ya hak'ura da kiran number Basheer don tak`i shiga sam, haka ya kwanta jiki a sanyaye babu k'wari, fargabarshi shine _"Kada dai ace wrong number ya bashi.!!_
_________________
Bayan su Hafsah sun koma, gida, d'aki tayi shigewar ta, tana ta tunani, so take ta samo hanyar da zata fara kudurinta akan Jamila. _Ki jawota ajiki._ wata zuciyar tace mata haka.
Kuma tabbas taga hakan don idan basu shak'u ba ko babu alak'a mai k'arfi a tsakaninsu irin ta da, babu yadda za,ayi ta iya aiwatar ta abinda ke ranta.
_Ya ilaahiy ka taimake ni._ Addu,ar da take tayi aranta kenan. Zuciyarta na k'ara hasko mata hoton Jamila a da da kuma yadda take a yanzu data ganta a yau.
_Dama can ana fad'a mata Jamila na zuwa unguwar, har gidansu tana zuwa, kawai dai wajenta ne bata zuwa._
Ta d`auki wayarta kamar zata yi wani abu da ita sai ta tuna cewa, ba ita ta amshi number Jamila ba, Jamilar ce kawai ta karb'i
tata Number.
Tana kwance, zainab ta shigo d'akin, da waya a hannunta, cikin k'asa da murya tace "Yaya ga Na'eem zaku gaisa a waya yace na baki."
Hafsah ta girgiza kai, alamar ba zata karb'a ba. Zainab tayi saurin katse wayar don kada a bata mishi lokaci ko Hafsah ta fad'i wata magana mara dad'i, ya jiyo.
Suka fuskanci juna Hafsah ta fara magana.
"Bana ce ki daina kula yaron nan ba."
Zainab tayi shuru ta sunkuyar da kai, haka kawai Hafsah bata son Na'eem ita kuma bata ga aibunshi ba.
"To zan fad'awa abbah tunda haka ne." Hafsah ta k'arasa fad'a.
"Haba Yaya wai me Na'eem din yayi ne.."?
Zainab ta fad'a cikin shagwaba.
"Ban sani ba, nidai nace ki rabu dashi."
Zainab ta turo baki sannan ta tashi ta fita.
_Duk da Hafsah bata fiya takura ba, amma bata barin k'annenta su fad'a halin da zasu cutu, haka kawai taji Na'eem bai mata ba, kuma don taga alama ba aure ne gabanshi ba kawai yana son ya b'ataw K'awarta lokaci ne._
_Shi kuma daya fuskanci cewa Hafsah bata yinshi, shine yake zuwa da siyasa, ko yaushe idan ya kira a waya sai yace a bawa Yaya su gaisa._
_Hafsah bata son hakan tana ganin ba zata zuba ido, k'annenta su fada irin halin da ta tab'a shiga ba shiyasa take tsaye kam akansu, duk wani motsinsu akan samari ta sani._
BASHEER
________________ B'acin ran Hafsah bai barshi ya zauna a gida ba. bayan sun dawo gida, yayi alwala ya fice, don ya tabbatar idan ya sake suka zauna zaman hira da ita, hirar Jamila zatayi ta masa, shikuma ba zai zauna sauraro ba, don haka daga masallacin, ya nufi wajen wata _snooker_ can bayan layinsu. Bisa Tsautsayi kuma, sai wasu suka fara cha-char baki har takai sun fara kokawa, akan musun _snooker._ Basheer ya shiga tsakiya, har da shi a masu rabon fad'an gashi wajen an cika. Lokacin kuma wayarshi na aljihun wandon shi ba baya, sai da komai yayi _settled_ sannan ya nemi hanyar dawowa gida, lokacin an kiran sallar isha'i.
Sai da ya shigo, gida, yayi alwala, zai fita ya laluba aljihunshi don yasa wayar a chaji, yaji babu komai.
Gun Hafsah ya nufa, tana palour tana cin abinci, _"Sister an sacen wayata fah._
"Ta zaro ido, a ina yaushe kuma."?
Gashi ban ganta ba, "Ina tunanin wajen snooker da naje ne."
Bata ce komai ba, tahau kiran wayar amma _is switched off_ ake ce mata itama.
