Author : Nil Category : Romantic Hausa Novels
yayi gum.
"Hmm wannan yarinyar ce ta wajen kabiru ta sami miji fa kaga yau ma sunxo neman auranta nidai nace wa kabirun babu wata matsala kawai su bayar ai komai lokacine, ni bada ban ma tafiyar dazakai ba aida ka kaini kanon sabida maganar wallahi" baban abuja ya ƙarasa maganar yana kallon ɗan nasa tare da jin mexe ce masa.
"Baba wai wace yarinyar ce acikin ƴaƴan abban naga dik yarane ina suka isa wani aure yanxun" murmushi baba yayi tare da cewa "to faɗima mana babar yarsa ai kaga daɗan aukinta ko?".
Wani shu'umin murmushi Hydar ya saki wanda yake dauke da ma'anoni da dama tare da cewa "aifa to ALLAH sanya alkairi" bai kuma cewa komai ba ya miƙe tare da cewa.
"Baba mu xamu wuce ai mana addu,a dan ALLAH" murmushi baba ya saki shima sannan yace "ai addu,a kullum muna cikin yi maku ita.ALLAH ya tsare kadaibi a hankali da ƙasar daba takaba babana. yanzu dai se ƙarshen shekarar zaka dawo kenan ko?" amman ni banji dadin wannan tafiyar taka ta gaggawa ba naso kunje kano can dangina sunga matar taka wallahi" baba ya karasa magana cikin wani yanayi.
"Karka damu baba insha ALLAH damun dawo zamuje wata shida kawai zamuyi fa mu dawo" yakai maganar yana duba a gogon hannunsa.
Cikin sauri sukai sallama da mahaifin nasa tare da barin wajan ya nufi cikin gidansu.
Sallama yake da momy mahaifiyarsa sannan yace ze shiga suyi da sauran ƴan gidan amman fafur momy taƙi yarda wai baxe jeba salon ai masa barbaɗe ba. (kujifa)
Ɓata rai yay sosai "haba hajiya wai miyasake kikeson shiga tsakaninmu da dangin mune wai?" mi sukai maki yadace ace zanyi tafiya wadda take da hatsari amman ace baxan sanar da matan mahaifina ba sabida wani zarginki nacan!!
"Aiko babu komai mun haɗa iri dasu nan kina da ƴaƴa mu goma su suna da ƴaƴa wajan ashirin aikam mun zama ɗaya babu yadda zamuyi dole dai jininmu ne dan ALLAH hajiyata ki daure ki cire komai aranki kinga mune manya acikin gidannan yakamata kina sauke wani abun aranki.
Duk kuma se jikinta yay sanyi sanin halin ɗan nata da kafiya da son ƴan uwansa dan haka setace "to naji yaya zanyi tashi kaje ai wallahi su hajiya salma ( mama ) sunmi illah babba" babu wata illa hajiya kece baki gane ba har yanzu wlh su mama basuda matsala"
Kaga rufen baki malamin gaskiya tashi kabani waje.
Kuma kai sauri ka koma part ɗinka kutafi dan nasan yanxu MARYAM (amaryarsa) tana can tana jiran ka, "dik jiran da zatai ai seta bari nagama da AHALINA dai ko" yafaɗi maganar cikin zuciya tare da dire mata bandir ɗin ƴan dubu dubu yabar wajan yana cewa 'hajiya ai mana addu,a".
"ALLAH ya tsare" ta faɗa tare da ɗaukar kuɗin tana murmushi.
Haka dik yabi sauran part ɗin yay masu bankwana tare da basu kuɗi sannan yabar gidan ƴan uwansa harda kuka! ƴan sauran ɗakunan.
Direct part ɗinsa ya koma yana zuwa ya tarar da maryam ta cika tai fam! zatai masa magana ya ɗaga mata hannu haka tai tsitt ganin babu fuska.
Driver ne ya shigar musu da kayansu boot daganan sukai airport karfe 12 rana jirginsu ya ɗaga kalaba.
Semuce ALIYU & MARYAM semun ganku watarana😭
*KANO*
BAYAN WASU KWANAKI!.
Duk yadda naso ganin umma ta saki ranta taƙi daga ƙarshema denamin magana tai.
Sedaga baya kuma ta sakko muka koma kamar da.
Abdul yazo sun gaisa da umma. yau kwana biyar kenan da zuwan ƴan uwan sa gidanmu kuma alhamdulillahi su abba sunyi binciken su babu wata matsala a tsakanin mu da abdul.
Nan da kwana uku ma zasu su kawo kuɗi da saka ranar auranmu duka.
