Chapter 24 Reading Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels Arewa Novels

Koba So Akwai Kauna Book Complete Hausa Novels

Author :  Nil Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   24 / 28

69K to 72K   out of 83.3K words

maryam" saboda tunda akai haihuwar banga beby ba.

Amsa masa nai cikin sanyin jiki sannan na nufi qofar fita.

Acikin falon momy nagasu rauda zuwansu kenan da bags a hannunsu suna ganina suka rungumeni "i miss you sis wallahi irin sosai ɗinnan bara muje muyi taking showwer muzo akwai labarifa"

Nima cikin farin ciki nace "babu damuwa ina jiranku anan ɗin nima naxo ganin bebyn mune" nafaɗa tare da nufar ɗakina.

Gyara katifata nai sannan na zauna duk naji bana jin dadin ganinsa danai a haka cike da alwashin baxan koma part ɗinshiba na kwanta kamar daga sama naji kukan jaririyar a falo kamar wadda aka mintsina na miqe har ina harɗewa na nufi falon.

Cike da sasaarfa na qarasa wajan jaririyar wadda take gab da faɗowa daga kan kujera cikin jin haushin abinda akaiwa yarinya na saka hannu na ɗauketa ina mitar dan hauka anbar ƴar beby anan ita ɗaya ai dole tai kuka!.

Rungumeta nai ajikina ina zagayen cikin falon da ita

Ina gab dazan ɗaga qafata daga gefen carpet naji wani mugun santsi kamar na karkashi yayi gaba dani cike da azama na qamqame bebyn ina kuka!! tana kuka!!

Amman kash ta zame daga hannun nawa inda ita ta bugu da qasa nikuma nai baya na kifa, hannuna yace qas!!! sau uku.

Cikin wani irin qaraji naji saukar muryar maryam "wayyo jama,a kuzo takashen beby shikenan ta kashan ƴata!! taja maganar tana wani irin kuka!!

Momy hartana harɗewa tafito waje tayo kaina da duka nima gwara na kasheki matsiyaciya tunda kika kashemin jikata.

Banida bakin magana se kuka sabida nasan karaya nai a hannuna haka suka taran jama,a cikin minti goma kowa na gidan ya hallara awajan idan ka cire uban ƴar!

Kowa ka gani yana yanayin ɓacin rai sabida yadda momy take faman soki burutsu ita da maryam yar yarinyar aka ɗago wadda kanta ya fashe hancinta ya tsage.

Salati kowa yake yana al,ajabi cikin minti biyar ALLAH ya karɓi ran abasar bata ko motsi.

Cike da hauka maryam tasoma birgima ita an cuceta na kashe mata ƴa!! babu momy babu dalilinta a falon.

Tsahon minti goma ina jikin mama bansan inda kaina yakeba sabida yadda komai ya tsayamin cak!!

Waini ake zargi da kisan kai "inalillahi wa'inna'ilaihirraju'un" na furta a bayyane cike da tashin hankali araina.

Bayyanar ƴan sanda mata a falon ita ta qamar da kowa bayansu momy ce nuna tai tare da umartarsu akan sutafi dani domin kamani da akai dumu dumu da gangancin sakin jikarta a qasa ƴar kwana biyu da haihuwa har hakan yakai data rasa ranta.

Ganin sunyo kaina da sauri zasu kamani yasa nai saurin ɓuya abayan mama ina kuka"wallahi mama ko kiyashi ban kasheba bare mutum" nakai maganar ina sakin kuka.

Su mama babu abinda suke se salati wannan wace irin qaddarace ta saukarwa ƴar mutane!

Gashi babu ALIYU babu baban abuja duk maxan gidan babu kowa haka ƴan sandan suka saka batula agaba suna janta suka fita da ita momy na bin bayansu.

Aka bar maryam durkushe tana kuka ga gawar ƴarta a yashe a gefe.

Dagudu rauda tafita......

*84 - 85*



Cike da tsananin tashin hankali raudah ta nufi part ɗin baban abuja tundaga bakin qofa farko tajita a rufe da alamun baya nan tun safe ya fice kuma daman mostly yana yin irin wannan fitar.

Baya ta juya ta nufi part ɗin yayansu sallama take shuru ba,a amsaba haka ta nufi bedroom cikin fitar hayyaci.

Kwance yake akan sopa idanunsa a lumshe jikinsa sanye da jallabiya marun, se carbin dake hannunshi wanda daga ganinsa lazimi ike.

