Chapter 39 Reading ZAZZAFAN SO COMPLETE HAUSA NOVELS BY KARIMA TIJJANI MANSUR.txt Arewa Novels

ZAZZAFAN SO COMPLETE HAUSA NOVELS BY KARIMA TIJJANI MANSUR.txt

Author :  KARIMA TIJJANI MANSUR Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   39 / 40

114K to 117K   out of 119.4K words

a wajenta.

Na zargi Samha kan zubewar ciki na amma sai nabar abin cikin iya zuciyata saboda itace ci na itace sha na.


Na zauna gidan su tsahon watanni da suka kusa rufa shekara.

Samha kullum sai tace in shirya nasa 'spare' uniform dinta muje makaranta amma sam naki saboda na tsani makarantar ma gaba-d'aya. Sai dai na bata sak'o a wajen Sir kan cin asabar daya min duk da baya makarantar yanxu amma ta isar d'in.


Nabar gidan su Samha bisa dalilai da dama na yau da gobe da kuma halayen Samha wanda na kasa ganewa.
Na fahimci Samha tafini wayewa da budewar idanuwa kafin daga bisani na fahimci ta shallake tunanina tunda har takan iya maida mata maza a wajenta.

Bansan tana da wannan dabi'ar ba sanda muna makaranta sai dai babu tabbaci kan ko batayi ne a lokacin amma sanda gwada min haka take lokacin naji bazan iya cigaba da zama da ita ba.

Rayuwar danayi a unguwar su yasa na saba da wasu makobtansu ciki har da wata mata maiwa yan aiki hanya.

Na je har gidanta na roketa kan ta samamin aiki na gaji da zaman gida.
Bayan dogon kallo daga matar sannan ta min shagub'e kan me zai kaini aikatau bayan ina k'awar Samha."? Duk wayewar mu. Domin babu wanda a unguwar baisan ni ba kawar Samha bace.
Wani abin mamaki shine yadda babu kunya matar ta ke tambaya ta. "Kodai abin ya daina karbar ki ne."? Inada wani malami da zai dawo miki da tauraruwar ki."!!

Banyi fushi ba kuma ban nuna mata ba haka nake ba tunda bani da mafita. Sai dai na nuna mata matuk'ar buk'atar aikin wanda daga k'arshe ta yarda zata kaini sai dai ta yanka min wasu kudade da zan biya ta idan na fara aikin. Ta nuna min tasan inda zata kaini. Bangane nufin ta ba sai dai naji tace..
Na fahimci k'afa kike nema so zan kaiki inda zaki k'ara goge wa dama haka irin ku kuke lumbe-lumbu kuke kuyi kwanton bauna ku goge sannan ku gagari masu gida.."!!

Sai ta sheke da dariya.

Na rok'eta hadi da bata cin hanci kan kada ta fad'awa Samha ina neman aiki. Ta nemi dalili ta rasa. Wanda da kyar na samu ta yarda duk da tana ta mamakin dalilin boyewa ta.

Mun saci jiki sau da dama munje gidanmu nida Samha na kwaso kayana sanda mahaifina bayanan. Mahaifiya ta nuna tsayawar ta duk da sanda baba zai koreni bata nuna wani abu ba domin tasan halin sa zai iya hadamu ya kora.


Nasha gwada in koma gidan mu amma babu damar hakan har mahaifiyata ta gwada min in saduda.


Daga karshe dai matar nan ta samar min aikin kuma nayi mamakin gidan da ta kaini. Gida ne na mata masu zaman kansu.

Takamaimai bansan wa zan dinga yiwa aiki agidan ba sai dai an fada min aikina.
Share-share da wanke-wanke da aike shine aiki na.


Sanda suka ganni sunyi complain kan nayi musu girma harda masu cewa ni uwar mata ce ko suce sumumu-kasau... da kyar suka yarda na fara aiki wanda dole nazama tamkar wata doluwa.

Nasha wuya sosai agidan nan mara dadin tunawa.
Domin mata ne su wajen goma sha amma babu yadda za'ayi wata ta sani aiki wata bata sani ba idan nabar na daya nasha zagi har da duka. Maza ke tururuwa a gidan ba dare ba rana haka kawai ake kyara ta wai mazansu na kallo na ni munafuka ceh..
Sun sha cewa zasu koreni amma ina basu hakuri har da kuka..

Azaman da nake a gidan ne tunanina ya fara sauyawa kan irin rayuwar da suke anya nima bazan fada ba domin neman mafita ta."?
Amma wallahi dana tuno ki sai inji bazan iya ba.


