Author : Nil Category : Romantic Hausa Novels
yake kamar yayi losing control ganinta yake ta rikiɗa ta koma masa wata zubin halittar daban ba batulan umman daya saniba sabida yadda anty zee ta dage wajan gyara batula dolene koma waye ya gigita da ita musamman idan yaci karo da lallausar fatar jikinta mai ɗan karen laushi da sulɓi.
Babu yadda ya iya haka yabi umarnin da zuciyarsa take basa akan yaɗan rage zafi da ita tunda daman yanzu maryam tazama se a hankali harya ɗan sunkuyo yana shirin gudanar da abinda zuciyar tashi take ƙudurtarsa dashi sekuma ya tsaya cak! kadafa ta rainani acewarsa cikin zuciyarsa wata kuma zuciyar tace masa to seme ai matarkace halalinka duk da ba sonta kakeba amman abun da kake shirin farawa da ita ayanzu shize ƙara maku kusanci da ita da shakuwa har hakan yasa ku dai daita kanku ku zauna lafiya ku faranta ran mahaifanku yana gama wannan tunanin yafara gudanar da abinda zuciyar tashi takeso.
Jin yadakata da tausar dayakemin ɗinne nasaki hammadala ina kokarin na mike na gyara jikina amman senaji wani salon daban wanda ya ɗagamin hankalina nan take gaskiya nidai baxan iyaba aiwannan ma iskancinne ko angaya masa ni sonsa nikeyi daxexo yana min wannan abin.
Ban gama tunanin abinda nakeba naji saukar bakinsa akan ƙuguna dai dai wajan danaji ciwon yakama fatar wajan da hakorinsa yana ɗan gogawa kaɗan kaɗan.
Wani irin numfashi naja tare da fesar da iska mai karfi kana na mirgina kaina gefe ina fesar da numfashi mai hade da nishi.
Hannunsa yasaka ya juyo dakaina yana mai tsareni da manyan idanunshi waɗanda suka koma kamar gauta dan tsabar jaan! su ni har mamaki abin yabani still kuma bakin nasa na west ɗin nawa batare daya cireba, harseda naji na daina jin wannan azababban zafin kuma kamar shima ya kula haka ya zare bakin nasa akai ya tallafo kaina da hannunshi ya tsirani da idanun nashi yana kallona.
Tsintar muryarsa nai akasan makoshinsa yana cewa.
"Fatie ahalin yanzu bazance ina sonki ko in ƙinkiba wanda daman can ni ban taɓa nuna maki ƙiyayyaba amman inason muhaɗe kammu ko ALLAH zesaka mana son junanmu kodan mu kwantarwa da mahaifanmu raia" yakai maganar yana mai kara kusanto da kanshi gareni.
Tura bakina nai gaba duk da banga sakin fuskar daxan kawo masa rainiba sabida ahalin yanxunma dukda kusancin dake tsakaninmu bai saki face ɗinshiba.
"Nifa yaya bana sonka dan ALLAH kada kaimin komai wallahi na yarda naitawa momy bauta daga nan har iya raina akan nikazo ka takuramin" nakai maganar cikin tsananin jin haushinsa.
Tabe bakinsa yayi tare da makamin wata katuwar harara batare dayace min komaiba, sejin bakinsa nayi akan bakina yana sakarmin wani irin mahaukacin kiss mai zafin gaske.
Seda ya zuƙe duk wani miyau na bakina tas kamar maye sannan yasoma bin fuskar tawa da lasa kuma duk abinda yake idanunshi arufe suke ruf seda ya gama bin fuskata da lasar sannan ya matseni a kirjinsa yana mayar da numfashi baki ɗaya ya sakarmin numfashinsa da nauyinsa ajikina.
Idan ka dubeni wallahi seka tausayamin sabida yadda nake faman raba idanu danni wannan abun walaha kawai nasha bawani abuba dan tsabar mugunta anwani zo an danneni wallahi se ALLAH yasakamin nakai maganar cikin zuciyata.
Shikam anasa bangaren hakan dayay mata shine kawai mafitarsa sabida idan har yacika romance da ita tofa tabbas zeyi aika aika kumashi sam bai shirya hakan a halin yanzuba impact bamaya kawo wannan lamarin a halin yanzu wannan reason yasa ya hadeta da jikinsa koya samu yaɗan samu nutsuwa a hakan.
Luff yayi asaman yana sakarmin numfashi kamar yasami wata kayan wanki.
