Chapter 9 Reading Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels Arewa Novels

Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels

Author :  Nil Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   9 / 28

24K to 27K   out of 83.3K words

futa ya kuma jin muryarta cikin kuka!
"Namiji kenan kana nufin kana sonta ka kuma karɓi auranta?"
Murmushin gefen baki ya saki tare da ayyana yadda zeci uwar batula agidansa sannan ya juyo tare da ce mata.
" *ƘAUNARTA* nake kinsan *KOBA SO* akwai sahihiyar *ƘAUNA* ta jini da ƴan uwantaka wadda tabi jini da ɓargo ta maƙale wadda babu mai iya yiwa wani se jini da jini waɗan da iya jinika ne kawai ze iya maka ita". yana kai maganar yayi saurin rintse manyan idanunsa yana sake danne abunda ke neman fasa masa zuciya tsantsar bakin cikin batula ne aransa sosai yakejin hakan amman gudun kada ya bada ita agaban matarsa wanda hakan har yajawo mata matsala yasa ya faɗawa maryam ɗin hakan amman bawai yafaɗa ne har cikin ransaba daman namiji idan yanason zaman lafiya to kada ka nuna wa matanka ɗaya tafi ɗaya kawai kabar hakan acikin ranka a iya kallonka ga itama mai hankali ze fahimta.
Tsintar muryarta yay tana cewa "amman kam anyi girman ƙwabo agaban kowa fa ta nuna bata ƙaunarka amman kai kazo nan kana wasa ta" dariya ya saki kaɗan ta mugunta tare da ce mata.
"Ita tata salon ƙaunar ce a haka nuna ƙi gaban wanda kakeso ki gane hakan" yana gama faɗa mata hakan ya bude kofar tare da cewa....
"idan kin gama haukan naki kya rufomun kofata ki tafi wajan momy batare dake nazoba wallahi bazan koma dakeba"
Dasauri yaja kofar yabar dakin yana saurin nufar ƙasa soyake yaje gidan abba can yaji kiran dayake masa shiyasa duk hankalin sa yayi gaba ga wannan banzar kuma taxo xata raina masa wayo wallahi yau bada ban cikin dake jikinta ba dase ya koya mata hankali da wannan tunanin ya futa daga hotel ɗin mai napep yatara tare da shiga ciki ya nufi gidansu batula......!!