Wannan lamari kamar a mafarki nake ganinsa ikon ALLAH.......!!
*13*
Cikin HUKUNCIN ALLAH komai yana tafiya yadda ya kamata., yau tun safe umma takira anty zee, bayan tazo nan suka hau aikin kayan soye-soye wanda ni sedaga baya ummi kecemin wai gobe INSHA ALLAH ƴan uwan ABDUL zasuzo kawo kuɗina da saka rana wannan lamari ba ƙaramin mamaki ya baniba, dik da nasan da hakan amman ban kawo cewar umma zata tsaya yin wannan hidimar dominsu ba sabida yadda tun farko naga ta ɗauki zafi da harkar.
Amman kuma se gashi yanzu naga ta sakko anata sabgar shagalin da ita.nima tun abun yana ɗauremin kai har kuma senazo na saki jikina harma na tsoma nawa hannun a murjin dubulan ɗin da anty zee keyi a bakin kicin ɗinmmu.
Cikin hirarsu naji anty zee na cewa umma wai ina labarin ɗanta Hydar da amaryarsa kuwa? umma kada baki tai "hmm zainab kwanci tashi babu wuya a wurin ALLAH kingafa wai bikin nan kamar yau mukaje shi amman har anyi wajan wata huɗu fa, ninaji jiyama agidan alhaji ƙarami anata maganar cikin matar tasa" wata irin zabura nai kamar ni akaiwa tare da zarowa umma ido......
"Umma ciki fa daga yin auren yanzu harta samu ciki,innalillahi ni wallahi umma bana ƙaunar cikin nan sabida wahalar danaji ance anasha wajan haihuwa" naƙarasa maganar idona yana kawo ruwa.
"Toyan zu uwar,,mu dake muke magana dazaki tsomamin baki"! shuru nai ina binta da ido danni dik zancen cikin nan na anty maryam matar ya Hydar ya tsoratani ba kaɗan ba danni naƙi jinin haihuwa saboda tun wahalar danaga umma tasha a haihuwar amir shikenan naji tafita a raina dik da ba,a gabana tayi ba amman ai naga yadda take fama.
Dariya anty zee ta saki tare da cewa "yaya aisha kwana nawa ne itama ta shiga daga ciki ɗin maye na ɗaukar zafi haka" ta ƙarasa faɗa tana dariya "bazaki gane ba zainab yarannan kamar sukai kansu gidan miji haka sukeji amman dan munafurci jibeta harda wani rau-rau da idanu zatai kuka!!" umma ta ƙarasa maganar tana nuna'ni da hannunta.
"ALLAH umamah tsoro naji nagafa yadda kikaita shan wahala acikin amir" nafaɗa ina sunne kaina a ƙasa. "hmmm to ita dai gaskiya maryam ɗin naji ance da sauƙi bata wannan laulayin amman naji ance hajiya zainab. tacewa hydar ya dawo masu da ita gida".
Shewa anty zee ta saki tare da cewa "ALLAH ya kyauta ai yanzu daman hakane daga anyi aurannan kamar jira ake sekaji ɓur!" haka dai sukaita hirarsu nidai jikina dik yayi sanyi da wannan lamari damma naji ance anty maryam ɗin bata laulayi ai da sauki.
Bamu muka kammala ba se daf da magariba.
Ina tashi nai wanka tare da cin abinci tunda ina fashin sallah.
Fita nai zuwa ɗakin umma anan na tarar suna magana da anty zee bayan sun gama sukai sallama mu'muka ɗaukar mata kayanta muka rakata zuwa titi tunda yaranta dik suna gida acan tabarsu.
Adawowar mu ummi kecemin "yanxu fa anty batula kema haka zamuna rakaki idan kinyi aure ko" dariya na saki tare da bata amsa "to kika sani ma ko tare abba ze haɗamu tunda naga ya shamsu na gidan kawu kamar yana ciki fa" tura baki tai gaba tare da cewa "ALLAH ya kyauta mukam aure semun zama DR. insha ALLAH" to ALLAH ya amsa".
nafaɗa lokacin da muka kai zuwa kofar gidanmu.
Ɗakinmu Ummi ta shige nikuma nayi ɗakin Ummah domin na shaida mata anjima fa ABDUL yace idan yazo ze shigo cikin gida su gaisa.
Dakatawa nai abakin kofar bedroom ɗinta jin kamar tana wayane kuma da alama wayar tana da muhimmanci tunda naji muryar umma ƙasa-ƙasa.
