Author : Nil Category : Romantic Hausa Novels
ya hydar ike zaune sannan yaja baya ya ƙame.
Dazafin nama nima na saka hannu naja marufin gefen danake tare da fitowa waje miƙa nayi tare da salati sannan na godewa ALLAH.
Rufe idanuna nayi gam tare da karanta addu,a bayan na gama na roƙi ALLAH daya sadani da dukkan alkairin dake wannan gida yakuma yimin tsari da sharrin cikinsa.
Wannan kuma bawai wanine ya sanar dani hakan ba face mahaifiyata.
Ina bude idanuna naga su ashe har sunyi nisama sunkusan kaiwa part ɗin tsakiya wanda nake tunanin shine na momyn.
Cikin yanayin gajiya nima nake ɗaga ƙafafuna waɗanda sukaimin tsami sabida zama tare da nufar inda naga sunyi.
Adai dai bakin ɗan matsakaicin gate ɗin daze sadaka da cikin part ɗin na sake tsayawa wannan karon addu,a nayi mai tsaho tare da neman tsarin ubangijina akan zamana da momy sabida yadda naji gabana ya faɗi.
Kuma cikin ƙudurar ALLAH ina gama addu,ar bayan nashafa naji na sami nutsuwa acikin jikina da zuciyata.
Cikin azama naja ƙafafuna na nufi cikin nima ina godewa ubangijina domin dama indai bawa ze roƙi Allah to shikuma ALLAH ze amsa masa sedai idan bawan mai sakacine tabbas yazama dole na yarda son jikina in miƙe indiga ibada ina kaiwa ALLAH kukana domin shikadaine ze kawomin ɗauki a hannun momy dama sauran dukkan lamarina.
Ganin wata babbar ƙofa mai adon zaiba a buɗe ya bani tabbacin nance ƙofar dazata sadaka da ainihin cikin ɓangaren batare da wani duhun kaiba na ja jikina har zuwa bakin kofar tare da saka ƙafata ta dama nai bisimillah sannan na shiga.
Ƙatuwar harabace mai ɗauke da fulawowi masu kyau wanda naga ƙofofi a ƙallah zasuyi huɗu da sassarfa na ƙarasa ƙofar farko ina neman inda zanyi na shiga falon tunda ni duk a tunanina ba haraba zan tarar ba falo zan tarar amman se aka samu akasin hakan.
Gashi kuma ni tuni na nemi ya hydar na rasa sam nakasa gane inda suka shiga domin kuwa ni sun ɓacemin ɓatt!
Tura ƙofar farkon nai da sauri kuma na saketa nayo baya sabida yadda naga tsakar gida dawasu ɗakunan dana kasa gane kona miye.
"Baiwar ALLAH lafiyarki kuwa?"
Dasauri naɗago kaina ina duban wadda taimin wannan maganar, dattijuwace dan daga gani ba yarinya bace dan ta manyanta amman kallo guda zakai mata kasan aiki ma take ta taso gareni.
Faɗaɗa far,ata nai tare da saurin tsugunnawa.
"Baba dan ALLAH ya hydar nake nema ban san inda yay ba".
Cikin mamaki wadda na kira da baban tace.
"A,a ƴarnan kardai kice uban ɗakin nawa har yashigo gidan".tafaɗa cikin farin ciki.
"Ai tun ɗazu muketa taya hajiya girkin uban gidan namu kice har ya shigo shida hajiyar,amman dai ke baƙuwace bakisan takan gidan ba?"
Ta kuma jefomin tambayar a karo na biyu?
"Eh ni baƙuwace yau na biyosu to kuma nazo sena nemesu na rasa".
"Ayya ALLAH sarki jikata kinga nan kicin ne da store anan duk ƴan aikin hajiya momy muke zaune,waccan ƙofar ta yamma itace ta momyn da yaranta waccan ta tsakiyar kuma itace ta alhaji idan yana gari.waccan ta hagun kuma itace ƙofar Aliyun shida matarsa inda ya taɓa.zama farkon aurensa kafin subar gari amman yanzuma naji ance zasu ɗan zauna anan ɗin kafin matar tasa ta haihu.
