Author : Nil Category : Romantic Hausa Novels
tun asali rubutaccene daga ubangijinsa sedai mu mutane mukan manta da hakan a wasu lokuta da'dama, kokuma muyi watsi da abunda yake na dai dai muɗauki wanda bana dai dai ba daga ƙarshe idan wani mummunan lamari ya faru semu dangana shi da ƙaddara, wanda har yanzu ni ina mamakin mutanan da basa bam-bance ƙaddara da ganganci mafi akasarin mutane yanzu suna yin abune daka amman da zarar wani abu marar kyau ya afku sekiji ana cewa ai ƙaddarace.
Tabbas komai ya faru da bawa rubutaccene daga indallahi amman kuma muma bayin semu rage ganganci sannan kuma mutsaya akan turbar gaskiya muyi abinda ALLAH yace da manzon sa sannan mu gujewa abinda ALLAH ya hanamu,semuga komai yana tafiya cikin tsari ALLAH yasa mudace duniya da lahirarmu sannan ku kuma wannan labarin na mahaifiyarku yana da kyau kuyi koyi da darasin cikinsa koda ba,a kankuba wannan ma wata ishara ce daga ALLAH.
Sannan kuma ke batula! ta juyo kaina tare da cewa "yanzu ke kin shiga sahun manya bayan haka kuma yakamata ki nutsu ki saita rayuwarki, da kina gaban mahaifanki ne baki san komai na rayuwaba da abinda ke cikinta amman yanzu ALLAH yasa da aure akanki kuma gidan daza,a kaiki babban gidane, gidane daya tara mutane ƴaƴa da jikoki gakuma kishiya sannan kuma ga uwar miji tabbas gamai hankali wannan ma kamar wani gwajine da ubangiji ze miki akan gyara rayuwarki, abin da nakeso dake.kizama mai hakuri kizama mai tsafta kizama mai juriya duk abinda za,ai miki agidannan dan ALLAH ki kauda kanki kada ki tanka domin acan ɗin kamar bare ce ke a wurinsu kada ki nufi kowa da sharri domin mu ƴan alkairine kuma insha ALLAH zamuga alkairi kowa yace sharri ya koma masa kansa daga ƙarshe ina maki fatan alkairi ALLAH kuma ya baku zaman lafiya amin".
Cikin kuka! umma ta tace "Amin zainab wallahi ni abinda yafi komai ɗagamin hankali kenan' Batula! da kika ganta ƴace marar kazar kazar burinta a kullum taci ta kwanta ga sakarci ga rashin kunya uwa uba son jiki to tsakani ga ALLAH da haka zataje gidan kishiya? ga kuma ƙiyayyar uwar miji? uwa uba kuma gashi shi kansa Alin bawani damuwa yay da lamarinta ba.wannan fa kamar wata gasa ce zata shigeta domin kuwa se ta gyara sannan har hankalin Alin ze dawo kanta..nifa zainab a wannan lamarin addu,ar kawai danake ALLAH ya dawo da hankalinsa kanta idan har shi muka samu yana kula da lamuran ta tofa wannan duk abun mai sauƙine domin nasan baze bari a taka taba.sedai kuma wani hanzari ba gudu ba wallahi dole ki sauya duk wannan sakarcin naki sekin daina daman faɗan danake miki kenan Akullum kina ganin kamar bana sonki ga darasin nan kin gani tun kafin ai nisa abin takaici yau ko tuwo baki iya tukawa ba to da wannan halin zaki gidan kishiya?"
"Allah ze gyara ta insha ALLAH kedai yaya aisha addu,a zaki mata kawai, kinga inda da lokacima da an siyo mata litattafan girki da wasu abubuwan amman ba matsala idan zamuje daga baya se mutafi mata dashi"cewar anty zee kenan tare da kallon umma tana son jin mi zata ce kuma.
"Hakane kam zainab ALLAH ya shirya mana alkairi ALLAH kuma yasa wannan abun ya zama alkairi garemu baki ɗaya" cewar umma kenan tana ƙara goge hawayen dake xubo mata.
