Author : Nil Category : Romantic Hausa Novels
anty zee mai sunan ummammu.
Tsaki naja tare da nufar bayi zubar da miyan bacci nayi sannan naja hijabin amira nabar ɗakin.
Afalon umma na kwanta akan ɗaya daga cikin kujerunta na ƙudundune jikina tare da takurewa waje guda sabida yadda sanyin asubar ke ratsani.
Wani baccinne mai dadi ya kwasheni batare dana yi tsammani ba.
Dama bana sallah ina up shiyasa na baje ina shaƙar baccina batare dana tuna tafiya na gabammu ba.
Danni gani nake kamar ba tafiyar za,aiba
Tun ina jiyo maganar su umma waɗanda suke bedroom ita da anty zee nidai har baccina yayi nisa.
Daƙyar ya samu ya tashi maryam da asuba sannan ya wuce toilet yayi abinda ze yabar ɗakin ya nufi masallaci.
Jikinsa sanye da baƙar jallabiya wadda tai matuƙar haska masa farar fatar jikinsa.
Acikin masallaci suka haɗu da abba gaisawa sukai sannan suka miƙe suka jero domin zuwa cikin gida.
Abakin ƙofa suka rabu inda abba yayi falonsa shi kuma yayi falon umma domin ya gaisar da ita daman wannan tsarinsa ne tun kafin yay aure.
Ganin falon umma da duhu yasa ya nufi wajan makunnin ƙwan falon ya kunna sa dayake ƙwan mai haskene shiyasa nan danan ya haske falon baki ɗaya.
Cikin mamaki yake kallon wanda ya matse kansa acikin kujera kamar ze tsagata ya shiga.
Da sauri ya ƙarasa gaban wadda ya gani akan kujerar danshi dik tunaninsa ma bai basa batula bace.
Gyaran murya yayi kafin yaɗan leƙa yana son ganin wannan maiwa kan nasa azaba.
Da mamaki ya ƙara wara idanunsa yana kallon yadda ta wani matse kanta tanata sharar bacci batare data tashi tayi sallah ba.
Jin shuru yasan su umma sallah suke dan haka cikin azama.
Ya saka hannunsa yaɗan bigi gefen kujerar amman ko gezau batai ba sema sake ware ƙafa datai tana sharar baccinta.
Cikin zafin nama kaɗan ya kuma kai hannunsa gefenta yaja ƙafarta tare da mayar da hannunsa jikinsa yana kallonta.
Da masifa na farka tare da cewa.
"Wai dan ALLAH ke amira miye haka idan hijabinki zan baki basekimin magana ba shine dan raini zakina jamin ƙafana".
Nafaɗa ina sosai idona batare dana kalli wanda nikewa maganar ba.
"Malama dallah miƙe kiyi sallah duba yanzu ƙarfe nawa banza ke ko kunyar ALLAH bakyaji bazaki sallaha akan lokaci ba".
Naji saukar muryarsa akaina.
Da sauri na buɗe idona tarwai ina kallonsa ina shafa fuskata alamun na watstsake baki ɗaya.
"Fatie idan na sake magana wallahi zan mareki!.
Gunguni nahau yi tare da ƙoƙarin sakkowa daga kan kujerar.
Banyi aune ba sejin saukar yatsunsa nai biyar akan fuskata.
Da sauri na koma saman kujerar ina toshe bakina.
"Dan ubanki ni sa,anki ne daxaki na min ƙunƙuni wannan yazama na farko yazama na ƙarshe usless kawai".
Yafaɗa tare da barin falon a fusace.
Sosa wajan nai ina maijin zafin marin tare da jinjina muguntar ya hydar wallahi se ALLAH ya sakamin nafaɗa tare da mayar da kaina na kwanata kamar dole.
Gari na ƙarasa wayewa su anty zee suka hau shirinsu sabida motar drivern sa zatazone wajan ƙarfe goman safiya wadda su zasu shiga shikuma zebi jirgi tare da matarsa amman sunji ma ance harda batula yace wai zasu tafi ajirgin.