Sukuma sauran matan alhajin suma part ɗinsu yana daga gefen namun amman sekin futa waje haɗe yake dana mazan gidan".
Takai maganar tana min murmushi
"To jikata maza fito na sadaki da ƙofar ɓangaren hajiyar kafin muzo kwasar gaisuwa".
Tafaɗa tana fita daga cikin kofar binta nayi abaya ina jinjina maganar matar amman kuma daga gani tana da kirki sedai magana datake da ita sosai.
Tun kafin ma mukai ƙofar momyn na hango giftawar ya hydar kuma kamar yana saurine se can kuma naga ya nufo inda muke.
Cikin sauri wadda na kira da baba ta ƙarasa gabansa.
Rissinar da kanta tayi tare da furta.
"Yallaɓai barka da zuwa ya hanya?".
Ga mamakina senaga ya saki fuskarsa yana cewa.
"A,a baba harira sannu da gida ya aiki dafatan nasameku lafiya?".
"Lafiya ƙalau ɗan albarka munata ganin hidima mungode ALLAH ya ƙara ɗaukaka....!! ya katseta ta hanyar ɗaga mata hannu alamun tabar gaisuwar.
Juyowa tai ta dubeni.
"To jikata gama Alhaji alin nan kya karasa tare dashi kinji ko"
Murmushi na sakar mata jin yadda ta shiga raina tafarar ɗaya sannan nace.
"Tom kakata nagode senazo cin tuwo".
Nakai maganar tare da jan ƙafata na taka gabansa.
Seda baba harira ta ƙule sannan naga ya dubeni.
Tare da ɗan rage tsahonsa gabana cikin wata munafukar murya wadda tai ƙasa sosai yacemin.
"Ina kika tsaya?"yafaɗi maganar a dake tare da shan kunu.
"Kawar dakai na nai gefe cikin basarwa nace.
"Natsaya mu gaisa da waccan tsohuwar ne sabida naga suna aiki yasa naje nai musu sannu".
Na tsinci bakina da faɗin hakan sabida nasan nace masa ɓata nai yanzu seya yarfani.
Tunda ta fara magana ya tsirata da mayun idanunshi yana bin bakinta dasu yana kuma jin yarinyar tashi ɗaya ta burgesa danshi arayuwarsa baya ƙaunar wulaƙanta ɗan adam musamman babba wanda ya girmeka shiyasa data ce masa hakan yaji tayi mugun burgesa ba kaɗan ba.
"Kin kyauta maza wuce muje".
Yafaɗa tare da wucewa bayana ya sakani a gaba har cikin kofar wadda ta kasance kamar ta ruwan glass.
Adai dai bakin step ɗin dazaka taka kashiga ƙaton falon naja na tsaya sabida wani sanyi danaji har cikin ɓargona.
Juyowa nai domin na tambayesa su anty zee aikuwa karaf muka haɗa.ido dashi yawani matso gaf dani kamar ze hau gadon bayana.
Tsareni yayi yana bina da kallo fuskarsa babu walwala nima basarwa nai sannan na dubesa.
"Yaya su anty zeefa?"
Matsowa yayi kamar ze haɗeni tare da ɗora hannunshi a gefen danake tsaye tare da bina da kallon dana rasa na miye.
Cikin fargaba naja baya kaɗan ina raba idanuna gefe tare da yin ƙasa da kaina.
"Fatie.....!naji yakira sunana cikin ƙasa da murya sosai, baijira cewata ba ya ɗoramin"fatie wallahi inda ba abba ne ya haifekiba senace a ƙauye umma ta ɗaukoki,miyasa baki san yadda zakinawa mutum maganaba,nidai kinga ba mazauni bane bare na dinga karɓarki wajan momy sabida haka ya kamata ki gyara tun wuri".
Yakai maganar yana ɗora hannunsa akan kirjinshi ya tokare.