Hankaɗo kofar tai tare da shiga kanta tsaye da gudu taje garesa tana cakumarsa "yaya yaya katashi ƴan sanda agidannan suntafi da fatima" takai maganar tana jan hannunsa.

Cike da mamaki ya buɗe idanunsa ya dire akan qanwar tasa tare da furta"wace fatiman a ina wai?" yakai maganar cikin mamaki, kuka take a wannan karon "yaya fatiman abban kano matarka, momy ta ɗauko mata ƴan sanda wai ta kashe jaririyar da anty maryma ta haifa shekaran jiya" tana gama gaya masa tai hanyar waje zata gudu.

Cak ya riqe tsintsiyar hannunta yajata a matuqar firgice sukabar ɗakin qafarsa ko takalmi babu, direct hanyar gate suka nufa tundaga bakin gate ɗin farko hankalinsa ya soma tashi sakin hannun rauda yay ya fita abinda ya ɗaure masa kansa shine.

Hango gayyar jama,ar dayay a wajan wanda idan ba idonsa ke gizoba harda ƴan jarida, "Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un" yafurta hakan cikin tashin hankali.

Duk mai ya kawo hakan? yana kuma ina wannan qazamin lamarin ya faru.

Da sanyin jiki ya qarasa waje inda wani ɗan jarida yay sauri kara masa abin magana. "Yallaɓai saninka babban mutum agarinnan kuma babban soja wanda ya riqe mukamai da dama sannan kuma mahaifinka yanada kuɗi, mizakace dangane da yadda mahaifiyarka take zargin amaryarka dayin ganganci da jaririyarka da aka haifa a shekaran jiya mizakace dangane da wannan lamari dan yanzu haka duk zancan ya karade duniya " doke ɗan jaridan yay cike da tashin hankali ya nufi wajan qatuwar motar dake shaqe da jami,an tsaro acikinta.

Lokacin yayi dai dai kuma da sanda ƴansandan mata suka taso qeyar batula agaba da ankwa a hannunta gabanta da bayanta duk jami,an tsaro gakuma ƴan jarida suna ɗaukar hotonta dana ƴansandan gaba ɗaya ya rasa mai yake masa daɗi da gudu ya nufi motar amman kafin yakai har sun ɓacewa ganinsa.

Cikin tashin hankali ya tsugunna akan qafafunsa yana karanto addu,ar data zo bakinsa ƴan jarida sunmasa caa haka qaninsa ɗan ɗakin mama umar ya ɗagasa yay cikin gida dashi.


Shigarsu cikin gidan yayi da lokacin da wata mace ƴar jarida take ɗaukar muryar maryam wadda take kuka kamar ranta ze fita.

"Eh nice mahaifiyar jaririyar kuma mata ga CAPTAIN ALIYU MUHAMMUD UBA MAGINI, daman can bata qaunata shine na aje yarinyar dan na ɗauko mata pida aɗaki tana kuka kafin na dawo nazo na tarar da ta shaqe mata wuyanta wanda haɗa idanun damukai da ita ya saka tasaki ƴar tawa aqasa har kanta ya fashe da hancinta, tayi ganganci da ɗiyata ta kashemin ita ina roqon manya dasu shiga cikin wannan lamari itama a kasheta kamar yadda ta kashen beby" wannan maganar ta maryam ita ta daki dodon kunnensa da sauri ya rintse idanunshi yana furta addu,a acikin bakinsa.

Da qyar umar yajasa kamar raqumi suka isa falon momy gawar ƴar yashe a qasa da sauri ya nufi gaban ƴar tasa qafarsa hartana rawa tabbas dagaske ƴarsa da aka haifa masa ta rasu......!!



Ummi kizo ki ɗaukomin radio ta mana kinsan yanxu ake labaran hantsi muryar umma kenan wadda take zaune a falonta tanawa amira tsifar kai sukuma su amir suna zaune suna home work yarfe hannunta tai daga cikin abinda take yankan salak ɗin sannan ta miqe taje ɗakin abba ta ɗauko radion ta kawowa umma.
Cikin sa,a umma ta kunna jim tai sannan tacewa ummi matso kiji wani labari kuma bara muji kai amir yimin shuru umma ta faɗa.

