Author : KARIMA TIJJANI MANSUR Category : Romantic Hausa Novels
dake falon tace "Ku d'akko Assignment d'inku mana."
Nan suka mik'e harda rige-rige.
Nan ta hau nuna musu yadda xasuyi,sannan ta basu lokaci su gama su bata ta duba.
Littafin zainab ta karba taga duk tayi shirme.
A karo na uku ta kuma nuna mata ta kasa. Ran Hafsah ta b'aci sai ko takai mata duka,ta sameta a fuska.Aiko ta kwalla ihu.
Kukanta abbansu ya jiyo shi da mama wadanda suna falon abban.
Dukkansu suka nufo d'akin
"Zainab me akai miki? Abban ya fad'a yana kallonta.
kafin tayi magana Amira tace abba yaya Hafsah ce ta dake tana ana ta nuna mata yadda xatayi assignment ta kasa, nifa har na gama nawa".
Ya d'an yi shiru, kafin yai magana Mamansu ta saka baki "Au shine zaki dake ta, bada koyo ake iyawa ba?"
Ta fad'a tana kallon Hafsah. "Mama wallahi fa ko a makaranta wasa take."
Abba ya Kalli maman kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. ya wuce ta nufi falonshi. Itama Maman binshi tayi ta zauna kusa da shi. Ya kalleta ahankali yace "Amma dai kinsan halin Zainab d'inkoh?
"Bana son tana dukansu ne"
Ki daina yi mata fad'a a gabansu,sai su rainata ai.
Ya fad'a ya juyar da kai gefe.
Ta kalleshi "To na daina in sha Allah"
"Ayi haquri"
Ya juyo yana murmushi "Nace kinyi laipi ne?
tayi dariya "ai an tab'a maka 'yar lelenka." Yai dariya
"Haka kika ce kenan."
Ya kwalawa Zainab kira. Ta zo
Tayi sallama sannan ta durk'usa.
"Abba gani"
Ya d'an tsare gida
"Ke ba kya ji Koh?
A haka kike son zama doctor d'in kina wasa?
Cikin muryar mai son yin kuka tace "Abba ba wasa nake ba"
To me yasa ba kya Mai da hankali, kina so ace sunfiki k'ok'ari Koh?
"Kayi haquri Abba"
Ya d'an sassauta murya
"To ki daina wasa kifisu ko'kari kinji ni nasan abinda xan baki"
"Kije ki ba yaya Hafsah haquri, kuma kice nace tazo"
"To abba"
ta tashi ta fita.
Hafsah taji kamar fad'uwar gaba da Zainab tace kije inji Abba.
Ta d'an zauna a d'osane. "Abba gani"
Ya zubo mata ido.
"Me kika tsaya yi a k'ofar gida d'axu?
"Babu komai abba"
"Babu komai?
"Um"
"Wa na ga kina ma magana."??
Ta kwaso in'ina tace
"Am wa wai cewa yayi tambayata zai yi."
Ya jinjina kai.
"Ki daina kawai daga yau, kinsan na hanaki kula samari Koh?
"Allah Abba ban sanshi ba"
"Ya isa tashi kije na dai fad'a miki."
Kuma kuyi addu,a kafin ku kwanta.
"To mama sai da safe"
"Allah tashe mu lpia"
Ta baro falon cike da Murna. bata zaci fad'an abba zai tak'aita a iya haka ba....
*Need your comment to encourage me* ππΌππΌ
*Idan anga kuskure ayi haquri ajizanci na d'an adam.sannan ni sabuwa ce a wannan fage!*
*HAJEEYAH KAREEMERH ce dai*π
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): *ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart story*
ππ
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to:*
*Unique In Your Love Heart Members.*
π *7*
*A WANI B'ANGAREN*
wani madaidaicin gida ne na k'asa, acikin wata unguwar da kai tsaye za,a kirata ta talakawa.
Wata budurwa ce wacce baxata wuce shekara 17 ba (sa,ar Hafsah) ta fito daga d'aki sanye da uniform na makarantar gomnati a jikinta.