Cikin azaba na ɗago kain ina kallonsa murya can ƙasa nace"yaya dan ALLAH ka ɗagani wallahi kamar zan mutu" nakai maganar ina kuka kaɗan kaɗan.
Gogamin kwantaccen sajen fuskarshi yake ahankali ahakali yana ɗan saka harshenshi yana lasar fatar wuyana batare daya tankaniba.
Seda yaji ana kiran sallah sannan ya ɗagani cak ya nufi kofa seda yakai bakin kofa sannan naji muryarsa can qololin qasa yana cewa "kitashi kiyi wanka kiyi sallah sauran indawo baki tashiba raguwar mata kawai"yafaɗi maganar yana danne dariyar data zo masa sabida yadda idanunta suka basa dariya tawani zarosu kamar taiwa sarki qarya ga ragwanci nan qarara yana kallo acikin idanun nata gami da firgici da ɗimuwa kala kala.
Haka ya bude kofar ya fice yana cigaba da dariyarsa aishikam yaga hanya dan daga yanxu ta wannan salon zedinga hukuntata tunda ya hango tsoron hakan acikin idanunta.
Yana fita na mayar da idanuna na kulle gam in jan tsaki sannan na tattre towel ɗin jikina nayi bayi seda na fara wanka sannan na ɗauro alwala na fito na tayar da sallah ina zune akan sallaya segasu rauda sun faɗomin waɗanda suketa raba idanunsu wanda kana ganinsu kasan fakar idanun momy suki suka shigomin.
Na'eem ce ta dire dan kwanon silvern hannunta agabana tare da cewa "sis yaufa samuwa mukai,wallahi mamace ta aiko mana da fara tokinsan momy tagani baxata barmu mu ansaba shiyasa mukazo nana muci",takai maganar tana min dariya nima dariyar nai tare da cewa"wallahi aje mana muci nikam ina mugun son fara ba kaɗanba" aikuwa haka muka saka kwanon a gabanmu muka zagayesa muka haucin farar babuji babu gani da wannan ɗan yayume yayumen nidai naji naqoshi.
Hira muka kaure da ita kuma duk rabi akan yadda momy ke hanasu hulɗa da ƴan uwansu sukemin complain anan na fuskanci cewar ashe duk laifin momyne ita ke hanasu hulɗa da family ɗinsu na uba hatta ga ƴan gidan ƴaƴansu mama momy wai ba,ason ranta take barinsu suke harkaba dan dai baba ya tsawatar ne.
Sosai na zauna na dinga basu shawara akan suna ɗanyi mata wa,azi kaɗan kaɗan sannan suna sakata acikin addu,arsu akan ALLAH yadawo da ita hanya madai dai ciya.
Anan kiran sallar isha mukaji turowar qofa shine ya shigo fuskarsa adaure ganina dasu rauda nan ma naga ya kuma hade ran fiye dana da, nidai kallo guda nai masa na dauke kaina ganin yana makomin harara ko dasu rauda suna gaidashi haka naji ya amsa masu murya can ciki nidaman banyi karan bani ba.
Diremin katuwar ledar hannunshi yayi agabana batare daya cemin komai ba ya juya yabar dakin.
Jikinsa sanye yake da wani dark blue din yadi mai ɗaukar idanu kansa babu hula amman kallo guda zakai masa ya burgeka da kallo na bisa ina ayya miskilanci irin nasa sannan na juya wajansu rauda mukacigaba da hirarmu.
Seda naga zasu tafi sannan na jawo ledar kayan makulashe ne acikinta rabawa biyu nai na nasu kaso daya sannan mukai sallama suka bar dakin inata mamakin yadda sukacemin wai duk ƴaƴan momy sunyi farin cikin aurena da yaya sabida wai tanan suke tunanin momy zata aje makaman yakinta.
Tashi nai na mayar da sallar isha sannan naje na saka key sabida tsaro naxo na baje naci abinda zanci sannan nai brush na kwanta.
Washe gari bayan nai sallar asubahi ina lazimi sega sakon momy haka na mike naje kodanaje cin zarafi kala kala tai min sannan ta hadani da gyara cavet dinta.
Wunin ranar ban sakasa a idanuna ba nima ban saka akaina ba sabida wahalar danasha ranar tafi ta koyaushe ban sami kaina ba sedare kum ikon ALLAH yau tabani abinci naci amman dai bautar aikice dai nashata danma dai su rauda sun faki idanunta sun tayani wani aikin.