*26 - 27*

Dawani irin firgici mai tsananin gaske maryam ta juya cikin ɗakin,ragwaf ta faɗa kan gado tana mai dafe saitin zuciyarta tare da sakin wani irin ɗan banzan kuka! mai taɓa zuciya sosai take kukan tana kuma sake mamakin abinda Hydar yay mata wanda ko a marfaki bata taɓa kawowa Zemata hakan ba.
Kai itafa har yanzu gani take abun kamar abun a mafarki yake yau ita maryam akaiwa kishiya duka-duka auran nasu yaushe ma aka yisa bare ace har an ɗauko mata wata da sunan abokiyar zama, wata irin tsanar mahaifin mijin nata taji atake wadda take ganin kamar dan ya ƙuntata mata ne yasaka yay hakan sosai take gursheƙen kuka a cikin dakin ahaka wayarta ta kuma yin wani ringing! ɗin a karo na barkatai da sauri ta jawo wayar cikin tashin hankali take danna wajan ɗauka tare da karawa a kunnenta.
"Hellow mamy na kimin boking jirgi wallahi gida zan taho.ina cikin tashin hankali mamy na waini yau Hydar ya gayawa magana akan wannan shegiyar yarinyar wallahi mamy bana zaman gidansa.
Seda mamy taɗan nisa daga nata bangaren sannan tace "to maye na wannan kukan! haka kefa dadina dake hauka kinsan idan kika sake kika dawomin gida a yanxu dadynki ze ɓata mana raine dagani harke, sannan kuma abinda nakeso dake shine ki kwantar min da hankalinki duk abinda yake faruwa hajiya zainab ta bugo ta gayamin wannan dalilin nema yasa naketa zabga miki waya tun ɗazu amman baki ɗaukaba.
Daman ke idan kina cikin tashin hankali sam bakya control mind ɗinki to a kull ɗinki kada ki sake kice zakizomin gidana a wannan lokacin ban lamunta ba, ke wacece da baza,ai miki kishiyaba? shin waike wace irin shu'umar yarinyace ne daman idan mijinka yana neman aure koyayi aure so ake ka ɗaga masa hankali? Wallahi wannan haukan da wasu matan suke shine yake ƙara harzuƙa wasu mazan akan ƙarin auren da sukai ko suke nema.
Ace tsakani ga ALLAH wai dan kina mace dan mijinki yana neman aure ko yay miki kishiya seki ɗagawa kanki hankali kiƙi nutsuwa bakisan a wannan lokacin shikuma mijin yake sake jin shauƙin yin auren ba.
To bara kiji ni mahaifiyarki ce iya gaskiyata zan gaya miki idan kin ɗauka kanki idan baki ɗaukaba keki ka jiyo nina san ko a ƙiyama ALLAH baze kamani ba.Idan zaki riƙe mijinki da kishiyar ki ku zauna lafiya to idan kuma baxaki riƙeshiba babu abin da ya shafi aminatu.
ALLAH yayi miki luɗufi yabaki miji ɗangaske miji nagari mai sonki ɗan mutunci wallahi kikai wasa ya kufce miki kekika jiyo babu ruwana ni anan shawara ta rage gamai shiga rijiya idan zaman gidan kikeso gaki gashi nan kina kallon mahaifinki tunda ya faɗi a zaɓen nan lafiyarsa tai ƙaranci kinfison kixo ki zauna mu haɗa kai a ɗaki kishiyoyi na mana dariya daman suna bakin cikin auran dakikai to idan haka kikeso bisimillah ALLAH ya baki sa,a bada aminatuba".
"Ai daman nina san haka zakice wallahi mamy idan kina min wasu abubuwan senaga kamar bakya ƙaunata yanzu ace aiwa yarki kishiya amman ki gaza ɗaukar wani mataki se wannan maganar to wallahi zanbi yadda kikace na zauna amman wallahi sena jagulawa wannan yarinyar rayuwarta sena hanata zaman lafiya dan tayi ƙarya in haɗa miji da ita" takai maganar tana jan numfashin ta.
Salati mamy taja cikin sauri cike da tsananin mamaki tace "amman maryam wannan ba halina kika ɗauka ba tabbas sedai daga wani wajan kika dauki wannan ɗabi,ar kina kallo acikin gidannan sedai ni su cuceni nai hakuri amman yau ke ki kecewa zaki ɗagawa ƴar mutane hankali tokiyi a hankali dan kada reshe ya juye da mujiya garin kallon ruwa gwaɗo yay maki ƙafa, sannan ki dinga tuna abu ɗaya tak!! har yanzu a matsayin MATAR HAƊI kike a wajan Aliyu ba MATAR SO ba agabanki mahaifiyarsa tazo gidanmu ta rokeni akan idan ina da ɗiya na bawa ɗanta ya aura sabida ita tun a aikin hajji data haɗu dani taji tana son haɗa zuri,a dani sabida kyawawan halina tana tunanin idan ɗanta ya auri ɗaya daga cikin ƴaƴana zata samu xuri,a ta gari kuma cikin ikon ALLAH data turoshi ya ganki yaji yana sonki har ALLAH ya kaiku ga aure to ina son jan kunnenki da kada kiyi watsi da damarki a wajan ɗa mai alkunya mai tarbiya mai daraja surukansa ki taka a hankali nidai iya shawarata a gareki kenan nabarki lafiya".
Mamy tana dire wannan maganar ta katse wayarta. Barin maryam tayi da sakin baki wadda ko kaɗan kalaman mahaifiyar tata bai ratsata ba,bare taji wani ɗar aranta illa ma wani mugun nufin data ƙara ɗasawa acikin ranta. Cikin wani irin yanayi mai cike da saƙe-saƙe kala kala a ranta ta miƙe tare da nufar kofar futa cikin fushi dole ta nuna masa ita macece wallahi seta ɗauki mataki akan batula dan baxata zauna da wannan mai baƙar fuskar a matsayin matar tsadaddan mijinta ba sam hakan baxe yuwuba.
Tana futa ALLAH ya taimaketa ta samu mai napep seda tai da gaske sannan ta gane gidan aminyar momy sauka tai sannan ta dauko naira dubu ta bawa mai napep ko sauraran canjinta batai ba haka tai cikin gidan cikin sauri a falo ta tarar da hajiya turai suna lissafi itada da ƴarta sannu kawai taiwa hajiya tare da shigewa ɗakin dataga momy ta aje musu kayansu jiya.
Dagudu ta ƙarasa Cikin dakin tare da faɗawa kan momy tana kuka! cikin tashin hankali momy ta ɗagata tare da cewa "lafiyarki meke damunki?" ta jero mata tambayar a jere "wani abun wannan yaron yay miki?"
"Momy Aliyu ya cimun mutunci yau" Sosai ta zauna tana gayawa momy ƙarya da gaskiya wanda yayi tsananin tasiri acikin zuciyar momy Cikin fushi ta jawo wayarta tare da danna masa kira sanin halinsa na bakar zuciya yasa taɗan sassauta fushinta sabida idan har ta nuna masa maryam ce ta kawo ƙararsa tofa kashin maryam ɗin ya bushe shiyasa ta sassauta fushin nata.

