Chapter 19 Reading ZAZZAFAN SO COMPLETE HAUSA NOVELS BY KARIMA TIJJANI MANSUR.txt Arewa Novels

ZAZZAFAN SO COMPLETE HAUSA NOVELS BY KARIMA TIJJANI MANSUR.txt

Author :  KARIMA TIJJANI MANSUR Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   19 / 40

54K to 57K   out of 119.4K words

gyaran gashi, wankin qafa da sauransu.
Lokacin da suka je, ana ta yiwa wata amarya gyaran jiki, suna kwa shigowa ma,aikatan wajen suka hau gaida Mama, wacce suke kira da Mommy. Cikin fara,a ta dinga amsawa sannan ta wuce ciki.
Akwai wani d`an office madaidaici wanda yafi kama da palour, nan suka shiga maman ta zauna a kujera, Hafsah ma ta nemi waje ta zauna. K`amshi ne kawai ke tashi, gefe ga _show Glass_ turaruka ne aciki da humra duk na siyarwa.
"Baki tab'a zuwa wajen nan ba koh."?
Mama ta tambayi Hafsah dake faman kalle-kalle. Ita dai wajen ya burgeta sosai.
Tayi murmushi, "Mun taba zuwa da Mamanmu sau biyu, cikin nan ne dai ni ban tab`a shigowa ba."
Suna hirar aka k'wank'wasa kofa, mama, ta bada izini a shigo.
Lemo tazo ta ajye musu, sannan ta fita.
"Kisha lemon kinji Hafsah na ko kina son ki fita kiyi kallo."?
Ta d`aga kanta.
"To kisha sai ki je ki kalla.
"Tom."
Anyiwa mutane biyu gyaran k'afa dana gashi, wato _Saloon_ za,ayi wa ta ukun kenan mama ta sa aka kira mata Hafsah.
Ta miqe ta tafi kiran.
Tanajin dad`in zaman har suna ta hira da ma,aikatan wajen.
"Mama gani."
"Zauna kici abinci." Mama ta nuna mata abincin da ta musu order aka kawo.
Ta fara ci kenan, maman ta miqe ta fita, zagayawa don ganin meke gudana.'
Babu dad'ewa kuma maman ta dawo Hafsah nacin abincin tana janta da hira so take tayi mata wasu tambayoyi masu muhimmanci.
" `Yan mata kinga Yenda ake gyaran jiki koh."?
Hafsah tayi murmushi,
"Ko kina so ayi miki."?
Hafsah na murmushi ta d`aga kai alamar Eh."
"To anqi d`in sai dai anzo bikinki ayi miki yanzu sai dai ayi miki a fuska kawai."
Cewar mama cike da zolaya.
Hafsah ta sinne kai alamun jin kunya.
"Ai kina da saurayi koh."?
Hafsah tayi murmushi jin kunya tana girgiza kai alamar a,a.
"Gidanku!! kina da dashi mana."
"Bani da shi.!!
"Au kikayi magana ko toh kina dashi."
"A,a mama" tayi maganar tana 'yar dariya.
"To wanda ya baki ledar nan fah."?
Ehe."? Inji Hafsah, ta ke yanayinta ya chanja, zuwa damuwa.
"Am um, ba saurayi na bane."
"Hmm, koh."?
Hafsah zaton ta mama ta yarda don haka qara d`aga kai alamar tabbatar wa.
Mamanki tasan da ledar."?
"Aa."
"To meyasa baki nuna mata ba..?
Bata da amsa don haka tayi shuru.
"Kiyi magana mana Hafsah."?
"Babu komai."
Kinga irin laifin da kike koh."?
"Daga yau kada in qaraji kin qara yin laifi me kama da wannan."
"Ta d`aga kai alamar, Toh."
Mama ta d`ora, "Kin ce ba saurayin ki bane, amma meya kaiki amsar kyautar shi, kuma meya sa kika karb`a."?
Hafsah tayi shuru tana tuno amsar da zata bayar.
"Um, am wallah.. hi, ba saurayi na bane."
To menene had`in ki dashi.
"Ni..ni bana kulashi yanzu." ta fad'a cikin in`inah..Fatanta kawai mama ta yarda da zancen ta."
_An kusa zuwa inda mama take son azo don haka tace:_ "To me yasa kika daina kulashi meya had'a ku."?
Ai k'iris ne hafsah bata sa kuka ba.
Take muryata tayi rauni, har rawa take yi.
"Babu abinda ya had`a mu."
"Hmm, kina wasa dani koh."?
"Aa Mama."
"To ki fada min gaskiya."
Shuru babu magana har wajen wucewar muntuna wajen biyu. Sai Hafsah dake faman kokawa da qwallar dake son zubo mata."
"Kawai na daina kula shi ne saboda mama bata so."
"Mama bata so, to meyasa."?
Mama ta tambayeta da sigar irin tayi mamakin maman ne."
Tasan ba zata sami amsa ba, don haka tayi amfani da damar wajen cewa, "Shine kuka fita dashi ranar bikin abdallah koh."?
Gaban Hafsah yayi wata mummunar fad`uwa, ta k'osa wannan lokacin ( _Moment_) d`in ya shud`e, ta gaji da tambayoyin, don ana neman qureta.
Mama bata jira amsarta ba ta d'ora.
"Kinga dalilin d`aya sa mamanki ba ta so koh.. Meyasa zaki bishi wani waje."? Ke aganinki ya dace kiyi haka."?
Cikin nadama Hafsah ta girgiza kai.
"Duk mutumin da bazai taya ki yiwa iyayenki biyayya ba, ki rabu da shi kinji."
Hafsah ta d'aga kai alamar Toh."
Sai wajen la,asar suka tafi gida wanda a hanya tunanin Hafsah ya kasu kashi-kashi, wanda yafi tsaya mata a rai shine, nasihar mama, sai kuma jin asarar barin Basma, haka taci bulus. Dole ta bata mata rai ita ma kamar yadda tasa ranta dana iyayenta b'aci.
Sunje gida da daddare, mama ta kira fateema d'akinta, so take ta sa Fateeman wani aiki akan Hafsah.
"Fatee, kun tab'a wata hira ne da Hafsah, wacce tayi kama data samari."?
Fatima ta tsorata da tambayar don haka ta bud'e baki, gwara ta fad'awa Maman gaskiya kada taje tayi laifi don da alama akwai babban case wanda yake faruwa.
"A,a mama, saidai ta ari wayata tasa wata number, ta duba a Whatsapp amma bata kira ba kuma batayi magana ba."
"Me yasa baki fad`amin jiya ba."?
Mama ta tambaya da fad`a-fad`a.
"Kiyi hak`uri mama, bayan ta sa number sai ta tsaya kallon profile d`in kuma sai ta fashe da kuka."?
"Kuka kuma."
"Eh Mama."
"Amma duk kika k`i fad`amin koh."?
"Mama kiyi hak'uri."
Kada ki sake boye min abu makamancin wannan, tashi ki d`akko wayarki ki nuna min photon yaron..
Kafin na fad`a miki abinda zaki min..."
Nan Fateema ta miqe ta nufi d`akinsu don d`akko wayar.



