Author : KARIMA TIJJANI MANSUR Category : Romantic Hausa Novels
11:00am, don haka sai tayi tambaya "Su wane"?
Dan aiken yace, Hajiya dana tambaye su cewa sukayi, su ba baki bane, surukaine don haka in barsu su shigo.
Kamar zata sake magana sai kuma k'aguwa ( _eager_ ) taga su waye, yasa tayi saurin cewa shigo dasu kawai.
Suka shigo da sallama kamar, gaske, hajiya ta dago ido tana kallonsu da murnushi.
Duk abinda Hajiya Halima ta had'iyo sai taji tana shayin matar kuma tayi mata kwarjini, _mutum a gidansa kenan_
Sukayi shuru, bayan ta basu gurin zama, tare da musu tarbar da murmushi had'e da musu _sannu da zuwa._
Itama cikin son tuno ko ta sansu yasa take ta bin karamar da kallo, don ita tafi yi mata kama da _idon, sani._
Ta gaji da hasashen da kuma shurun da bak'in sukayi tace, cikin murmushi, _"Naso na shaidaku kuma na kasa, ko zaku min bayani."?_
Sai lokacin bakin Hajiya Halima ya bude, ta sami kwarin gwiwar yin abinda take ganin shiya dace, kuma zai jawo fasuwar al, amran."
Yes babu lallai ki sanmu, especially ma ni..
Hajiya ta zubo musu ido, don taji maganar kamar babu _salama_ cikin ta.
Kafin tace wani abu hajiya Halima ta nuna 'yarta,
Wannan 'yata ce Basma, itace danki yake shirin aure, to shine nazo na sanar muku gaskiya, _ni da ita bama son auren nan ubanta ne ke shirin kullawa,_ kinga kuwa gwara a hak'ura kada anayin batacciya don yata ba so take ba.
Ta kalli Basma, "Basma ko kina so."?
Duk rashin kunyar Basma sai taji tana shayin matar itama, kuma tayi mata wani irin kwarjini, amma don kada ta kunyata uwarta sai ta girgiza kai.
Hajiya Halima cike da k'warin guiwa ta dora, to kinji dai daga bakinta, yarinya bata so don, haka sai azan abinyi gaskiya, idan da zaki tambayi yaron ma, shi kanshi yasan...
Hajiya Rabi , bata bar Hajiya Halima ta k'arasa, zancen ta ba, ta daga mata hannu, sannan ta kafe ta da ido, da yanayin fuskarta da ta ke ta sauya zuwa kalar matsanancin fushi.
Ya isa, kin fad'i magana, kuma, sako yazo, saboda haka zancen ya yasheni haka."
Abin mamaki kuma sai ga Hajiya Halima ta kasa, mayar da martani sai shuru da tayi kawai tana jiran taga mai Hajiya rabi zatayi, don taga ta dauki wayarta.
Cikin tunanin t tsinkayeta tana cewa cikin wayar, "Kazo palour ko me kake yi."
Bayan d'an shuru kuma taji, tace, cikin fada nace kazo koh, babu ruwana da me kake, ko aya kake idan ba zaka zo ba tom... "
Sai ta katse kiran.
Minti baifi daya ba, sai sukaji sallama, ta bayansu, basu waiga ba, shikuma shigowarshi kai tsaye gun mahaifiyar shi ya nufa, cike da jin kunya.
_Dama mama tasan da baki tasa ya fito a haka babu wata cikakkiyar riga."?_
_Ya fito daga wanka ne, yana shirin fita, yana sa kaya ta kira shi, yasa wando, baisa riga ba sai singlet._ Abinda yake fada mata a waya kenan Cewar, _kaya yake sawa._ amma sai ta nuna fushi.
_Ashe bak'i tayi take son su gaisa.??_ Shidai yayi mamakin dalilin mama na azalzala haka, ya dan dosanu gefen ta, cike da kunya, sai lokacin ya lura da su wa ke zaune a wajen.
Ciken da rudu, ya fara magana, "Ba Basma..!!??
Mamanshi ta daga mishi hannu.
Dakata.!!
Kasanta ne."?
"Ba bas, Basma ma cehh ma mama.!
Ya fada cikin in'ina.
Uwar ta jinjina kai, sannan ta mike tsaye shima ya mike, gabadaya ya rud'e.