Seda tai kusan minti biyar tana kiran sannan ya ɗaga daga jin muryarsa kasan akan titi yake "Assalamu alaiki hajiya ya akai?" "Kana ina baba?" saninsa mutum marar ƙarya ko boye boyen magana yasa yace mata "gani a gadon ƙaya lafiya?" zaro ido tayi waje tare da cewa "mekaje yi acan ɗin?" adake yace mata "naje wajan abba yana son ganina gani acikin napep"muskutawa tayi kaɗan sannan tace "to kabar zuwa can kazo nan court road gidan hajiya turai ina son ganinka".

Lumshe idanunsa yayi tare da kallon agogon axurfar dake daure a tsintsiyar hannunsa sannan yace mata "Afuwan hajiyata insha ALLAH da zarar na gama da nan ɗin zan samu nashigo komin dare,Wallahi na riga nama kai kawai shiga cikin layin nashi zanyi".

Zare wayar tayi daga kunnen ta tare da kallon sunan tabbas Aliyun tane wannan ɗan nata maijin maganarta marar son ganin ɓacin ranta marar son saɓa maganarta wanda baya ƙetare dukkan wani sharaɗinta amman yau shike bata hakuri akan zeje gidan maƙiyanta.

Shikam daga nashi bangaren yanata "hellow!! hellow!!" jin shuru yasa ya katse wayar tare da mayar da ita aljihun sa.

Itama da sauri ta mayar da wayar kunnenta jin shuru yasa ta ƙara mayar da idanunta kan screen ɗin wayar sedai kash ya katse da sauri ta zabura "nashiga uku ni zainab mai yake shirin faruwa dani"........!!!