Cikin sanyin jiki dana zuci na ɗago ina binsa da kallon tsana jin yadda wani haushinsa ya kamani waishi ba mazauni bane bare ya karɓeni awajan momy,sekace jaka aka ɗauko musu.
"Indai ALLAH ze kareni ai bana jiran karbar waninsa kayi ƙoƙari wajan zuga momynka ta kasheni kotaimin illa tanan ne kaɗai zan gane cewa kuɗin maƙiyana ne"....!!!
Ina kaiwa nan na wuce fuww nabarsa a wajan a dashe.
Babban falone wanda ya haɗa manyan kujeru babu abinda bai haɗaba na dangane da kayan more rayuwa da jin dadi.
Tsakiyar center carpet naja na zauna tare da ɗora hannuna a kuncina na zuba tagumi sabida da alama.anty dasu ummi basu ƙarasoba.
Shikam cikin mamaki da wani irin yanayi yaja ƙafarsa yabar wajan baima shiga part ɗin momyn ba kawai seya koma da baya ya nufi nasa part ɗin.
Mamaki fal ransa yake nanata maganarta acikin zuciyarta tome take nufi dasu maƙiyanta ne?
Shikam ko a farce baya jin sonta a matsayinta na mata garesa sedai yana jin sonta a matsayinta na ƙanwarsa.
Koda kuma ace ɗaukota yayi daga gaban abba ya kawota nan baxe bari aci zarafinta ba,bare kuma yanxu datake a matsayin matarsa wanda hakkinta da dukkan wani nauyinta ya rataya a wunyansa tabbas baxe bar wani abu marar kyau ya gifta garetaba sedai idan baya wajan.
Shidai akankin kansa idan tai masa ba dai dai ba ze hukuntata hukunci mai zafi amman bai yarjewa wani yaci zarafinta ba.
Yama kuma.gayawa momy ɗazu kafin ta shigo yace komai tai a gaya masa shidai baya son aci zarafin ta sabida amanar ALLAH ce awajansa dakuma amanar zumuncin ALLAH dakuma ta aure.
Wannan furucin daya ma momy ɗazu kafin ya fito shine ya harzuƙata hartaji haushinsa ta miƙe taja maryam ɗaki suka bar falon.
Da wannan tunani ya karasa part ɗinsa wanka yay tare dayin sallah sannan ya nufi kicin ya haɗowa kansa tea yasha ya kwanta duk da acikin satin nan ma yana da tafiya, da tunanin tafiyarma bacci ya kwashe sa.
Nafi ƙarfin minti ashirin zaune acikin tsananin sanyi A/C kuma ikon ALLAH har yanzu babu mahalukin danaga giftawarsa acikin falon gawani irin zazzaɓi dayake neman kamani wanda nasan bana komi bane ba face na tsantsar sanyin danake ji haɗi da yunwa.
Gashi ya hydar ɗinma daya sakoni gaba naimasa rashin kunya yaji haushi ƙila ya koma, tur nai da maganar dana masa ɗazu wadda nasan inda ban masa ba da tuni yanzu ya cikani da abinci naci na hantse.
Amman nan dan tsabar wulaƙanci jibi ko tsuntsuma ban ganiba bare ataimakamin da inda zan rage marata tare da cin abinci kuma.
Jan jikina nayi ina sakin wani marayan kuka mai cin rai tare da saka hannuna na rufe fuskata na cigaba da kukan danake.
Baccin minti talatin kawai ya samu ƙarar wayarsa ya farkar dashi cikin zafin ciwon kai yaja tsaki tare da ɗaukar wayar tasa dake jikin bedside drower duba wayake kiran nasa yayi ganin abokinsa najeeb yasa ya ɗira daga kan gadon.
Jikinsa sanye da singlet baƙa irin ta kakin soja se farin 3qrt daya tsaya masa iya ƙwaurinsa.
Toilet ya shiga ya wanke fuskar sannan ya koma gaban gadon ya zauna ya ɗauki wayar ya shiga kiran najeeb ɗin tunda wanda najeeb ɗin yay masa ya katse.