Uwar ta nuna shi da yatsa sannan ta nuno Basma.
"Tabbatar mata ka fasa aurenta kaima."
Cike da rud'ewa ya hau rarraba ido kamar baya gani, tsakanin mamanshi da su Basma.
Uwar ta k'ara daga murya, sannan ta nuna Hajiya Halima da yatsa, Me kikace game da 'yarki. "?
Hajiya Halima ta mike tsaye. "Basai kin nuna ni da yatsa ba, cewa nayi ni da 'yata bama son auren nan idan akayi shi za,ayi b'atacciya.!!
Ta kalli, Basma ta k'ara cewa, ko kina so."?
Basma ta girgiza kai kamar d'azu.
Hajiya rabi ta kalli danta, cikin daga murya tace, zaka aureta ko ka fasa kaima"?
Nour ya zubowa Basma idanu, itama shi take kallo, yana k'ara kallonta, tanajin wani rauni yana shigar ta a hankali.
Ahankali shima ya bude baki yace, "Nima na janye, na fasa auren ki.!!
Yana fadar haka ya dauke idonshi daga kan Basma ya juya ya kalli mahaifiyar shi, kwalla fal idanun shi.
Hajiya Halima ta bude baki, "Ahto gaskiya kunyiwa kanku....
Dakata ke!!
Hajiya rabi ta fad'a da daga sauti sai da ta razana Basma, sannan tasa Hajiya Halima dakatawar babu shiri.
Hajiya rabi ta nuna su duka tare da cewa, tunda abinda ya kawo ku ya wuce, to ku bace daga gidannn kafin na gwada muku kalar nawa ikon, don ba ahaifi yar da akanta, za, ayi min dibar albarka ba. Idan kuma kuka k'ara koda minti cikin gidan nan to tabbas zaku gane inda kuka zo.!!!
Ta juya ga d'anta tana mishi wani kallo.
Jeka karasa shirinka kaji dana.
Nasan baka da damuwa koh.'?
Cike da dakiya ya kirkiro murmushi ya jinjina kai.
Abinda ya bawa Basma madaukakin mamaki kenan.
Ina tarin naci, da dumbin son da Nour ke mata.??
Har suka koma gida jikinta a sanyaye, ta kasa nutsuwa da abinda suka aikata ita da mamanta.
"Anya kuwa batayi abinda zai zame mata nadama ba."?
Wata zuciyar tace, _wacce iriyar nadama bayan kin rabu da alakakai."??_
_________________
Agidansu Nour kuwa, bayan fitar su Basma, Nour ya fada kan kujera, ya dafe kai, kuka yake shirin yi amma kukan ma yaki zuwa, yana mamakin abinda ya faru kamar a mafarki yanzun nan.
Ya sani bazai iya bawa mahaifiyar shi kunya ba, a yadda ta hak'ik'ance zai goyi bayanta, a lokacin da ake nuna mata iyakarta akanshi.
Itama Hajiya Rabi zama tayi kusa dashi, tana son ta bashi baki. "Kayi hakuri kaji Nour, ka d'auka komai kaddara ne, kada kaga agabansu nace ka fasa aurenta. Bani da iko akan aurenku haka suma, Allah shike kaddara komai Idan ya nufa sai Anyi ko basa so. Amma hakan bazai sa na bada damar su ci mana zarafi ba har cikin gida, saboda kana son 'yarta, kaima kayi taka tsantsan kaji, ka nemi zabin ubangiji, amma ka girmama kanka, kada ka wulakanta kanka inda baza,a taba ganinka da daraja ba, bayan Allah ya girmama ka ( _amatsayinka na dan adam._)
Zanyi maka addu,a kada ka damu kaji.. "? Zamuyi magana da abbanka, tashi kaje, kayi fitarka kaji, Allah ya zaba maka abinda yafi alkhairi.
"Da kyar ya ambata Amiin mama."
Ya tashi babu k'wari ya nufi d'akinshi, fitar da tasha ruwa kenan, don ya samu rauni matuka ajiki da kuma zuciyarshi.
Da daddare Abbansu Nour, na dawowa, Hajiya Rabi tayi mishi bayanin komai, sannan ta dora da nata ra,ayin.