*28 - 29*

Cikin minti tuna kaɗan Aliyu ya sauka daga cikin keke napep ɗin daya kaisa gidan abba gudar dubu ɗaya fara ƙall ya zaro ya miƙawa mai napep ɗin tare da juyawa cikin zafin nama ya nufi hanyar ƙofar gidan abba.
"Ranka ya dade ga canjinka".
Cewar mai napep ɗin daya biyo hydar har ƙofar gidan abba wanda yake kokarin tura ƙofar gidan ya shiga, cakk ya tsaya tare da juyowa ya kalli mai napep ɗin tare da ce masa.
"Nabaka duka ne ay"
Faɗaɗa far,arsa yayi tare da cewa.
"Kai amman nagode sosai yadda ka taimakamin kaima ubangiji ya taimaka maka ya duba ka ya duba lamarin ka amin.Nagode sosai".
Wata irin kunya ce ta kama Aliyu gami da mamakin wannan lamari, ace daga kyautar naira dubu amman yake masa wannan godiya haka shi se abun ma ya basa mamaki.shafa aljihunsa yayi tare da zaro wasu kuɗin waɗanda a ƙalla zasuyi 10k ya kuma miƙawa mai napep ɗin tare da cewa.
"Dan ALLAH kada ka kuma min godiya kaji abokina".
Cikin sauri mai napep ɗin ya zaro idanunsa tare da mamakin alkairin wannan mutumin dake gabansa.
"ALLAH ya baka zuri,a ɗayyiba mai albarka ALLAH ya kareka daga dukkan abunƙi amin".
Lumshe idanunsa yayi batare daya ce komai ba amman kuma a ƙasan laɓɓansa ya furta.
"Ameen Ya Rabbil Alamina".
Ta yadda ko kana kusa dashi bazaka jiba bai kuma juyowa ba ya sa kai yayi cikin gidan abba.
Mamakine ya kama mai napep ɗin cikin murna da farin ciki yabar ƙofar gidan yana yiwa Aliyu fatan alkairi a rayuwarsa.
Cikin hankali gami da nutsuwa wadda ta zama ɗabi,ar sa ya kai kansa cikin gidan bakinsa ɗauke da Sallama.
Da Ummi yaci karo tana alwalar sallar magariba.
Cikin sauri ta yarfe hannunta sannan ta ƙaraso gabansa.
"Ya Hydar barka da yamma"
Bai kalli saitin datake ba sejin muryarsa tayi yana cewa.
"Waya gaya maki idan ana alwala ana katsewa?" Maza koma ki sauya wata shasha kawai".
Tura bakin tayi gaba batare data bari yagani ba.
"Shi wannan ya hydar ɗin wallahi ba,ai masa gwaninta.yanzu inda ban kuma gaida shiba seya hau min bala'i".
Tafaɗa cikin ƙasa da murya batare data bari yajiba.
Wanda shi tuni ma yakai falon umma batare daya lura da shirmenta ba.
Aƙasan leɓansa yayi sallama wadda ba lallai mutum yajiba tare da ƙarasawa cikin falon ya zauna a ƙasan carpet ɗin umma yana kallonta wadda take zaune bisa sallaya tana lazumi.
Seda ta shafa sannan ya ɗaga muryarsa kaɗan ta yadda ita kaɗai ce zataji miya ce.
"Umma barka da dare dafatan na sameku lafiya?".
Cike da far,a umma ta kallesa.
"Lafiya Aliyu yaya gajiyar ka ta tafiya?".
Murmushi kawai yayi batare daya amsa mataba.
"Abba fa?".
"Yana sallah a masallaci amman nasan yana hanya yanxun haka".
Hannu yasa ya fiddo wayarsa yana dubawa batare daya cewa umma komai ba.
"Aliyu aka wo maka abinci nasan zakaci mutumin naka tuwon shin kafa".
Cewar umma wadda take kallon sa cike da mamakin halinsa na rashin son magana wanda bata kuma tabbatar da shiɗin muskili bane se yanzu.
"Yanzu dai zan jira abba amman idan muka gama se a kawomin tea ma is ok"
Yafaɗa idanunsa kafe bisa wayarsa yana opperating ɗinta cikin nutsuwa.
"Tom ba damuwa".
Umma ta faɗa tare dajan bakin ta tai gum amman kuma deaf down na zuciyarta tana maganar lallai batula taga ta kanta daman haka yake da sarauta da muskilanci ashe ita da zaman dayay dan ba zama suke kusa da juna ba shiyasa bata san halinsa ba lallai akwai jan aiki agaban ɗiyar tata.
Sallamar abba itace ta katse tunanin Umma tana kuma amsa masa tabar ɗakin baki ɗaya tayi waje domin ta basu waje.
Seda abba ya zauna sannan Aliyu ya rissina ya gaida shi sannan yaja bakinsa yayi shuru.
"Aliyu kaga na kiraka daga sama ko?".
Murmushi yayi tare da waro manyan idanunsa waɗanda suke ƙara masa madarar kyansa ɗan asali sannan yace.
"Haba Abba ya kafaɗi haka ai kamar yadda baba ya kirani nazo a yau to koda kai ɗinne kaimin kiran hakan zanzo dan ALLAH kada ka kuma cewa haka please".