Sunkai good 20 minutes suna tattauna maganar auren najeeb ɗin da,ayi nan da wata biyu sannan ya katse wayar ya miƙe.
Cikin sauri ya zira silifas a ƙafarsa ya nufi hanyar waje.
Bai tsaya a faloba kai tsaye ƙofar fita ya nufa tare da ɗaukar hanyar part ɗin momy yana addu,ar kada ALLAH yasa abinda yake tunani bai tabbata ba.
Aikam yana tura ƙofar ya hangota kamar marainiya ƙudundune cikin tsakiyar cinyar da alama ma ko kuka take! yamutsa sumar kansa yayi da hannunsa tare da jin babu daɗi cikin wani irin sanyin jiki yaja ƙafarsa zuwa gareta durƙusawa yayi gabanta batare datasan yay hakan ba ya zuba mata ido yana kallonta zuciyarsa na zafi najin kukanta!
Cikin kukana naji saukar hannun mutum a fuskata da sauri na ɗago idona wanda yake sharɓe sharɓe da hawayena na ɗorasa akan fuskarsa wanda yake tsugunne a gabana da alamun fushi agaresa.
Cikin daƙilewar murya naji yace.
"Me akai maki kikewa mutane wannan kukan kamar wadda akama duka?"
Matso wani hawayen nayi tare da kallonsa sosai.
"Yaya yunwa fitsari zazzaɓi tsoro duk su suka kamani wallahi yaya tunda ba zauna anan babu wanda nagani anan ɗinfa".
Naƙarasa ina kuka!!
Sunkuyar da kansa naga yayi kafin kuma naga ya miƙe cikin sauri naga ya shiga ƙofar hannun damarmu.
Batare dayamin magana ba.
Momy zaune akan tumtum na pillow se maryam a gefenta wadda take faman zuba abinci mai rai da lafiya acikinta.
Na'eem da Raudah yaran momy ƴammata da basuyi aureba kwance a kan ƙafarta kowaccensu da waya ƙirar iphone 11pro a hannunsu wanda da alama charting sukeyi cikin farin-ciki babu damuwa ko kaɗan atare dasu kana ganinsu kaga ƴan madara ƴan ajin tubarkallah top class ƴan gayu ajebotar.
Kamar anjefoshi ya faɗo ɗakin yana muzurai cikin ƙufula.
Ko sallama baiba ya tsaya agaban momy yana watsawa su rauda harara.
Cikin sauri momy ta ɗago tana binsa da kallo kafin tace.
"To dogari meke tafe dakai?".
Kallo ɗaya ya watsawa su rauda tare da kauda kansa gefe ya furzar da zazzafan hucin zafi.
Da sassarfa naga sun miƙe tare da shigewa bedroom ɗin momy.
Hatta ita ma maryam ɗin yana juyowa ta mike tabar wajan yarage dagashi se momy.
*50 - 51*
Cikin kuzari ya rage tsahonsa a gaban momy tare da ɗora hannunshi akan tumtum ɗin da momy ke kai ya kafeta da jajayen idanunsa yana kallonta dasu.
Cikin dashewar murya mai cike da tarin ɓacin rai ya dubeta.
"Hajiya kiyiwa ALLAH da manzonsa kitayani riƙon amanar da aka damƙa min,hajiya! kituna da cewa ɗana kowane idan har akaiwa rauda ko na'eem ko hafsa ko zubaida ko mamy nasan baxakiji daɗiba tokema mai yasa zakima ƴar wasu haka?"
Yakai maganar yana tsareta da ido.
"Hajiya kituna da maryam da fatiemah duk a yanzu matana ne to maye na zaɓar ɗaya kibar ɗaya tun kafin akai ko'ina har kin fara ban bantasu,yanzu kun shigo nan kunbar ƴar mutane awaje ni wallahi momy gwara na tattara na tafi da ita lokojan dan bazan iya kallon abba da idona ba idan har wani abu ya samu gudan jininsa....."!
Yakai maganar yana kallon idanun momy.