Cikin sa,a lokacin ake watsa labaran kuma yayi dai dai da lokacin da maryam take magana..miqewa tsaye ummi tai ko ina na jikinta yana faman rawa ( my fans wallahi wannan page ɗin kuka nake ina rubuta makushi ina kuka ya ALLAH karabamu da sharrin maqiyan fili dana boye ya ALLAH ka rabamu da sharrin dukkan abin halitta ya ALLAH kabamu kariyarka a koda yaushe amin 😭😭🙏 ) itama amira miqewa tai kanta duk a hargitse a tare suka kalli mahaifiyar tasu "umma bakiji wannan labaran ba wallahi kamar daga gidansu yaya hydar fa" umma wadda duk jikinta rawa yake ita ta dubi ƴaƴan nata cikin fitar hankali amman bakinta yagaza tace komai.

Wayar ummace ta ɗauki qara cikin sauri hanif ya ɗauka yana ganin anty zee ce ya ɗaga danyaga mahaifiyar tasu kamar bata cikin hayyacinta murya cikin kuka tafara magana "yaya Aisha kunna redio shikenan batula sun haɗa mata sharri munshiga uku!" tana faɗin maganar tana kuka sakin wayar hanif yay ya zauna daɓas a qasa yana kuka ilahirin falon ansara mai bakin magana kamar mahaukaciya umma ta yayibi hijabi tai hanyar waje.


Da gudu suka bita "umma ina zaki tafi kuma"suka ce mata cikin kuka! "ku barni abujan zantafi naga halin data ke ciki"takai maganar tana tsananin kuka babu yadda basuyi da itaba amman fafur taqi yarda ALLAH yasa hannunta da pos da gudu ummi tabi bayanta ganin ta tari abin hawa yasa ummin tabi bayanta tun a motar umma take gursheqen kuka ( uwa kenan ALLAH yasaka wa da duk wata mahaifiya da alkairi🙏 ) cikin qanqanin lokaci suka kai tasha bayan wani lokaci suka sami mota cikin ikon ALLAH motarsu ta ɗaga.

Da baya amira taja ta ɗauko wayar umman wadda take a qasa hanif ya yada tanemo no ɗin abbansu ta kirasa cikin kuka take bayyana masa komai, shima alokacin yana cikin gari suna qoqarin tafiya shida ƴan uwansa ne sabida mama takira iya tun ɗazu ta gaya mata daman yay shurune bayason umma taji sabida tanada hawan jini sedai kash alqalami ya bushe dan umma tuni ta wuce a yadda amira ta shaida masa.

Haka ya saki wayar cikin tashin hankali ya shaidawa ƴan uwan nasa suma duk jikinsu yay sanyi haka suka rufu sukabi motar driven alhaji qarami suka ɗauki hanya.

Cikin mintituna kaɗan duk wasu dangin umma sun cika gidanta sabida yadda zancan ya bazu tuni anty zee ta sauka agidan umma itama tana haɗa.kayanta zata bita seda akai ta bata haquri da qyar aka ce tazauna wajansu amira kafin aji mike wakana yanzu.


****************

Salatin baban abuja shine yasa hydar ya ɗago idanunsa waɗanda sukai kamar gaushin wuta ya zubawa mahaifin nasa, "Wannan cin zarafin ba kowa akaiwa seni tabbas zainab kinci zarafina ƴar ɗan uwana kikaiwa sharrin kisan kai yanzu dame zan kalli dangina wallahi tallahi fatima ko kiyashi baxata kasheba bare ɗan mutum kuma insha ALLAH duk wanda yay mata sharrin nan qarshe akansa ze qare" baban abuja yakai maganar yana ɗaukar gawar tare da umartar ƴaƴansa dasu wuce aje a suturtata! gabaki ɗaya suma kuma ƴaƴan gidan kowa ya lallara awajan daga mai dafe kai sesu rauda dasuke kuka wanda sunsan sharri ne kawai akaiwa fatima amman baxata taɓa aikata hakanba.

Seda umar still ya kuma ɗaga hydar wanda yake durqushe yakasa magana sannan suka wuce abakin qofa mama kecewa baban abuja aje asibiti mana cikin masifa ya ɗago ya kalleta babu wani asibitin daxamu je badai ƴa bace ta rasu to baxamu ko ina ba itakuma zainab avinda takesone ta samu ko to ɗanta ze sakarmin ƴa ayau ɗinnan nikuma zanyi belin ƴar ɗan uwana koda kuwa ace duk abinda na mallaka ze qare amman itama ta sani wallahi babu aure a tsakanina da ita daga nan har abada.......!!

*86 - 87*


Yana gama faɗin haka yay hanyar waje fuww! da gawar a hannunsa inda duk sauran iyalin nasa suka mara masa baya.

