Chapter 6 Reading Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels Arewa Novels

Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels

Author :  Nil Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   6 / 28

15K to 18K   out of 83.3K words

wata ƴar uwarta daga ganin umma kai kasan dik wannan dambarwar bata san ana yintaba duba da yadda taci uban ado na kece raini bazaka taɓa cewa ma itace uwar batula ba sabida yadda ALLAH ya bata kyan sura gami da tsari ɗan gaske.


Da sauri Hanif ya nufi mahaifiyar tasa tare da miƙa hannunsa ya jawo nata tare da mata inkiya akan ta fito waje suyi magana( namiji kenan dik ƙanƙantarsa yafi mace hankali) cikin kulawa umma tabi yaron nata tare nufar hanyar falo.


Kafin ma su ƙarasa fitar sega amira mai bin amir ta shigo aguje! hartana bangaje jama,ar wajan cikin wani irin yanayi mai wuyar misaltawa cikin kuka! tace "Ummah kinji bala,in daya samemu umma anfasa bikin anty batula!!.


Sabida dik zance ya baza gida cewar anfasa bikin batula wasuma har suna cewa momy ALLAH sarki ashe tausayi ne yasa ta faɗi dan wasu basu san an daura da hydar ɗinba daga cikinsu kuwa harda su amiran.


Dishi-dishi umma ta soma gani kafin idonta ya sami damar rufewa ruff' bata kuma sanin inda kanta ike ba se a bakin gadonta danginta dik sun zagayeta suna mata Sannu.


Raba idanunta tasomayi ɗaya bayan ɗaya tana son gano wani abu acikin ɗakin nata, cikin sauri anty zee ta ƙaraso tana mai jan majida wadda Daga gani taci kuka! ne ta godewa ALLAH.


"Yaya Aisha sannu, yaya kike jin jikin naki?" da kallo tabi Anty zee kafin tace "Zainab hakika yau zuciya ta gaza ɗaukar wannan mummunar ƙaddarar data riskeni ashe ni Aisha zanga irin wannan rana ranar tonon asiri mai yasa wasu mutanan basuda imanine mai yasa komai za,ai baza,ai akammu ba se akan fatima wadda batan mai hakan yake nufi ba" takarasa maganar tana mai sakin wani irin kuka mai cin rai.


Saka hannun ta tai tare da share hawayenta kana tace "Zainab ina batula wani hali batula ke ciki kinemo min ɗiyata" Cikin dauriya anty zee tace "ki kwantar da hankalin ki har yanzu batula batasan abin da yake faruwa ba, tana can part ɗin baya nai mata dubara na barta da anty beby maƙociyata kuma na rufo part ɗin har zuwa a samu nutsuwa" "ina baban su yake?" cikin damuwa anty zee tace "yana can cikin gari shida sauran ƴan uwansa gidan iya amman naji ance jikin nasa da sauki kema dan ALLAH ki kwantar da hankalin ki, komaifa yazo da sauƙi tunda ALLAH ya sauya lamarin an mayar da auran akan ALIYU"


Dasauri Umma ta miƙe tare da saka wani irin kuka mai ban tausayi tare da cewa "a,a nikam zainab kice kawai an kasheni mai yasa abbansu ze amince da wannan auran bayan yasan abin da ke ƙasa, kekina tunanin har abada Hajiya Zainab zata so zuri,armu ne? nida an barmin ɗiyata ahaka har ALLAH ya kawo mata ɗauki amman wallahi nasan jaka zasu mayar min da yarinya" umma ta ƙarasa maganar tana sakin kuka!

Daƙyar anty zee take bata baki da haka har ALLAH yasa tai shuru se ajiyan zuciyar datake saki jifa-jifa hakama sauran danginta na jiki sukaita bata baki tare da misalta mata ƙaddara kala-kala wadda take riskar bawa har ALLAH yasa ta ɗan daina kukan nata amman bakin ta yagaza cewa komai.


Daga ɗakin da aka kwantar da momy kuwa da ƙyar da siɗin goshi aka samu numfashinta ya dawo kuma tana dawowa hayyacin nata ta soma koke-koke gami da tsinuwa ga dik wanda yake da hannu akan wannan aure kishiyoyinta su mama dasuka zagayeta suna bata baki akan tai hakuri haka dik ta bisu da zagin cin mutunci wai ai hadin bakine su ai da ƴaƴansu mana, ganin cin zarafin yayi yawane yasa suka tattara suka barta ita da ƴaƴanta.