Shuru falon namu ya kuma ɗauka babu abin da ke tashi se sautin ajiyar zuciyata wadda nakeyin ta da sauri da sauri ban iya cewa komai ba illa tashi danai aguje nai cikin ɗakin umma, kwanciya nayi akan gadonta ina mai dafe saitin zuciyata jin yadda take kokarin fasowa ta fito dan tsabar rudanin data shiga.
Wai ni yau batula rayuwa taiwa haka tabbas wannama wata makaranta ta musamman ALLAH ya sakani fata dai ubangiji ya sa nashiga a sa,a abinda yake kuma bani tsoro da wannan lamarin shine yadda zan shiga gidan baban abuja amatsayin matar hydar tabbas akwai gagarumin lamari agaba mai firgitarwa.
Yaya Ali baya sona nima bana sonshi momy bata sona nima bana sonta! anty maryam taimin wallahi bazan bartaba wadda nasan zan ragawa ɗaya agidan momy itama dan taci darajar auran yayan mahaifina datakene amman bawai darajar auran ɗanta danake ba.
Dan Wallahi koshi Hydar yay min babu sauki dan gwara naje na girgiɗe auran na dawo gidanmu na zauna oh! ni batula sauran kaɗan ashe a haifoni a shegiya ALLAH ya rufan asiri.lumshe idona nayi tare da cewa "ALLAH ka yafewa iyayena" afili na furta hakan tare da ƙara rufe idona ruf se barci ya kwasheni mai cike da tarin gajiya da tunani kala-kala.
A falo kam suma su amira da ummi duk jikinsu yayi sanyi da jin labarin mahaifiyar tasu amman dayake da ƙarancin shekaru ajikinsu basu kai batula hankaliba shiyasa anty zee tana sako wata hirar suka watsar da maganar suka koma kanta. kuma basu suka mike ba secan wani lokaci sannan anty zee ta haɗa kayanta suka rakata tai gida suna dawowa suka saka umma agaba da murnar sufa wannan haɗi na ya hydar da batula.yay musu daɗi wai yanzu zasu dinga zuwa abuja babu takura.
Murmushi umma tayi gami da tashi tabar wajan tare da ce musu suje kicin su haɗawa abba abinci dan yace mata gashinan yana hanya.itama tashi tayi tare da nufar ɗakinta ganin batula kwance tana sharar baccinta yasa umma sakin baki tare da cewa "lallai mai hali baya fasa halinsa ALLAH ya kawo miki mafuta" tare da shigewa toilet abinta.
***************************
Momy tana gama waya da hydar bayan ta saka driver yakai maryam hotel ɗin da hydar ya kama, shigowa cikin falon hajiya turai ƙawarta tayi tare da zama akan ɗaya daga cikin kujerun falon tare da kallon hajiya turai aminiyarta sannan tace "wallahi hajiya jinake yau kamar nai hauka tuburan wannan wani irin tashin hankaline, kinsan ALLAH turai bana ƙaunar zuriyar Aisha wallahi! bantaba jin tsanar wani bawa kamar Aisha ba tun asali yarinyar batai min ba yanzu kuma kiji wata ƙaddarar Alhaji ya dauki ɗana wanda yafi soyuwa araina ya aurawa ƴarta kinsan ALLAH kozanyi yawo tsirara sena ɓata auran nan wallahi ni zainab bazan haɗa iri da ragowar zina ba wadda babu tartibin ƴar sunna ce ko ƴar soyayya" taƙarasa maganar tana jan numfashi tare da miƙa hannunta gefen kujerar ta ɗauki ruwa a roba ta hau sha.
Seda hajiya turai ta bari ta shanye ruwan tass sannan ta dubeta tare da cewa "Ke yanzu zainab naga har yanzu bakisan kankiba keko kinata lahirarki mai ya kaiki ɓata sunnar ma'aiki s.a.w baki san aure yana daga cikin manyan sunnonin ma'aiki s.a.w ba wallahi.dik wanda yaja da lamarin aure ƙarshan sa a ƙasa dan kuwa haɗuwar bazatayi kyauba.
Nidai ina mai baki shawara da ki zauna ki nutsu kikuma zubar da makaman yaƙinki tunda kikaga andaura wannan aure toki barwa ALLAH ikonsa kar ayi babu ke".