Acan D`akin kuma, Hafsah ganin ita kad`ai ce a d'akin sai tayi alwashin kawai aiwatar da abinda zuciyarta ke raya mata, don ta sami dama, tana gudun kada ta wuce ta.


Cikin zafin nama ta d'akko wayar dake gefenta, ta danna wasu numbobi, ringin d`in har ya katse ba,a d`aga ba, ta qara dannawa karo na biyu.
Wannan karon an d`aga.
"Hello."
Aka fad'a daga can b'angaren.
Cikin kaushin murya, Hafsah ta fara magana.

"Hi Master of snatching H. Habeeb Hamid ke magana.!!
"Hmm, I already know it's you _good for nothing.!!_
Kada ki d'auka abinda kika yi kinci bulus, karuwar gida kawai.".. Bata bari ta sami kalmar mayarwa ba ta d`ora.. _"Ashe ke b'arauniya ce ban sani ba, b`arauniya, mai sace samarin mutane, yar iska mara tarbiyya._
"Haha Haha, dariyar basma ta cika kunnen Hafsan,
_"I already know zaki fadi irin haka tun ba yau ba loser.!!_
"Kiji kawai da rashin Yusuf da bazai kara dawo miki ba, idan kuma kina son ki tabbatar gobe k'arfe shida mu had'u _Garden_ idan kin isah.