Har dare ban gansaba haka nai sallah na kwanta abina washegari da sassafe baccine ma akaina naji alamun shigowarsa ya tsaya akaina jikinsa sanye da kayan sojoji magana can kasa yakemin bayani zetafi lokoja shida anty maryam zasuyi sati uku ko wata sabida haka na kula da kaina duk abinda nake bukata naiwa momy magana bai kuma yarda na fita ko wajeba idan na fita kuma bai yafe ba yana gama fadin haka yasaka kai ya fita.
Kuka nasaka qasa qasa tare da komawa baccin bakin ciki sabida ai koba komai yana tausayamin dan wallahi adan zamana dashi na fuskanci mutum neshi mai tsananin tausayi.
Baifi minti goma da barin gidan ba sakon momy ya zogareni haka na fita wajan bauta.
Yauma wuni nai abu guda ban samu kainab se dare dakinsu rauda naje na'eem ta hadamin ruwa nai wanka sannan nai sallah na kwanta agadonsu banyi aune ba se baccin wahala.
Kwanci tashi babu wuya wajan ALLAH yau kimanin satina uku kenan agidan momy kuma haryau su yaya basu dawoba bani da labarin gida sabida babu waya a hannuna daga azabar momy kuwa yanxu tafi tada idan k ganni baxaka taba cewa batulan umma bace sabida makarantar momy ta mayar dani silent girl marar son hayaniya ko tsiya sam yanzu babu wannan atare dani yanxu babu abinda na tara se ɗan banxan tsoron momy wanda ko tari tai jinsa nike har raina..
Zamana dasu rauda kam ya koyamin gayu fiye dana da ya koyamin tsafta wadda ta ninka tawa danni yanxu duk wannan son jikin babu atare dani.
Shikam yaya hydar baki ɗaya ma na manta dashi dan wata katuwar ƙiyayyarsace take yawo araina gani nake duk wannan bala,in danake ciki shiya sakani tunda inda bai amimce da aurena ba ai da tuni ina gaban iyayena amman yanxu idan ban da bauta mai nake haka wataran idan na tuno gida nai dariya wataran kuma nai kuka!
Yau watana guda agidan momy kuma babu alamun dawowar yaya ayadda najima ance wai yanxuma baya can garin an ƙara turasu wani garinne domin kwantar da tarzomar datake faruwa ga wasu yankuna na kauyukan garin da aka turasun kuma duk wannan labarin daga wajan kannensa nakeji domin ni momy bata bani wayama mugaisa bare naji labarinsa hmm base naga fuskar hakan maba.
Idan ka ganni yanxu naɗan fada kaɗan amman kuma fatata taɗan kara murjewa na sauya sosai tundaga kan halina har zuwa jikina.
Yau tunda muka tashi muke girke girke baban abuja ze dawo daga tafiyar dayayi wanda tunda akai aurenmu baya garin seyau ze dawo.....
*************************
Abdul kam sedai muce sam barka domin yanxu kimanin sati biyu kenan da fitowarsa daga asibitin kuma babu laifi ya dangana da ALLAH ya fitar da tunanin fati aransa sabida jin labarin aurenta dayayi yasan tai mashi nisa daman haka akeson bawa mai yarda da qaddararsa sedai kuma zaman kanone yaji yayi masa kunci saboda missing sahibarsa dayayi babu shiri yasa dady ya nema masa transper zuwa babban asibitin abuja tunda daman likita ne.
Cikin sati ɗaya abdul ya haɗa tarkacensa ya nufi birnin tarayya tare da fawwalawa ubangiji lamarinsa dakuma mayar da hankali akan aikin dake gabansa bawa alumma taimako da iya karfin da ALLAH yabasa.....!!
Wannan kenan.
62 - 63
Yau gidan na hajiya momy da hidima muka tashi na dawowar baban abuja daga qasar waje wanda tun bayan bikinmu dayabar kasarnan bai kuma waiwayarta ba se yau dayake shirin dirowa sosai momy take faman zirga zirga tashiga nan tafita can babu abinda takeyi sefaman haɗa masa kayan abinci masu daɗin gaske wanda bata yarda dako masu aiki sun shigar mata kicinba a wannan ranar.nikam daman part ɗinshi ta turani wai naje na gyara masa tare da fitar da duk dattin da part ɗin yayi cikin mamaki naja qafafuna na nufi part ɗin ina mamakin halin momy na sonkai duk ƴaƴanta me suke dabazata turasu ba seni haka dai na karasa har cikin babban falon nasa ina mamakin wannan lamari.