_"Alhaji ina ganin tun da har abin ya zama haka, to gaskiya a hak'ura, tunda har suka magantu, kuma abin yakai ga anzo har gida to ina ganin Nour ya hak'ura Allah ya bashi wacce tafita, don idan har yarinya ta furta bata so to za,a sami rashin jituwa._
Alhaji ya jinjina kai jin duk bayananta, sannan ya bude baki, baya son ya nuna mata ra,ayinshi, a lokacin don haka yace, "Tom duk naji abinda kikace kiyi addu,a Allah yayi zab'in alkhairi, zan tuntubi shi Nour din da kuma mahaifin yarinyar."
Daga nan bai sake bata damar k'ara yin magana ba.
______________
Abban Basma yayi mama kin yadda ya dawo yaga Basma bata gidan. Aikuwa ya sauke fushin kan ya ya yayar Basma da ita kanta Hajiya salman, inda ya dora musu laifi duka. Sai da ya sassauto sannan ya fara binciken inda zai samo ta, sai ya fara da Halima.
Ya kirata a waya a fusace, itama tana ganin kiran ta share. Ya kara kira karo na biyu sai taga ma gwara ta daga suyi ta ta k'are.
"Hello ya akayi ne." Ta fada a fad'ace.
Halima ki dawo da Basma, don ba muyi dake zata zo wajenki ba."
Hmm, bazan dawo da ita ba da yake jaririya ce ita da zakace na dawo da ita.!!
Nace ki dawo da itan da waye yace ki zo ki dauke ta.
Tayi dariya au ni na d'auke ta ma koh."?
"Hmm, Alhaji Yunus yarinya fa ta girma sannan ba a kauye muke ba bare kayi mata auren dole tunda tace bata so to fa bazan zuba ido ayi ba. Sannan dawowa ba zata dawo ba.
Haka kika ce koh. "?
"Eh, haka nace.!!
Cikin fusata ya kira sunanta.
"Halima.!!
Ki shiga hankaliki dani wallahi ke kin isa ki hana ni iko akan 'yata."?
To bari kiji ko kinki ko kin so aure sai na aurar da Basma, sannan koma komawarta wajenki bazai sa na fasa daura mata aure ba, sai dai in bata numfashi.."!!
Hajiya Halima ta sheke da dariyar data bashi takaici. Take ya katse kiran tunaninshi ya kira Basma, sai ya tuna cewa ya kwace wayoyinta. Yayi jigum yana tunani tabbas akwai aiki gabanshi.
Wani abu daya bashi mamaki shine kiran Abbah Nour daya gani da daddare.
Da sauri ya daga yana fatan Allah yasa lafiya.
Suka gaisa cike da girmama juna. Kafin Abban Nour ya fara magana.
Am Alhaji dama inaso ne ka bani dama ko zuwa gobe ne ina so nazo na ganka.
Fargaba ta kama Abban Basma. Ya bude baki da sauri yana tambaya "lafiya dai Alhaji."?
Cikin murmurshi yake magana, "lafiya lau, ina so ne mu tattauna wata magana ne.
Da kyar Abban Basma ya kwantar da hankali sannan ya bawa abban Nour dama daya zo gobe su tattauna din.
Yammaci nayi Abban yayi sallama, a gidan su Basma. Abban Basma ya mishi iso a falon bak'in shi.
Ya tarbe shi da ruwa da abin sha. Sun gaisa sosai. Abban Basma yayi jugum cikin fargaba, yana fatan Allah yasa zancen kawo lefe ne ya kawo shi.
Alhaji mukhtar ya muskuta, sannan ya fara jawabi. Yayin da alhaji Alhaji Yunus ya bashi duka hankalin shi.
"Am Alhaji dama wata magana ce nazo da ita saboda maslaha, kuma naga ya dace muyi magana daga ni sai kai.
Ya danyi shuru, ya lura da dan tashin hankalin dake kan fuskar Alhaji Yunus. Sai kawai ya kauda kai ya cigaba da magana.
Wato wani al,amari ne ya faru jiya da maraice. Ita mai mai da dakinka da ita yarinyar da ake nema sun zo har gida sunyi magana kan cewa basa buk'atar wannan aure.!!
Sannan an tambayi yarinyar agaban ita mai dakinka shin tana bukatar auren tace bata so, sannan ta jaddada hakan agaban shi Nuran bayan mahaifiyar shi ta kira shi."