Umma ce ta dubi amira wadda take faman loda kaya a bag tare da ce mata ina batula ne?
Cemata tai ai tun asuba sudai sukaga tai cikin falon umma amman sunsan bacci take may be.
Cikin jin haushi umma tacewa ummi ta tasota aikuwa koda ummi taje taso batula nan ma seda akai faɗan da aka saba sannan ta miƙe tayo ɗakin umma tana faman tura baki.
"Umma gani"
Nafaɗa ina kokarin zama akan gadonta.
Cikin masifa anty zee tayomin ka.
"Kekam batula wacce irin sokuwar ƴacene yanzu dan ubanki kinsan yau zamuyi tafiya amman kiketa sharan bacci".
"To idanma zaki sauya ki sauya dan wallahi maza basa son mace mai son jiki bareke mijinki ɗan gayu mai tsafta".
"Idan kuwa baki sauyawa ba wallahi kya dawwama a ƙasan matarsa dan kada kiga kunada alaƙa dashi koze raga maki".
Nanfa taketa faɗa ta inda ta shiga bata nan take futa ba.
Babu shiri nai bayin umma har ina tuntube.
Ruwa mai ɗumi na haɗa na cuɗe jikina sosai sannan na fito waje.
Ɗakinmu na koma na sauya pant da pad sannan na saka atamfar dana ware zan sakata wadda nai mata marching da mayafi mai kyau.
Nidai ina wannan shirin naji umma na kirana.
Ina fita kuma abinda ya bani mamaki yadda naga ana fita da kayana waje wai har motar tazo.
Falon umma na ƙarasa cikin mutuwar jiki.
Zaune na iskesu jikinsa sanye da wani ruwan madarar yadi ɗan gaske tsayawama faɗin yadda yay masa kyau ɓata bakine.
Itama anty maryam taci ado na futar hankali tana gefensa danni se anan ma naga yadda cikin jikin nata ya ƙara girma masha ALLAH.
Abbanmu dake zaune na ƙarasa na gaisar sannan na gaisar da umma.
Shima na gaisar dashi wanda ya amsamin a daƙile kamar nai masa dole.
Ko kallon matarsa banyi ba bare ta saka ran xan gaida ita haka na mayar da hankalina kan abba wanda ya fara bude taron da addu,a sannan ya dora mana da nasiha musamman ni dayafi jan kunnena sosai.
Babu abinda naga anty maryam nayi se hararata nidai na sunkuyar da kaina ƙasa ina faman kuka!
Seda abba ya gama sannan naga sun miƙe alamun tafiya zamuyi tunda su daman su anty zee sunama cikin mota a waje.
Fafur umma taki yarda ta rakamu airport haka na rungumeta ina kukan kewarta.
Daƙyar ya cireni daga jikinta yaja hannuna har mota ya cillani ciki sannan suma suka shiga driver ya jamu zuwa airport.
Baƙaramin kuka naciba wanda seda ya zageni sannan naja bakina nai tsit.
Ko acan airport seda akai da gaske san nan na iya shiga jirgi.
Da kansa ya sakamin belt sannnan ya sakamu a tsakiyarsa ganin yadda duk na furgice haka jirgin ya ɗaga damu.
Wanda lokacin daxe tashi seda nai ihun tsoro harar daya sakarmin ce ta saitani.
Daman su su ummi motarsu ta riga data ɗauki hanya acan zamu haɗu.
Haka jirgin ya cigaba da tafiya cikin keta hazo izuwa garin abuja.......!!
*44 - 45*
Tun ina jin wani irin tsoro acikin raina kasancewar wannan karon shine na farkon hawa jirgina har kuma nazo na maze nacigaba da sabgar gabana.
Tun ina tunani acikin zuciyata har wani bacci mai daɗi ya sureni.
Ban kuma farkaba seda naji tafin hannunsa akan fuskata.
Da sauri na buɗe idona cikin haɗe rai naga yana kallona.