Ƙarasawa cikin bedroom ɗinshi nayi na sharosa gami da sauya zanin gado sannan na karkade kurar dayayi kana na nufi bayi nanma wankesa nai tas sannan na haɗa ruwan goge tiles ɗin nan na hau faman mopping wanda shiya batamin lokaci ba kadanba ina gamawa na kunna turaren wuta wanda ta bani nakoma falon nan ma nahau gyarasa cikin mintunan da basu wuce gomaba nagama da falon tunda baya da datti shi sosai.
Ina kammalawa na haɗa tarkacena na nufi part ɗin momy ahanya naci karo da mama abokiyar zaman momyn wadda tunda nazo gidan banga ƴaƴansu ba kuma suma ban gansuba sabida banga fuskar dazan tambayi zuwa gaidasu ɗinba.
Da sauri na tsugunna nagaida ita cikin ladabi ina sunkuyar da kaina qasa.
Itama cikin kulawa take amsamin gaisuwar tawa sannan da ɗora da cewa."Oh nikam fatimah kinyi ɓatan dabo ace tunda kikazo gidannan baki leqo garemu mun ganki ba, koda yake jeki ba laifinki bane ALLAH yi maki albarka" ƙwallace taɗan tahomin ta ɓacin rai batare dana ce mata komai ba naja jikina na nufi part ɗin momy ina lissafin maganganun mama,wato dai duk ƴan gidan sun san halin momy kuma babu babbar matsalar cikin gidan kamarta.
Tun daga bakin parloun momy na tsinkayo muryarta cikin ɗan sauti kaɗan tana tsaye daga ɓangaren karamin kicin ɗinta na cikin falon ludayine a hannunta wanda da alama ina tunanin juya wani abun ma take.
"Zonan ke! abinda ta gayamin kenan tana nunoni da ludayin hannunta da sarsarfa na qarasa gabanta tare da tsugunnawa a qasa ina sunkuyar da kaina"momy gani" nafada muryata tana rawa sabida azabar tsoronta daya kamani danni yanzu mugun tsoro momy take bani.
"Dan qaniyarki kedawa naganku a tsaye a waje kardai da munafukan gidannan kika soma hada kai to wallhi bazan dauka ba tun wuri ma ki sake"! takai maganar cikin hargagi! "momy wallahi ALLAH ban tsaya da kowa ba mama..."! bankai ba ta kwadomin ludayin hannun nata a fuskata wanda ya dauki zafi zau kamar wuta! da wani irin ihu naja jikina na hantsila nai baya ina kuka! "wallahi momy ni ban mata magana ba" "rufemin wannan banxan bakin naki munafuka mai bakar fuska wallahi baxaki zamemin alaqaqaiba dan haka na kuma ganin koda haqorinki ne gawani ɗan can gidan wallahi sena illataki" takai maganar tana shureni da qafarta.
Sekuma naga fuw tai cikin kicin ɗin tana mita kukana na cigaba dashi tare da mamakin halin momy yanxu ƴan part ɗin su mama sune ƴan can gidan.
Da azama na mike tare da nufar bedroom ɗina na faɗa katifa seda naci kukana na more sannan na kwanta duk da azaharce amman aina huta tunda rabona da barci tun asubahi ina wajan kwakwa😭
Tunani kala kala sune suka ɗarsu acikin zuciyata gefe guda ga kewar gida ta addabeni wallahi ayanxu hanya kawai nake nema zakara yabani sa,a matuqar nasamu hanya sena gudu gida sedai ko yankani umma zatai tayi dana zauna anan amayar dani kamar baiwa.
Ganin wannan tunanin baxe kainiba yasa na miqe nai bayi alwala na dauro tare da gabatar da sallar azahar bayan na idar na kammala addu,oina na ninke sallayar tare da cire hijabin sallar danai na fita.
Kai tsaye babban kicin na nufa cikin ikon ALLAH kuwa na haɗu da baba wadda nafara gani tun zuwanmu na farko cikin far,a ta nufoni tana cewa "a,a lale da jikata yaushe rabon dana ganki seyau", faɗaɗa far,ar fuskata nayi sannan na ɗan jaho hannunta kaɗan zuwa wani ɗan lungu "baba dan ALLAH kiɗan bani aron wayarki insha ALLAH zuwa anjima zan dawo maki da ita amman idan baxaki damuba" nakai maganar fuskata tana ɗigar da hawaye.