A haukace momy ta diro daga kan gadon da aka kwantar da ita mayafi kawai taja tare da futa tsakar gida zagi da cin mutunci marar adadi gami da tone tonen asiri kala-kala tai tawa umma kuma ikon ALLAH babu wanda ya tanka mata a dangin umma seda ta gaji dan kanta sannan taja ƴaƴanta suka bar gidan.


Kai tsaye cikin gari suka nufa acan ɗin ma taso tai cin mutuncin amman ganin baban abuja a gidan yasa tai muƙus amman fa se faman harare harare takeyi.


Iya mahaifiyar abba ita ta dubi baban abuja tare da basa umarni akan ya kira sauran ƴan uwa saboda wannnan gagarumin lamari daya kwancewa kowa kai yazama dole ai taron gaggawa dole Zuri,ar malam uba magini ta zauna domin a san yadda za,a bullowa bakin zaren.


Cikin mintuna kaɗan dik wasu ƴan uwa na asalin zuri,ar gidan sun halarta sedai ƴaƴan abba ne basu isoba waɗan da yanzune sakon ya tarar dasu.

Shima Hydar baban abuja yay masa waya akan lallai lallai ya biyo jirgi yazo kano ayau ɗinnan sabida kiran mahaifiyar tasu na gaggawa datace bata daukewa kowa na cikin zuri,ar tata ba.

Cikin damuwa ya dauki driver sa sukai airport dan shikam baya da wani shirin zuwa kano ɗin yanzu amman yaya ya iya.


Lokacin da saƙon kiran ya tarar da Umma ba karamin kiɗima tai ba haka ta tattara ƴaƴanta a gaba domin tafiya cikin garin aka bar dangi cikin zulumi.



Tun wajan ƙarfe ɗayan rana nake baza ido domin naga wanda zezo yay min koda buɗa ce irin ta amare amman shuru banga kowa ba tun ina biyewa anty beby muna hira har nazo na ƙosa ga wayata tana dakinmu tsaki naɗan ja kaɗan nasan abdul yana can yana kirana ƙila.


Ganin ƙarfe biyun rana tayi yasa na mike tare da nufar kofa zan fita sabida yadda nakejin zuciyata tana wani irin BUGU kamar zata faso.


Amman ga mamakina kofar tana rufe abin haushi nazo na tarar da anty b tana bacci haka naja na zauna can kuma sena soma kuka wanda ban san na maye ba.


Nan da nan jikina kuma seya soma rawa cikin haka naji muryar anty zee tana magana "batula maza fito ina beby ɗin itama?" ban bata amsaba haka na mike da sauri na nufeta "anty zee ina su ummi dan ALLAH haka ake kin barni ni kadai anan bara na je wajan umma" nafaɗa ina nufar hanyar waje.


Jawo hannuna tai gami da rikeni batare data cemin komai ba ta sakani agaba mukai waje ta kofar baya ma ta fitar dani ganin motar gidan Alhaji ƙarami yasa naji wani iri araina kenan har anzo tafiya dani lallai amman an shammaceni shine ko hoto ba,a barni nayi da ƴan uwana ba.


Daman mu dik wanda za,ai wa biki a danginmu ta cikin gari ake daukar sa shiyasa ban kawo komai ba har anty zee ta sakani a gidan baya.

Abin mamaki yadda naga Umma a kusa dani a zaune fuskarta dik tai ja alamun taci kuka ta godewa ALLAH.



Gakuma ummi da amira agaba amir da hanif a gefe se anty zee data shigo nan driver yaja motar muka bar layin .


Kaina ya rigada ya kulle shiyasa banga fuskar dazan tambayi mai ake cikiba.

Ga Umma daga na haɗa ido da ita senaga ta sunkuyar da kanta ƙasa tana goge hawayenta?

Tabbas akwai Lauje Cikin Naɗi.....!!

muje zuwa.