"Qarya kike mayaudariya...

Iya zancen da kunnen Fateema yaji kenan anayi a wayar ta sanda ta shigo d'akin da azama ta warce wayar,
"Wacece..wacece mayaudariya.."??
Wa kika kira a wayata.. Me.. me yasa haka Hafsah."???
_Cikin in'ina fateema ke magana.._





📝
*HAJEEYA KHAREEMERH*
♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔
*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group members.*


I DEDICATED THIS PAGE TO YOU _(RUKKY NAILA GROUP 1)_ SURELY YOU ARE A TRUE FAN.. 😊





📄 *41*




*Ki kyaleni..* Ni ki kyaleni.. Wallahi bazan rabu da ita ba, bazan bar mata shi ba.!"

Abinda Hafsah ke fad'a kenan cikin kuka, yayin da Fateema ta riqe ta a tsorace.
"Kiyi hak'uri Hafsah don Allah ki fad`amin me ya faru, wa kika kira.?

Cikin kuka tace "Nidai, kiyi hak'uri na daukar miki waya, amma ki kyale kawai.
Fateema taga bada da lokacin b'atawa don mama na jiranta don haka ta wuce zata fita. Ta kai bakin k`ofa kenan ta jiyo Hafsah na magana.
"Don Allah kada ki fad'awa mama, nayi kira a waya."
"To kawai fatima tace ta fita."
"Me Hafsan keyi."?
Mama ta tambayeta tana zama.
Cikin son rufawa Hafsah asiri fatima har zuwa sanda zataji aikin da maman xata sata don haka tace, "Babu komai tana kwance ne."
"Tom, muga yaron."?
Fateema ta budo profile d`in yusuf ta miqawa mama.
Muntuna uku tana qare wa Yusuf kallo, sannan ta miqo mata tare da jan siririn tsaki.
"Daga ganinshi bashi da cikakkiyar tarbiyya.!!"

Ita dai fateema kallo tabi mama dashi ta mayar da kai k'asa.
"Ki bani hakalinki nan.
Cewar mama, tana zubawa Fateema ido, yayin da ita kuma ta gyara zama ta bada hankalin nata ga Maman.
"Inaso ki dinga janta da hirar samari har ki gano min matsalar ta."
Fatima ta jinjina kai, mama ta d'ora.
"Akwai alamu yaron nan yana hure mata kunne, ada, don (Ameenah/maman su Hafsah) har qarar ta ta kawo min. Amma yanzu naga alamun tana da damuwa, kuma naga kamar yaron ya yaudare ta ne, shine nake son ki hilace ta da hira, ki gano min gaskiyar me ya faru."
"Kingane."?
Fateema ta jinjina kai "Eh, Mama."
Yawwa, ku dinga hirar samari da ita, da kuma hirar makaranta.
"Toh mama."
"Yawwa nasan zaki iya koh."?
Fateema ta d'aga kai alamar Eh." Tana murmushi.
"Yawwa Allah ya taimaka yayi albarka."

Da Fateema taso ta fad'awa mama zancen wayar da ta tarar Hafsah nayi, sai kuma ta fasa, gwara ta kawo mata cikakken bayani gaba-d'aya."
"Ta miqe ta zata fita mama ta kirata."
Kada fa ki matsa mata da tambayoyi ki bari a hankali, zaki bi abin, ba sauri nake ba."
"Okay mama.!
"Yawwa."
Wajen Hafsah ta koma, ta tarar da ita tayi tagumi, ga gumi da ta had`a.
Fateema tazo kusa da ita ta dafa kafad`unta.
"Am sorry my sister, kin sani cikin duhu, kiyi hak'uri ki fad`amin me yake faruwa."?
"Ni yar uwarki ce ko ba komai, zan taya ki da shawara da addu,a."
Hawaye suka qara zubowa, Hafsah, "Kada ki damu, wannan abin ni ta shafa kawai."
"A,a wallahi nima ya shafe ni, don Allah ki fad'a min."
Shuru babu alamun, Hafsah zata ce komai, sai ajiyar zuciya da take tayi tana cije leb`e.