Nayi akallah shekara agidan kafin wani mutumi da yake zuwa wajen wata ya yaudare ni.
Mutumin ya dade yana nuna min wasu abubuwa har saida yasan yadda yayi ya fita dani a motar shi kan zan karbo wa uwar dakina sako a wajen shi.

Mutumin ya kasance mutum na biyu wanda bazan taba mantawa dasu ba a rayuwata. Zan sa shi layin wadanda suka taimaka wajen gurbacewar rayuwata.


Ya huren kunne da hilata kala kala wanda tun bana yarda da shi har na fara sakin jiki.


Naci duka sanda suka gane haka a lokacin ne suka nemi su koreni...
Aunty sadia kawarsu ce don tana yawan zuwa gidan. Allah ne ya kawo ta Aranar ta ceceni itace ta tafi dani gidan ta lokacin ina ga ina da shekaru 18 lokacin tasan yan ajinmu sunyi candy.


Na kasa gane irin rayuwar da take ko irin tasu ce. Nasan dai tana business sai sai yawan bak'i maza a gidan ya zarce misali.

Ta nemi taji tarihi na daga bakina da kuma gaskiyar abinda ya faru dani. Na fada mata komai a lokacin ta gargade ni kuma tayi min fada mai shiga zuciya.


_Ke yarinya ce kinyi kankanta kisa rayuwarki cikin wannan abubuwan kada in kara jin hakan ya faru.. tunda komai daya faru a rayuwar ki ki d'auka kaddara ne mu idan zaki ji namu tarihin zaki ji naki ba komai bane._

Tayi min jan ido wajen cewa duk ranar da taga wani abu shigen wanda nayi acan to zamana ya k'are.
Tayi min wani gargadi da cewa "Ki bar manya suyi ke yarinya ceh."
Na kasa fahimtar me take nufi sai dai na gimtse abun nabita yadda taxo min. Nidai nasan na wuce sahun yara kuma zuwa lokacin nasan abubuwa da dama..


Mun zauna nida ita tana kula dani har yau bazan manta da ita ba.
Jamila ta share hawaye.

Ta yi kokarin maida ni gida sanda tayi wani tunani a kaina amma baba ya koremu. Cewar shi naje na k'ara tambadewa sannan zan kara dawo mishi gida. Har Allah ya isa yayi hadi da tsinuwa idan har na k'ara zuwar mishi gida. Duk abin matan gidan sai da suka bashi hakuri amma yaki hak'ura.

Mun rayu da ita babu tsangwama tayi min komai ban rasa komai ba amma kullum gargadinta dani akan na fita harkar maza ne.

Tana yawan fada min cewa "Maza mayaudara ne badon yaudarar su ba da bata zata tsinci kanta cikin wannan rayuwar ba."

Bata taba ban labarin ta ba har muka rabu amma nasan tasha wuya fiye da tawa.
Mamakina shine yadda yan uwanta ke zuwa gidan ciki harda mahaifiyar ta kuma suyi hira sannan su tafi da kayan arziki.

Na goge da rayuwa a zamana da ita tayi min komai sai dai bata taba min tayin maida ni makaranta ba kuma nima ban zarge ta ba.
Tayi min abinda iyayen a basu min ba ina sa mai kyau inci mai kyau sai dai na fahimci yan uwanta basa k'auna ta.

Na gane ne da irin kallo da kyarar da suke min.

Munyi shekaru a kallah uku kafin dole Aunty ta sallama ni nake tsayawa da samari. Sai lokacin na sake fahimtar yadda mutane suka bata rayuwar su. Yawanci basa zuwa da alak'ar gaskiya Sao dai kowa da manufar shi.

Sanda na lura aunty ta rage tara maza a gidan ta ma'ana sun rage zirga-zirga shine sanda wani mutumi ya nuna yana son zai aureta. Tayi murna sosai nima kuma naji dadi sai dai kash sai da komai yazo daf da daf komai ya ruguje..
Mutumin yasan komai game da ita sai don bazance zaman da take yi ne ita daya bai sani ba. Sai dai lamarin ya tsayawa jama'a da dama aransu musamman k'awayen ta yadda suke ganin zata daga ta barsu.
Ban taba ganin matar nan cikin tashin hankali ba kamar lokacin nan tasha kuka wiwi a gabana. Ta dinga fadamin maganganu kamar ba cikin hayyaci ba kamar ta manta dawa take maganganun.