Cikin mamaki momy ta saki baki da hanci tana binsa da kallo saka hannunta tayi tana goge idanunta kafin ta sami damar magana cikin firgici.
"ALIYU! takira sunansa a karo na farko a rayuwarta.
Ɗaure rai tai sosai sannan ta cigaba da cewa.
"Wallahi! tallahi! har abada bazan taɓa son wannan yarinyar ba kai barima kaji bada ban ubanka yay min kurari da igiyar aurena ba da tuni yanxu maganar saki ake ba wannan ba nikuwa mai yaymin zafi haɗa zuri,a data Aisha".
Takai maganar tana jan numfashi sama sama.
Kallon mamaki yakebin mahaifiyar tasa dashi batare daka gane a wani yanayi yake ba.
"Hajiya ALLAH ya huci zuciyanki, awani ɗakin zata zauna?".
"Bangama tunanin hakan ba tafara zama a B.Q kafin nagama shawarata".
Zaro manyan idanunsa yayi cikin ɗumbin mamakin LAFAZIN mahaifiyar tasa sannan yace.
"Hajiya B.Q fa?" cikin maids ɗin gidanman ina hajiya kiyi haƙuri iyalina bazata zauna anan ba kiyiwa ALLAH bani ba kirufawa mutuncina asiri kijanye wannan LAFAZIN naki hajiyata".
Yakai maganar yana jin zuciyarsa babu dadi akan maganar hajiyar.
Tasan halin ɗan nata da kafiya da taurin kan tsiya dole seta rage takurarta agabansa idan tana son gudanar da komai cikin sauki.
Murmushi ta saki tare da cewa.
"Kardai kacemin kafara sonta kenan?"
Tajefo masa tambayar babu zato.
Kaɗa kafaɗunshi yayi alamun ko ajikinsa sannan ya saki wani shu'umin murmushi.
"Hajiya kin taɓa ganin mutum yaƙi jininsa ai ko babu so akwai ƙauna ta jini a tsakanina da ita".
Yana kai maganar ya miƙe tare da cewa.
"Bara na kaita wancan ɗakin na kusa da danasu raudah hajiya ko abinci baki bawa yar takiba".yafaɗa yana sakin dariyar tsokana.
'Daukar pillow tai ta jefo masa tana faman masa masifa kamar zata ari baki.
"Wallahi sena miƙe tsaye dan naga alamun baba yafara zarmewa babu wani ƙaunar jini kota hantace sena raba ni ba ruwana, dannasan halin baba matukar yafara son yarinyar nan kashina ya bushe".
Momy ita kadai keta faman zubar gadon wannan maganar kamar wata zautacciya.
Cikin yanayi na nishaɗi ya ƙarasa falon sabida yadda momy ta basa dariya ita watakan da gaske take bata son fatimah shifa yanzu abinma dariya yake basa lallai da sauran kallo a nan gaba.
Gabanta ya ƙarasa har yanzu tana raɓe a inda ya barta batayi ko motsiba.
Gyaran murya yayi wadda ta jawo hankalina garesa na ɗago ina kallonsa tare da jiran daga garesa.
"Taso ki biyoni" abinda yafaɗa kenan naga ya nufi cikin falon ƙofar ƙarshe ya tura wadda daga ita se wadda zaka futa daga falon baki ɗaya.
Shiga cikinta yayi wanda nima ya bani damar bin bayan nashi.
Babban ɗakine mai dauke da toilet ɗinsa aciki dannaga ƙofa wadda nake da tabbacin ta toilet ɗince se ƙatuwar katifa tare da wadrov a gefenta amman babu madubi.
Iya abinda ke cikin ɗakin kenan.
Ja yayi ya tsaya ajikin wadrov ɗin ya ji ngine jikinsa da bangonta yana kallona na minti ɗaya sannan ya kauda kansa gefe.
Adaƙile naji saukar amon muryarsa.
"Ga ɗakin ki nan ki samu kiyi abinda zaki kafin su kawo maki abinda zakici".
Yafaɗi hakan yana ƙoƙarin juyawa ya fita daga dakin.