*16 - 17*
Gabaki ɗaya kaina ya riga ya kulle da wannan lamari shin meke faruwa ne? bani da wanda ze bani amsar wannan tambayar ga su ummi naga sun sami wata irin muguwar nutsuwa kwata kwata banga wata alamar murna a tare dasuba.
Ahaka muka ƙarasa cikin gari direct motar a ƙofar gidan Iya naga tai parking cikin sauri anty zee ta fito tare da kamo hannuna cikin nata muka nufi cikin gidan Iya, tun a bakin kofar da zamu shiga cikin gidan nafara jin tashin hayaniya sama-sama baya na duba naga Umma na biye dani dik jikinta a sanyaye:.


Tun daga soron farko muka kuma jin hayaniyar kamar tana kuma ƙaruwa ne ahaka muka kutsa kammu cikin tsakar gidan abin da ya bani mamaki shine Yadda naga su Abbanmu dik a tsaye sunyi cirko-cirko kamar waɗan da aka aikowa da saƙon mutuwa.

Muryar momy ce naji ta karaɗe wajan cikin kuka take cewa "Alhaji ni kake jifa da waɗannan kalaman dannace ɗana baze AURI......."dakata Zainab naji muryar baban abuja ya buga mata tsawar data sakani na koma bayan anty zee na laɓe jin allurar sojan nasa zata Motsa.


"Wallahi tallahi kika kuma magana akan AHALIN ƊAN UWANA JININA wallahi tallahi abakin igiyar auranki" naji muryar baban abuja ta karade gidan baki ɗaya babban abunda ya sakani zaman ƴan bori a wajan shine "Wallahi zainab muddin kika yarda Auran Aliyu da Fatimah ya lalace tofa ki sani dai dai yake da lalacewar naki auran" wannan maganar ita ta sakani sakin anty zee nai zaman ƴan bori ina mai dafe *ZUCIYATA* ( My next love and romantic novel in sha ALLAH) "Wace fatiman badai niba" nafaɗa cikin zuciyata ashe ban saniba maganar ta fito fili.


Nidai bana cikin hayyacina har anty zee ta tarairayeni muka shiga cikin babban falon Iya wanda na tarar da duk ƴan uwanmu acikin sa kowa a zazzaune fuska babu alamun far,a daga gani ana cikin jimami ne.
Kallo nakebin kowa dashi lokacin da nazo zama a ƙasan carpet ɗin falon idona ne ya hangomin anty maryam matar ya hydar tana jan hancinta fuskarta tai kamar tumatur dan tsabar jaa!mamakine ya kamani ganin yadda ta zabgamin wata ƙatuwar harara haka na kau da kaina tare da kallon sauran ƴan falon dik wani ahalina ya bayyana a wajan hatta ƙannan babana mata da ƴaƴansu kowa yana wajan duk inda ka duba zuri,armu ce iya mu imu ƴaƴan iya da jikokinta idan ka cire anty zee kaɗai data kasance ƙanwar ummah.

Umma da amira da ummi dasu hanif suma dik sun shigo sun zauna umma amman ta matsa can kusada matan su kawu dasu inna haule ƙannan abbanmu ta sunkuyar da kanta a ƙasa ta gaza kallon kowa.


Nima sunkuyar da kaina kasa nai ina share hawayena😭.


Seda mukai wajan minti goma sannan su abbanmu suka shigo falon suma suka zauna daga can bangaren babu iyalai masu yawa acikinmu kamar na baban abuja sabida ƙwansu da ƙwarƙatarsu sun hallara a wurin hatta ga mazan dayake sunzo ɗaurin AURE.


Iyama tana daga can gefe ɗaya a zaune hannunta ɗauke da carbi tsohuwar arziki kenan babu ruwanta da duniya sam.

Se daga baya naga momy ta nemi waje ta zauna itama amman daga can nesa tana faman harare -harare ita ɗaya.

Addu,a baban abuja ya fara yi kafin kuma alhaji karami ya dora da nasiha mai ratsa jiki.

Bayan ya gama mukaji kuma yayi shuru kafin naga kawu ya miƙe tare da cewa baban abuja "kaga yaya Aliyun ma ya karaso amman jirgin yayi sauri awa uku yanzu yana airport bara na sa aje a daukosa" fita yay nan naji falon yayi tsit kowa yana nazarinsa cikin ransa.