"Hafsy..Hafsy,!!
Nazeer ya kwalo-mata kira.
Har aranta bataji dad`in kiran ba, bata son abinda yake mata bare yanzu cikin yanayin da take, da ita kad'ai ce babu abinda zai hanata yin _burus_ dashi, amma kuma ga k'anwarshi gefenta dole ta amsa, ko dan gudun kada ta ji haushin hakan, tunda ance _d`an-uwa rabin-jiki."_
"Hafsah Ya Nazeer fa yana kiranki."
Fateema ta qara qarfafa mata guiwa da haka. Ala dole ta miqe, ta fita, bata da qarfin muryar da zata amsa.
Yana tsaye a parlour ta motsa baki, zatace _"Gani."_ ya tare ta.
"Haba Sisi na, kiran ma baza,a amsa min ba."?
"Banji ba ne." ta fad'a murya a dashe.
"Nidai ayi hakuri idan ni na b'ata miki rai, dama abinci za,a taimaka min dashi."
Ya fad'a yana qare mata kallo.
Abin ya bata kunya, taji kunyar kanta, ta dan saki rai sannan tace, "Ciwon kai nakeyi."
"Ayya sannu kinsha magani."?
Ta girgiza kai.
'To kije kisha bari na zuba abincin da kaina."
Ta girgiza mishi kai, bata son ya dinga karantar k'osawar da tayi da shi don haka ta wuce kitchen.
Shi kuma ganin ya sami abinda yake so sai ya wuce d`akin shi.


Ranta ya qara b'aci bata son shiga d`akinshi sam, da yaran suna nan babu abinda zai hana ta basu su kai mishi. Amma babu yadda ta iya.
A bakin kofa ta tsaya. "Ga abincin."
Ta fad'a a qasan mak`oshi.
"Kiyi hakuri ki miqo min ciki."
"Shima yayo magana da ga cikin dakin.
Ta ajye abincin ko kallonshi bata yi ba, zata juya taji yace.
"Don Allah Hafsah, ki zo kiji."
Ta juyo ta tsaya tana kallon shi.
"Ki zauna mana please."
Ta dan d`osanu a Kujera.
Ya juyo gaba-d`aya Ya fuskanto ta.
Cikin marairaice murya ya fara magana.
"Jibi zamu shiga _camp_ Hafsah, gobe zan tafi in barku."
Shuru tayi tana, nazarin zancen, mene alfanun fad'ar kalmar nan."?
Tana tsakiya da mamaki taji yace.
"Zanyi kewar ku Hafsah.!!
Binshi da kallo tayi kawai.
"Baki da waya koh."?
Ta gaji da irin salon nashi me yake nufi, a irin wannan lokacin da take cikin halin k'ila wa k'ala, akan Yusuf, zai dinga zuwa mata da wani zance ?? don haka, ta had'e rai.
Ya lura da hakan, nan ya shiga tunani,
_"Ya dace, ya bar yarinya da wannan batun don da alama hankalinta ba akanshi yake ba kuma, akwai sauran yarinta a tattare da ita."_
_Zai barta zuwa wasu lokuta yaga idan akwai rabon shi._
Ya saki ajiyar zuciya, "Okey thank you, kije ciki na gode."
Ta miqe kamar akan qaya take.
_Ya bi bayanta da kallo yana kissima abubuwa da dama, ko dai ya hakura ne kawai.?_
To, babu yadda Fateema bata yi ba, don "Hafsah ta fada mata dawa tayi waya amma fir taki fad'a.
Don haka ta rabu da ita, sai kawai tayi saving number, da Hafsan ta kira.
Daren Hafsah, cike da mafarke-mafarken Yusuf da Basma mara sa dad`in bada labari, haka ta wayi gari da alwashin sai taje inda Basma ta fad'a mata don a banbance tsaba da tsakuwa tsanin ita da ita.