"Jamila nasan nayi rayuwar da bata dace ba amma na dade da dainawa na tuba yanzu ba da bace halak d'ina nake nema amma meyasa mutane zasuyi min haka."?
Maganganu ta dinga furtawa wasu ma sirrikan ta ne. Nima babu abinda nake sai kuka da bata hakuri.

Anduki lokaci mai dan tsaho kafin aunty ta dawo daidai.

Takan barni nayi mu'amala ta da samari na sam bata hana ni fita da samari. Har mu fita.
Sai dai a kullum zancen ta daya "Kiyi taka tsantsan."

Har kamar ranar da muka hadu dake. Amma nida kaina nake baya baya da mutanen saboda yadda suke nuna min wuce makad'i da rawa.

Aunty da kanta ta sama min hanyar samun kudi a cewarta dogara da abin wani ke jawowa komai ke faruwa.

Na koyi kwalliyar zamani wato makeover da ita nake yiwa kaina abubuwa da dama. Lokacin na k'ara tunowa da gidanmu. Dole na k'ara nemar gida domin bani da wanda inda ya fishi. Ina kaiwa mahaifiya ta alkhairan da wataran har shi mahaifina ake ciki domin komai ya k'are mishi. Kowa a gidan ta kanshi yake.

Da wannan abin nake samun damar zuwa gidanmu kai tsaye.

Sanda nazo wajenki lokacin aunty tayi min alkawarin zuwa dani Dubai domin siye siyan kaya. Nima tace na k'ara gogewa da sanin rayuwa.

Shine tafiyar da na sanar miki zanyi rakiya. sai dai kash mun shirya komai amma Allah bai nufa ba aunty ta rasu bisa wani hats ari da tayi a motar ta bayan ta fita babu jimawa na samu labari kamar a mafarki.

Jamila ta rushe da wani irin kuka mara misaltuwa. Sai da tayi mai isarta kafin tayi shuru wanda har Hafsah itama sai da ta share hawaye.

Hafsah a lokacin na rasa mutane biyu uwar dakina da kawata Samha wacce akace wata iriyar cuta ce ta kashe ta. Duk da ina ganin kamar nayiwa Samha butulci amma ita ta Nemo ni har take nuna min ko in kula kan gudar ta da nayi sai dai tace min. "Ai Jamila ko ina kika shiga sai na gano ki." Wato kin gama gadin gidan magajiyar shine kika dawo nan."?
Karaf a kunnen aunty ranar kuwa ta mata tatas ni kaina tun lokacin nake shakkar aunty domin ban dade gidanta ba hakan ta faru..

Hafsah rayuwata ta shiga garari yanxu haka babana yana kwance rai a hannun Allah dawowa ta gida ta kara kwantar dashi duk da yayi ikrarin cewa ya yafemin domin korata bai mishi amfani ba. Nima don da karar tsanata da aka dasa mishi a zuciyarsa ne. Domin bayan ni yayyena wanda muke uba daya har shegu biyu suka ajiye mishi acikin gidanshi kuma babu yadda ya iya dasu dole duka suna gidan.

Hafsah nayi mamaki dana ganki ba kiyi aure ba kema kuma banyi murna da hakan ba ina Yusuf din."?

Da sauri Hafsah ta mata nuni kan tayi shuru don bata son ko jin sunan Yusuf.

Jamila ta girgiza kai ta d'ora.
Hafsah wallahi aure nake so shine kawai burina.. saboda sam ban amfani rayuwata ba na rasa yadda akayi rayuwata ta zama haka bane cika koda daya da yaga cikin burikana ba..

Hafsah nayi asara dayawa a rayuwa ta..aure kawai nake son yi shine zan san na ribaci kuruciya ta sai dai ina tunanin ko za'a barni nayi Auren."? Duk da bani da wani tsayayye da zance yana sona da aure.

Hafsah ta numfasa. Ki yi hakuri ki daina kallon ayuwarki a baya kowa da irin yadda aka tsara mishi rayuwa Allah yana sane dake ki gode masa domin kinfi wasu."

Jamila cikin hawaye tace Allah Hafsah banyi irin k'azamar rayuwar da mutane ke zargi na ba imma hakan ne a farkon bari na gida ne amma kada ki so kiga yadda mutane suke kallo na."!
Hafsah tayi shuru Allah yaso bata zargi Jamila ba ita dai tasan bata gidansu kuma koda ta bawa Ukhasha labarin ta ce mishi tayi "tabar garin ne zuwa wajen dangin mahaifiyarta.
Bata soma fada mishi cewa Jamila garari ta dinga yi ba ko dan k'are nata mutuncin.. Domin maza akwai zargi.