Cike da farin ciki abba ya dubi ɗan yayan nasa tare da cewa.
"To Alhamdulillahi naji dadin bani matsayina dakai kuma nagode ALLAH yayi maka albarka".
"Amin"
Ya amsa a ƙasan murya.
"Aliyu sekuma kaji maganar auren wannan yarinyar ya sauya ko?"
Cikin kulawa tare da son kwantarwa da abba hankali yace.
"Abba daman ai sha,anin ALLAH haka yake mu muna tamune shi kuma yana tasa amman kuma tasan itace haqqun".
"Hakane Aliyu ALLAH yasa hakan zama alkairi gareku baki ɗaya.Sannan kuma dan ALLAH dan annabi fatima ƙanwarka ce nidai daga yanzu nabaka amanarta kazama mahaifinta kazama mahaifiyarta abun da tai na ba dai dai ba dan ALLAH ka hukuntata".
Wani irin nauyin abba ne ya kamasa nan danan tare da tausayin sa acikin ransa.
"Karka damu abba daman ko ba aure ma ai ƙanwata ce bare kuma tana da aurena insha ALLAH zan bata kulawa".
Dasauri ya cije leɓensa na ƙasa yana mayar da kansa jikin kujerar falon.
"To nagode Aliyu ALLAH yay maka albarka yadda ka karɓi auran nan batare dakai mana turjiya ba kaima ALLAH ya baka masu maka hakan".
"Amin abba nagode"
Tashi abba yayi tare da futa tsakar gida umma ya kirawo tare da cewa ta kira batula.
"Alhaji ai ina jin tana ma cikin ɗakin amman bara na kirawota".
Komawa sukai ciki yadda abba ya barsa haka yazo ya sameshi yana zaune yaɗan miƙe ƙafafunsa a saman carpet ɗin.
"Aliyu nabarka ko kayi haƙuri batula za,a kirawo min".
Abba ya faɗa tare da zama ita kam umma wucewa tayi cikin bedroom ɗinta.
Salati Umma ta saki lokacin data hango batula kwance kan gado tayi ɗai-ɗai da alamun ma batasan anyi sallah ba.
Dasauri takai mata duka.
"Ke dan ubanki baki san magariba tai bane!!".
Zumbur na miƙe tare da sakkowa aguje nai hanyar falo.
"Kai nina shiga uku haba umma wallahi dukan fa da zafi".
Nafaɗa dai dai sanda nake kaiwa wajen falon tare da ƙarasa maganar cikin kuka!.
Biyoni tayi tana cewa.
"Wuce malama kiyi sallah ga abbanki can yana kiranki".
"Umma fa yau banayi dama ni baki tasheni ba kinmanta ɗazu agidan iya fa na ɓule".
Kunyace ta kama Umma cikin sauri tayo waje tare da nufar wajan su abba ta zauna tana kallona wadda na juya bayana batare dana san waɗanda ma suke cikin falon a zaune ba.
Juyowar dazanyi domin nai magana karaf muka haɗa ido da Ya Hydar amman senaga kamar ma harara ta yake tare da kauda kansa gefe.
Nima juyawa nai ko ajikina na nufi komawa cikin ɗakin umma.
"Jaririya kixo mana bakiga abbanki bane".
"Umma hijabi fa zan ɗauko naga da Namiji a wajan".
Nafaɗa cike da rainin wayon wanda na faɗi maganar dominsa.
Wani malolon takaici da baƙin cikine suka tokare Aliyu amman sam bazaka taɓa gane hakan ba sabida yadda fuskarsa take kamar yadda take a koda yaushe kadaran-kada hakan.
Seda na juya na ɗauko ƙaton hijabi na sallar umma sannan naxo na zauna tare da gaisar da abbanmu.
"Ya hydar ina yini?"
Bamma samu arzikin amsawa ba bare ya kalleni sema ƙasa dayayi da ƙwayar idanunsa yana duba wayarsa.
Cikin hikima abba yake mana nasiha nidashi wadda tunda aka somata nake zafga kuka! kamar babu gobe.
Abba yana direwa itama umma tasoma wanda anan naji ana zancan nan da kwana biyu zamu tafi abuja wata irin dira nayi tare da cakume umma.
"Ni wallahi umma bazani gidan mugayeba ni wallahi umma bana sonshi"
Dasauri naga ya ɗago idanunsa karaf kuma muka haɗa ido dashi sam baxaka fuskanci a wani hali yakeba sedai kana kallonsa kasan maganata ta basa haushi ba kaɗanba.
"Wai miyasa ke batula baki da kunya ne?" cewar umma.
"Dan ubanki shima aka ce maki yana sonkine batai maka miki yayi ze kwashekiba banza marar hankali yo idan bama ƙaddarar aureba kiga yaro fari tass jinin larabawa amman ki dinga iskanci wanda kinsan ko kama ƙafar matarsa bakiyiba".
Nan fa umma tahau zazzagan masifa "Kuma wallahi gashi nan keda shi kije can kice zaki wannan tsiwar taki ya bubbugeki.kuma kinsan daga ranar dakika barmin gida koda wuni bana nemanki bare da

9 / 28