Tsaki momy taja tare da cewa "nifa daman tsiyata dake kenan wannan wa'azin haba turai anfa yimin yankan ƙauna kiduba fa duk ƴaƴan Alhaji yarasa da wa ze haɗa se Aliyu! wanda yasan shine garkuwata agidan amman shine ya daukesa ya haɗasu shin dawama nake taƙamane idan ba dashi ɗinba kina kallon yanzu gidan namu ba kamar daba wallahi ɗannan shiyake mana komai hatta ga ƙannan sa na ɗaki karatun su da komai hatta ƴan sauran ɗakin sannan kuma ze wani zo ya haɗashi da wannan masifar salon yanzu suma ya dinga musu"
Dariya hajiya turai tai tare da cewa "dadina dake zainab wauta to maye dan Aliyu yaywa danginsa abu? shin wannan matar tasa ba bare bace? maye baya musu ita da iyayenta mai ya shafeki ai dadin arzikin kenan ALLAH ya baka wani yaci, dan ALLAH ki saki wannan makaman naki ki rungumi surukanki dukkanmu bamu san mai ALLAH ya boye ba babu mamaki ma da rabon ƴaƴa masu yawa a tsakaninsu".
Da sauri momy tai wata irin dirowa tare da saurin kallon hajiya turai sannan tace " ALLAH ya kiyaye ai wallahi ko kusantar ta baxan bari yayi ba bare wani zancen ciki ya shiga dan ALLAH kada ki ƙaramin wannan fatan tsiyar.
"Zainab kada ki zama marar ilimi mana idan ALLAH yayi kefa baki isaba' ina gaya miki izzar ALLAH da girman sa da buwayarsa ga bayinsa ne wallahi idan ALLAH yacewa bawa ji! ƙaryar wani yace a,a kuma idan ALLAH yacewa bawa gashi ƙaryar wani bawa ya ƙwace shiyasa kumfa yakun ɗin ubangiji da bawansa take da matuƙar tasiri sabida haka ki kiyayi kanki kada ki zama baiwa mai butulci da hassada ga abinda ALLAH ya tsarawa bawansa ina gaya miki hakan ki kuma lura da hakan kodan gudun faɗuwar baƙar tasa a gaba.
"Naji turai kuma na san da haka amman a gaskiya bana fatan ma Aliyu ya kusanci wannan yarinyar barema wata alaqa ta haɗasu ta aure sabida nafi kowa sanin halin ɗana wallahi muddin Aliyu yaywa wannan ƴar ciki tofa ni tawa ta ƙare sabida yadda yake da masifar son ƴaƴa tofa wannan cikin shi ze saka komai ya dai daita dan ALLAH turai daina gayamin wannan bakar ranar bana fatan tazomin" tafaɗa cikin sauri tare da tashi tabar falon ta nufi ɗakin hajiya turai.
Da kallo hajiya turai tabi momy tana mai mata fatan ALLAH ya ganar da ita hanyar dai dai.
**********************
Tun a hanya maryam take faman zuba kuka hankalin ta idan yay miliyan tofa ya tashi da wannan auran na mijinta burinta kawai taje ta keɓe dashi domin ya farkar da ita daga mummunan mafarkin data keyi wayarta ma mamy mahaifiyarta tana ta uban kiranta amman sam bata da damar dagawa domin kota dauka ma batada hankalin dazata iya mata wata magana.
Drivern yana parkin a bakin babban hotel ɗin chilla dake a nasarawa gra da sauri ta bude motar aguje ko takan drivern bata bi ba tai cikin hotel ɗin tana matsa wayarta domin nemansa ya gaya mata a wani room yake......!
MANAGE PLS.
*24 - 25*
Dasauri take nufar bakin gate ɗin babban hotel ɗin chilla dake cikin nasarawa g.r.a da ƙyar ta tsaya securtyn wajan suka bata tiket dan hartana yada poss ɗin ta,seda wani ya biyota ya bata tana ansa ta kuma jan kafafunta waɗan da duk sukai mata tsami saboda yadda cikin jikinta ya zama matashi.Wayarta take dannawa cikin sauri tana dialing number sa wadda tai mata seving da MY ONE da manyan harufan turanci, hartai ringing ta gama ba,a ɗauka ba still ƙara dialing tayi a karo na biyu tana mai dafe Zuciyanta kamar zata shiɗe nan ma ba,a ɗauka ba.Cikin sauri ta ƙarasa babban reciption ɗin wajan ta zauna a waiting chair tare da rafka tagumi duk hawaye sun jiƙa mata mayafinta haka taketa faman zabga masa kira amman ba,a ɗaukaba.
