Chapter 4 Reading Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels Arewa Novels

Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels

Author :  Nil Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   4 / 28

9K to 12K   out of 83.3K words

da saka hannuna nai tagumi ina kallonsa.

Bantaɓa ƙare ma sa kallo kamar nayau ba gaskiya ya haidar baƙaramin kyau ALLAH ya basa ba lallai wannan dole ma yay wulaƙanci da jin kai dik da dai ban misalta yadda kyan nasa yakeba amman nabarwa makaranci ya ƙisma da kansa domin kyansa shi akewa laƙani da asalin kyau ɗan gaske mai shiga rai da zuciya da kwanciya a ɓargon jiki.



"Ki wuce bedroom na ki wanken tiolet malama kinzo kin sakani agaba da wannan banzan fuskan naki" yana kaiwa nan naji wayansa taɗauki ringing! wani shu'umin smile ya saki akan face ɗinsa tare da ɗauka yana karawa a saman kunnensa.


Tsaki naja araina ina cewa "wlh bazan wanke banɗaki da wannan magariban ba salon wani aljanin ya shigeni abanza da wofi.

Banajin mi suke faɗa a wayar amman daga gani maganar love sukeyi duba da yadda naga yanata lumshe idanunsa.

Tsaki naja kaɗan a raina sannan na mike na nufi hanyar waje.


"Ke dan ubanki ina zakije?" na tsinci muryarsa akaina yana maganar.




Batare dana juyoba na tsaya cakk ina faman tura bakina gaba.


"Ke zonan" nakuma jin muryarsa akaro na biyu yana min magana.

Jan kafata nai tare da nufar wajansa ina faman tura bakina gaba.

Tsugun nawa nai tare da cewa "nidai kayi hakuri bazan iya wankin bayi yanzuba darefa yayi" nakarasa fadar maganar ina tura bakina gaba kamar zan saka kuka!


Ƙaro handsfree ɗin wayar yay tare da ajeta agefensa sannan ya dubeni "FATIEMAH! yafaɗa dawani irin jan sunan kamar shi ya raɗamin shi batare daya jira mi zance ba ya cigaba da cewa.........

"Miyasa kike da taurin kai ne?" ya ƙarasa maganar cikin wani irin yanayi "nifa yaya ba taurin kai nai maka ba iya gaskiyata na faɗa" kiff ya kaimin duka a gefen fuskata "dan uba nki waike kam wace irin banzar yarinyace ne?" dan bakida mutunci ina magana kina magana ni sa,ankine!! jada baya nai tare da saka hannu na dafe wajan ina sakin wani irin kuka.


Da sauri na tashi tare da barin falon aguje na nufi waje ina ihu!


"fatie!! fatie! fatie!!! inajin yana faman kiran sunana nikam nai mashi banza tare da fita daga falon aguje!!


Abakin famfon wajan wurin na tsaya na wanke fuskata sannan na nufi cikin gida ina ƙunshe dariyar iskancin dana shuka masa ai wallahi babu gardin dazanwa wankin banɗaki yanxun nan haka kawai salon nabar umma da yawon gidajen masu magani.



Da sauri na faɗa cikin falon umma ina haki cikin sauri na gyara nutsuwata tare da ƙarasawa cikin falon ina cewa.

"La MOZA yaushe kika dawo?" dayake yawanci sunan danake gayawa umma kenan idan ina cikin nishaɗi.

Kallona umma tai tsaff kafin tace "kekuma daga ina haka?" "au umma basu gaya maki ba daga fa part ɗin ya hydar nake nai masa gyaran ɗakinsa" nakai ƙarshe ina zama agefenta hannuna na miƙa gefenta na ɗauki agwaluma guda ɗaya ina kokarin ɓareta.

"Sannu uwata keki ka aiken da zaki daukarmin baki tambayenba" ALLAH ya baki hakuri moza tuba nake" nakai maganar ina sakin dariya.

Danni yau komai za,aimin baxanji haushi ba coz abin da ABDUL yagayan ɗazu shiya barni cikin wannan nishaɗin.

Umma ce ta dubeni tare da cewa "jaririya yau abinda kikaimin naji dadi ALLAH yay maki albarka" ameen umma" nabata amsa ina kai agwalumar bakina bayan na bareta.