Sunyi jugum Hafsah na bawa Jamila baki kan ta tsananta da addu'a. Bayan nan Jamila ta dame ta da zancen Yusuf ta damu ta bata labarin rabuwar su.

Da kyar Hafsah ta mata a takaice kawai ta nuna mata Abbanta ne ya rabasu saboda karatu kinsan dama lokacin bana kula kowa.

Jamila ta girgiza kai Allah sarki kuma yayi aure koh."?
Hafsah ta girgiza kai bansani ba gaskiya bani da alaqa dashi yanxu.
Jamila ta fahimci Hafsah bata son zancen don haka tabar zancen sukayi shuru. Inda Hafsah taga dacewar ta je ta duba baban Jamila don ko ba komai uba uba ne don haka tace. In sha Allah gobe zanzo duba Baban.
Jamila ta nuna jin dadin ta.
Hafsah tasan sai tayi magiya Sannan mama zata barta don haka tace sai gobe.

Tana son sanarwa Jamila batun bikinta amma kuma tana jin nauyi don haka fa bari sai abu ya matso sosai..


Ita ta raka jamila har waje sannan ta dawo jiki a sanyaye tana tararrabin yadda rayuwar Jamila ta kasance kuma tana k'ara gode wa Allah..

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah yau bikin Hafsah da Ukhasha ya rage saura wata daya da sati biyu.

Sun sha gaisawa da Hajiyarshi a waya haka
Wata rana idan zai zo yakan zo mata da "Najwa" Tayi ta sa Hafsah dariya tayi ta bata labarin su ya Fadwa da yadda suke tsokanar Ukhashatu.

Mama ta d'auke ta takanas ta maida ta gidan Hajiya Nafisa wato maman ya Nazeer.

Komai da ya dace maman tayi mata sosai Hafsah sai taji rayuwar da tayi agidan da gwagwarmayar da mama ta sha da ita ya dawo mata sabo kamar yanzu. Ita da kanta sai tayi ta dariya ita kadai tana qara gode wa Allah.


Takan yi wani tunani wato 'komai dai da lokacin shi.' Idan taga yadda ya'yan Nazeer su biyu suke cika gidan da hayaniya. Da tuni fa yaranta ne. Sai tayi saurin kwab'ar kanta "Kada ki zama mara godiyar Allah Hafsah kowa da wanda Allah ya rubuta zai aura a rayuwa.
Amma tana tuno Ukhashatunta da yadda yake sai taji wani farinciki mara misaltuwa har ta _kirashi da daya tamkar da dubu!!_


Tanajin kunyar mama yadda take zaunar da ita tana koya mata abubuwa babu wata shakka.

Ya zame mata dabi'a kullum kafin su fara gyaran jiki sai tayi mata nasiha da nusar da ita yadda rayuwar aure take.

Takan fada mata ko yaushe.
_Rayuwar aure wata iriyar rayuwa ce wacce ba zaki taba gane ya take ba har sai kinyi ta. Tana da matuk'ar dadi sannan akwai wahala da kalubale acikin ta amma idan har kika saka hak'uri komai zaki same shi da sauki._ Ita zaman ibada ne dole ki hadu da abubuwa masu dadi da kuma akasinsa. Amma matuk'ar kika sa aranki ibada kike to zaki sami komai da sauk'i.


_Kuskure da yanmata kuke yi shine kunfi fifita soyayya akan komai cikin rayuwar aure._
_Duk da tabbas itace ginshiki amma kuma hak'uri da biyayya sune makaman yaki da kowacce irin fitina._

Ina son ki rike abubuwan nan da zan fada miki.

Ki rike tsafta da kamshi
Sai kuma ki zama mai ka mun kai da biyayya kada ki zama mai girman kai ga mijinki.


Hafsah ta koyi abubuwa cikin sati hud'un da tayi tun daga girke girke data k'ara gogewa dasu sai kuma dabarun zama da miji da zamantakewar rayuwa ita kanta. Adduoi kuwa kullum cikin yin su take babu dare babu rana.

Bata iya sanarwa da Ukhashatu cewa bata gida ba saboda nauyinshi da take ji sai dai idan ya nuna yana son ganinta ta bashi uzuri. Ya k'osa sosai har yake fad'a mata.