Secan wajan minti 30 sannan sega kiransa kuma. wata gwagwruwar ajiyar zuciya ta saki tare da picking cikin azama"hellow beby wai kana wani room ne tun ɗazu naketa kiranka amman baka ɗaukaba why?" ALIYU wanda fitowarsa daga wanka kenan yaga kiran matar tasa murmushi yaɗan saki kaɗan gami da shafa kwantaccen gashin dake lulluɓe akan kirjinsa sannan yace "afuwan madam daga wanka na fito yanxu, lafiya dai?" tura baki tayi gaba kamar wata beby sannan tace "hm watakan kai har kana da interrest ɗin shiga wanka kenan ni kabarni cikin tashin hankali shin kenan baka bakin ciki da wannan ƙaddararran AURAN ko?" murmushi ya kuma saki yana mai lumshe manyan idanunsa as usal tare da cewa "Cold mana my wife ban sanki da fushi ba"daga bangaren ta sake tura baki batai "kana wani room yanxun haka dan baxan iya bacci yau wallahi"mamakinta ne ya kamasa amman seya danne gami da cewa "Romm 003" yana gama faɗin haka ya yanke kiran.
Da zafin nama ta miƙe tana cije bakinta ta nufi upstair na hotel ɗin da ƙyar take taka ƙafarta har ta samu ta hau saman amman fa tasha ƴar wahalar hawan kaɗan.
Maryam bakaramin yawo tayi asaman ba kafin ALLAH yasa tasami wanda ya nuna mata ɗakin seda tai nocking sau uku sannan yazo ya buɗe mata.Jikinsa ɗauke yake da blue ɗin babban towel wanda ya ɗauro a iya ƙugunsa babu komai ajikin nasa se wannan towel ɗin wanda ya baiwa kwantacciyar sahihiyar baƙar sumar dake manne a fatar jikinsa damar bayyana musamman wajan tsakiyar kirjin nasa da kuma gefe da gefen nipples ɗinsa anan gashin yafi yawa kai masha ALLAH agaskiya ALIYU baƙaramin haɗaɗɗan namiji bane wanda tafarar ɗaya ze iya tafiya da zuciyar mace komai izzarta.
Cikin sauri maryam ta faɗa saman kirjinsa tana mai sakin wani irin firgitaccen kuka! mai tsuma zuciyar wanda ake yiwa shi.
"Wallahi beby wannan mafarkin danake mai tsayine pls dan ALLAH ka farkar dani wayyoni maryam"!! takai maganar tana sake kwanciya akan faffaɗan kirjinsa wanda ya jiƙu da ɗan danshi-dashin lemar ruwan wankan daya fito.
Babu abin da ALIYU keyi illah shafa mata gadon bayanta cikin wani irin birkitaccen salon daya saba mata dashi wanda da shi ya siye zuciyarta har take jin duk duniya babu wata macen dazata raɓesa idan ba ita ka ɗai ba domin ji take dan ita akai ALIYU kuma shima danshi aka yita su biyu zasuyi rayuwarsu daga su se ƴaƴansu bata tunanin zata ragawa kota bar dukkan wata ƴa mace a doron ƙasa mai shirin raɓarsa daga ciki kuwa harda mahaifiyarsa.
Babu wani abun da ke tashi acikin room ɗin illah sautin kukan! maryam wanda shi yake jinsa kamar saukar dalma acikin ƙahon zuciyarsa sabida yadda yake jin matar tasa acikin ransa bare kuma ga babbar kyautar da ilahu ya bashi kwance a ƙasan mararta wannan abubuwan shiyake sake dulmiyashi acikin tafkin kogin son matar tashi.