Mayar da hawayena nayi sannan na ɗan biyosa a baya.
"Yaya hydar zazaɓi ke damuna, sannan kuma nace maka ina su anty zee kaimin banza ko basu ƙarasoba".
Kamar bazece komai ba naga ya ƙarasa gaban ƙofar tare da saka hannunshi ya kama handle ɗin sannan naji yace.
"Idan ma zaki nutsu ki nutsu idan banda shirmanki waye ze rakoki ai ko kaza baza,a haɗota dake ba bare kuma mutum, keda ganin su ummi harse kinyi hankali, ga gayanki can driver ya kawo zansa ashigo maki dasu and kuma bana buƙatar inga ƙafarki koda a bakin gate ne wallahi kikai hakan sena ɓallaki"!
Yana kaiwa nan yaja handle ɗin tare da ficewa daga ɗakin.
Mamaki fargaba takaici baƙin ciki sune sukai min caa!
Da sauri naja jikina na faɗa kan katifar gwanin tausayi na rungume pillow ina kuka!!
Ashe daman wayo umma taimin dan kar na ɗaga hankalina yasa akaimin shigo-shigo babu zurfi har aka saka anty zee tazo ta kwana?
Ashe daman duk hirar da umma takeyi da anty zee danna zata zasu biyoni ne?
Wallahi inda nasan hakane da tuni zakara yabani sa,a nayi gidan iya wani haushi ne ya kamani watakan horon daza,amin kenan shikuma wannan ɗan rainin hankalin wai senai hankali zani gida.
Juyawa nai ina kallon ɗakin nan danan naji kewar ƴan uwana tayi mugun kamani"wayyo ummi amira"nafaɗa a fili.
Ƙarar buɗe kofar danaji ita ta dawo dani daga tunanin danake ganin ƴar budurwa agabana tana turo kaya a babbar bags ɗita ya bani tabbacin maganar dayay min gaskiyace.
"Anty gashi nan inji oga" cewar yarinyar tana rissinamin.
Batare da nai far,aba nace mata"to" tare da juyawa cikin jin haushin kowa....!!
Fita tayi wanda naji ƙarar! buɗe ƙofar tata ko kallon kayan banyi ba na miƙe zaune tare da cire hijabin jikina na cire ɗankwalin kaina nai zaman dirshan akan katifar ina sakin kuka! mai fitar sauti.
Ƙarar ɓuɗe ƙofar na kuma ji da sauri na ɗago kaina ganinsa nayi ya juya baya yana rufe ƙofar yasa nafara ja dabaya.....!!
52-53
Jada baya nasomayi ina faman raba idona ni duk atunani wannan maganar ta ɗazuce ta sakasa jin haushi yazo ya huce takaicinsa akaina amman unexpected sena gansa akaina a tsaye batare daya saki muryanshi ba naji yace,"Malama dallah matso kici abinci ga drugs nan kisha maza kafin na dawo kiyi sallah" yana gama faɗamin haka naga ya dire ledar dake hannunsa ya fuce daga cikin ɗakin, ɗan zamo da jikina nayi tare da ɗaura ɗan kwalina sannan na jawo ledar cikin zaƙuwa nasoma kai abincin cikina wanda babu ko tamtama na siyowane cikin mintinan da basu wuce biyarba nagama ci sannan najawo ledan drugs ɗin na ɓalla gami da watsasu bakina na kora da ruwa miƙewa nai tare da shiga cikin toilet ɗin dake manne acikin ɗakin babu laifi yanada ɗan girmansa se ƙaramin towel ajikin ƙarfen, haka na tari ruwa a famfo nasoma alwala ina kammalawa na fito waje na shimfiɗa sallaya na tayar da sallah ban tashiba seda naji ana kiran sallar isha'i sannan na mike gami da mayar da ita, bayan na idar nai addu,a na shafa sannan na koma na ƙara ɗaukar ragowar take away ɗin naci sannan na haye kan katifar na ƙudundune, wallahi wani irin tsorone