"Innalallahi wa in inna ilaihi raji,un."
Shi Alhaji Yunus yake ta maimaitawa, ji yake kamar yayi hawaye, wannan wane irin wulak'anci ne halima tayi wa yasan iya abinda taje tayi musu a gidan mutane."? Halima ta zubar masa da k'ima.
Ganin yanayin da ya shiga na tashin hankali yasa abban kokarin kwantar mishi da hankali,
To shine nace Alhaji kada azo ayi abu da son zuciya, ya dace a tsahirta a samu amincewar tasu tunda ita yarinya dai da ita za,a zauna, kuma auren nan fata muke ayi ya d'ore. Saboda haka shima yaron zan bashi dama idan ya iya shawo kanta toh, Allah ya tabbatar da alkhairi, zamu gani zuwa wasu lukuta ko ya kace alhaji."?
Abban Basma yasa Handkerchief din sa, ya goge gumin daya tsatstsafo masa.
Rauni sosai cikin muryarshi wanda zai yake nuna tsananin tashin hankalin da yake ciki.
"Don Allah Alhaji kayi hakuri don manzon Allah wallahi ban san abin nan ya faru ba...!!
Alhaji Mukhtar ya dakatar dashi yana fad'in, "ashsha.. ashsha Alhaji ya da magiya haka."?
Wallahi maganar nan saboda maslahar yaran yasa nazo maka da ita ko kadan ni ban bata raina ba akai, don bana nan ma suka zo dake da safe ne. Kayi hakuri ka dauki komai a sannu, su sha'anin mata sai a hankali. Kada ka dawo Alhaji.
Abban Basma ya kara gyara zama..
Dole na roki afuwarka Alhaji. Domin wannan cin mutunci ne, ya za,ayi azo har gida saboda rashin hankali haba ai abin babu mutunci. Don Allah kayi hakuri wallahi bani da masaniyar hakan. Kuma ita matar ba ma tare da ita shiyasa take kokarin hana auren. Amma kayi hakuri don Allah a bawa mutanan gidan hakuri suma don Allah."!!
Cike da kunya alhaji mukhtar yake magana domin bai so yasa abban Basma cikin wannan halin ba.
Babu shiri ya mike da shirin tafiya. Kayi hakuri kaima don Allah sannan kabi komai a sannu. Wallahi babu komai a wajena wannan abin ba komai bane illa neman samun maslaha, kuma mu cigaba da addua Allah yasa alkhairi dama harkar aure dole ana samun kalubale. Amma wannan abin ba komai bane balle kuma kasan sha,anin mata sai su. Ayi hakuri dai Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
Ya mik'a mishi hannu jikin abban Basma a sanyaye sukayi musabiha.
Ya mike da kyar ya raka Alhaji Mukhtar cike da kunyar shi. Don abin da Halima tayi yaja mishi kunyar manyan mutane irin su Alhaji mukhtar. Kuma yasan ta gama zubar mishi da k'ima.
Tafiyar abban Nour kenan Alhaji Yunus ya shigo gida.
Yanayin sa ya tada hankalin Hajiya Salma ta bishi dakin shi da sauri..
Ta tarar ya yaye babbar rigar shi, ya cillar a tsakar dakin yana shirin juyawa zai fita. Alhaji lafiya ta tambaye shi.
Sai da ya juya zai fice sannan yayi mata magana a fusace yana huci.
Billahil-aziim sai Halima ta gane wanene ni.!! Ya cigaba da tafiya bai kara magana ba.
Hajiya Salma ta bishi da sauri kiranshi ta tsorata da yanayin nashi amma ina tuni ya fice. Ta biyo shi har Harabar gidan tana kira amma ya fice ko mota bai dauka ba.
Ta dawo gida cike da rudu tana tambaye tambayen da babu amsarsu. Fatima meya faru da Abban ku. Ina tunanin gidan halima zaije fa. Ina tsohon abinda zai faru ko me tayi masa oho."
"Kinga dakko hijabin ki muje wallahi ban aminta da fitar Alhaji zuwa gidan ta ba. Fatima ta taso babu shiri. Itama hankalinta duk ya tashi.