Nikam wata gudawa ce ta zomin jin LAFAZIN kawu tome hakan ke nufi kodai akwai abin da ke faruwa danine dik an sakani acikin duhu wallahi!


Zaman awa guda mukai lokacin ƙarfe biyar na yamma sannan na fara jin tashin muryar kawu alamun ya dawo shigowa ciki yayi ya zauna.


Minti biyar da zuwan kawu naji wani irin sassanyan ƙamshin turare ya bayyana wanda ya samu damar cika ilahirin falon gabana nane naji yayi wani irin bugawa tare da faɗuwa lokaci guda.


Da sauri na ɗago kaina na kalli bakin ƙofar shigowa falon idona ne ya sarƙe dana Ya Hydar cikin shiga ta ɗanyen baƙin boyel mai ƙwabo ƙwabo babu hula akansa amman ba karami kyau yayiba kansa tsaye naga ya nufi wajan da momyn sa take tare da tsugunnawa ya gaida ita.


Tashi yay ya koma gaban iya sannan ya cigaba da gaida iyayensa nan ma sauran ƴan falon suka fara gaidashi kasancewarsa babba acikin zuri,armu a Maza.

Matsawa yayi ɗan nesa da anty maryam ya zauna tare da tanƙwashe ƙafafunsa waje guda ya sunkuyar da kansa ƙasa yana matsa wayarsa.

Koda wasa banga alamar ma ya ganni ba sabida nima kara nutsewa nai a gefen anty zee kamar zan shige cikinta.

Baban abuja shiya kuma bude taro da addu,a a karo na biyu sannan ya fara da yimana nasiha itama a karo na biyu sannan ya ce.

"ALIYU! dasauri naga ya hydar ya ɗago ya kalli baban abuja batare daya ce komai ba, "Aliyu ni wanene agareka?" nan ma bai ce komai illah sunkuyar da kansa ƙasa daya kumayi cikin muskilanci yagaza cewa komai.

"Idan har nine mahaifinka kuma na isa dakai to ina son kaimin halacci guda ɗaya ka nuna min kai ɗanane na hakika shine, ka amince min da auran dana ɗaura maka yau da fatima batare da saninka ba, sabida na HUCE zuciyar ɗan uwana, nasan KOBA SO kai da fatima AKWAI ƘAUNA,ta jini ka taimakeni ALIYU kai min wannan halaccin".

Baban abuja yakai maganar adake tare da cewa "wannan shine dalilin kiranka na gaggawa danai domin kasan ance TILASHIN WUYA MAƘOƘO!.


Wata irin zabura nai wadda bansan na yitaba tare da taka mutanen gabana aguje nai wajan abbanmu tare da faɗawa kansa ina cewa "abba ka farka da abdul za,a ɗauran aure bada Hydar ba Wallahi abba bana son ya hydar NA TSANESHI....!!!

*18 - 19*

"Na tsaneshi abba wallahi bazan zauna dashi ba, bana ƙaunarsa"! naƙarasa maganar ina mai cakume abbammu ina cigaba da gunjin kukan! danake ɗiff falon yayi babu wanda yayi magana hatta ga abban namu wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar wanda ruwa ya cinye nima maida kaina nayi jikin abba ina mai cigaba da kukan danake kan jiki kan ƙarfi.
Seda akai kusan minti goma sannan baban abuja yayi gyaran murya tare da cewa "haba fatima ya ina son toshe wannan ƙullin kekuma kike son bullo mana da wani ballin kiyi hakuri ki zauna da ɗan uwanki nasan ALLAH ze dai dai taku.

Ban sami zarafin cewa komai ba illah sake rungume abbanmu danayi ina cigaba da kuka!marar dalili wannan wani irin lamarine mai rikitarwa yake kusantoni ni batula? shin ina abdul waima shin a wani matsayi aurena da abdul yake yaya akai aka fasa aurena da abdul waɗannan tarin tambayoyin sune suka taru sukaima zuciyata ƙawanya wadda nagaza kasa boyesu a gaban kowa.

Da sauri na saki abbanmu tare da jan ƙafata kamar wata gurguwa na nufi gaban baban abuja ƙafarsa na kama guda cikin tsananin tausayin kaina na fara magana wadda nasan mafi yawancin ƴan falon sesunmi hawaye sabida yadda na ɗauki salon tausayin kaina a yayin faɗin maganar.