Ganin ina ɓata lokacina yasa naɗan ja ƙafata kaɗan na ƙarasa cikin room ɗin ni anufina zata iya hangoni ta dakata dayin wayar tunda ina saurine naje na ƙarasa kintsawa.
Wayar umma tana a handsfree ne shiyasa na nutsu sosai jin murya na cikin wayar kamar na santa.
Tabbas ba muryar kowa bace ba face ta Ya Hydar kuma dagaji suna magana akaina nane. tsaida raina nai tsamm jin yana ce mata.....
"Ki kwantar da hankalin ki umma insha ALLAH komai ze tafi yadda baki tunani ba tunda kuna addu,a ai"
"Amman Aliyu kana kallonfa wannan maganar bazata iya kawo mana cikas ba?" insha ALLAH umma babu komai karki damu daman dai da abban ya ƙara bari nan gaba kaɗan se ayin hakan yafi amman tunda rabonta a kusa yake ai semuyi mata fatan alkairi".
"Hakane kam ALLAH ya zartar mana da alkairi amman wlh ni hankalina ya gaza kwanciya" umma ta faɗa kamar kuma tana kukane lokacin"
Sosai naji muryar ya hydar yana yiwa umma magana cikin tattausan LAFAZI tare da gaya mata wasu maganganu wanda kunnena yagaza jinsu.
Gaba ɗaya kaina ya kulle da wannan lamari dik jikina ya jike da zufa shin wani abunne wannan da uwata take tsoronsa gareni har tasa take boyen shi? bani da mai bani amsar hakan dan haka shiyasa naja kafata na koma da baya har na futa.
Babu yadda ABDUL bai dani akan yazo ya gaida umma ba a yau amman naki basa dama saboda bana jin dadin jikina sam.
Hirarma tayau gata nan dai haka mukai muka gama.
Kuma ikon ALLAH koda na koma ciki banga wani tashin hankali a fuskar umma ba dan haka nima na saki raina na manta da wannan maganar danaji sunayi tunda nasan may be bata shafeniba.
Alhmdh yau laraba yau aka kawo kudin aurena da saka rana ta da ABDUL wai abin da yabani mamaki shine yadda abba ya amince a wata gudan da suka zo dashi kamar ya gaji dani wallahi har kuka nai dan haushi.
Haka dangi suka cika gidanmu kamar ana biki anata shagali nidai ina daga ɗaki nidasu mufida ƴaƴan gidan yayan abba alhaji ƙarami se tsiya sukemin nidai bance musu komai ba haka nai kwance ina tunanin ABDUL ɗina.
Gidanmu bai bar ganin jama,aba seda aka ci sati guda ciff da kawo kudina sannan aka tsagaita da zuwa murna abinka da ɗan dangi.
Babu laifi suma ƴan uwan ABDUL sun nuna min so domin kuwa dik yanzu ina kiransu a waya muɗanyi hira dasu.
Kuma har ƴan ɗakin suma ya kawomun su mun gaisa nima kuma naje gidansu da daddare harda ummi da amira suka rakani naga hajiya mahaifiyarsa sedai dady ne baya nan yay tafiya kuma wallahi seson barka domin na sami goma ta arziki agidan sosai.
ikon ALLAH dik ƴan gidan baban abuja sun kirani a waya sunmi ALLAH sanya alkairi amman babu ɗan ɗakinsu ya hydar ko guda akiran nawa abin ya bani mamaki kuma na jinjina wannan ƙiyayyar amman ban damu ba saboda nasan daman momy bazata barsuba.
BAYAN SATI UKU.
shirye-shirye ya kam kama ta kowani ɓangare nifa senace ma har ƴan gidansu ABDUL sunfimu zumuɗin wannan lamari duba da yadda naga suna addabata da waya akan yadda za,a gudanar da events ɗin bikin da sauran abubuwan ni watarana ma abin har kunya yake bani wallahi.
Idan ka dubeni bazaka iya kauda kanka ba sabida yadda naci uban gyaran amare awajan HAJIYA ZARAH mai kayan mata takanas anty zee ta ɗaukomin ita tun daga garin GUSAU tazo da kaya kala-kala na gyara ko ina domin jin dadin ango cewar ta ita da kanta anty zarahn.
Agidan anty zee na tare gaba ɗaya wuni ake ana faman yimin dilka da halawa da sauran gyara ni kaina idan na kalli kaina farin ciki nakeyi sabida yadda na koma kamar wata black amerincan.
Babu yadda ABDUL ya iya sabida anty zee ta dakatar dashi zuwa wajena domin kuwa idan ba,ai wasaba ze iya ɓata mana aiki dan wannan gyaran na musamman ne dole se anaja baya baya da namiji sabida tsaro.