"Yawwa nace ranar asabar zamu tafi abuja zaku zauna anan ne koko zakuje gidan zainab?" haɗe raina nai tsamm "umma mezaki acan ɗin?" kayan lefen ALIYU zamu kai gidan minista kinsan bikin fa sauran sati biyu ɗazu ake gaya mana" au haba amma umma ko labari?" dariya umma tai tare da cewa ai labarinne bai zoba tukunna amman yanxu ai gaya nan kinji.


"To ALLAH ya sanya kairan"

"Ameen"

"Umma zamu zauna anan ɗin kawai"


"Toshikenan ALLAH yakaimu ai yau sauran kwana biyar ma"

Haka dai mukaita hirarmu muda umma gwanin sha,awa har abba ya dawo yau abba harda tsokana ta.

Ban bar ɗakin umma ba se wajan goman dare.

Dakinmu na koma dik su ummi sunyi bacci nima sallah nai tare da kwanciyata.

Washe gari ban fitaba seda na tabbata daya fuce office sannan nai wuff naje kicin nai abin da zanyi na bar kicin ɗin.

Tunda yamma umma ta akeni gidan anty zee naje na kai mata wasu kaya anan muka hadu da ABDUL muka kuma tattaunawa har bayan magariba sannan nayo gida.

Yauma seda nasha faɗa wajan umma amman nikam ban damuba sabida burina ya kusan cika


Yau kusan kwana uku kenan da faruwar komai muna waya sosai da ABDUL harda ma mahaifiyarsa da ƙannensa.

Kuma sosai muke maganar kawo kudin aurena yace sunata shirye shirye a bangaransu.

Ya hydar kuwa haryau naki yarda mu hadu dashi amman shi ina ganin ma ya manta dani tunda ta hidimar auran sa yaketayi dan yau yana kano ne gobe yana abuja duk haka yake wannan zaryar.

Yau asabar tun safe umma ta shirya ta yakasai ta wuce sabida zasu tafi da matan su alhaji ƙarami gida ya rage sauran mu da abbanmu dan shima angon ya wuce tun jiya ƙilama kuma se bayan bikin nasa zezo kokuma yama tafi shikenan oho masa tunda naga ya dauki manyan jakunkunan sa tare da kayayyaki sosai harsu hanif naga ya kira ya babbasu abubuwa harda kuɗi da yawa sannan ya rufe part ɗin nasa.


Harkokin mu mukeyi acikin gida kuma bama wannan faɗan kamar da munyi waya da umma wajan sallar magariba lokacin harsun sauka daman umma a bangaren mama take sauka domin momy bata kaunarta shiyasa bata sauka anata bangaren.

Kwanan su biyu suka dawo anan umma kece mana an saka biki sati mai zuwa zaro ido mukai muna mamaki lallai abin se son barka nan umma ta zauna tana bamu labarin dukiyar da aka lafta alefen.

Hoton less ɗin dinner umma ta nuna mana tace gobe zata bawa anty zee taje kasuwa ta sai mana.

"Ni dai umma banda ni wallahi bana so nifa baxani ba gidan iya zani na zauna ko gidan anty zee" akanme baxaki ba kinsan abbanku ma baxe bari ba ko dan iskanci dik yan uwanki zasu taru zakice baxaki jeba" shuru nai mata amman araina na kudiri aniyar wlh babu inda zani ana igobe zasu tafi zan gudu gidan anty zee.

Danni bana son wulakanci shiyasa nake gujema inda ake yinsa.


Kwanci tashi babu wuya wajan ALLAH yau alhamis tun safe su umma suke shirinsu na tafiya har ɗinkunan mu sun karbo nidai da ido nake kallonsu.

Ƙarfe goma saura nabi ta bayan kofa nabar gidan bayan na saka kayana a yar akwatina.

Seda naje gidan anty zee sannan mukaiwa umma waya lokacin suna tare da abba nan umma taita faɗanta tare da cewa senaci ubana idan ta dawo.

Murmushi abba ya saki tare da cewa "batula sarkin riko watakan abinda hajiya zainab take makine yasa yarnan taki zuwa bikinnan ALLAH dai ya daidai tamu" amin umma ta faɗa anan sukai ta tattaunawa kafin kuma driver yaxo su wuce har abban tunda ze tsaya daurin aure.


Agidan anty zee bani da wata matsala sosai muke waya da ABDUL nan nake shaida masa da cewar abba baya gari su ɗaga zuwan nasu se wani satin dagajin yadda ya amsamin nasan yaji babu dadi amman haka mukai sallama babu yadda zeyi.


Waya babu dare babu rana nida ummi dik abinda akai seta gayamun ta wayar umma.