________________
Mamaki da razani ne suka tarar tararwa Hajiya Halima ganin Alhaji Yunus a gidan ta kuma babu neman izini daga sallama ya shigo cikin falon.
Ta mike tsaye a dan tsorace, ya nunata da yatsa. Sannan ya rigata fara maganar da take shirin yi cikin fushi.
"Halima kinyi abinda kikayi kinji dadi kuma yayi kyau bazan ce kinfi karfi naba, don idan nayi niyyar daukar matakin zakiyi mamaki amma zan nuna iko a inda nafi ikon sosai, don wallahi baki isa kin iko akan yata ba kuma aure babu fashi.!!
Kan tayi wani yunkuri ya wuce ta ya nufi bedroom dinta.
Aikuwa sukaci karo da Basman daya shigo nema don tajiyo muryarshi tana shirin fitowa taga me zaiwa mahaifiyar tata.
Ai kuwa ya kife ta da mari kafin ya jata fii ya zubar da ita a kasa.
Cikin tsananin fushi yake maganar.
Kinje kinyi abinda kukayi ke da uwarki yayi muku kyau wallahi idan hakan ya zama silar fasuwar auren ki Basma hakkina sai ya biki don nayi iya kokari na kuma bazan sake saka hannu akan al'amarinki ba. Don na sauke hakki na a kanki.
Meye haka me kake ji dashi ne zaka shigo min gida kana min hayaniya kuma don wulak'anci har uwar daka me kake nufi.
Ya juyo a fusace komai ma ina nufi.. Don baki isa kin hanani iko akan yata ba.
"To wallahi ka fita kafin na tara maka jama'a."
Ya daga muryarshi ya fuskanto ta shima.
Ki tara mini jama,ar Halima sai me aini kin gama zubda min da k'ima kuma sai Allah ya saka min abinda kikemin ina yiwa yata tarbiyya kina rusawa."
Hankalin Basma ya tashi har taji ta dan fara nadamar abinda tayi. Don bata san abin zai zama haka ba. Yau abban ta har cikin uwar daka saboda ita."? Shida da wuya ma ya shigo cikin gidan tun da can ma idan yazo ganinta."?
"Hmm, kada ka manta ba kai kayi min nakudar ta ba ehe kuma wallahi ka kara tabata sai sharia ta rabamu don baka isa ba ka nuna mini iko."
Bai tsaya komai ba saboda xuciya.. ya rufe Basma da duka tana ihu. Yana fad'in idan na karya ta sai naga naki matakin..wallahi Halima nayi nadamar haihuwa tare dake da kika haifa min abinda zai bujure min.
Basma cike da nadama take bashi hakuri tana kuma yayin da hajiya Halima ta kasa kwa kwatarta duk kurinta.. Don abban mahuci yasaka da ya gani a gefe sai da ya kakkarye sannan ya kyele ta. Lokacin Hajiya Halima ta fita waje neman dauki inda ta hadu da hajiya Salma suka ranks rankaya babu tsayawa ce-ce-ku-ce.
Huci yake yana ta sababi. _"Saboda baki dauke ni mahaifi ba kinfi son ki ta garari kina wayo a gari kina son ki lalace ko." Kina biye mata tana doraki kan hanyar banza. Wai har ke kinsan ki je gidan mutane kuyi musu cin mutunci don kawai dansu na sonki.? Cewa nayi miki Alhaji mukhtar sa,a nane ko itah matar tashi sa'ar uwarki ce."? Idan daraja da mutunci ne kin isa ku nuna musu."? Saboda ki nuna baki da tarbiyya yar mace ce ke koh"?_
_To Allah ya gani bada yawuna kuka je ba kuma mutunci na da kuka zubar na barku da Allah kuma illa kanki kikayi wa..._
Hajiya Salma ta dakatar dashi. Don Allah Alhaji kayi hakuri kada ka aibatata. Kayi hakuri kazo mu tafi tun farko bai dace kazo bama. Basma yarka ce ka dinga mata adduar shiriya ba fada ko aibatata ba.
Ya goge gumi ya juyo ya kallesu. Mataki daya zan dauka ko ta bini ko kuma idan bata bini gida yau ba to na rantse bazata kara taka min cikin gidana ba.
Aikuwa bazata bika ba. In yaso ka cireta cikin yayan naka