"Malama mi zakici?"
Yafaɗa batare daya saki fuskarshi ba nima ban masa far,arba sabida wani haushi dayake bani.
"Bana buƙatar komai".
Nafaɗa cikin basarwa tare da kawar da kaina gefen window ina kallon hazo.
Cikin rashin damuwa da lamarina naga ya kaɗa kafaɗarsa alamun ko ajikinsa.
Juyawa yayi wajan matarsa yana kai mata cup cikin bakinta.
Ita kuma se wani langwaɓewa take tana yatsina fuska.
Nidai abin dariyama ya bani amman ganin ni kaɗaice gefensa kada ya kawaɗamin mari yasa nabarta cikin raina.
Juyawa na kumayi nan da nan bacci ya kuma kamani cike da jin yunwa.
Shikam aliyu mamaki yarinyar take basa ace ita bacci baya mata wuya komai bacci komai bacci.
Ya ƙarasa tunanin cikin ransa bayan ya ɗan kalleta ta gefen idanunsa ya watsar.
Nidai ban farkaba seda naji yunwa tamin tsaye acikina har wani jiri nake gani.nidaman gani gwanar ci gashi kuma yau tun abincin daren jiya ban kai koda ruwa cikin bakina ba.
Buɗe idona nayi tarwai tare da matso da hawaye.
"Yaya zanci abinci yunwa nakeji".
Najuya ina kallonsa.
Ina jiran naji kuma mai zece min.
Fuskarsa ɗaure ya juyo yana kallona.
"Seki bari kuma mu sauka nan da 30mnt bawani abinci dazaki ci yanzu".
Tsintar muryar anty maryam nai cikin wani iri salo tana cewa.
"haba beby kayi magana a kawo mata abincin mana ai tamayi ƙoƙari kasanfa muntaho da gara so dole seda zuri".
Takai maganar tana yin wata sakarar dariya.
Batare daya fuskanci mitake nufi ba yahau faɗan nasa kamar ko yaushe.
"Haba maryam kina kallofa ɗazu nace mizataci tace ta ƙoshi sabida haka sedai yunwar ya kasheta amman babu abinda zan bata".
Yakai maganar cikin sautin zafi.
Dariya taɗanyi ƙasa ƙasa.
"pls beby....."shii!! yafaɗa mata tare da saka hannunsa akan lip's ɗinta.
Cikin takaicin jin maganar datai min mai kama da jirwaye mai kamar wanka nace.
"A,a ba gara ba sedai kaza, yataho da ita ƙarewar gara kuma nagodewa ALLAH tunda badaga yunwa na fitoba, dan ALLAH daga yau har abada kada yabani abincin yaga kozan mut......."!! bankai ƙarsheba naji saukar hannunsa akan bakina ya dokemin baki dashi.
Cikin jin haushi na ɗago tare da toshe bakin nawa jin wani irin zafi ya ratsani sannan nace.
"Wallahi se ALLAH ya sakamin wayyo umma kina ina mugu ze cirewa ƴarki haƙori"!!
Nakai maganar ina sakin wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Da sauri maryam ta ɗago tana kallon batula jin yadda takewa hydar rashin kunya tana kuma jiran taji wani taking action ze akan hakan.
Amman ga mamakinta setaga ya sunkuyar da kansa ƙasa yana shafa sumar kan nashi.
Cikin takaici ta juya masa baya tana mamakin shurun daya yi wanda inda itace tasan da yanzu wani zancen ake ba wannan ba danseya bata kashi.
Shikam sunkuyar da kansa ƙasa yayi ganin idan yace ze biye mata ze ɓata lokacinsa ne sannan kuma ya bawa kansa kunya a gaban jama,ar cikin jirgin.
ƙasa-ƙasa nake sakin kukana mai ɗauke da ma,ana biyu na farko yunwa na biyu dukan daya kawomin agaban matarsa salon ta rainani.
Tsintar muryarsa nayi a dake yana cewa.