_Basheer ya fice, kawai ya nufi masallaci ya barsu suna, jajantawa.._
📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*
♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh )*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*
📄 *47*
*Da* safe Ukhasha, da kiran number Basheer ya karya, amma _still is switched off._
Wata irin zufa ce ta hau tsatstsafo mishi, _ya Ilaahi_ anya kuwa number daidai ce, kada fa ace _yaga samu yaga rashi._
Ya tuna cewa yana da d'aurin auren _JB_ dole ya tashi ya hau shiri. Yana toilet wayarshi nata ringing.
Har ya fito, kira na k'ara shigowa, ya duba, sunan _JB_ ne ya fito wato angon.
_UK me kuke nufi ne, ya zaku barni ni kadai gashi har na shirya banga ko dayan ku ba."_
"Kai Dallah can wanka nake, kaga sarkin zumudi dududu, k'arfe tara da rabi fa yanzu, zaka dami mutane."
_"Iyehh, Lallai ma UK wato kaima kabi layin su Mubarak kenan koh, kada ka manta ni yayanka ne yanzu."_
Ya shek'e da wata dariya, "Haha, gaskiya ne, dan rainin wayo."
_Please UK don Allah ka taho."_
_
"Okey ganinan Allah, k'arasa shiri zanyi kawai.
"Yawwa aboki, abokin gwauran taka."
"Hmm, Allah sai kasa na fasa, zuwa yanzu."
Ahh yi hak'uri, rufamin asiri.!!
Ukhasha yace,
"Kai da bikin naka ma, damuwa ya gadar min."?
_"Ahaba UK kada dai wannan matar, ta k'ara kiranka neh."?_
"No no no, ba ita ba, wata yarinya ce fah ranar yinin nan."
"Oh wai wacce akace ta yarfa ku koh."?
Suka shek'e da dariya duka.
Hmm, au kace har kaji labari, gaskiya su _NZee_ (_Nazeef _)munafukai ne.!!
"Ka bari kaidai ku nutsu don sai kun nemo min ita kaida amaryarka.."
_"Haha, UK ashe gaske ne, kenan ka zurma".._
Yai ajiyar zuciya. "Ya na iya.? Suka had'a baki _JB na cewa "Allah ne ya kamaka"_
Shima na cewa "Allah ne ya kamani ni."
Haha, kaima ka fad'a ko da kanka, amma babu komai aboki Allah ya sanya alkhairi.
To ya zakayi da 'yar kwailar can.
"Kai chab zaka b'atan rai wallah, kusan yadda zakuyi da ita dai."
_"Hmm, Allah ya kiyaye ka Aboki, amma akwai dan barwa.!_
Amin ango, bari na shirya kada mu b'ata lokaci.
An kammala komai anyi d'aurin aure, su Ukhasha ansha zirga zirga har zuwa lokacin kai amarya. Hidimar da suka shiga ne, yasa ya d'an manta da damuwar shi, don bai ma samu ya zauna ba. Allah-Allah yake washegari tayi, ya bujurowa da ango abinda yafi damunshi, wato inda zai sami
Hafsah..
___________________
Ta tsammaci kiran Jamila amma shuru, sai yau da daddare, sai ga kira, da wata number.
"Hello,
Hafsah ma tace Hello,
"Kina magana da Jamila ne."
Murna ta cika Hafsah, "Oh ya kike.?
"Lafiya lau, wannan ne number sai kiyi save."
Okey Hafsah ta fad'a.
"Bye bye."
Jamila tace, tare da katse wayar.
Hafsah bataji dad'in takaitacciyar wayar da sukayi ba, taso suyi 'yar hira, don ta gano wane mataki Jamilan ke kai."?
Amma kuma taji dad`in samun number, tayi saving d'inta da nufin gaba ita zata kira..
Ukhasha, yayi juriya, har ya bari akayi Kwanaki uku, da bikin Jabeer ( _kafin ya fara mishi zancen Hafsah_ )
Duk kwatancen da yayi mishi kuma, sam Jabeer ya kasa gano wacece..
Kuma yaga alamun Ukhasha d`in ya damu sosai.
"Wai Aboki na baka san sunanta ba neh."?