Tsorone ya bayayana a fuskarta qarara kafin taɗanyi jim kana ta ɗora "a,a fa ƴar nan idan zamu tauna tofa mu gatsa karfa kije kijaho min wata fitinar ina neman abincina" takai maganar tana jan abun a ranta wanda ya bayya har kan fusakarta.
"Shikenan baba tunda baxaki aramin ba nagode" najuya zanbar wajan, karaf naji tajawo hannuna tare da damƙamin wayarta qirar beby nokia a hannuna sannan tace "amman idan zaki dawon da ita karki bani agaban sauran damuke aikin nan dasu kinji ɗiyata kinsan mutane da saka ido" mayarda qwallata nai tare da danne abinda yaxomin wuya wainike ƴar murya akan abani aron waya lallai rayuwa babu tabbas.
Qaqalo murmushin dole nai "baba karki damu zan kula sosai nagode ALLAH yasaka maki sa mafificin alkairi amin". nakai maganar ina zubar da hawaye.
Da sauri naja jikina har ina ɗan gudu kaɗan nai wuf na faɗa falon momy tare da nufar ɗakina sanin nagama mata aikinta baxata neman ba kuma su rauda suna airport ɗauko baba nice kaɗai ba,a tafi daniba wai acewarta tana gudun masifar ya hydar tunda wai daxe tafi yace mata kada tabari ko bakin gate na leqa.
Mayar da key nai na rufe tare da faɗawa kan katifa nai ruf da ciki lambar abba nakaina dan haka na zayyano ta tsaf acikin wayar tare da danna masa kira
Dayake yau week end ne babu aiki nasan insha ALLAH idan yaga kiran ze biyo shiyasa ina danna wa sau ɗaya danaji ta shiga na katse kiran.
Minti biyu baya sega kiransa.
Ɗagawa nai tare da qarawa akunnena "hellow abbana barkanka da rana" ɗan mutstsuka fuskarsa yayi daga nasa ɓangaren tare da cewa."wanakeji kamar batulan abba" da kuka da dariya na haɗa duk alokaci guda "eh nice abban bayan kun manta dani kun barni cikin azaba da bauta" nakai maganar ina kuka! daga nasa bangaren ya karo sauti tare da taɓo umma wadda take kusa dashi tana hada masa abinci duk tsuru sukai suna jin yadda sautin kukan batula ke fita ta cikin wayar.
"Abba ni wallahi sena taho gida nagaji abba nagaji baxan iyaba idan ma nutsuwa kukeso kuga nayi wallahi abba nayi kullum bani da aiki sena bauta ɗazu momy har dukana tai da ludayi" nakai maganar ina kuka, ɗan jim abba yayi tare da cewa "to kiyi haquri batulan abba daman rayuwar aure haka ta gada kinga hajiya zainab daman koda bakya auren ɗanta itaɗin mai tsawatar maki ce sabida haka ina son ki kwantar min da hankalin ki insha ALLAH zanwa Aliyu waya akan ya kawomin ke ko sati kiyi" yakai maganar cikin son ya kwantar min da hankalina, mayar da ajiyar zuciya nai sannan nace "to abba dan ALLAH kagaya masa hakan ni koda kaina yace nataho wallahi zanzone" cikin tsananin tsoro abba ya dakatar da ita sanin halinta na wautar tsiya tabbas kaɗan da aikinta ta taho kanon shiyasa ya taka mata burki tun wuri.
"Yanzu in mijin naki bashi muyi magana dannaga ma sabon layine hala waya ya sauya?" abba ya jefomin wannan tambayar bayan ya gama tsoratar dani da yimin faɗan kada koda wasa nace zan taho gida.
Tura bakina nai gaba tare da ƴar shagwaɓar dabanyi ba kwana biyu sannan nace "nima nasan inda ya tafi yau wajan sati uku rabona dashi" nakai maganar batare dana taunata ba, zaro ido abba yayi tare da furta "akwai matsala aqasa" sannan yacemin "to wannan wayar tawa kika samu batula?" yakai maganar yana son taji gaskiyata, "abba ta rauda ce nakai maganar dason bagarar dashi, mayarda ajiyar zuciya yayi tare da sakemin nasiha sosai mai ratsa