"Wallahi idan baki rufemin wannan ƙazamin bakin nakiba ALLAH zan ƙara maki wani".
Ɗago da kaina nai na kallesa har yanzu kansa a ƙasa yake kuma idonsa a lumshe yake.
Sedai salon yadda yay maganar tasa dagaji kasan da abinda yake damunshi domin ga vioce ɗinshi nan tai ƙasa sosai.
Tura bakina nayi gaba.
"Ni wallahi bazanyi shurun ba yaya za,a dakeni a hanani kuka! dan anga babu iyayena a wajannan".
Nakai maganar cikin rashin kunyar dana saba.
Da sauri naga ya ɗago kansa baki ɗaya tare da zubamin idanunsa.
Cikin sauri na mayar da kaina cikin Tsakanin cinyoyina ina boyewa sabida yadda naga idanun nashi wanda bani ba koma waye baze jure kallonsu ba.
Ban kuma ɗagoba seda naji ana sanarwar jirgi ze sauka.
Cikin tsoro na ɗaga kaina ina kallonsa wanda shi sam hankalinsa ma ba,a kaina yakeba yana can sunkuye da kai gefen anty maryam suna magana.
"Yaya ka gyaramin belt ɗina kada na faɗo ƙasa".
Nafaɗa ina kai hannuna kan cinyarsa.
Cikin mamakin furucinta ya ɗago batare daya kalleta ba amman kuma mamaki ta bashi matuƙa na yadda take maganarta kai tsaye.
"Maganin marar kunya kenan ALLAH yasa ki faɗa".
Batare daya kalleniba yacemin hakan.
Ban basa amsaba na sunkuya ina matsar ƙwallata.
Jin saukar hannunsa a ƙuguna yasakani dawowa daga tunanin dana ɗan faɗa.
Kamar yanamin tafiyar tsutsa ajikina haka nakeji har wani ranƙwaɓowa yayi yana gyaramin belt ɗin yana gama saitawa naji saukar muryarsa.
"Kinci darajar umma mayyar maza"!
Wata harara na zabga masa nima na mayar masa da amsa.
"Nida kai aga waye maye nidai nagode ALLAH tunda bana shan....!
Ban ƙarasa faɗa ba na kunshe magana acikina ganin yadda ya waromin ido yana hararata tare da jan ƙwafar zamu haɗune.
Cikin amincin ALLAH jirgi yafara landing zuwa ƙasa nima kuma nai landing jikinsa domin cikin furgici na rungumesa tsaff ina sakin numfashin tsoro.
Seda ya daidaita tsayuwa sannan naji ya tureni daga jikinsa nan fa jama,ar suka fara futa daga cikin jirgin.
Ganin sun tashi yasa nima na tashi tsaye muka fara sauka daga step ɗin jirgin.
Seda komai ya kammala sannan muka fita zuwa harabar airport ɗin garin abujan.
Wasu manyan motocine jere kusan guda uku naga wasu ƙartin sojoji sun fito daga cikinsu sun nufo inda muke salute naga sun masa tare da ɗora hannunsu akan goshinsu sannan suka ɗauki bags ɗinsa shida maryam suka nufi cikin motar dasu.
Motar farko naga wani soja ya buɗe masa sannan ta biyun aka zuba kaya.
Ta ukun naga ya nufa riƙe da hannun matarsa nima kuwa na mara musu baya.
Seda ya bude mata murfin motar baya ta shiga sannan shima naga sojan ya bude masa ya shiga.
Da sauri nima nai kokarin budewa na shiga seji nai yace.
"Bose kaita motarsu musa tabisu nan zamu takura madam ne".
Wani bakincikine ya kamani jin yarfin daya min kamar zan kuka.
Haka na zabga masa harara mai zafin gaske sannan naja musu mugun tsaki nabar wajan.
Ko kallon inda bosen yake banyi ba haka naja ƙafata na nufi vakin gate batare dana san inda zan nufa ba......!!