Tace tunda sukaje ma sau ɗaya sukaje part ɗin momy su suna part.ɗin mama hakama umma kuma tace tunda sukaje ake event kala kala banda zubar da nera da akeyi.


Ina ango na tambayeta hmm anty batula wlh seda yace mana kina ina wai mukace kina gida kince baxaki zoba.

Nanfa nahau bala,i haka nace muku salon yaji haushina, wlh kam yaji dan dana kallesa lokacin senaga yayi sakk takarasa fadan tana dariya.

Any batula bakiga amaryar ba ranar dinner wlh mai kyau kuma tana da kirki har wajan su umma tazo ta gaida su ga iyayenta masu kudi.


"Kuma anyi abubuwa masu birgewa sema kinga yadda abokansa sukai masa kara harda mata fa sojoji dik sunci uniform ɗinsu ƴaƴan gidansu kuwa bakiga yadda suke rawa ba kai anty batula inama muma munada yawan nan gaskiya yawa da haɗin kai yayi arayuwa.
Hmm nace tare da katse wayata.

Kwanan su hudu suka dawo ranar talata nikam ban koma gidaba se ranar laraba ranar kwana mukai ana labarin bikin banda dukiyar da aka kashe agidan amaryar wanda aka ware mata acikin gidan su ya hydar ɗin.


Tunda ya hydar yabar gidanmu ban sakejin duriyarsa ba bare labarin sa haka muke ta harkokinmu danni yanxu sangarta se wadda ta karu saboda babu mai takura min kamar da.


Ranar juma,a bayan an sakko daga masallaci dadyn su ABDUL ya turo ƙannensa guda biyu wajan abbanmu danshi yayi tafiya.


Lokacin da abba yay masu iso zuwa seatroom ɗin gidanmu ba karamin mamaki abba yashaba da sukace wai sun xone akan neman auran batula.

Wace batulan?"

yaushe tafara ma zancen?"

Dawa kuma take?"

Duk wanna abun su suka tarar ma abba har hakan yasa ya shiga tamtama acikin zuciyarsa....!!

*12*
Nisawa Abba yay kaɗan tare da jan doguwar ajiyar zuciya batare daya kuma cewa baƙin nasa komai ba. amman cikin zuciyarsa cike ike da mamaki kala-kala gami da ɗumbin zulumi,shin yaushe ma batula tayi wani girman daza,azo neman auranta wai taka maimai ma yaushe aka taɓa yin haka shi tunda yakema baitaɓa sanin ƴar tasa tanada wani saurayi ba bare kuma har azo da wannan magana. shin hakama ake neman aure ai dafarko se saurayi yazo ya gabatar da kansa gaban iyayen yarinya kafin daga baya kuma dik wata mahimmiyar magana ta biyo baya.

Ɗaya daga cikin baƙinne ya katsewa abba tunaninshi da cewa,"Alhaji kai mana shuru,shin bakai bane Alhaji kabir uba yakasai ba?"da sauri abba ya ɗago dik hularsa ta jiƙe da zufa kafin yace,"eh nine wallahi".ɗayanne yakuma cewa."to masha ALLAH daman abin da yazo damu shine zancen ɗammu ABDULLAHI yaga ƴar wajanka yana nemanta da aure dafatan,za,abamu wani bai mana shigar sauriba".gaba ɗaya abba yagama sarewa da lamarin dan haka seya mike tare da cewa"ai ba wurina ya dace kuzo neman aurenta ba akwai ƴan uwana acan cikin garin danan kuka fara zuwa tukunna ai.amman yanzu tunda kunzo nan yakamata in fita in sanar musu abin da mukai zan sanar daku, bisimillah kusha ruwa ina zuwa"abba ya tura musu farantin da aka zubo musu ruwa akai sannan yabar wajan ya nufi cikin gida.


A falon umma ya zube tare da kiran sunan umma da ƙarfi "AISHATU! yaki nan kirawo min faɗima"cikin sauri umma ta fito daga cikin ɗakinta hannunta riƙe da carbi da alama lazumin juma,a take,"gani alhaji lafiya ?" "maza kirawo min faɗima nace maki aisha! abba ya kuma bawa umma wannan umarnin.

Da sauri umma ta miƙe zuciyarta fal mamaki haka ta nufi ɗakinsu batula.