Falon ya rage se iyalansa mata ƴaƴan momy babu abinda suke se kukan jin furucin mahaifin nasu.

Dole tasa umar ya nemo likita aka ɗauki hoton jaririyar tare da ɗaukar duk wani abu mai mahimmanci sannan aka rufe, bayan nan aka haɗa yarinyar aka kaita gidanta na gaskiya se asannan mahaifin maryam ya diro gidan cikin alajabin wannan lamari.

Tunda ake wannan budurin hydar yaqi magana yaqi cewa da kowa komai kuma duk uban kiran da ake masa a waya yaqi ya ɗaga bare yay magana shikaɗai yakejin wannan lamari idan ya tuna fuskar yarinyarsa da yadda take kama dashi seyaji wata qwalla ta tarar masa.

Miqawa sirikin nasa hannun yay bayan andawo daga kai yarinyar makabarta sannan yay masa gaisuwa, cikin dakushewar murya ya dubi mahaifin maryam yace masa" ina ganin kawai ku wuce da maryam gida duk yadda shari,ar ta kama bayan angama ta dawo dan nasan dole kotu zasu kai maganar" yaja maganar yana dafe saitin zuciyarsa yanajin yadda take harbawa da qarfin gaske.

Cikin mamaki mahaifin maryam ya dubesa "ai inaganin ALIYU kamar ɗakinta yafi mata zaman lafiya akan gidan namu ko?" kaɗa kafaɗarsa yay alamun ko ajikinsa sannan yace "gaskiya Alhaji baxan boye maka tunda nake ba,a taɓa cimin mutunci kamar na yauba ansan ko ina kana da mosoyi kana da maqiyi miyasa da abin yafaru ni baxa,a sanarmin ba ainafi kowa sanin wani mataki zan ɗauka, duk da fatima matata ce ai ƴar nan da aka kashe tawace kuma inada haqqi akanta zanbar fatima hakane? dole zan ɗauki mataki idan har da gaske ita tai kinsan! miyasa zasu ɗauko mana jami,an tsaro abu acikin gida ba waje ba wanima munafukin ne ya kirawo ƴan jarida! yanxu wallahi shugaban wajan aikinmu shiketa min waya akan yaji maganar agidan redio yanxu kana tunanin mutum dubu nawa ne sukaji wannan maganar an tozartan aure ansaka matata ta sunna ankwa antafi da ita agaban baynan nasi wanda har yanzu babu wata babbar shedar data tabbatar datai kisan wallahi ko mahaifiyata a yanxu baxan iya gani ba bare wata maryam sabida haka tsuntsun daya ja ruwa shi ruwan ze doka yadda suka kai qara sesu san yadda zasuyi amman ni babu ruwana kuma matata yau ɗin nan zan san yadda zanyi tabar sitation na yarda kullum ina kaita kotun amman wallahi indai ni ALIYU ke aurenta to baxata kwana acanba"

Yana gama faɗin haka yabar wajan baki ɗaya takalmi kawai ya ɗauka da waya da key yabar gidan acikin baqar motarsa yanufi sitation ɗin, tundaga bakin gate ya hango motar baban abuja kirjinsa ne ya ɗauki bugu. cike da tashin hankali ya nufi ciki.

Da baya ya dawo ya ɗauki id card ɗinshi ya nufi ciki seda ya nuna musu sannan suka bar sa ya shiga wajan.

A office ɗin babbansu ya sami baban abuja suna magana zama yay tare da bawa mutumin hannu suka gaisa sannan yacigaba da sauraran abinda officern yake gayawa baban abuja.

"Yallaɓai kai haquri wannan case ɗin is a criminal case but baxamu iya baku bellin taba harse munji daga sama sabida yadda ƴan jarida suka watsa abin yanxu haka commissioner of police yay mana waya akan cewa dole mu riqeta harse anga mi case ɗin ze kai nan gaba"

Qarar table ɗin da hydar ya buga ita ta saka officern ɗagowa haka ma baban abuja duk suka zuba masa idanu suna kallonshi.
Card ɗinshi na wajan aiki ya miqawa officern tare da cewa "wallahi sekun buɗen naga halin da matata take ciki shi shugaban naku wani irin daqiqine marar tunani da babu wani evidance da ya nun matata tana da hannu akisan zece kuriqen ita idan bakai wasa ba wallahi sena ɗaureku dukanku!! yakai maganar yana huci.