*46 - 47*
Kuka kawai nake gawani baƙin ciki daya min tsaye acikin zuciyata har wani duhu nike gani acikin idanuna dan tsabar takaici.
Ina jiyo ihun bose yake ko waye yanata min magana cikin gwaranci dan naji hausarsa ba kamar tamu ba.
Seda nakai ga bakin gate ɗin wanda zan fita waje sannan najiyo muryasa "Fatie!Fatie! wallahi idan kika fita daga gate ɗinnan sena cire ƙashin cinyarki da belt".
Cak na tsaya ina jan numfashi batare dana juyo na kallesaba sema ƙara bashi bayan danayi.
Hucin numfashinsa a saman wuyana danaji shine ya bani tabbacin dayana bayana kenan.
Cikin zafin nama ya juyo dani tare da kamo tsintsiyar hannuna yajani zuwa cikin gate ɗin.
Bakin motar daya bada damar na shiga ya tsaya tare da kokarin bude murfin motar ya sakani.
Da sauri naga bosen ya taho tare da kai hannunsa jikina ze shigar dani cikin motar.
Wani banzan kallo naga ya watsawa bose din tare da cewa.
"Bose are you in sense!!" kana cikin hankalin ka,!!
Yafaɗa cikin tsawa kaɗan da sauri naga bosen ya mayar da hannunsa ya ƙame jikinsa har rawa yake sannan naji yace.
"Sorry sir"!
Tare da ƙara ƙamewa waje guda.
Tsaki naji yaja tare da fusgoni ya daki murfin motar da ƙarfi yabar wajan dani.
Azuciye ya wurgani gefen anty maryam sannan shima ya shiga ta ɗaya side ɗin ya zauna muka sakata a tsakiyarmu.
Tsaki naji ya kuma ja da ƙarfi sannan naji ya dakawa kurtun sojan daze jamu tsawa!!
Cikin sauri kurtun sojan yaja motar muka bar wajan.
Titi motocin suka hau a jere kuma tunda muka hau titin tsitt garin yake kamar babu biladama a kan titin.
Nidai tunda ya wurgani cikin motar na raɓe a gefe ban kuma motsin kirkiba dan gano rikicin danai a cikin idanunsa wanda tunda nake bantaɓa ganin tamkarsaba tabbas yau KUSAR YAƘIN ne akusa sosai dan naga tunda yayi ƙasa da kansa har yanxu bai ɗagoba maganar duniya matarsa tai masa amman yay mata banxa.
Ƙarshe ma data kuma masa maganar daya ɗago ya watsa mata wani kallo ni kaina seda na tsorata da ganin idanun nasa.
Cikin wata unguwa mai yalwar bishiyu gami da sanyi da nutsuwa motocin namu suka kutsa kai.
Babu wasu gine ginen kirki acikin unguwar se tsiraru waɗan da idan kaga wannan gidan anan tose kai tafiya mai tsayi kafin kaga wani gidan kuma mafi akasarin gidajan dik manyane masu ɗan karen kyau da mahaukatan gate-gate.
Tuni na buɗe idanuna tarwai ina kallon tsarin gidajan waɗanda baƙaramin ƙayatar dani sukaiba.
Wayarsa wadda naga ya ciro a jikinsa mai ɗan karan kyau da tsada itace ta hau ringing!!
Cikin azama naga ya danna wayar alamun katsewa sannan naga ya shiga kira wanda ina ɗan leƙensa ne daga gefen idanuna.
"Hellow hajiya ta barka da yamma".
Naji muryarsa ta daki dodon kunnena.
Ƙaro handsfree yayi sabida yadda muke tafiya may be ko muryar tata rawa take masane oho!
Daga nata side ɗin naji tace.
"Baba tun ɗazu nake try number ka swich off hala yanxu kuka iso ne?"
Lumshe idanunsa naga yayi alamun yana tare da damuwa sannan naji yace.
"Eh wallahi Yanzun haka ina hanyar gidana na gwarumfa zamu sauka, anan kafin mu shigo ko gobe karki damu hajiya da motar barrack muka taho".