Da sassafe, Nazeer ya gama shiri tsab, ya fito da jakarshi sab'e zai musu sallama, dakin Mamanshi ya fara shiga ta dad'e tana yi mishi addu,ar samun nasara da tsarin ubangiji..
"Amin mama Nagode." haka yake ta fad'a.
Suka fito shida mama zuwa palour, yaran duk suna nan dake Lahdi ce, mama ta qare musu kallo babu Hafsah aciki, "Fateema jeki kira Hafsah suyi sallama.
Yaji dad`in hakan sosai.
Tare suka dawo da Fateeman.
Ta saki fara,a kuma. "Har da cewa yaya tafiyar ce."?
Shiko abin nema ya samu, murmushi yayi mata. "Eh mun fito sai Allah ya dawo damu, kwana biyu kema ki huta da zubamini-zuba-mini."
Dariya, sukayi musu, mama nacewa, "Ah toh, ashe dai ka sani."
Har habar gidan aka fita raka shi, Hafsah taga bata da zab'i sai illa itama ta bisun. Don haka tabi bayansu.
Kallonta yake sosai, kallon da kowa yaso lura dashi. Kallon da Hafsah ta kasa fassara shi. Daga bi sa-ni ya d`auke idonshi yana da murmushi had`i da daga musu hannu bye-bye."
Yace musu. Driver yaja, suka dawo ciki anata hirar kewa.!
Kusan Yinin ranar Hafsah a d`aki tayi shi, tanata kissima abubuwa da dama a ranta.
_Tabbas sai taje ga Basma. Dole taje ta nuna mata, shuru shuru ba wasa bane, kuma dole ta nuna mata cewa tabbas tayi kafuwar da ita bazata tab'a yi ba har abada a zuciyar Yusuf._
Mama bata takura mata da tambayoyi ba yau, tun bayan da ta tambayi Fateema _"Ko akwai bayani.?_ fateema tace mata babu, amma kuma a bisa dole, ta labarta mata batun wayar da, Hafsah tayi a jiya.
"Ki dinga kaffa-kaffa da wayarki kema, sannan sai kin qara qaimi, kinsa dabara ko in koya miki dabarun."?
Fateema tayi dariya "Aa, ki bari mama, zan iya."
"Yawwa, ko kefa."?
Tun da rana mama ta zubawa duk wani motsin Hafsah ido, tana gani tayi wanka da la,asar ta shirya cikin kaya masu kyau, shirin dai yafi kama da na wanda zai fita.
Bata tanka, mata ba, amma a zuciyar ta ta kissima, _"Kada dai ace yarinyar nan wani ta jawo min gidan nan._
K'arfe 5:30pm, Hafsah nata kallon agogo, ji take kamar akan qaya take, gashi mama ta kasa ta tsare a parlour.
''Oh my God.!! Take ta fad'a a zuciyarta hira kawai ake, amma sam ba fahimta Hafsah take ba, hankalinta na can wani guri, zuciyar ta na raya mata abubuwa da dama bata so, Basma ta ce _tsoro taji_ shiyasa ta qi zuwa.
Ana hada wayar mama tayi qara, ta d'auka ta fara waya, sai kuma tayi d'akinta.
Damar da Hafsah ta samu kenan ta, wuce daki cikin hanzari Fateema na kwance ta ganta, da azama kafin tayi magana ta d`auki jakarta da mayafinta ta fice.
A parlour, sai su Al,ameen da Nour, ta kakkkalle su kawai ta fice.
Yaya Hafsah ina zaki."?
Inji Al,amin.
Abinda mama taji kamar kunnen ta ya jiyo mata take ta yanke wayar. Itako Hafsah, ai jin yaran sunyi magana tuni ta qara da gudu-gudu har ta isa gate ta bude kofa ta fice."
Fitowar mama kenan taci karo da Fateema ita ma.
Maman ta fara magana kenan tana tambayar yaran "Ku Hafsah ce ta...
Kafin ta Ida tambayar su taji fateema na cewa "Mama aiken Hafsah kikayi."?
Cikin rud'ewa mama, ta qarasa tambayar, "Nace muku Hafsah ce ta fita."?
"Har sun dan fara rud'ewa, suna in'ina, "A,eh" fita tayi, muma bamu san ina ta tafi ba."
Mama ta tafa hannaye tana salati, yarinya zata ja mata masifa, ubanta ya amince ya bata ita amma kuma tayi mata haka, du-du-du, ko sati bata cikasa a gidan ba.
Da azama mama ta figi mayafinta, fateema ta bita cike da rud'u.
Me yake faruwa da Hafsah ne, gaskiya bata san halin mamansu ba da bazata dinga, irin haka ba. Da ace ita ce, ai kashinta ya bushe..."
_Har rige-rigen fita suke ita da mama, kuma babu wanda yacewa wani uffan, to ina ma suka ga lokacin magana."??....._