Ta leqa d'akin babarsu wacce ke zaune ita da uban a d'akin "umma zan tafi"
Ta tab'e baki "Sai kin dawo."
Ta Kalli babannata Baba kud'in makaranta?
"Bani da shi"
Kai tsaye ya fad'ar
ta langab'ar da kai tom na tafi"
"Shashashar banza!
Dama zama kikai kina mata tallan kunun da kun sami kud'in kashewa, mtss wai ke 'yar Boko!
Ita dai ta fita cike da takaici.
Tana fita titi ta hango motar su hafsah na tawowa xa,a kai su makaranta.
Hafsah ma ta hangota tace wa Nura "Don Allah kaga Jamila can mu d'auketa yace "Tom."
Suna parking ta bude motar ta shiga.
Bashir kusa da driver sai Hafsah, Zainab da Amira a baya.
Hafsah ta kalli jamila "Ya naga idonki yai ja?"
Hawaye ya zubo mata "Babu komai.
"Kiyi hak'uri"
Inji hafsah.
"Na gaji wallahi Hafsah wai Salim ma... Sai ta sa kuka..
"Ki daina sanya damuwa.
Daidai lokacin anxo k'ofar makarantar su jamila.
Hafsah nagode yau xan shigo da wuri kafin lokacin islamiyya.
Ta fad'a tana goge fuskarta..
"Tom jamila" ta mik'a mata wata leda snacks ne aciki da ake musu gida saboda zuwa makaranta.
Ta karb'a tayi godiya
Ta bude motar ta fita.
Hafsah ta girgiza kai cike da tausayin jamila.
Mufida ta Kalli Hafsah "yaya wai wannan k'awarki ce?
"Eh"
"Amma naga uniform d'inta duk squizing?"
"Ke ina ruwanki?
cewar Hafsah.
Ahaka har suka isa makaranta, driver ya sauke su. Hafsah ta nufi ajinsu SS 2, Bashir SS 1, Zainab Jss 2, Mufida primary 5.
Bayan an taso kuwa babu da'd'ewa jamila tazo gidan.
Yau mama bata nan.
Suka k'ule a d'akin hafsah.
"Hafsah. Rayuwar gidanmu na bani mamaki kamar ba gidan iyayen da suka haifeni ba.
Don kawai ina da son karatu?
Ta d'anyi shiru sannan ta d'ora.
Duk gidanmu babu wanda ya zarce primary yaya Habu, yaya jamilu Babu abinda suka sani sai shaye-shaye.
Ahaka rayuwar su rukayya ga su shafi,u (k'annenta) xata cigaba? ko fa makarantar allo basa zuwa... Kinga banda 'yan d'akinmu ga 'yan d'akin su Ummi Banda talla da yawo..
ya isa jamila komai yai farko zai yi k'arshe ki ci gaba da addu,a Allah ya taimake ki ki ci qualifying."
"Allah yasa hafsat"
"Rayuwarku na ban sha,awa iyayenku masu kud'i...
Hafsah ta d'an dake ta a baya "Kinjiki" "ke ina salim"?
Hawaye ya ciko a idanunta
"shekaranjiya ya zo yace min Mamansu tace wai 'yar k'anwarta zai aura... Ta fashe da kuka..
"Ya salam"
inji hafsah.
Hafsah ina son salim, wallahi tunda aka rabamu ji nake bani da wani sauran buri a rayuwata. Kinga duk da shi d'an masu kud'i ne (rufin asiri) yana sona har cewa yayi zai d'auki nauyin karatu na, duk da talaucina ahaka yake sona, amma an raba ni da shi... Bikin nashi ma baifi wata biyu ba.. ta kuma fashewa da kuka..
Hafsah ta d'an daddaki bayanta kiyi hak'uri ki dinga addu,a Allah ya baki wanda ya fishi.
ki daina kuka kinji...
Hafsah ta mik'e ta zubo musu abinci shinkafa da miya da Naman kaji fal,
"Ki tashi ki wanko fuskarki ki zo ki ci abinci"
Cewar Hafsah tana ajye plate d'aya agaban jamila..
ta mik'e ta shiga toilet don yin yadda Hafsah tace..