Hangota tai kwance kan gado tana sana,ar tata watakan bacci da sauri umma ta ɗaka mata duka tare da cewa"ke tashi abbanku na kiranki maza miƙe" cikin sauri na tashi ina tura baki gaba tare da cewa "Tom umma bara na wanke fuskata" babu ruwana keda shi" tana gama faɗan haka tabar wajan.


Nima da sauri nabar kan gadon tare da wucewa bayi fuskana na wanko tare da saka hijabi na nufi ɗakin abba abin mamaki baya ciki dan haka naja kafata nai ɗakin umma.


Sallama nai a falon tare da shiga. cikin ɗimuwa na ƙarasa ciki sabida yadda naga umma tai tsuru agaban abban wanda da alama faɗa yake mata.

Zama nai a gefen ƙafar abba tare da cewa "abba gani" "hmmm naganki faɗima nutsu sosai na tambayeki domin ALLAH" Abba ya faɗan haka yana kallona.

Duk senaji tausayin abba ya kamani amman sena dake tare da cewa "to abba ina sauraranka" na mayar da hankalina kansa baki ɗaya,ina kallon umma tana aikamin da harara nidai na kawar da kaina gefen da abba ike.


"Faɗima waye ABDULLAHI?kuma a ina kika sanshi shin kuma maye alaƙarki dashi?" abba ya jeramin wannan tambayar cikin tsarewa da ido.


Sunkuyar da kaina nai ƙasa batare dana ce komaiba amman gaba ɗaya jikina rawa yake.

"Faɗima!!! dake nake magana" abba ya dakamin wata irin tsawa! wadda ta amsa dikkan falon.


Muryar umma ce ta biyo bayan tasa "hmm alhaji kenan kaima bata bakinka kake ai walllahi nina haifi yarinyar nan nafi kowa sanin halinta wallahi bazan kaffaraba fatima ita ta aiko wannan yaron kuma ba yau suke tare ba yanxu kawai abinda ya rage mana. seta gaya mana ta yaya ta haɗu dashi har wannan maganar ta haɗasu".


"Zaki bamu amsa kosena fasa maki fatar jikinki!!umma ta faɗi maganar tana mai kawomin duka.

Da sauri abba ya jawoni jikinsa tare da cewa "kull aishatu kada ki soma dukanta duka baya gyara ai" "faɗima ki gayamin abin da ke tsakaninku da yaron nan kinga gaya nan har ƴan uwansa sunxo wajena kiyi hakuri ki gayamin kinji ƴata"."karkiji tsoro ni bazan kuma tafka kuskure ba! gwara ki gayamin idan aure kikeso wallahi ko gobe ne zan daura maki aure kinji faɗimata"abba ya kare maganar yana share hawayensa.


Da sauri na kai kaina jikin abba na kwantar tare da fara labarta masa labarin haɗuwata da abdul har kawo yau ban boye masa komaiba.

"Alhamdulillahi ALLAH nagode maka Faɗima kinason shi?" girgiza kaina nai alamun eh" to masha ALLAH karki damu aure kike so ko to nikuma zan maki aure faɗima nan bada jimawa ba maza tashi kitafi ALLAH yay maki albarka ALLAH yaƙa shirya mana ku".


Dagudu na mike tare da barin falon ina doka tsalle.

Acan falo kuwa bala,ine ya kaure tsakanin umma da abba ita tace wlh baza,amin aure yanxuba shikuma abba yace se anyi shifa tinda na nuna aure nakeso to gwara ammin gudun fitina ai suma godewa ALLAH daba mayaudari na hadu dashiba.

"Haba alhaji yanxu daga zuwa se a fara maganar aure dika dika fatima nawa take ni wallahi bazan yardaba ainima inada hakki akanta". umma ta karasa maganar tana kuka kamar wata karamar yarinyar.


Seda abba ya sauko dan kansa nan ya dinga bawa umma manyan misalai wanda harya nusar da ita abin da ita ta manta dashi sannan ya samu ta saukko da gyar.

Ƙara sawa yay da cewa "ai mugodewa ALLAH ma dayasa abin yazo mana da sauƙi. kuskuren da faɗima tai shine da bata kawo mana yaron nan gida mun gansa ba amman nikam hakamma na godewa ALLAH kuma hakan ze ƙara sakani na saka ido akan ƙannenta domin yanzu zamani ya lalace sekaga yaro yafi iyayensa dubara ALLAH dai ya iyamana"


Ita dai umma bata ce komai ba sema tashi datai tayi cikin ɗakinta aguje tana danne kukan daya tawo mata.

Murmushi abba yay tare da cewa "mata se abarku".