Um kai dai bari JB wallah, na fada maka har ganinsu na karayi ranar dinner d'inka, ( _Ya bashi labarin yadda abin ya faru._) ka ga amma kullum sai nayi trying number amma har yau _is switched off._
Kasan taimakon da zanyi maka."
JB ya fad'a.
"A,a"
Kaga nan da k'arshen sati zamu, d'aga (_zasu bar k'asar_) so kazo gobe kawai akwai photos da video na biki ko za,a dace.!!
Murna ta cika ukhasha, kuma fa JB ya kawo shawara.
"Wow thank you angon Aisha, gobe da asuba zaku ganni.
"Hah, kazo d`in kaga mana."
"Nagode kai dai."
"Okay UK ana tare fah."
Sukayi sallama, suka katse wayar.
Ya tashi ya nufi d'akin hajiyarshi.
Suna zaune ita da su maryam da Fadwa suna kallo.
Ya nemi guri a k'asa ya zauna, Hajiya ta kalleshi a zubo maka abinci."?
Ya daga kai alamar "eh.
Maryam jeki zubo mishi abinci.
"To Hajiya."
Sannan ta mik'e ta mik'e, ta fita.
Sai lokacin kuma ya kalli Tv, d`in, wani shiri ake gabatarwa, dama an hasko wata mata ne tana ta jawabi, sai yanzu aka hasko mai gabatar da shirin.
Gabanshi, ya fad'i, saboda bayyanar fuskar da yake ta bulahin nema.
Ya ware ido, yana kallonta, yanayinta, kamannin ta, Itace dai daya gani a zahiri.
Zata fara magana, kenan d'if TV ta d`auke da alama NEPA ne suka d`auke wuta.
Ranshi yayi bak'i ya mik`e zai fice, shi ko jira ma a kunna solar ko yaje ya kunna ma baiyi ba.
Hajiya ta kalleshi. Ina kuma zakaje."?
Ina zuwa Hajiya.
Ya fice ya nufi d'akinshi.
Number JB ya kira.
_"Ya akayi kuma."?_
"Kaii yarinyar nan zata zautani fah."
_Meya faru."?_
Wallahi a TV na ganta yanzunnan tana gabatar da program.
"Hmm, kaii UK kodai zaucewar ce ta sa take maka gizo."?
"Ka manta, ai ban zama _majnoon_ d`in ba tukuna.
Jabeer yayi dariya, "ah to naga abin naka yayi over ne, ni ka dameni ma fah.
Hmm, to ya zakayi dani, ni nace ku gayyatota bikin ku."?
"Hmm, haka kace koh."?
"Aa sorry Yayana tuba nake."
Abin ya bawa JB dariya, _"Lallai, su Mubarak su zo akwai labari._
A,a JB kada kamin haka plz ka san halinsu bazan iya dasu ba.
Shikenan toh, amma ko ban fad'a ba zasuji labari kaidai sai kazo.
Washe-gari daya je, Gidan JB, bai bata lokaci ba ya k'ara mishi jawabi, amarya na zaune na jinsu, sai da angon yayi tambayeta sannan ta magantu, _"Aysha kin gane ta._?
"Ina tunanin ko H Hamid, ko kuma Ummi nuhu, sune suke service a gidan tv."
Please ki taimaka bari naga photos d`in.
Photo album, na bikin suka miko mishi, sai da yaje kusan tsakiya kowanne photo kallon k'urilla yake mishi, ango nata zolayar shi shida amarya. Sannan da kyar yaga wani photo, ta gefe, fuskarta bata fito sosai ba, anyi, musu tana lik'i.
"Wannan ce.!!
Ya fad'a da sauri kuma da k'arfi.
ango ya karb'a ya mik'awa amaryar.
"Eh Itace.
Tare suka hada baki shida JB wajen cewa, "wacce daga ciki."?
"Hafsah H. Hamid ce."
Azuciyar shi ya maimaita sunan _Hafsah_ sunan hajiyarshi kenan fah.!!
"Duba don Allah ki taimaka min da number ta."
"Ai kasan chanjin layin nan da nayi Allah yasa akwai contact d`in."
Ta fada tana duba cikin wayar, kaf babu number aciki.