Yakai maganar cikin kwantar da muryarsa.
Cikin wata iriyar murya mai cike da rikici naji momy tahau salati.
"Haka nai da kai? nace haka nai dakai baba?".
"Watakan tunma kafin aja lokaci mai tsaho kafara min wasa da magana ko? lallai sena tashi tsaye an haɗoka da ƴar gidan mai ganye, to ban lamunta ban kuma amince ba wallahi kuma juyo dakan motarku gida ita maryam a gyara mata part ɗinka na da idan ta haihu ta koma ita kuma waccan ƴar gaba da fatihar ta zauna a B.Q......! da sauri naga ya cire handsfree ɗin wayar yana sauraranta.
Ban samu naƙarasa jin mitake gaya masaba.
Nadaiga yana ta bata haƙuri sannan sukai sallama da ita.
Cikin harshen turanci naji yanawa kurtun sojan magana.
Da sauri naga kurtun ya juya da kan motar wanda naga ya baiwa sauran na bayanmu damar sauya akala suma suka mara mana baya.
Muka dauki wata hanya ta daban kuma.
Akaron farko tausayin halin dazan shiga da tausayin kaina naji ya kamani wannan shi ake cewa rana zafi inuwa ƙuna.
Ba uwa ba uba ba wa ba ƙani se dangi waɗanda ba ƙaunata sukeba.
Wata irin nadamace ta kamani tare da tausayin kaina da tausayin rayuwar dazan shiga wanda bantaɓa kawo hakan araina ba se yanzu.
Wama ze zaman katangata acikin gidan momy?
Maryam data kasance kishiyata da bata ƙaunata ko ya hydar da ko kallon kirki bana gani atare dashi?
Koko momy da yaranta waɗanda ko sunana basa kira dan tsabar kiyayya.
Baban abuja ba mazauni bane tunda yay ritaya seya koma harkokin business na ƙasashen waje wanda naji abba yana cewa seya shafe watanni baya ƙasar yanxun ma hakan ce dan kuwa bayan sun koma abuja da kwana biyu yabar ƙasar nan baya nan.
Gashi babu damar naje part ɗin su mama kishiyoyinta yanzu a laƙabamin tambarin yarkai rahoto.
Dannaji su yusra ƴaƴan alhaji ƙarami sunce momy idan tana sabga dakai bata ƙaunar ka kula su mama idan ba haka ba yanzu seta ce maka munafuki idan kuwa kana hurɗa dasu tosedai ita kudaina sabida macece ita marar yarda gata da zargin tsiya.
Ina gama wannan tunanin naji jikina yay wani irin sanyi har wani gumine ke zubomin ta ƙasana.
Ɗago kaina nazanyi naga ashema mun shigo unguwar tasu tunda na ɗan taɓa zuwa gidan sau ɗaya shiyasa bazan kasa gane hanyarba.
Kuma ita unguwarsu babu laifi akwai jama,a sosai dan harda ƴar kasuwa agefe da kuma kantina.
Cikin nutsuwa sojan ya cigaba da jammu izuwa cikin wani babban layi wanda gidaje biyar ne rak acikinsa gaskiya na manta yadda gidan baban abuja yake dan unguwarma dan inada hattarane na ganeta amman tabbas najima banzo garin ba.
Tun kafin tunanina ya katse naji ya danna horn abakin wani babban gida mai baƙin gate da sauri naga masu gati su uku sun bude ƴar ƙofar tare da fitowa.
Seda suka ƙaraso suka zube suna gaidashi sannan naga sun koma aguje tare da wangale ƙaton gate ɗin.....!!
*48 - 49*
Cikin nutsuwa motar tamu ta kutsa cikin harabar gidan wanda yake ɗauke da motoci birjik ga kuma irin manya manya dogayen bishiyu masu tsananin kyau, dai dai ta parking yayi daga gefe kafin ya kashe motar cikin lokaci kaɗan kurtun sojan ya zagayo aguje tare da buɗe side ɗin da