Wayarsa ya ciro tare da dannawa babban yayansu waya kuma uba agaresu wato *ALHAJI MUHAMMADU UBA YAKASAI TSOHON GENERAL ƊIN SOJA MAI RITAYA ( BABAN ABUJA )* Ringing! ɗaya biyu baban abuja ya ɗauki wayar cikin farin ciki suka gaisa da abba nan abba ya soma yi mashi bayanin dik halin da ake ciki da komai da komai.


Hatta kukan! da umma tai seda abba ya labarta wa baban abujan tare dayin shuru yana sauraran sa yaji mi zece dashi.

Dariya baban abuja ya saki irin tasu ta manya sannan yace "Alhamdulillahi ya ALLAH ai hakan mukeso yanxu idan banda abin aishatu ai setama godewa ALLAH yammata nawane yanzu gasunan agabammu babu mijin ita ƴar tamu ta samu shine take kuka! ai wannn ma kamar nuna butulcine. karka damu kabiru yanzu ka kira shi usman ( alhaji ƙarami) da umaru ( kawu ) sesu tattauna dasu ɗin yadda akai seka gaya min kaji ko ALLAH ya zartar da alkairi" baban abuja ya ƙarasa maganar cike da dattijantaka nagartacciya.

"Ameen Yaya" abba ya amsa cike da jin soyayyar babban yayan nasu aransa.


Katse wayar yayi tare da kiran su kawu nan ya sanar musu da halin da ake ciki suma fatan alkairi sukai tare da cewa insha ALLAH zasu shigo yanzunnan.


A mutunce abba ya koma wajan ba'kin tare da basu hakurin barinsun dayay su kaɗai sannan ya ƙara da cewa suyi hakuri ya sanar da ƴan uwansa ne amman insha ALLAH zasu zo suna hanya.


Minti arba'in da wani abun su alhaji ƙarami suka sauka gidan ɗan uwan nasu ƙarɓa ta mutunci sukaiwa iyayen abdul anan aka tsaida magana akan su bawa su abba sati ɗaya suyi bincike kafin a kawo kuɗi sannan abba ya bawa abdul damar fara xuwa zance.

An rabu cikin mutunci da girmama juna tare da barkwanci sannan su kawu suma suka wuce gida jensu.


Tunda abba ya koma gida yake fama da umma da ƙyar ya samu ta sakko sannan ya fita.


Cikin damuwa umma ta kira anty zee tana shaida mata yadda ake ciki buɗa anty zee ta saki tana faman farin ciki tare da fatan alkairi.


Se bayan magariba umma ta kirani tare da saukemin kwandon masifa tasff hatta ƙara da cemin munafuka mai fuskar kwaɗi!!


Hakuri na bata sabida ni yanzu dik jikina yay sanyi haka naja jikina na koma ɗaki ina faman jin kunyar abin da nai.



Su ummi babu abin da suke se tsalle suna murna wai harda cewa suma tun yanzu zasu fitar da ankon bikina haka dai sukaita shirman su ina jinsu.

Ana sallar isha'i ABDUL yay min waya akan cewa yana kofar gida.

Seda na shirya tsaff sannan na nufi ɗakin umma na sanar da ita.


Korata tayi tare da cewa na fice na bata waje tunda bana jin magana ita a son ranta na zauna nai karatuna mana amman tunda banga hakan ba ita babu ruwanta gaba ni zanyi kuka da kaina.


Haka na share hawayena tare da fita waje a ɗakin abba na waje na shigar da abdul ummi ce ta kawo masa ruwa suka gaisa har yana tsokanarta.

Munyi maganganu sosai dashi na mutunci sannan yace ze tafi.

Har waje na rakasa sannan na koma cikin gida bamma je naiwa umma seda safe ba sabida tsoron abinda zeje ya dawo.

Haka na tafi ɗaki na kwanta dik jikina yay sanyi bada ban ma ina fashin sallah ba da nafila zanyi kona ji dadin raina.

***************************
*ABUJA*

Baban abuja suna gama waya da abba ya dubi babban ɗansa wanda yafi soyuwa aransa fiye da kowa a ƴaƴansa tare da ce masa "Babana kaji abinda yake faruwa da gidan abban naka ko?" ALIYU wanda kansa yake sunkuye agaban mahaifin nasa shine ya ɗago yana cewa "A,a BABA ban fahimta ba wallahi" yana kaiwa nan yaja bakinsa

4 / 28