Kullum mukai waya dashi seyay min complain akan yana missing ɗina wataran har gwalo nake masa haka zeji haushi ya kashe wayar amman dayake maye ne gobema seya kirani.
Yau Alhamis yau muka fara events ɗinmu anyi kamu washe gari juma,a akai mothers day, nan ma babu laifi anyi casu ƴan uwa sunmi rawar gani musamman ma yadda naji ana zuzuta ɗakina yadda abba ya zuba kuɗi abin seson barka sabida daman tun ana sauran sati biki sukai min jere anan rijiyar zaki.
Gidanmu babu masaka tsinke sabida yadda dangi sukai masa caaa!!
Danni kam da gyar na kutsa ɗakin umma sabida yadda nakejin gajiya kamar na mutu ga uban ciwon kai.
Ikon ALLAH acikin ɗakin umma harda momynsu ya hydar da matarsa anty maryam da ƴan gidan baban abuja dik sunzo baki ɗayansu ni wallahi bamma saniba ashe sunzo.
Ƙarasawa nai na gaida kowa na ɗakin amman momy bata amsa min ba wanda daga ganin face ɗinta kasan seda akai babu dadi sannan tazo bikin.
Da yake nasan matar ya hydar a hoto shiyasa na ƙarasa muka gaisa da ita kuma babu laifi ta sakar min fuska itakam dan har tsokanata take daga ƙarshema tace na samo mata kunu dan ALLAH zata sha.
Fita nai waje tare da umartar ummi takai wa anty maryam kunu nikuma nai ciki tare da kwanciyata a ɗakinmu gobe ɗaurin aure da dinner daga nan kuma se gidan ABDUL.
Tunda na tashi yau nakejin babu dadi ga ciwon kai nidai haka naja jikina nai wanka ina fitowa na koma kan gado na saka kuka wiwi.
Seda anty zee tajani mukai ɗakin umma nan ma rungume umma ina mata kuka nan fa ƴan uwa sukaimin ca mai tsokana nayi mai hoto nayi.
Babu abinda momy take se jan tsaki daga karshema ta saka matar ɗanta da sauran ƴaƴanta agaba suka bar dakin gaba ɗaya.
Sukam su mama dasu akaita bani baki har anty zee ta janyeni mukai can cikin gida domun ta shiryani.
************
Acan cikin gari kuwa unguwar yakasai babban masallaci ya cika taff da ɗan adam! liman ya tashi domin sheda daurin auren FATIMA KABIR UBA YAKASAI DA ANGONTA ABDUL.......!!
Dakata malam!! dakata!! cewar wani babban mutum kenan dayake kutso kai cikin masallacin.
Da sauri ABBA! BABAN ABUJA! ALHAJI ƘARAMI dama sauran ƴan uwa suka mike tsaye suna bin mutumin daya shigo cikin masallacin da kallo batare dasunce komai ba.
Wallahi!! tallahi indai nine uban daya haifi ABDUL to ban amince da wannan aure ba....!!
Bazan taɓa yarda ba!!!! da sauri abba ya ɗago kansa yana zubawa mutumin ido cikin tsananin tashin hankali.
Eh kabiru kalleni da kyau kada kaga kabar unguwarmu kadawo nan tofa ka tuna shi wannan abin dake bibiyar AHALINKA har abada zeta binka ne aduk inda zaka kasance!!! dan haka babu wannan aure sam ɗana baxe auri ƴarkaba!!!
zaman dirshan abba yay tare da saka kuka ABDUL cikin sauri yayo kan mahaifinsa yana tambayarsa amman inna tuni yasaka wasu ƙarti sunyi waje da ABDUL ɗin.
Shima tuni ya take musu baya yabar jama,a da tambayar abin dake faruwa.
Cikin fushi baban abuja ya kalli liman tare da cewa.....
Meyasa wasu mutanen kan son tozarta ƴan uwansu musulmine?
Innahlillahi wa'innah ilaihirraju'un.
Liman sake shaida ɗaurin auran nan ya koma kan ɗana nina san *KO BABU SO* atsakanin ALIYU DA FATIMA tofa akwai *ƘAUNA* ta jini ɗaya!!!
kuma mu zamu ɗauki kaddarar data hau kan fatima dik da haka domin hannunka baya rubewa ka yanke ka yar.