📝
*HAJEEYAH KHAREEMERH*

♥️♥️♥️♥️
*ZAZZAFAN SO*
(masoyin k'warai )
*Cigaban littafin Zazzafan so*
*(Guba ne)*
💔💔

*By:*
*Karima Tijjani Mansur*
*(Hajeeyah khareemerh)*
*Dedicated to Unique in your love heart group member*




📄 *42*


*Acan* wajen qarshen layinsu suka hango ta tana qoqarin tsare napep.
"Ki bita da sauri mana."
Mama ta fad'a da fad'a-fad'a.
"Gudu gudu, sauri sauri Fateema keyi tana, kwalawa Hafsah kira.
Ai kuwa ta jiyo kamar ana kiranta sai ta juyo.
"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un.
Shine abinda Hafsah ta shiga furtawa ganin mama na nufo ta, yau ta kad'e, ina zata kai kunyar mama."?
Allah yaso Nazeer baya nan da yaya zatayi, da kunyar shi."??
Bata bi takan me napep d`in ba ta juyo, suka had'u da Fateema, ta riqe hannun Hafsah jikinta duk yayi sanyi.
Ina zaki je Hafsah."?
Bata da bakin magana sai jikin ta dake yin rawa, tsabar tsoro m, lallai tayi ganganci da rashin tunani.
Suna qarasowa daf da Mama, takaici yaja maman ta daga hannu ta wanke ta da mari.
"Yau na tabbatar da cewa baki da mutunci yarinyar nan, shiyasa Amiina take cewa, kina neman fin qarfinta.!!"
Ta talle qeyar ta, ta tusa su gaba ita da fateema wuce muje gida ki fad'a min gidan uban wa zaki tafi."
Dukkansu sauri suke kamar zasu tashi sama, sai gasu cikin abinda baifi minti d'aya ba har sun iso gidan.
Kiii, mama taja Hafsah sai d'akinta.
"Nema kike ki wulaqanta ni koh, shiyasa zaki fita bada izini na ba koh."?
"Kuka kawai Hafsah keyi kukan nadama, da Kukan rashi.
Ki rufe min baki ko in tattaka ki anan, kuma idan baki fad`amin inda kikayi niyyar zuwa ba, sai naci mutuncinki a gidan nan.
"Idan kuma don in maida ki gida, kikai min haka ina mai tabbatar miki babu inda zaki, idan nace kin dawo nan babu wanda zan hana ni hakan..."
Takaici ya tuqe mama ta dafe kunci tayi shuru.
Tabbas yarinyar ta bata mamaki, ya akayi ta zama haka ne, yarinyar da aka santa da nutsuwa da ladabi da biyayya, amma gaba-d`aya ta chanja.
Kaii idan ka biyewa yaran yanzu sai ka b'ige da hakan jini ko ciwon zuciya.
Shirun Maman, ya tsorata Hafsah, tabbas an kai ta bango, shiyasa ta rasa abin cewa.
Tsanar Basma ta nunku a zuciyar Hafsah ninkin ba ninkin.
_Ba don ita ba babu abinda zai dinga kawo mata sabani da iyayenta haka._
Tayi mata Allah ya isa tafi dubu zuciyarta. Take hawaye suka fara zarya a kuncinta.
Mama ta riqe haba da takaici, kafin ta miqe zumbur, ta kaiwa Hafsah wani mugun bugu da takaici, Allah yaso ta kauce.
"Ni banyi kuka ba sai ke."? Saboda kin raina ni, zaki dinga kuka.? Me nayi miki.."? Tsabar sharri koh, dama haka kike ban sani ba, dama haka kike yiwa Aminan..?
Gaskiya kin cuci kanki kam, baki yiwa kanki adalci ba..
Cikin kuka ta fara bada hak'uri "Don Allah

19 / 40