"Don Allah ayi hakuri amarya adaina jamin rai ina son ganinka Allah."

Babu abinda take mishi sai dariya wanda da ya gaji sai ya sami lokaci yaje gidan.
Mufida ce ta fada mishi tana Kabuga.
Ya dawo gida asanyaye.
Yana dawowar kuwa ya kirata.

Tana dagawa taji yanayin shi kamar ba shi ba.
"Kin kyauta nagode."
Take tasha jinin jikanta.
Cike da fargaba tace hubby me ya faru kuma."?
"Hmm baki sani ba."?
Um."
Tace dashi.
Okey ya wuce nagode kawai.!!
Tayi shuru tana tunani me tayi toh."?
Sai ta marairaice.
Please Dear meya faru ne."?
"Hmm nace miki babu komai fah."
Please ta sake cewa.
Wai da gaske kike baki ce san me kikayi ba."
Murya cike da rauni tace.
Allah bansani ba I'm sorry plz tell me."
Ya danja dogon numfashi sannan yace.
"Meyasa zaki je unguwa baki sanar min ba."?

Take annurin fuskar ta ya dawo tace cikin shagwaba.
"Dear mama ne fa ta aikani sati na daya ma tace sai biki saura sati biyu na dawo."?
"What.. ina kika je haka ya fada a tsorace."

Abin ya bata dariya har tayi ta afili sannan tace "ina Kabuga gidan Yayar Mum dinmu.
"Hmm baki fad'a mini ba koh."?
I'm sorryy luv."
Ban hak'ura ba.
Tace plzzz"!!
Ya d'anyi shuru kafin yace.
To fad'amin me kikaje yi haka da har zaki dade kuma baki fad'a min ba."?
Hafsah ta bude baki sannan ta rufe kafin ta lalubi abincewa don bata son tayi b'aran b'arama.
Dear sallama naje mata fa.

"Hmm kuma har 1month koh."?
"Oh my God!! ta fada a zuciyarta. Yau na gamu da dan Jarida.
Dearrrh!!
Ta ja sunan kamar ta k'osa.
Shima yace uhum."?
Na zauna gidan fa da so mum bazata bari na yi kwanaki kadan ba.
"Okeyy shima yace.
Yaushe zan ganki toh plzzz kada ki hanani ganinki nayi missing dinki so bad dear plzzz"
Tayi mishi yar dariya.
"Really fah kike min dariya dama ke baki damu ba koh."?
ta shagwabe tace "Noo Dear.!!
"Umm bawani nan..in zo gobe ba don hali na ba."?
Tomorrow!!?
Yess"
Yace.
"Ka bari sai day after goben."
"Ok" yace mata sannan yayi dif.
Tasan fushi yayi don haka ta mishi dariya itama.
"I'm joking Dear kaxo goben kaji nima inason ganinka.
Ukhashatu ya lumshe ido saboda jin dadi.
"Thank you WiFi.
"U wlcm Data.!!
Tace mishi.
Suka sheke da dariya "Hmm ke koh..??
"Me kike so in taho miki dashi.
Ta girgiza kai kamar yana ganinta. "Nothing Dear.
"Ban yarda ba."
Tayi murmushi "Okey You You and You.!!
Yayi murmurshin jin dad'i "Amarya me wayo.!!
"Come with you alone." Ta sake fad'a.
Ya kara darawa "Nak'i din."
"Idan kukazo ba yanda nace ba zaku koma.!! tace.


Lokacin kuma tajiyo mama na kiranta sai lokacin ta tuna girki take duk da dama su aiki amma Mama sata take don ta saba sosai.

"Mum na kirana byee.
"Ok dear kije ki gaida mum."

__________________________

Biki saura sati biyu Basheer ya dira. Duk wasu shirye shirye sun tsara shi babu tsawwalawa saboda amaryar da angon basu san bid'a. Duk wani wanda ya dace yasan da bikin zuwa lokacin ya sani. Hafsah ta tura katinan gayyata ga contact d'inta.

Kowa na mata fatan alkhairi. Musamman Aysha Daheer dake da 'yaya biyu a lokacin. Su Nasreen sune organisers na komai.
Za'ayi kamu ne had'i da kauye Day sai Dinner sai kuma mother's eve. Ranar asabar k/ amarya.

Banda murnar Abbah data fi ta mama fitowa fili ita saboda kunya. Babu wanda za'ace yafi kowa farinciki da

39 / 40