Dafa kafaɗarsa officern yay cikin lallami ganin alluran sojan zata motsa sannan yafara masa bayani cikin kwantar da murya"yes naga id ɗinka kuma koda baka nunan ba nasan kai waye kuma nasan matsayinka, wallahi muma bamuyi niyar kai mota gidanka domin muci zarafin iyalinka ba sedai kasani akwai kotu acikin sitation ɗinnan kuma duk rana irin tayau muna gayyato ƴan jarida domin su ɗauki rahoto akan irin shari,ar da aka yanke, to cikin haka bayan munkai record ɗin yau sega wata mata ta shigo mana a hargitse cikin tashin hankali anan tai mana bayanin cewa ita mahaifiyarka ce kuma matar wannan! yanuna baban abuja kuma duk tafaɗi sunayenku wanda ya kasance ku sanannu ne ba ɓoyayyuba tace tanason muzo muje gidanku mu shaida yadda matarka ta kashe ƴarka sabida baka nan kuma mahaifinka baya nan idan har bamu gani da idanunmu ba zaku musa idan tagaya maku, wannan dalilin yasa muka dauki mota da jami,anmu mata muka nufi gidan naku.

Wanda ita da kanta ta nemi ƴan jarida dasu biyomu dan a watsa labarin tokaji yadda abin yake kuma kasan tunda maganar daga tushenku ta fito dole a riqe case ɗin har agama bincike sabida asan gaskiyar abin, amman nikaina abin ya taɓani yadda naga mahaifiyarka tafi kowa zaqewa wanda ita yakama tafi kowa rufa wannan asiri koda kuwa wannan lamarin gaskene bare wallahi nima yadda naga ƴar yarinyar tana kuka kamar zata mutu nasan bata aikata hakanba andai yi mata ZARGE ne"

Officern yakai maganar yana dafa kafarɗar hydar wanda yay star a wajan yana mamakin abinda mahaifiyarsa tayi.

Cikin ɓacin rai baban abuja ya kalli hydar "you see kana jin dai abinda mahaukaciyar uwarta tayi ko to wallahi wannan haukan akanta ze qare ai qiyayya ba hauka bace kuma wallahi ni yanxu babu wani aurena da ita" yakai maganar cike da ɓacin rai " kuma kaima seka sakarmin ƴata ayau bara dai agama wannan case ɗin setaje ta jiqaka tasha tunda duk akanka take wannan sakarcin" duk maganar da baban abuja yake bai ɗaga kansaba seda yaji zancan saki sannan ya ɗago.
"Baba ni miye laifina anan idan har daman can bada target ɗinka na insaketa aranka ba, baba koso kake na rasa raina da baqin cikin rashin ƴata zanji koda wannan bala,in da aka kunnomin dan ALLAH baba ka sauke zancen sakin nan ni zan nuna maka ɗan halak ne na haifu insha ALLAH zan tsaya tsayin daka akan zumuncinmu baxan saki fatima ba kuma zanyi yadda zan komai yatafi da sauqi baba idan har na saketa wallahi har abada abba baxe taɓa ganin farinmu ba" yakai maganar yana sauke numfashinsa.

Sosai shima officern yay na,am da maganar hydar anan shima ya taushi baban abuja harya samu ya ganar dashi sannan suka ɗunguma suka fita daga office ɗin da ya kaisu wajan fatiman..

*88 - 89*

Tafiya miqaqqa sukai kafin suje section ɗin da ake aje masu laifi irin na batula ma,ana criminal section tunda suka soma tafiya hydar yake jin wani iri aransa sabida yadda yaga yanayin wajan baqaramin tsaro aka zuba ba.

Wata qoface mai qarafa wadda aka rufeta da ankwa abakinta akwai security's wajan guda 10 dukkansu ɗauke da bindigogi a hannunsu ganin ogansu yasa suka bude masu qofar
batare da jinkiri ba, sosai yanayin wajan da yadda aka bawa wajan tsaro ya firgita hydar amman dayake yasaba ganin irin hakan bai nuna aransa ba.

Sun wuce qofofi da dama kafin aqara buɗe masu wata qofar daban wadda tafi sauran faɗi babban wajene se ƴan bancina da aka warewa masu ziyara, seda officern ya dakatar dasu a wajan sannan yaje office ɗin mai kula da section ɗin sukai magana tare da neman alfarmar ganinta sannan ya dawo yana shaida musu cewar anbasu damar ganinta.

Cike da bakin ciki duk suka nufi ɗakin da aka kulleta, nanma seda aka bi diddigi sannan aka barsu suka shiga wanda hydar jiran

24 / 28