Suna cin abincin jamila tayi wani murmushin takaici tace "Rabon da Inci nama wajan wata d'aya kafin salim ya daina zuwa wajena... Kin san har 'yan rahoto ne da babarsu a unguwar mu wanda in yazo ake xuwa a fad'a mata"
Hafsah tace "tab"
Akwai Sa,idinai"
Hmm abinda ya sa ma yaxo jiya ya fad'an kada inji labarin bakinshi a gari (hawaye ya xubo mata) ta girgiza kai "Allah sarki salim d'ina wai an raba mu??
"Wai aure xai"?
Ta kifa kanta kan gadon Hafsah..
Hafsah ji sakwato tana kallonta mamaki abin ya bata 'tana cikin cin abincinta kuma sai kuka??
"Jamila don Allah ki cire shi a ranki!'
Kamar an tsikareta ta d'ago cikin hawaye tace "Hafsah baki san so ba shiyasa. Banjin xan tab'a daina son salim har abada..
Naji ki k'arasa cin abincin mu tafi islamiyya kinga lokaci ya k'ure."
Ta fad'a batare da ya bawa furucin jamilar na k'arshe muhimmanci ba don bata ga wani abin damun mutum ba alhalin uwarshi bata so!
Abu d'aya maganar tata ta tuna mata 'Saurayin da yazo jiya'
Ta d'an tab'e baki,sai kuma tayi murmushi da ta tuna hausarshi..
Aiko suna fita suka ganshi a k'ofar gida aiko ya nufo su..
Hafsah ta cake ta tsaya "yan mata"
Ya fad'a ad'an tsorace tace
"wai kai meye ne?
"Gobe ne zan koma schl kuma bamu sami time na magana ba koh?
Ta k'ank'ance ido ta Kalli jamila.
ita dai jamila tayi kasa fahimtar su.
"Am kaga please kada ka k'ara xuwa wajena kaji?
ya waro ido why, please baby why..?
"am tawo mu tafi"
ta jawo hannun jamila,suka fara tafiya.
yabi bayansu
"plz baby when kike so naxo?
Hafsah ta juyo tsoro take kada yau ma Abba ya ganta
"I don't know!
suka cigaba da tafiya yana binsu a baya har suka kusa zuwa islamiyyar.
jamila tace "Hafsah wannan baturen naki bai bar binmu bafa?
"shi yaga zai iya"
"Aiko Hafsah wannan ba kalar wukak'anta wa bane "
"Mts to me zanyi mishi?
to ki Sallame shi don Allah"
dai dai lokacin ya kuma cewa
"Please baby yaushe xan dawo?
cike da shak'iyanci tace "Sai bayan wata bakwai
"Mene kika ce?
"after seven months ehe.
suka shige cikin makaranta suka barshi yana kallonsu.
yayi murmushi ya juya zai koma k'ofar gidansu inda ya bar motar sa.
ya tafe yana tunanin gobe zai bar k'asar don k'arasa karatunshi wanda zai d'aukeshi wata bakwan da ta ambata mishi.
yayi murmushi
"I will come back to you again!...
*Hajeeyah Kareemerh ce*
*I need your comments to encourage me!*ππΌππΌ
[1/11, 12:09 AM] Hajeeyah Karimah (Writer): β₯β₯β₯β₯
*ZAZZAFAN SO*
(Guba ne)
*A broken*
*heart story*
ππ
Story and writing by:
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah Kareemerh)*
*Dedicated to:*
*Unique In Your Love Heart Members.*
Wannan page naki ne aunty nah *AYSHA NIGER* ALLAH YABAR ZUMUNCI AMINπ
π *8*
*BAYAN WATANNI BAKWAI*
*A* bubuwa da yawa sun faru cikin wad'annan watanni bakwai a rayuwar Hafsah, yusuf da kuma jamila..
Yamma ce mai cike da ni'imar hazo daya mayar da yanayin garin kamar hadari, kamar kuma duhun magriba..
Tafiya Hafsah take yi cikin rashin kwarin jiki, kana ganinta kasan akwai rauni acikin zuciyarta..
Ta tura gate d'in gidan su ta shiga.