Ta dube shi itama ya dan bata tausayi wallah kaga babu.
_Innalillahi."!!_
JB ya dafa shi, kada ka damu, ai bazamu bar k'asar nan ba, sai an samar maka solution, don bazan zuba ido a zautar min da UK ba.!!
Ukhasha, yaso ya tambayi amaryar _"ko tasan gidansu ta kwatanta mishi.?_ Amma sai ya fasa, yaji nauyin hakan, kada suga kamar ya takura musu.
Abisa tilas ya hak'ura, ya dawo gida a sanyaye, don kafin ya taho ma, sai da aysha ta gwada number wata k'awarsu, don ta turo musu number amma wayar tak'i shiga..
_Sun rabu akan, ana samu JB zai turo mishi. Yayi musu godiya sosai, sannan yabar gidan.._
A takaice dai sai ranar alhamis da dare, sannan number tazo, wajen ukhasha, shima da daddare wajen k'arfe shad'aya, duk zumud'inshi, dole ya hak'ura zuwa da safe. Yayi godiya ga Allah ba adadi.
Washegari sakayau yake jin shi, cikin nishad`i da karsashi yayi shirin fita office.
Ya nufi d'akin hajiyarshi ya mata sallama, sannan ya fito. Har ya isa bakin motar shi zai sa mata _Key_ yaji an kwalo mishi kira. _Yaya Ukhasha!!_
Mahseem ce autarsu cikin uniform.
Ta Kara'so da gudu ta d'ane shi.
"Muhaseem zaki karya ni fah.
Tayi dariya. Sannan ta sake shi.
"Yaya don Allah na bika ka sauke ni a school."?
"Eh muje." Ya zagaya ya bud'e mata k'ofar ta shiga. Sannan shima ya dawo ya shiga ya zauna. Ya tada motar aka bude musu gate, suka fita.
Suna tafiya tana damunshi da hira, "Yaya, wai yau Friday koh."?
Eh, ya akayi."?
"Zaka je dani Masjid d`in abba."?
"Waya ce miki mata na zuwa masjid."?
"Our islamiyya teacher, kuma su yaya Maryam suna zuwa wataran, amma sunki suje dani."
"To zanje dake, amma ni ba masallacin Abba nayi niyyar zanje ba, amma tunda kinaso to zamuje sai ki shirya da wuri, nima zan dawo da wuri."
"Thank you, Yaya."
Tayi shuru, sannan ta kuma samun abun cewa, "Yaya wai aunty Fadwa tace wai an kusa bikinka."?
Yayi murmushi me sauti, _"Kai fadwa ta raina shi, wato abin ma har ya kai a gaban Mahseem suna gulmar shi._?
Ta katse mishi tunani "Eh Yaya."?
Ya d'aga mata kai, alamar Eh."
"To ya sunanta."?
Ahankali yace mata, "Sunan Hajiya ne da ita."
"Yehhh, yaya mu dinga ce mata hajiya itama."
"To, kiyi mana addu,a idan mukaje masallaci."
"Yaya me zance toh."
_Kice Ya Allah ka taimaki Yaya ukhasha!!._
"To yaya zanyi, dama "Abba kullum sai yace mu dinga yin addu,a."
"Yawwa, 'yar autar mama, nagode.
Yayi parking, sannan ta fito, don anzo k'ofar makarantar su.
"Yaya adawo lafiya, zan shirya da wuri.
Ya daga mata hannu. Yana gani ta hango wasu k'awayenta ta tafi da gudu wajensu, sai ta bashi dariya ma.
Sanda ya dawo har Mahseem ta gama shiryawa, lokacin, shikuma, yana d'akinshi ya gama shafa mai, tazo bakin k'ofa ta tsaya.
Yana jiyo, hayaniyar su Zainab daga cikin gida, suna tsokanarta, _"Inyeh yau za,a masallacin Abbah!!_
"Salamu alaikum. Tayi sallama daga waje, yayo mata magana daga ciki, don bazai bata izinin shigowa ba, "Mahseem ki jirani kinji, kije d'akin Hajiya."