"Baba dan ALLAH dan Annabi S.A.W katai maka min baba ka mayar da aurena kan abdul wallahi baba ya hydar baya sona nima bana sonshi dan ALLAH baba kada kuyi mana auren dole ba......" Ban kai ƙarshen maganar tawaba naji saukar muryar momy kamar wadda aka angazo tafara cewa "yoke mema babana ze dake kije ki fara bincikar iyayenki shin ke wacece kafin ki fara ƙin ɗan ......"!! Dakata Zainab! baban abuja ya daka mata wata razananniyar tsawa data sakani mikewa aguje nai kan umma ina sakin wani irin marayan kuka!
Duk da haka momy batai shuru ba "haba alhaji kamar waccan shegiyar ƴar agaban kowa ta dinga furta kalmar ƙi ga ɗanka sannan ka barta dan tsabar Aisha ta jiƙaku ta shanye to.wallahi nima bazan yarda ba sedai dik abin da za,ai ayi amman wallahi kowa yasan ALIYU yafi ƙarfin wannan matsiyaciyar yarinyar mai kalar alala" babu abin da baban abuja yake se salati sabida wannan cin ZARAFI na momy yay yawa kowa kallonta yake yadda ta zage se lafta masifa take kamar ta ari baki.
"Kuma kije ki binciki waɗannan tsofaffin iyayen naki mai ya hana a ɗaura maki aure da wancan yaron har aka ƙaƙabawa ɗana kafin kizo kina mana wannan haukan" momy ta ƙara jefamin wannan maganar cikin fusata.
Zata kuma wata maganar ce baban abuja ya daka mata tsawa "wallahi zainab idan kika ƙara magana kowa ya shaida ni muhd na sakeki wallahi! kika kuma magana abakin dukkan igiyoyinki.
Babu shiri ta mike tsaye tare da janyo hannun anty hafsat ƴarta mai aure ta biyu tana kokarin yiwa sauran magana baban abuja yace "ai da kika tashi zuwa gidana ke ɗaya kika zo bada ƴaƴana ba wallahi kika kuskura kika bari ɗa ɗaya ya tashi daga nan wallahi abakin auranki nagaya maki" yakai maganar cikin fushi.




Zama tayi tana harare harare cikin sauri umma ta miƙe tare dajan hannuna muka bar falon umma tana tsananin kukan dana rasa na menene anty zee ce ta biyomu itama nan danan su amira suka mike suma suka rufo mana baya batare da ɓata lokaci ba muka nufi mota se gida kuma babu wanda ya gaza cewa kowa komai.

Babu abin da kakeji acikin motar da zamu koma gida se kukana dana umma dana amira dan ita ummi naga ɓacin rai ya hanata tace komai anty zee ce ke bamu baki amman itama kukan take a ƙasan ranta.


Su Batula na fita daga falon shima abbansu ya miƙe yana haɗa hanya ze futa da sauri kawu ya riƙo shi tare da mayar dashi cikin falon ya zaunar yana gaya masa magana mai kwantar da zuciya da haka har ya samu hankalin abba yaɗan dawo jikinsa.


tsananin tashin hankali iya mahaifiyar su abba tajishi wanda harya hanata cewa ƙala a yayin da momy ke tujararta.


Cikin fushi baban abuja ya dubi momy tare da cewa "Zainab kin kyauta da duk haukan da kikai agaban surukarki da ƴaƴanki da kishiyoyinki amman kika zauna kike cacar baki akan abinda yake ba haram bane wallahi tur da halinki,amman fa ki sani wallahi!tallahi! auran Ali da fatima kamar rai yake da aljali kokin ƙi ko kinso wallahi seya zauna da ita indai ɗana ne na cikina" baban abuja yakai maganar cikin tsananin fushi.

Dasauri ta miƙe tsaye batare data ce komai ba gudun saki😜taja hannun anty maryam wadda take ta kuka suka bar falon kamar wasu masu iskoki, "anji kunya dai" cewar baba haule ƙanwar abba cikin haushi ta faɗi maganar tare da nufar wajan iya mahaifiyarta tana bata haƙuri.

Haka dik ƴan falon sukai cirko cirko kowa kagani dai abin bai masa

6 / 28