Bayan tayi sallama tare da cewa "Mama na dawo"
(yau su bashir sun rigata dawowa)
Kasancewar daga islamiyya take..
D'akinta kawai ta nufa, don alokacin babu abinda take so sai kad'aici..
Ta ajye Jakarta a ma,adanarta ta cire hijabin sannan ta sauya shigarta daga uniform zuwa, 'yar doguwar riga mara nauyi.
Ta kwanta akan gadonta shiru tayi, wani abu take son tunowa na kamar shekaru biyu baya...
Ahankali ta rufe idonta tana tuno lokacin.
*HADUWARSU DA JAMILA*
Wata rana suna tafiya ita da bashir an taso su daga islamiyya, ranar kawai sai suka biyo ta wani layi..
Sunzo daida k'ofar wani gida wata ta fito da gudu daga gidan da bokiti akanta (ruwan garai) kullin kunu ne aciki.
Zasu gifta ita kuma ya fito aiko sai ta tank'ad'e bashir, saura k'iris ya fad'i..
"Kai Kai Kai"..kika bugeni??
Bashir ya fad'a yana mata kallon k'askanci.
,"Don Allah kuyi haquri wallahi biyo ni akayi ni bana son tallar nan.."
"Mts"bashir ya ja tsaki.
Hafsah ta kalleshi "Haba bashir ka hak'ura mana..
"Hmm, kina ga ta buge mutane..hmm
Shikenan dai."
"Ta Kalli Hafsah tayi murmushi da hawaye a fuskarta.
Ina son islamiyyar nan taku, nima xan tara kud'i in shiga."
"Tab da kud'inki sai kace baki da iyaye??
Yusuf ya fad'a cike da izgili. Hafsah ta harare shi, Kai bashir ina ruwanka?
Sai da suka isa titi suka rabu tace wa Hafsah "In sha Allah. xan shigo islamiyyarku ina so ki zama qawata"
Hafsah tai mata murmushi. "Shikenan to bye bye".
Da suka isa gida bashir ya fad'a wa mama Wai "yaya Hafsah ta zama k'awar mai kunu. Sai da ta taka mishi birki sannan ya daina tsokanarta.
Ba,a fi sati biyu ba aka kawo jamila islamiyyarsu Hafsah cikin sa,a kuma ajin su hafsan aka kawo ta.
Hafsa na son jamila sosai, duk da haka fahimci jamila 'yar talakawa ce amma tana da k'ok'ari da son karatu.
"Zan dinga zuwa gidanku kina koyamin turanci, ni makarantarmu ba,a mana.."
Cewar jamila, lokacin da suke tafiya bashir yai wa Hafsah magana da turanci
"wllhi yaya, am tired!"
Hafsah tace "To sai dai alhamis da juma,a bayan an taso daga makaranta Koh?
"Eh"
"Ajinki nawa inji hafsah"
Jss 1 nke
Nima haka "we are d same."
Jamila tayi murmushi.
Tun daga ranar jamila ke xuwa wajen Hafsah duk ranar alhamis da juma,a, mama tun bata so harta hak'ura dama abba bai san da ita ba.
Azuwan da take ne in suna hira take bawa Hafsah labarin gidansu.
'Shidai mahaifinta irin mutanen nan ne 'yan gargajiya da babu ruwansu da harkar addini balle Boko..
Ya tara 'ya'ya a kallah 23,da mata uku.. Banda wadanda suka shigo suka fita. Mahaifiyarta, kuma irin matannan ne wad'anda suka d'auka cewa amfanin 'ya mace a wajensu shine 'ta nemo musu kud'i.'
Jamila yarinya ce mai hazaqa da baiwa(ko wanne d'an Adam na da baiwa)
Yawancin yaran gidan talla suke yi inda iyayen su mata ke d'ora musu. Jamila ta tsani talla shiyasa tayi bak'in jini gurin mahaifiyarta.
Yawan shige shigen mak'ota da kwad'ayi halin yan gidansu ne saboda basa wadata da abinda ake basu.