Ta koma ciki shi kuma, ya cigaba da shi shirin shi, cikin nutsuwa, gefen zuciyarshi da tunanin Hafsah, so yake sai ya dawo daga masallacin sannan ya gwada kira. Yana so ne sai yayi addu,a sosai ya nemi d'aukin Allah da alkhairansa cikin abin.
Yayi kyau cikin farar shaddar shi, da bak'ar hula, bakin takalmi, da kuma agogo.
Ya nufi d'akin hajiyar, shi kanshi daya ga Mahseem sai da dariya tazo mishi, taci hijabi har k'asa, ga tasbaha a hanunta.
hajiyar bata nan ma. Tana ganinshi ta taso da gudu ta rik'e hannunshi.
Shima ya kama nata, idon Fadwa akansu, zatayi magana irin ta zolayar data saba ya kafe ta da ido. "
Zoki mana photo, sai kiji dad`in kallon mu sosai."
"Kai Yaya ni baku nake kallo ba.!
Ta matso ta amshi wayar, tayi musu, sannan ta mik'a mishi kayarshi.
_Ya karb'a sannan yaja hannun Mahseem, suka fita, tana mishi hira.._
📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*
♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai)
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh )*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*
📄 *48- 49*
*Yaune,* suke yinin, Fateemah, sun kacame, a wajen biki, ana ta rawa...
Bikin na matuk'ar dad'i a gurinsu, sun had'u duka 'yan matan, har da matar Nazeer ma, anata rawa, da yake, yinin iya mata ne babu mazaa, ko ango bai halarci wajen ba.
Adaidai wannan lokacin kuma Ukhasha nata kiran number Hafsah tana ringing amma ba,a d'aga ba. Da ya kira karo na uku, sai ya hak'ura kawai.
Yayi shuru ya zuba wa _number_ ido, tunani yake kodai, ya hak'ura ne."? Sai kuma yayi wani tunani. _"A yadda take, kuma tana irin wannan aiki a media, dole baza,a rasa, masu damunta da kiraye-kiraye haka ba. Saboda haka zai jinkirta zuwa wani lokaci kawai._
Zai cigaba da addu,a idan da alkhairi akan abin, Allah ya sauk'ak'a mishi samunta. Wani tunani mara dad'i ya d'arsu aranshi. _Yanzu idan an riga an bada ita fah?_
_"a,uzubillah_
Ya fada a fili, bai ma san ya zai kwatanta halin damuwar da zai shiga ba idan haka ta faru..
Da Wannan tunanin kuma ya shiga wani tunani, na daban, wata zuciyar ta karanta mishi.
_To ita yarinyar mutane da kabar ta da damuwa akanka, ya zakayi da ita.. Ko kana ganin zaka samu yadda kake so, alhanin kana da alhakin wata akanka."?_
A hankali ya furta, _"Allah ya gani bana sonta, bazan iya zama da ita ba._
_To ka sama mata mafita, tunda kana kokarin kulla taka soyayyar a wani waje._
Wata zuciyar ta fad'a mishi haka.
To wacce irin mafita, menene mafitar."?
Ya tambayi kanshi.
Kamar an tsikare shi ya jawo wayarshi, ya danna kiranta.
Cike da farin ciki ta d'auka.
Tayi mishi sallama, ya amsa cikin sakin fuska. Tana mamakin sauyawar shi, cikin kwanakin nan.
"Bahijja!!
Ya kira sunanta.
Na,am.
Ta amsa ad`an sanyaye don tana tsoron abinda zai fito daga bakin shi.
_Sau dayawa indai zaiyi mata magana mara dad'i yafi bata hankalin shi, da kuma jawo hankalinta._
Yaushene ma kika ce min zaki cika _twenty years.?_
Farin-ciki ya mamaye ta. _Kodai party zai had'a mata ne."? Sai kuma ta tuna irin gidansu, sannan ta tuna data gayyace shi partyn graduation, yace mata baya zuwa party._
Tana son jin abinda zai fad'a mata don haka tace, "Nan da _three months._
"Okey.." yace mata kawai.
Tayi shuru tana son taji k'arin bayani.
_Wato ma ko 20yrs yarinyar bata cika ba. Ya fada a zuciyarshi. Baya son ta shiga damuwa a k'ananun shekarunta. Tabbas ma yaga tsaurin ido da k'ok'arin