Cikin minti goma dubban jama,a suka shaida ɗaurin auren CAPTAIN ALIYU MUHAMMADU UBA YAKASAI DA FATIMA KABIR UBA YAKASAI cikin sadaki mafi daraja da Najeeb abokin hydar ya wakilci abokin nasa ya bayar wanda shi yana can ABUJA bai san wainar da ake toyaba😳😳
Da ƙyar su baban abuja suka ɗaga abba sukai mota dashi yana faman gunjin kuka sabida yasan tashin hankalinsa lafulane akan na matarsa da ita kanta ƴar tasa wadda bata san wace ƙaddara ce ke yawo ajikinta ba.
Acikin minti goma da wani abu har labari yakai cikin gidan su batula dama cikin unguwarsu baki ɗaya.
Ahau kace momy ta saki wata razananniyar ƙara tare da zubewa a sume saboda jin wannan mummunar jarabar da aka liƙawa ɗanta.......!!tabbas jarabace auran batula da hydar itakam an cuceta!!!
Inalillahi wa'innah ilaihirraju'un cewar.....!!
*MENENE YASA BABAN ABDUL YAƘI AMINCEWA DA AURAN NAN*?
*WACE ƘADDARAR CE TAKEBIN AHALIN ABBA DA UMMA HARTASA SUKA BAR TSOHUWAR UNGUWARSU SUKA DAWO NAN*?
*YAYA AURAN BATULA DA HYDAR ZE KASANCE*?
*TASHIN HANKALIN WAYE ZEFI TASIRI NA MARYAM MATAR HYDAR KONA MOMY MAHAIFIYARSA KONA SA SHI KANSA WANDA BAI SAN WAINAR DA AKE TOYAWA BA*?
*WANI HALI ABDUL ZE SHIGA*?
*YAYA LAMARIN BATULA WADDA BATA SAN KOMAI DAN GANE DA WANNAN LABARIN BA*?
*SHIN TAKA MAI MAI MA MAYE WANNAN ABIN DAKE BIBIYAR AHALIN ABBA WANDA YA SHIGE WA KOWA DUHU HARTASA AKA FASA ƊAURA AURAN ƳARSA*?
MY FANS WANNAN SALON FA NA DABANNE AKWAI HARGITSI ACIKIN PAID GROUP.
AKWAI LOVE AKWAI SARƘAƘIYA AKWAI TAUSAYI AKWAI TSAYAWA ARAI.
AKWAI GWARAMA TSAKANIN BATUL DA ALIYU FA.
YAYA RAYUWAR BATULA ZATA KASANCE NAN GABA AGIDANSU hydar ga ƙiyayyar momy gata kishiya ga uwa uba shi kansa mai kankat ɗin
Tabbas akwai babbar tafiya acikin wannan littafin gaskiya akwai salo kala kala a wannan tafiya kedai hanzarta siyan naki kada ki bari ya huce da tururunsa!!!
*WANNAN SHINE LAST FREE PAGE GAMAI SO YAYMIN MAGANA DOMIN SAMUN CIGABANSA*
*LAST FREE PAGE*
*14 - 15*
"Innah lillahi wa'innah ilaihirraju'un" cewar ɗiyar momy ta biyu hafsa mai bima Hydar tare da nufar inda momy ta zube aguje tana faman sakin ihu! wanda shiya jawo hankalin sauran mutan gidan waɗanda suka halarci bikin.
Cikin wani irin yanayi hafsat take jijjiga!momy gami da furta "Dan ALLAH momy karki mutu ki barmu wallahi wannan auran ma sunan sa rusash she tunda baza,a liƙa mana ƙarbai ba dan ALLAH momy kita shi pleaseeee!!" hafsat takai maganar tana mai zama a kusa da momy itama cikin haka sauran yaran momyn suma suka shigo gidan aguje nan fa waje ya kaure da koke!-koke.!
Daƙyar wasu daga cikin matan ƴan uwa suka ɗaga momy wadda batasan inda kanta yake ba sukai ɗakin abba da ita tunda shine babu jama,a acikinsa sosai.
Itakam maryam matar hydar bata masan ana yiba tunda tana can gidan wata aminiyar momy tada tura ta can wai ta huta acewar momy ɗin.
Cikin tsananin tashin hankali Hanif mai bin ummi ya shigo tare da nufar ɗakin umma aguje yana haki jikinsa sanye ike da farar shadda ƙar wadda Abba ya dinka musu ta ɗurin aure da ƙyar ya sami damar kutsawa cikin ɗakin gadon umma wanda tsabar dangin umma da suka cika wurinne ya sa da ƙyar ya samu damar samun shiga.
Hango ta yay zaune a gefen gado taci uban ado tana magana da