Jamila naso taga rayuwarta ta chanja kullum burinta Allah ya sa ta xama mai kud'i. Tana da himma ko wajen karatu takan zo ta biyar ko ta shida, akwaita da son kwaikwayon abinda taga wani yayi ya burgeta imma a film ko a rayuwar xahiri. Amma dake iyayenta basu da damuwa kan cigaban rayuwar 'ya'yansu basu lura cewa jamila 'Kadara' bace! ko abar a lura da karatunta bace.
Tana primary 6 aka kawo musu wani Malami d'an Tp. A irin surutun jamila ya gane irin rayuwar gidansu haka yasa ya sanya a ransa xai kaita gaba da secondary. Ya ko kaita..
Wanda haka ya q'ara jawo tsanarta a wajen iyayenta kiri-kiri xa,a ce ta d'auki tallah tace ita dai makaranta xata.
Mutsiyaciya! 'yar iska ni halin wannan yarinya kamar bani na haifeta ba!
Iri-iren aubun da take samu kenan daga bakin mahaifanta duk da ba ita kad'aiba kowa ma agidan yanayin laifi bai wuce a dake shi ace "tsinannen yaro, shege Mutsiyaci!
Ai ko tsiyar na binsu tunda duk yaran babu na mora.
(iyaye a kula da furuci ga 'ya'ya)
A hakan jamila ke rayuwarta cikin k'unci har lokacin da ta shiga Jss 3, inda suka had'u da 'salim' yana taimakawa rayuwar karatunta sosai tana matuqar sanshi har xuwa lokacin da aka rabasu.. take fad'awa Hafsah..
"Nifa Hafsah xuciyata tayi k'ek'ashe, duk gidanmu babu wanda ake ganin d'abi iska sai ni.. Bayan ga yayyena mata nan duk suna yawonsu abinsu, amma wai ni ake cewa salim ya lalata shiyasa yake kashe min kud'i akan bokon k'arya.."
Wallahi Hafsah in kinga yadda in salim yazo baba ke korarsa sai kin d'auka bashi da zuciya a k'irjinsa shiyasa yake dawowa"
Ni ba wannan ba ma aibun da suke ja min "Wai in je indai duniya ce xan gani!"..
Wallahi idan suna min kallon 'yar iska ji nake kamar in bar gidan in tabbatar musu da hakan!!
"Ke jamila don Allah ki yi ha'kuri ki saba da irin wannan rayuwar kada ki k'ara ja wa kanki masifar yawon duniya.."
Shikenan Hafsah amma wallahi rayuwar gidanmu na rasa da sunan da xan kirata, ace babu wanda zai fahimceni? Babu mai gane cewa ina son kawo mana sauyi ne? Ta fashe da kuka.. Kinga ya Habu duk da yana shaye-shaye shi kad'aine ke tausayin yana cemin
"ai su baba ne ya cucesu,tun farko ba ruwanshi da makarantarsu sai dai daga yaro yayi 15 yace ya cire mishi kwano daga gidan ya fita ya nema.. "Gsky kiyi karatu "a dama da ke kema!!
Haka fa yake fad'an Hafsah..
"Allah y kyauta.. Abin Hafsah ke iya fad'a kenan idan jamila tana mata halayyar k'orafin gidansu, don bata da abin cewa d'in... in ba haka ba.
...Yanxun da take tunanin nan wani labari ta jiyo a islamiyya '
wai Jamila tayi cikin shege babansu ya koreta'
Xata iya tuna rabonta da jamila wata d'aya kenan bata xuwa islamiyya kuma bata xuwa gidansu.. ita kuma Hafsah ba xuwa gidansu take ba, mama ma ba xata barta ba.
A yadda aka bata labarin wai cewa akayi jamilar wani malaminsu ne a makarantar boko suke soyayya har ya yi alk'awarin kawo mata kud'i..to kuma sai yace xai biya mata kud'in Waec da Neco don bataci qualifying ba. Ance har fita sukeyi da ita da shi..
Labarin dai ruwaya kala-kala.
A iya sanin Hafsah jamila ta fara bata labarin 'sir Garba' bayan kamar wata d'aya da bikin salim..