"Shiii!! my dear bana son wannan tashin hankalin naki" yafaɗa mata cikin raɗa dawata irin murya mai cike da salo kala-kala wanda zeyi saurin tsunduma mai sauraran hakan cikin tafkin son abinda yake tare dashi.
Janyota ya kumayi kirjinsa tare da saka ƙafarsa ya ƙara tura ƙofar sannan ya saƙalata a kafaɗarsa har zuwa cikin room ɗin, inda babban gado yake malale da farin bedshit se ƙaton mirrow da t.v tare da ɗan wani tebur wanda aka aje yar wata silver ƙarama akansa.
Abakin gadon ya sauketa bayan ya cire mata mayafin jikinta, saka hannunsa yayi guda ɗaya ya share mata hawayenta. sannan ya sunkunya ya cire mata takalmanta still hannunsa nakan ƙafarta yana ɗan yi mata tausa kaɗan kaɗan ganin yadda ƙafar tata ta tasa kaɗan.
Yakai at list mintuna biyar yana faman mata abu guda sannan ya ɗago kansa yana mai tsareta da narkakkun lulu eye's nasa farare ƙar waɗanda dan tsananin farinsu har wani ruwa-ruwane ya kwanta acikinsu, yaune kaɗai Hydar ya tsaya sosai yana mai tsare matar tasa da kallo tunda daman shi mostly kallonsa na ƙasan idone amman yau sosai yake kallonta yana kuma noticing ɗin yadda matar tasa ta shiga tsananin tashin hankalin kishinasa mai tarin yawa.
"Kiyi shuru madam kinga abinda ke cikin kima kukan yake" yafaɗa tare da kai tattausan hannunsa kan skirt ɗin jikinta yana shafa saman cikinta dashi.
Ture hannunsa tayi "ni dan ALLAH ka rabu dani yaya za,ai nazo maka da damuwata amman ka ringa yawo da hankalina" mamakine ya kamasa jin yadda take son raina masa hankali amman tunawa dayay tana ɗauke da ajiyarsa a cikinta yasa yaɗan taune leɓensa kaɗan tare da mayar da fushinsa sannan yace "to shikenan idan na dawo miki da hankalin naki semuyi maganar" yafaɗa cikin miskilancinsa tare da mikewa ya nufi gaban mirrow seda ya gama shirinsa tsaff tana zaune sannan yazo gabanta ya saka hannu ya dauki wayoyinsa tare da nufar kofa ze bar mata ɗakin.
Sanin hali yafi sanin kama! tasan halinsa sarai baya daukar rainin mace bare iskancinta yanxuma tasan darajar cikin jikinta taci amman bada ban haka ba da tuni ya goge raininta domin tasan duk son dayake mata baya daukar rainin wayo shi sam arayuwarsa shiyasa duk ƴan gidansu suke shakkarsa hatta ga ita momyn ba komai take masa ba sanin waye ALIYU muskili mai taurin kan tsiya da kafiya da saurin fushi kuma baya daukar raini ko dai dai dana minti ɗaya.
Cije leɓenta tayi tare da miƙewa tsaye tasha gabansa "beby baka cemin komai ba wai shin kai zaka karɓi wannan rabi da rabin a matsayin mata?" tafaɗa masa cikin sigar rainin wayo. yatsina fuska yayi batare daya sakar mata fuska ko sau ɗaya ba sannan yace "menene rabi da rabi?" yafaɗa yana mai lumshe idanunsa tare da saka hannunsa guda a saman kirjinsa ya dafa yana son jin daga gareta.
"Ita batulan mana dan naji ance ba,asan tartibin tushen haihuwarta ba ko shegiyace......ko...." stop!! Maryam yafaɗa cikin wani irin fushi mai razanarwa. dasauri taja gefe ganin yadda idanunsa suka sauya kama zuwa jajur.
"This is the last worning da zanyi miki akan AHALINA kada ki kuma jifanta da wannan mummunar kalmar domin idan kikai mata tamkar ni kikaiwa ne.ki tuna da mahaifinta da nawa cikinsu guda ke ba namiji bace bazan iya nuna miki true fushina ba amman dayau sekinyi danasanin faɗin wannan maganar" yana gama faɗin haka ya nufi kofa cikin fushi.yakama ze