"Hafsah yanxu wani malaminmu ne yake so na,kuma yana da mutunci saurayine black beauty, kuma ya Had'u,Allah sai naji duk ya sa na manta da tabon da salim yai min.."
"Allah ya tabbatar da alkhairi"
Abinda Hafsah tace kenan.
Bayan haka kuma jamila tazo mata da k'orafi..
Hafsah sir ya fiya wayewa da yawa "ko dan English ya karanta?.. bai da buri sai na ya rik'e Hannuna, ko yace na mishi kiss!!"
"What??
"Jamila ki rabu dashi"
Tai mata kallon rashin fahimta
"Tab Hafsah kin san son da nake mishi kuwa..?
Wallahi ko baba wannan karon baxan yarda ya tabani da 'Sir Garba' ba, d'an gayu nah"
Shikenan jamila ni na rasa me kike ji a soyyaya"
"Haha Hafsah, yaushe xakuyi biki ne a familynku ina son bikin 'yan gayu wallahi"
Hafsah ta harareta "ke mayyar biki ce!"
Daga lokacin halayyar jamila ta d'an so ta chanja Don 'idan Hafsah ta lura jamila ta rage fad'a mata tsakaninta da sir, sannan ya sai wa jamilar waya, kuma xa,a ganta cikin kaya masu kyau, Wanda da Indai ka ganta da suturar arziki to kwancene Hafsah ta ba ta..
Hafsah ankawo wata yarinya ajinmu SS 2 d'innan kanta na hayaki..bata kallon kowa da gashi kinganta kuwa tasha bleaching..Amma ni kuma muna mutunci da ita.
Gata komai taxo dashi sai ta bani kamar dai yanda muke dake..
"Hmm Hafsah tace.
Hafsah wai don felek'e yarinyar nan har tambayata take wai "Ance wancan Malamin saurayinki ne?"
ni ko nace mata ''eh mana"
"Wai keko me kika gani mai xai Baki? "
Niko nace "bansaniba"
shine harda ban hak'uri yanxu ko da ita muke xuwa wajanshi ma?
"Wajanshi kuma?
Eh mana karbar pass questions muke xuwa."
yanxu kuma tace min
"Wallahi bai da aibu musha soyyarmu"
To tun daga ranar jamila bata kuma xuwa gun Hafsah ba yau wata d'aya kenan..
Kiran sallar da ake ne ya dawo da ita daga tunanin da yasa ta jik'e sharkaf da gumi.. Me yasa sai yanxu? Saida jamila ta fara tasawa a sha,anin rayuwa sannan xata b'ata rayuwarta..?
Sai da taci fiye da rabi na gwagwarmayar ta sannan xata b'ata shirinta?
Duk wad'anda suka taimaka mata abaya bata basu kanta ba sai shi??
Ita ko bata ga amfanin soyyayya ba tun da bata da rana.. Ta share hawayen fuskarta ta tashi ta d'akko Diary d'inta ta fara rubutu acikin cikin k'unar xuciya da takaici.
*The day I will never forget*
Haka ta rubuta sannan ta cigaba da rubutun..
Mamansu ta turo k'ofar d'akin "Au na dauka a kwance kike.. To anyi sallar magariba ma ki ajiye shirmen nan.
"To mama"
Ta rufe ta Mik'e ta shiga toilet tayo alwala, tasa hijabi ta tayar da sallah..
Ta da'de tana addu,a bayan ta idar har da hawaye, ta nemi dalilin aikata haka da jamila tayi ta rasa don aganinta 'Talauci ba hujja bane.'
Tana zaunen kuma tana tunane - tunane barkatai bashir ya shigo cikin magana kamar rad'a yace "Yaya Hafsah yanxu xan shigo gida wani d'an gayu yace in kiraki don Allah"
Ta zaro ido ta dafe k'irji "Ni kuma bashir.?
"To waye?
Ya had'u fa gayen, ki fita ki gani tunda abba baya nan..
"Ni irin motarshi cema tamin." Ya fad'a yana dariya..
Ta shige toilet kamar antsikareta ta wanko fuskarta
Ta chanja doguwar rigarta xuwa b'akar after